Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w09 1/1 p. 19
  • Mahalicci da Ya Cancanci Mu Yabe Shi

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Mahalicci da Ya Cancanci Mu Yabe Shi
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Girmama Wanda Ya Cancanci Girmamawa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
  • Jehovah—Mai Ƙarfi Cikin Iko
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Su Waye Suke Ɗaukaka Allah A Yau?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Jehobah “Mai Girma Ne”
    Ka Kusaci Jehobah
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
w09 1/1 p. 19

Ka Kusaci Allah

Mahalicci da Ya Cancanci Mu Yabe Shi

Ru’ya Ta Yohanna 4:11

KA TAƁA tunani, ko ‘Menene ma’anar rai?’ Waɗanda suka gaskata cewa rai ta bayyana ne kawai ba su yi nasara ba wajen neman amsa. Amma ba haka yake ga waɗanda suka gaskata cewa Jehobah Allah ne Tushen ba. (Zabura 36:9) Sun sani cewa yana da dalilin halittarmu. Dalilin yana rubuce cikin Ru’ya ta Yohanna 4:11. Bari mu bincika yadda waɗannan kalaman da manzo Yohanna ya rubuta suka bayyana dalilin da ya sa muke nan duniya.

Yohanna ya rubuta waƙa da ake yi a samaniya domin yabon Allah: “Kai ne mai-isa ka karɓi ɗaukaka da daraja da iko, ya Ubangijinmu da Allahnmu: gama kai ka halicci dukan abu, saboda nufinka kuma suka kasance, saboda nufinka aka halicce su.” Jehobah ne kaɗai ya cancanci irin wannan ɗaukakar. Me ya sa? Saboda shi ne ya ‘halicci dukan abubuwa.’ Menene ya kamata waɗannan halittu masu basira za su yi?

An ce Jehobah ya cancanci ya “karɓi” ɗaukaka, daraja da kuma iko. Babu shakka, shi ne mafi girma, ɗaukaka da kuma iko a sararin samaniya. Yawancin mutane ba su gaskata cewa shi ne mahaliccin dukan abubuwa ba. Duk da haka, akwai waɗanda suka fahimci “al’amura na [Allah] da ba su ganuwa” ta wurin abubuwan da ya halitta. (Romawa 1:20) Da zuciya cike da godiya, suna ba Jehobah girma da ɗaukaka. Suna gaya wa duka waɗanda za su saurari tabbaci da ya nuna cewa Jehobah ne ya halicci dukan abubuwa kuma ya cancanci mu ɗaukaka shi.—Zabura 19:1, 2; 139:14.

Ta yaya Jehobah yake samun iko daga masu bauta masa? Hakika, babu halittar da za ta ba iko ga mahalicci Maɗaukaki. (Ishaya 40:25, 26) Duk da haka, da yake an halicce mu cikin sifar Allah, muna da halaye irin na Allah, wanda ɗaya daga ciki shi ne iko. (Farawa 1:27) Idan da gaske muna godiya ga abin da Mahaliccinmu ya yi mana, hakan zai motsa mu mu yi amfani da ikonmu da ƙarfinmu mu girmama kuma mu ɗaukaka shi. Maimakon mu sa kuzari don mu ci gaba a na mu aikin, ya kamata mu fahimci cewa Jehobah Allah ya cancanci mu bauta masa da dukan ƙarfinmu.—Markus 12:30.

Me ya sa muke nan? Ƙarshen Ru’ya ta Yohanna 4:11 ta ba da amsa: “Saboda nufinka kuma [dukan abubuwa] suka kasance, saboda nufinka aka halicce su.” Ba mu muka halicci kanmu ba. Mun rayu ne saboda nufin Allah. Saboda haka, yin rayuwa ta son kanmu kawai ba ta da wata ma’ana. Don mu sami salama, gamsuwa, kuma mu yi farin ciki, muna bukatar mu koyi abin da nufin Allah yake nufi kuma mu sa rayuwarmu ta jitu da nufinsa. Ta haka ne kawai za mu san dalilin da ya sa aka halicce mu da kuma dalilin da ya sa muke wanzuwa.—Zabura 40:8.

[Picture Credit Line on page 19]

NASA, ESA, and A. Nota (STScI)

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba