Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 8/15 pp. 3-7
  • Jehobah Ba Zai Yashe Amintattunsa Ba

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Jehobah Ba Zai Yashe Amintattunsa Ba
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Sa’ad da Suke Fuskantar Zalunci
  • Sa’ad da Muke Fuskantar Tasirin ’Yan Ridda
  • Sa’ad da Ake Yin Aikin Allah
  • Jehobah Zai Kāre Amintattunsa
  • An Raba Mulkin
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • An Raba Mulkin
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Ka Kasance Da Aminci Da Zuciya Ɗaya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • ‘Kai Kaɗai Ne Mai Aminci’
    Ka Kusaci Jehobah
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 8/15 pp. 3-7

Jehobah Ba Zai Yashe Amintattunsa Ba

“[Jehobah] ba ya yarda tsarkakansa ba; ana kiyaye su har abada.” —ZAB. 37:28

1, 2. (a) Menene ya faru a ƙarni na goma K.Z., da ya sa aka gwada bayin Allah? (b) A waɗanne yanayi guda uku ne Jehobah ya kula da amintattunsa?

ƘARNI na goma K.Z., lokaci ne da bayin Jehobah za su yanke shawara. Masarautan ƙabilu goma na Isra’ila ba su yi yaƙin basasa ba domin sun ɗan samu ’yancin kansu. Don ya sami iko sosai, Jeroboam sabon sarkinsu da aka naɗa ya kafa sabon addini a ƙasar. Yana son talakawansa su ba shi goyon baya sosai. Menene amintattu bayin Jehobah za su yi? Za su kasance da aminci ga Allahn da suke bauta masa? Mutane da yawa sun yi hakan, kuma Jehobah ya kula da su sa’ad da suke riƙe amincinsu.—1 Sar. 12:1-33; 2 Laba. 11:13, 14.

2 A zamaninmu ana gwada amincin bayin Allah. Littafi Mai Tsarki ya yi gargaɗi: “Ku yi hankali shimfiɗe, ku yi zaman tsaro: magabcinku Shaiɗan, kamar zaki mai-ruri, yana yawo, yana neman wanda za ya cinye.” Za mu iya yin nasara mu ‘tsaya masa muna tabbatawa cikin bangaskiyarmu’ kuwa? (1 Bit. 5:8, 9) Bari mu yi la’akari da waɗansu abubuwa da suka faru a lokacin da aka naɗa Sarki Jeroboam a shekara ta 997 K.Z., kuma mu ga abin da za mu iya koya daga labarin. A waɗannan lokaci mai wuya, an tsanantawa bayin Jehobah. Kuma ’yan ridda suna rinjayarsu, sa’ad da suke yin aiki da ke jawo ƙalubale. A cikin dukan waɗannan yanayin, Jehobah bai yashe amintattunsa ba, kuma ba zai yi hakan ba a yau.—Zab. 37:28.

Sa’ad da Suke Fuskantar Zalunci

3. Me ya sa sa’ad da Sarki Dauda yake sarauta bai zalunci mutane ba?

3 Bari mu yi la’akari da yanayin da ya sa Jeroboam ya zama sarki. Misalai 29:2 ta ce: “Sa’anda mugun mutum yana mulki, talakawa suna ajiyar zuciya.” A lokacin sarautar Sarki Dauda na Isra’ila ta dā, mutane ba su yi ajiyar zuciya ba. Dauda ba kamili ba ne, amma mai aminci ne ga Allah kuma ya dogara gare shi. Sa’ad da yake sarauta Dauda bai zalunci mutane ba. Jehobah ya yi alkawari da Dauda, ya ce: “Gidanka fa da mulkinka za su tabbata har abada a gabanka: kursiyinka za ya tsaya har abada.”—2 Sam. 7:16.

4. Albarka da aka samu a lokacin sarautar Sulemanu ta dangana bisa menene?

4 Sa’ad da Sulemanu ɗan Dauda ya fara sarauta an yi zaman lafiya kuma an yi nasara da ya kwatanta yadda Kristi zai yi sarautarsa ta Shekara Dubu a nan gaba. (Zab. 72:1, 17) Babu wani cikin ƙabilu guda 12 na Isra’ila ta dā da suke da dalilin yin tawaye. Amma, albarkar da Sulemanu da talakawansa suka samu ya dangana ne ga abin da suka yi. Jehobah ya gaya wa Sulemanu: “Idan ka yi tafiya cikin farillaina, ka hukumta shari’una, ka kiyaye dukan umurnina domin a riƙa tafiya a cikinsu; ni kuma sai in tabbatadda maganata da kai, wadda na faɗa ma ubanka Dauda. Zan zauna kuma a cikin ’ya’yan Isra’ila, ba ni kuwa yashe da jama’ata Isra’ila ba.”—1 Sar. 6:11-13.

5, 6. Menene sakamakon rashin aminci da Sulemanu ya yi wa Allah?

5 Sa’ad da ya tsufa Sulemanu bai kasance da aminci ga Jehobah ba, sai ya soma bautar ƙarya. (1 Sar. 11:4-6) Da sannu sannu Sulemanu ya daina yin biyayya ga dokokin Jehobah kuma ya soma zalunci sosai. Shi ya sa sa’ad da ya mutu mutane suka kai ƙararsa ga ɗansa Rehoboam magajinsa, kuma suka roƙi a sassauta musu. (1 Sar. 12:4) Menene Jehobah ya yi sa’ad da Sulemanu ya zama marar aminci?

6 Littafi Mai Tsarki ya gaya mana: “Ubangiji kuwa ya yi fushi da Solomon, domin zuciyatasa ta juya ga barin bin . . . Allah na Isra’ila, wanda ya bayana gareshi so biyu.” Jehobah ya gaya wa Sulemanu: “Tun da shi ke . . . ba ka kuwa kiyaye wa’adina da farillaina ba, waɗanda na umurce ka, hakika zan fizge maka mulkinka, in ba bawanka.”—1 Sar. 11:9-11.

7. Ko da yake an ƙi Sulemanu, ta yaya Jehobah ya kula da amintattunsa?

7 Sai Jehobah ya aiki annabi Ahijah ya naɗa wanda zai ceci Isra’ilawa. Wanda zai cece su shi ne Jeroboam, ƙwararen mutum wanda ya yi aiki a ƙarƙashin Sulemanu. Ko da yake Jehobah ya kasance da aminci ga alkawari na Mulki da ya yi wa Dauda, ya amince a raba ƙabilu 12 zuwa kashi biyu. Za a ba Jeroboam ƙabilu goma; zuriyar Dauda za su riƙe ƙabilu biyu wanda Sarki Rehoboam ne zai shugabantar. (1 Sar. 11:29-37; 12:16, 17, 21) Jehobah ya gaya wa Jeroboam: “Za ya zama kuma, idan ka kasa kunne ga dukan abin da na umurce ka, ka yi tafiya cikin tafarkuna, ka aika abin da ke daidai a gaban idanuna, garin a kiyaye farillaina da dokokina, kamar yadda Dauda bawana ya yi; ni ma in zauna tare da kai, in gina maka tabbatacen gida, kamar yadda na gina ma Dauda, im ba ka Isra’ila kuma.” (1 Sar. 11:38) Jehobah ya taimaki mutanensa kuma ya yi musu hanyar tsira daga zalunci.

8. Wane jarabobbi ne mutanen Allah suke fuskanta a yau?

8 Zalunci da rashin gaskiya sun yi yawa a yau. Mai Wa’azi 8:9 ya ce: “Mutum ya sami iko bisa wani, ikon kuwa ya ciwuce shi.” Kasuwanci na haɗama da sarauta na lalaci suna iya kawo mugun yanayi na tattalin arziki. Sau da yawa shugabanni na gwamnati, na kasuwanci, da kuma na addini suna kafa misali marar kyau. Kamar Lutu mai aminci, amintattun Allah a yau suna “ɓaci ƙwarai domin zaƙuwa ta masu-mugunta.” (2 Bit. 2:7) Bugu da ƙari, sa’ad da muke ƙoƙari mu yi rayuwa bisa ga mizanan Allah, mun zama abin matsi ga shugabanni masu girman kai.—2 Tim. 3:1-5, 12.

9. (a) Menene Jehobah ya riga ya yi don ya ceci mutanensa? (b) Me ya sa muka tabbata cewa koyaushe Yesu zai kasance da aminci ga Allah?

9 Mu tabbata da wannan gaskiyar: Jehobah ba zai ƙyale amintattunsa ba. Ka yi tunanin abubuwan da ya riga ya yi don ya canja lalatattun shugabannin wannan duniya. An riga an kafa Mulkin Almasihu na Allah a hannun Yesu Kristi. Yesu Kristi yana sarauta a sama kusan shekara ɗari. Ba da daɗewa ba zai kawo sauƙi ga waɗanda suke tsoron Allah. (Ka karanta Ru’ya ta Yohanna 11:15-18.) Yesu ya riga ya kasance da aminci ga Allah har mutuwarsa. Ba zai yasar da talakawansa kamar yadda Sulemanu ya yi ba.—Ibran. 7:26; 1 Bit. 2:6.

10. (a) Ta yaya za mu nuna cewa mun amince da Mulkin Allah? (b) Sa’ad da muke fuskantar gwaji, wane tabbaci ya kamata mu kasance da shi?

10 Mulkin Allah gwamnati ce ta ainihi da za ta kawo ƙarshen zalunci. Ya kamata mu kasance da aminci ga Jehobah Allah da kuma Mulkinsa. Da tabbaci sosai bisa Mulkin, za mu ƙi rashin ibada na duniya kuma mu yi ƙwazo wajen biɗan nagargarun ayyuka. (Tit. 2:12-14) Muna ƙoƙari mu kasance marasa aibi a duniya. (2 Bit. 3:14) Ko da wace irin jaraba ce muke fuskanta yanzu, mu tabbata cewa Jehobah zai kāre mu a lokacin da ake jaraba bangaskiyarmu. (Ka karanta Zabura 7:10.) Bugu da ƙari, Zabura 116:15 ta tabbatar mana cewa: “A ganin Ubangiji Mutuwar tsarkakansa abu mai-daraja ne.” Jehobah yana ɗaukan bayinsa da tamani shi ya sa ba zai ƙyale su su halaka gabaki ɗaya ba.

Sa’ad da Muke Fuskantar Tasirin ’Yan Ridda

11. Ta yaya ne Jeroboam ya zama marar aminci?

11 Ya kamata sarautar sarki Jeroboam ta kawo wa mutanen Allah sauƙi. Maimakon haka, halinsa ya gwada amincinsu ga Allah. Jeroboam bai gamsu da girma da kuma gatar da aka ba shi ba, sai ya soma neman hanyoyi da zai ƙarfafa matsayinsa. Ya yi tunani: “Idan jama’an nan sun hau garin su yi hadaya a cikin gidan Ubangiji a cikin Urushalima, sa’annan zuciyar wannan jama’a za ta sake juyawa zuwa wajen ubangijinsu, watau Rehoboam sarkin Yahuda; su a kashe ni, su koma wurin Rehoboam sarkin Yahuda.” Sai Jeroboam ya kafa sabon addini da maruƙa guda biyu na zinariya. “Ya sanya ɗaya cikin Beth-el, ɗayan kuma ya sanya cikin Dan. Wannan abu fa ya zama zunubi; gama jama’a suka tafi garin su yi sujada a gaban ɗayan, watau Dan. Waɗansu masujadai kuma ya maishe su gidaje: ya yi priests kuma daga cikin dukan jama’a, waɗanda ba na ’ya’yan Levi ba ne.” Har Jeroboam ma ya kafa nasa ranar ‘idi domin ’ya’yan Isra’ila,’ ya kuma “hau wurin bagadi, domin shi ƙona turare.”—1 Sar. 12:26-33.

12. Menene amintattun Allah a ƙabila ta arewa suka yi sa’ad da Jeroboam ya kafa bautar maraƙi a Isra’ila?

12 Menene amintattun mutanen Allah a masarauta ƙabila ta arewa za su yi yanzu? Kamar kakaninsu masu aminci, Lawiyawa da suke zaune a birnin da aka ba su a yankin masarauta ƙabilu biyu ta arewa sun ɗauki mataki nan da nan. (Fit. 32:26-28; Lit. Lis. 35:6-8; K. Sha 33:8, 9) Sun bar gadōnsu a birnin kuma suka ƙaura tare da iyalinsu zuwa Yahuda, inda za su ci gaba da bauta wa Jehobah ba tare da matsi ba. (2 Laba. 11:13, 14) Wasu Isra’ilawa da suke zaune a Yahuda na ɗan lokaci sun zaɓi su ci gaba da zama a birnin na dindindin maimakon su koma gida. (2 Laba. 10:17) Jehobah ya ga cewa wasu daga cikin masarauta ƙabila ta arewa a nan gaba za su iya ƙyale bautar maraƙi su koma wa bauta ta gaskiya a Yahuda.—2 Laba. 15:9-15.

13. A zamanin nan, ta yaya ne ’yan ridda suke matsa wa mutanen Allah ta hanyoyin rinjaya?

13 A yau, ’yan ridda suna matsa wa mutanen Allah ta hanyoyinsu na rinjaya. Wasu shugabannin suna ƙoƙari su kafa nasu addinin, kuma suna matsa wa talakawansu su bi addinin. Shugabannin Kiristendom da wasu masu girman kai sun yi ƙoƙarin da’awar cewa sune firistoci na ruhaniya. Amma, a cikin Kiristoci na gaskiya ne kawai ake samun shafaffu na gaske, waɗanda suka zama “priesthood basarauci.”—1 Bit. 2:9; R. Yoh. 14:1-5.

14. Menene ya kamata mu yi idan ’yan ridda suka rinjaye mu?

14 Kamar amintattun Lawiyawa a ƙarni na goma K.Z., a yau amintattun Allah ba sa barin ’yan ridda su rinjaye su. Shafaffu da abokansu Kiristoci suna saurin guje wa dabarun ’yan ridda. (Ka karanta Romawa 16:17.) Sa’ad da muka yi wa shugabanni biyayya a al’amura na jama’a kuma muka ƙi saka hannu a harkokin wannan duniya, za mu kasance da aminci ga Mulkin Allah. (Yoh. 18:36; Rom. 13:1-8) Muna ƙin halayen waɗanda suke da’awar cewa suna bauta wa Allah amma halayensu ba ya daraja shi.—Tit. 1:16.

15. Me ya sa ya kamata mu yi biyayya ga “bawan nan mai-aminci, mai-hikima”?

15 Ka yi tunanin yadda Jehobah ya yi wa masu zuciyar kirki tanadin fita daga muguwar duniya ta alama zuwa aljanna ta ruhaniya da ya yi tanadinsa. (2 Kor. 12:1-4) Da farin ciki, muna bin umurnin “bawan nan mai-aminci, mai-hikima wanda ubangijinsa ya sanya shi bisa iyalin gidansa, domin shi ba su abincinsu a lotonsa?” Kristi ya naɗa bawansa “bisa dukan abin da ya ke da shi.” (Mat. 24:45-47) Saboda haka, idan ba mu fahimci wani mataki da rukunin bawa ya ɗauka ba, hakan ba dalili ba ne da zai sa mu ƙi umurninsu ko mu koma wa duniyar Shaiɗan ba. Maimakon haka, yin biyayya zai sa mu nuna tawali’u kuma mu dogara ga Jehobah don ya bayyana al’amura.

Sa’ad da Ake Yin Aikin Allah

16. Wane aiki ne Jehobah ya ba wa wani annabi daga Yahuda?

16 Jehobah ya hukunta Jeroboam don halayensa na ridda. Ya naɗa annabi daga Yahuda ya je arewacin Bethel ya sami Jeroboam sa’ad da yake hidima a bagadi. Annabin zai idar da saƙon hukunci ga Jeroboam. Hakika, wannan aiki ne mai wuya.—1 Sar. 13:1-3.

17. Ta yaya ne Jehobah ya kāre manzonsa?

17 Sa’ad da Jeroboam ya ji hukuncin da Jehobah zai yi masa, ya yi fushi sosai. Ya miƙa hannunsa ga manzon da Allah ya aika, ya tada murya ya ce wa mazan da suke kusa da shi: Ku “kama shi.” Amma nan da nan, kafin su kama shi, sai “hannunsa fa, wanda ya miƙa a kansa, ya shanye, har da ba ya iya mayas da shi wurinsa ba. Bagadi kuma ya tsagu, toka kuwa suka zube daga cikin bagadi.” Hakan ya sa ya zama dole Jeroboam ya ce annabin ya roƙan masa Jehobah kuma ya yi addu’a don hannun da ya shanye ya dawo daidai. Annabin ya yi hakan, kuma hannunsa ya warke. Hakika Jehobah ya kāre manzonsa daga lahani.—1 Sar. 13:4-6.

18. Ta yaya ne Jehobah yake kāre mu sa’ad da muka ci gaba da bauta masa?

18 Sa’ad da muke yin aikin wa’azin Mulki da almajirantarwa, wani lokaci muna fuskantar mutane da ba su da fara’a ko kuma suna ƙiyayya. (Mat. 24:14; 28:19, 20) Ka da mu bari tunanin cewa ba za a saurare mu ba ya sa mu daina ƙwazo a hidima. Kamar annabi na zamanin Jeroboam da ba a ambata sunansa ba, muna da gatar “bauta masa [Jehobah] ba tare da tsoro ba, cikin tsarki.”a (Luka 1:74, 75) Ko da yake ba ma tsammanin Allah ya sa hannu ta yin mu’ujiza a yau, amma har yanzu Jehobah yana kāre mu a matsayin Shaidunsa ta wurin ruhunsa mai tsarki da kuma mala’iku. (Ka karanta Yohanna 14:15-17; Ru’ya ta Yohanna 14:6.) Allah ba zai taɓa yasar da waɗanda suka ci gaba da wa’azin kalmarsa da gaba gaɗi ba.—Filib. 1:14, 28.

Jehobah Zai Kāre Amintattunsa

19, 20. (a) Me ya sa muna da tabbaci cewa Jehobah ba zai yashe mu ba? (b) Waɗanne tambayoyi ne za a tattauna a talifi na gaba?

19 Jehobah Allhanmu ne mai aminci. (R. Yoh. 15:4; 16:5) Shi “mai-alheri ne cikin dukan ayyukansa.” (Zab. 145:17) Littafi Mai Tsarki kuma ya tabbatar mana cewa: Zai “kiyaye tafarkin tsarkakansa.” (Mis. 2:8) Sa’ad da suke fuskantar matsi ko kuma ra’ayin ’yan ridda, da kuma aiki mai wuya, ya kamata amintattun Allah su tabbata cewa Jehobah zai yi musu ja-gora kuma ya taimake su.

20 Abin da ya kamata kowanenmu ya yi tunani shi ne: Menene zai taimake ni na riƙe amincina ga Jehobah duk da irin matsi ko kuma gwaji da nake fuskanta? Kuma yaya zan ci gaba da ƙarfafa aminci na ga Allah?

[Hasiya]

a Ko annabin ya ci gaba da yi wa Jehobah biyayya ko a’a, a talifi na gaba za a tattauna abin da ya same shi.

Yaya Za Ka Amsa?

• Ta yaya ne Jehobah ya nuna cewa ba zai yashe amintattunsa ba sa’ad da suke fuskantar gwaji?

• Ta yaya ya kamata mu bi da ’yan ridda da ra’ayinsu?

• Ta yaya Jehobah yake kāre amintattunsa sa’ad da suke hidima ta Kirista?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba