Jehobah Shi Ne ‘Mai Cetonmu’
“Ubangiji kuma yana taimakonsu, yana cetonsu.”—ZAB. 37:40.
1, 2. Wace muhimmiyar gaskiya game da Jehobah ce za ta ƙarfafa mu?
INUWA ba ta tsayawa wuri ɗaya. Sa’ad da duniya take juyawa, inuwa tana juyawa kuma tana canjawa. Amma, Mahaliccin duniya da rana ba ya canjawa. (Mal. 3:6) Littafi Mai Tsarki ya ce: “Wanda sakewa ba ta yiwuwa gareshi, ba kuwa inuwa ta juyawa.” (Yaƙ. 1:17) Wannan gaskiya game da Jehobah tana ƙarfafa mu, musamman sa’ad da muke fuskantar gwaji da ƙalubale masu wuya. Me ya sa?
2 Kamar yadda muka lura a talifin da ya gabata, Jehobah ‘mai ceto’ ne a zamanin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki. (Zab. 70:5) Ba ya canjawa kuma yana yin abubuwa da ya ce zai yi, saboda haka, masu bauta masa a yau suna da dalilin dogara a gare shi don ya ‘taimake su kuma ya cece su.’ (Zab. 37:40) Ta yaya Jehobah ya ceci bayinsa a zamanin nan? Ta yaya zai ceci kowannen mu?
Ceto Daga Masu Hamayya
3. Me ya sa muka tabbata cewa masu hamayya ba za su iya hana mutanen Jehobah yin aikin wa’azin bishara ba?
3 Babu hamayya da Shaiɗan zai kawo da za ta taɓa hana Shaidun Jehobah su bauta masa shi kaɗai don ya cancanci hakan. Kalmar Allah ta tabbatar mana: “Babu alatun da aka halitta domin ciwutanki da za ya yi albarka; iyakar harshe kuma da za shi tashi gaba da ke, a shari’a za ki kayar da shi.” (Isha. 54:17) Masu hamayya sun kasa hana mutanen Allah yin aikinsu na wa’azi. Ga misalai biyu.
4, 5. Mutanen Jehobah sun fuskanci wace hamayya a shekara ta 1918, da wane sakamako?
4 A shekara ta 1918, mutanen Jehobah sun fuskanci tsanantawa da shugabannin addinai suka zuga don su hana su aikin wa’azi. A ranar 7 ga Mayu an ba da izini daga gwamnatin tarayya a kama J. F. Rutherford wanda yake kula da aikin wa’azi a dukan duniya a lokacin, da kuma wasu da suke hedkwatar Shaidun Jehobah. A cikin watanni biyu, aka yi wa ɗan’uwa Rutherford da abokanansa hukunci da bai dace ba kuma aka yi musu ɗaurin talala a kurkuku. Masu hamayya sun yi nasara ne wajen yin amfani da kotu don su hana aikin wa’azi na dindindin? A’a!
5 Ka tuna alkawarin Jehobah: “Babu alatun da aka halitta domin ciwutanki da za ya yi albarka.” Nan da nan abubuwa suka canja, a ranar 26 ga Maris ta shekara ta 1919, wato bayan watanni tara, aka yi belin Ɗan’uwa Rutherford da abokansa da aka ɗaure. A ranar 5 ga Mayu na shekara ta 1920 aka yi watsi da dukan abin da ake tuhumarsu a kai. ’Yan’uwan sun yi amfani da ’yancinsu suka ci gaba da aikin Mulki. Menene sakamakon hakan? An ci gaba da samun ƙari na ban mamaki tun daga wannan lokacin! Dukan yabo domin wannan ƙari ya tabbata ga ‘mai ceto.’—1 Kor. 3:7.
6, 7. (a) Menene aka yi wa Shaidun Jehobah a Nazi da ke Jamus, kuma da wane sakamako? (b) Menene tarihin Shaidun Jehobah na zamanin nan ya nuna?
6 Ga misali na biyu. A shekara ta 1934, Hitler ya rantse sai ya halaka Shaidun Jehobah a Jamus. Kuma ya yi niyyar yin abin da ya faɗi. Bayan haka aka kama mutane da yawa kuma aka saka su a kurkuku. An tsananta wa Shaidu dubbai; kuma aka kashe Shaidu da yawa. Hitler ya yi nasara ne wajen halaka dukan Shaidu? Ya hana dukan aikin wa’azin bishara a Jamus ne? Ko kaɗan! A lokacin tsanantawar, ’yan’uwanmu sun ci gaba da aikin wa’azi a ɓoye. Bayan faɗuwar mulkin ’yan Nazi, sun yi amfani da ’yancinsu su ci gaba da wa’azi. A yau, masu shelar Mulki sun fi 165,000 a Jamus. A wannan lokacin kuma, ‘mai ceto’ ya yi abin da ya yi alkawarinsa: “Babu alatun da aka halitta domin ciwutanki da za ya yi albarka.”
7 Tarihin Shaidun Jehobah na zamanin nan ya ba da tabbaci cewa Jehobah ba zai taɓa ƙyale a halaka mutanensa gabaki ɗaya ba. (Zab. 116:15) Mu kuma fa? Ta yaya Jehobah yake ceton kowanenmu?
Kāriya Ta Zahiri Kuma Fa?
8, 9. (a) Me ya sa muka tabbata cewa a wani yanayin ba za mu sami kāriya ta zahiri ba? (b) Me ya kamata mu tabbata da shi?
8 Mun san cewa Jehobah bai yi mana alkawari cewa zai kāre kowannenmu a zahiri a yanzu ba. Mun ɗauki matsayin Ibraniyawa uku masu aminci da suka ƙi bauta wa gunki na zinariya na Sarki Nebukadnezzar. Waɗannan matasa masu tsoron Allah ba su yi tsammanin cewa Jehobah zai kāre su ta mu’ujiza daga haɗari na zahiri ba. (Ka karanta Daniel 3:17, 18.) Al’amarin ya canja kuma Jehobah ya cece su daga tanderu mai zafi ƙwarai. (Dan. 3:21-27) Amma har a zamanin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki da kyar ne ake ceton mutane ta mu’ujiza. Masu hamayya sun kashe amintattu bayin Jehobah da yawa.—Ibran. 11:35-37.
9 Yau kuma fa? Da yake Jehobah shi ne ‘mai ceto’ zai iya ceton mutane daga yanayi mai wuya. Za mu iya faɗan cewa Jehobah ya sa hannu a wasu batutuwa ne ko bai sa ba? A’a. Duk da haka, wanda ya tsira daga mugun yanayi zai ji cewa Jehobah ne ya kāre shi. Ba zai yi kyau ba wasu su yi musu hakan ba. Duk da haka, ya kamata mu san cewa amintattu Kiristoci da yawa sun mutu domin tsanantawa, yadda yake a zamanin ’yan Nazi. Wasu sun mutu domin sun fuskanci yanayi mai wuya. (M. Wa. 9:11) Muna iya yin tambaya, ‘Jehobah ya kasa ‘ceton’ waɗannan amintattu da aka kashe ne?’ A’a.
10, 11. Me ya sa mutum ba zai iya guje wa mutuwa ba, amma menene Jehobah zai yi?
10 Ka yi la’akari da wannan: Mutum ba zai iya guje wa mutuwa ba, domin ba mutumin da zai iya ya “ceci ransa daga hannun Sheol,” ko kuma Hades, wato, kabari. (Zab. 89:48) Jehobah kuma fa? Wata ’yar’uwa da ta tsira daga tsoron abin da ya faru a Nazi ta tuna abin da mamarta Mashaidiya ta gaya mata don ta sami ƙarfafa don ƙaunatattu da suka mutu a sansanin fursuna, mamar ta ce: “Idan za a ci gaba da mutuwa har abada, wato zai fi ƙarfin Allah ke nan.” Hakika, mutuwa ba ta fi ƙarfin mai Tushin rai ba. (Zab. 36:9) Jehobah zai tuna da dukan waɗanda suke cikin Sheol, ko Hades, kuma ya ta da kowannensu.—Luk 20:37, 38; R. Yoh. 20:11-14.
11 Yanzu, Jehobah yana kula da rayuwar amintattu masu bauta masa. Bari mu tattauna hanyoyi guda uku da yake “cetonmu.”
Kāriya Ta Ruhaniya
12, 13. Me ya sa tanadi na ruhaniya yake da muhimmanci, kuma ta yaya Jehobah yake yi mana tanadinsu?
12 Jehobah yana kāre ruhaniyarmu, wadda ita ce mafi muhimmanci. Mu Kiristoci mun fahimci cewa akwai abin da ya fi rayuwarmu na yanzu muhimmanci. Abin da muke da shi mai muhimmanci shi ne dangantakarmu da Jehobah. (Zab. 25:14; 63:3) Idan ba don wannan dangantakar ba, rayuwarmu na yau ba za ta kasance da muhimmanci ba kuma ba za mu kasance da bege a nan gaba ba.
13 Muna godiya don Jehobah ya ba mu dukan taimako da muke bukata don mu riƙe dangantakarmu da shi. Muna da Kalmarsa, ruhunsa mai tsarki, da kuma ikilisiyarsa na dukan duniya da za su taimake mu. Ta yaya za mu yi amfani da tanadin da Jehobah ya yi mana? Ta wurin sa ƙwazo a yin nazarin Kalmarsa a kai a kai, za mu ƙarfafa bangaskiyarmu da begenmu. (Rom. 15:4) Ta wurin roƙon ruhunsa, za mu sami taimako don mu kauce wa gwaji da zai sa mu lalata dangantakarmu da shi. (Luk 11:13) Ta wurin yin biyayya da ja-gorar da rukunin bawan nan yake bayarwa a cikin littattafai da suke bayyana Littafi Mai Tsarki, taro, manyan taro, da kuma taron gunduma, za mu amfana daga ‘abinci a loto.’ (Mat. 24:45) Irin waɗannan tanadi za su kāre mu a ruhaniya kuma su taimake mu mu kusaci Allah—Yaƙ. 4:8.
14. Ka ba da labarin da ya nanata kāriya ta ruhaniya.
14 Don mu ga misalin yadda Jehobah yake kāre dangantakarmu da shi, mu tuna iyayen da aka ambata a talifin da ya gabata. ’Yan kwanaki bayan da aka gaya musu cewa ’yarsu Theresa ta ɓace, sun sami labari marar daɗi cewa an kashe ta.a Uban ya tuna: “Na yi addu’a don Jehobah ya kāre ta. A lokacin da aka ce ta mutu, da farko na yi tunanin abin da ya sa Jehobah bai amsa addu’a ta ba. Hakika na san cewa Jehobah bai ba kowanne mutanensa tabbacin kāriya ta mu’ujiza ba. Na ci gaba da yin addu’a don na samu fahimi. Sanin cewa Jehobah yana kāre mutanensa a ruhaniya, wato, yana tanadin abin da muke bukata domin ya kāre dangantakarmu da shi ya ƙarfafa ni sosai. Irin wannan kāriya ce ta fi muhimmanci domin za ta iya shafan rayuwarmu ta nan gaba. A wannan azanci, Jehobah ya kāre Theresa; ta bauta masa da aminci har mutuwarta. Na sami kwanciyar hankali da sanin cewa rayuwarta ta nan gaba tana hannunsa.”
Kāriya a Lokacin Rashin Lafiya
15. A waɗanne hanyoyi ne Jehobah zai iya taimakonmu sa’ad da muke rashin lafiya?
15 Jehobah zai iya kiyaye mu ‘a bisa shimfiɗarmu ta rashin lafiya’ yadda ya yi wa Dauda. (Zab. 41:3) Ko da yake Jehobah ba ya kāre mu yanzu ta wurin warkar da mu ta mu’ujiza, amma yana taimakonmu. Ta yaya? Ƙa’idodin da ke cikin Kalmarsa za su taimake mu wajen tsai da shawarwari masu kyau game da irin magani da za mu sha da kuma wasu batutuwa. (Mis. 2:6) Za mu iya samun bayani da shawarwari masu kyau daga talifofi da ke cikin Hasumiyar Tsaro da Awake! da suka tattauna irin rashin lafiya da muke yi. Ta wurin ruhunsa, Jehobah zai iya ba mu “mafificin iko” don mu jimre yanayinmu kuma mu kasance da aminci, ko da menene zai faru. (2 Kor. 4:7) Da irin wannan taimako, za mu guji mai da hankali ainun ga rashin lafiyarmu har mu manta da abubuwa na ruhaniya.
16. Menene ya taimaki wani ɗan’uwa ya jimre da rashin lafiya?
16 Ka yi la’akari da matashi da aka yi maganarsa a somawar talifin da ya gabata. A shekara ta 1998 an gano cewa yana da ciwon da zai shanye masa jiki.b Ta yaya ya jimre da ciwonsa? Ya ba da bayani: “Akwai lokacin da nake baƙin ciki sosai sa’ad da na ga cewa mutuwa ce kaɗai hanyar da zan samu sauƙi daga wannan ciwon. Sa’ad da nake baƙin ciki sosai, ina yin addu’a ga Jehobah ya ba ni abubuwa guda uku: kwanciyar hankali, haƙuri, da jimiri. Jehobah ya amsa addu’o’ina. Kwanciyar hankali ta sa na yi tunani a kan abubuwan da za su ƙarfafa ni, kamar yadda zama a sabuwar duniya za ta kasance sa’ad da zan iya tafiya, more abinci mai ɗanɗano, da kuma yin magana da iyalina. Haƙuri ya taimake ni na jimre da wahala da kuma ƙalubalen ciwon shan inna. Jimiri ya taimake ni na kasance da aminci kuma ban yi rashin ruhaniya ta ba. Na gaskata da mai zabura Dauda don na ga cewa Jehobah ya kiyaye ni a gadon rashin lafiyata.”—Isha. 35:5, 6.
Tanadin Abin Biyan Bukata
17. Menene Jehobah ya yi alkawari zai yi mana, kuma menene wannan alkawarin yake nufi?
17 Jehobah ya yi alkawari zai kula da bukatunmu. (Ka karanta Matta 6:33, 34 da Ibraniyawa 13:5, 6.) Wannan ba ya nufin mu ƙi yin aiki don muna ganin cewa za a biya bukatunmu ta mu’ujiza. (2 Tas. 3:10) Wannan alkawarin yana nufin cewa idan mun fara biɗan Mulki Allah a rayuwarmu kuma muna shirye mu yi aiki, Jehobah zai taimake mu mu samu abin biyan bukatunmu. (1 Tas. 4:11, 12; 1 Tim. 5:8) Zai yi tanadin abin da muke bukata a hanyoyi da ba za mu yi tsammani ba, wataƙila ta wurin ɗan’uwa da zai taimake mu ko kuma ya ba mu aiki.
18. Ka ba da labarin da ya nuna cewa ana iya biya mana bukatunmu sa’ad da muke da damuwa.
18 Ka tuna da wata mata da aka ambata a somawar talifin da ya gabata. Sa’ad da ita da ’yarta suka ƙaura zuwa wani wuri, samun aiki ya yi mata wuya. Ta ce: “Zan fita hidimar fage da safe kuma da rana na soma neman aiki. Na tuna wata rana da na je wani kanti na sayi madara. Na tsaya wurin ina kallon kayan miya, amma ba ni da isashen kuɗi da zan saye su. Ban taɓa yin irin wannan baƙin ciki a rayuwata ba. Sa’ad da na koma gida, na ga an cika mini zaure da kayan miya. Mun samu isashen abinci har na watanni. Na yi kuka, kuma na gode wa Jehobah.”’Yar’uwar daga baya ta gane cewa wani ɗan’uwa a cikin ikilisiyarsu da ke da lambu ne ya kawo mata kayan miya da yawa. Ta rubuta masa: “Ko da yake na gode maka sosai, na kuma gode wa Jehobah don ya yi amfani da alherinka ya tuna mini cewa yana ƙaunata.”—Mis. 19:17.
19. A lokacin ƙunci mai girma, bayin Jehobah suna da wane tabbaci, kuma menene ya kamata mu kuɗiri aniyar yi?
19 Hakika, abin da Jehobah ya yi a zamanin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki da kuma zamaninmu ya ba mu tabbacin dogara da shi a matsayin mai taimakonmu. Ba da daɗewa ba, sa’ad da ƙunci mai girma zai faɗa wa duniyar Shaiɗan, za mu bukaci taimakon Jehobah fiye da kowane lokaci. Duk da haka, bayin Jehobah za su dogara gare shi da cikakken tabbaci. Za su ta da kansu su yi farin ciki, domin sun san cetonsu ya kusa. (Luk 21:28) Kafin lokacin, ko da wane irin gwaji za mu fuskanta, bari mu ƙuduri aniya mu dogara ga Jehobah, mu kasance da cikakken tabbaci cewa Allahnmu, hakika, ‘mai cetonmu’ ba ya canjawa.
[Hasiya]
a Ka duba talifin nan “Coping With an Unspeakable Tragedy,” a Awake! na 22 ga Yuli, 2001, shafuffuka na 19-23.
b Ka duba talifin nan “Sustained by My Faith—Living With ALS,” a Awake! na Janairu 2006, shafuffuka na 25-29.
Ka Tuna?
• Ta yaya Jehobah zai ceci waɗanda aka kashe?
• Me ya sa kāriya ta ruhaniya ta fi muhimmanci?
• Menene alkawarin da Jehobah ya yi cewa zai biya bukatunmu yake nufi?
[Hoto a shafi na 8]
An jefa Ɗan’uwa Rutherford da abokansa a kurkuku a shekara ta 1918 kuma daga baya aka sake su kuma aka yi watsi da tuhumar da aka yi musu
[Hoto a shafi na 10]
Jehobah zai iya kiyaye mu a ‘shimfiɗa ta rashin lafiya’