Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 12/15 pp. 16-20
  • Ka Ƙudurta Ba Da Shaida Sosai

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Ƙudurta Ba Da Shaida Sosai
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ya Ba da Shaida Sosai!
  • Yin Bishara Sosai a Yau
  • Sakamakon da Wataƙila ba Mu Sani Ba
  • Ku Ba da Cikakken “Shaida”
    Hidimarmu Ta Mulki—2013
  • An Koyar Da Su Domin Su Yi Wa’azi Da Kyau
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Ka Koya Yin Tsaro Daga Manzannin Yesu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 12/15 pp. 16-20

Ka Ƙudurta Ba Da Shaida Sosai

“Ya umurce mu kuma mu yi ma jama’a wa’azi.”—A. M. 10:42.

1. Sa’ad da yake magana a gaban Karniliyus, wane umurni ne Bitrus ya ambata?

SHUGABAN sojoji ɗan Italiya ya tara danginsa da kuma abokansa a batun da ya zama canji mafi muhimmanci a yadda Allah yake bi da mutane. Sunan mutumin nan mai tsoron Allah shi ne Karniliyus. Manzo Bitrus ya gaya wa rukunin cewa an umurci manzannin su ‘yi ma jama’a wa’azi, su ba da shaida’ sosai game da Yesu. Shaidar da Bitrus ya bayar ta kawo sakamako mai kyau. ’Yan Al’umma marar kaciya sun sami ruhun Allah, suka yi baftisma, kuma suka zama sarakunan da za su yi sarauta tare da Yesu a sama. Shaidar da Bitrus ya yi ta ba da sakamako mai kyau!—A. M. 10:22, 34-48.

2. Ta yaya muka san cewa umurnin ba da shaida ba ga manzanni 12 ba ne ba kawai?

2 Hakan ya faru ne a shekara ta 36 A.Z. Shekaru biyu da suka gabata, wani mai hamayya da Kiristanci ya shaida wani abin da ya canja rayuwarsa. Shawulu ɗan birnin Tarsus yana kan hanyarsa ta zuwa Dimashƙu sa’ad da ya ji muryar Yesu kuma ya ce masa: “Ka shiga birni, za a faɗa maka abin da za ka yi.” Yesu ya tabbatar wa almajiri Hananiya cewa Shawulu zai ba da shaida ga “al’ummai da sarakuna, da ’ya’yan Isra’ila.” (Karanta Ayukan Manzanni 9:3-6, 13-20.) Sa’ad da yake tare da Shawulu, Hananiya ya ce: ‘Allah na ubanninmu ya [zaɓe] ka, . . . gama za ka zama shaidassa ga dukan mutane.’ (A. M. 22:12-16) Ta yaya ne Shawulu, wanda daga baya aka san shi da Bulus ya ɗauki aikin yin shaida da muhimmanci?

Ya Ba da Shaida Sosai!

3. (a) Wane labari ne za mu tattauna? (b) Ta yaya ne dattawan Afisa suka karɓi saƙon Bulus, kuma wane misali mai kyau ne suka kafa?

3 Abin sha’awa ce mu yi nazarin dukan abin da Bulus ya yi bayan hakan, amma a yanzu, za mu mai da hankali ne a kan jawabin da Bulus ya bayar a wajen shekara ta 56 A.Z., kamar yadda aka rubuta a Ayukan Manzanni sura ta 20. Bulus ya gabatar da wannan jawabin a kusan ƙarshen tafiyarsa ta uku da ya yi zuwa ƙasashen waje. Ya sauka a Militas, wato, tashar jirgin ruwa da ke Tekun Arjiya, kuma ya aika a kirawo dattawan ikilisiyar Afisa. Tafiyar kilomita 50 ce zuwa Afisa, kuma hanyoyi ne masu kwane-kwane. Za ka iya yin tunanin irin farin cikin da dattawan Afisa suka yi sa’ad da suka sami saƙon Bulus. (Gwada Misalai 10:28.) Duk da haka, suna bukatar su yi shirin zuwa Militas. Wataƙila wasu a cikinsu sun nemi a ba su damar yin tafiya ko kuwa su kulle shagonsu. Kiristoci da yawa a yau suna yin hakan don su halarci dukan sashen taron gundumarsu ta shekara-shekara.

4. Wane tafarki ne Bulus ya bi a ’yan shekarun da ya yi a Afisa?

4 Menene kake tunani Bulus ya yi a Militas a cikin kwanakin nan uku zuwa huɗu har sa’ad da dattawan suka iso? Da me za ka yi? (Gwada Ayukan Manzanni 17:16, 17) Kalaman Bulus ga dattawan Afisa ya taimaka mana mu san amsar. Ya kwatanta fasalin rayuwarsa a cikin waɗannan shekarun, har sa’ad da yake Afisa. (Karanta Ayukan Manzanni 20:18-21.) Domin ya san cewa babu wanda zai ƙaryata shi, ya ce: “Ku da kanku kun sani, tun randa na fara sa ƙafa cikin Asiya, . . . [na ba da] shaida.” Hakika, ya ƙudurta cika aikin da Yesu ya ba shi. Ta yaya ya yi hakan a Afisa? Hanya ɗaya ita ce ta wajen yin wa’azi ga Yahudawa, kuma ya je wajen da zai ga mutane da yawa. Luka ya ba da rahoto cewa sa’ad da Bulus yake Afisa a kusan shekara ta 52-55 A.Z., ya yi ‘magana da gaba gaɗi, yana rinjayar mutane’ a cikin majami’a. Sa’ad da Yahudawa “suka taurare, suka ƙi biyayya,” Bulus ya mai da hankalinsa ga wasu mutanen, ya koma wane sashen birnin kuma ya ci gaba da yin wa’azi. Da haka, ya ba da shaida ga Yahudawa da kuma Helenawa da ke wannan babban birnin.—A. M. 19:1, 8, 9.

5, 6. Me ya sa muka tabbata cewa sa’ad da Bulus ya yi wa’azi na gida-gida, ya yi magana ne ga marasa bi?

5 Wasu da suka zama Kiristoci, waɗanda Bulus ya yi wa wa’azi a Militas, da shigewar lokaci sun zama dattawa. Bulus ya tuna musu irin salon da ya yi amfani da shi: “Ban ji nauyin bayyana muku kowane abu mai-amfani, gida gida ni ke bin ku, ina koya muku a sarari.” A zamaninmu, wasu mutane sun yi da’awar cewa Bulus a nan yana maganar ziyarar ƙarfafawa da dattawa ke kai wa ’yan’uwa ne. Amma, ba haka ba ne. Kwatancin nan, koyarwa ‘gida-gida da kuma sarari’ ainihi yana nufin yi wa marasa bi wa’azi ne. Hakan ya fita dalla-dalla a kalamansa ta gaba. Bulus ya ce ya yi wa’azi ‘ga Yahudawa da Helenawa [game da] tuba zuwa ga Allah, da bangaskiya ga Ubangijinmu Yesu Kristi.’ Babu shakka, Bulus ya yi wa’azi ga marasa bi, waɗanda suke bukatar su tuba kuma su ba da gaskiya ga Yesu.—A. M. 20:20, 21.

6 A cikin wani cikakken bayanin da ya yi game da Nassosin Kirista na Helenanci, wani masani ya ce game da Ayukan Manzanni 20:20: “Bulus ya yi shekara uku a Afisa. Ya ziyarci kowane gida, ko kuwa a ce ya yi wa’azi ga dukan mutane (aya ta 26). Wannan shi ne umurnin da ke cikin nassi na yin bishara na gida-gida da kuma koyarwa a sarari.” Ko da ya ziyarci kowane gida ne a zahiri, kamar yadda wannan masanin ya ce, ko a’a, Bulus ba ya son dattawan Afisa su manta cewa ya yi wa’azi da kuma sakamakon hakan. Luka ya ba da rahoto: “Dukan mazamna cikin Asiya suka ji maganar Ubangiji, da Yahudawa da Hellenawa.” (A. M. 19:10) Amma ta yaya ne “dukan” waɗanda suke ƙasar Asiya suka ji bishara, kuma menene hakan ya nuna game da wa’azin da muke yi?

7. Ta yaya ne wa’azin da Bulus ya yi wataƙila ya shafi har waɗanda bai yi wa wa’azi ba kai tsaye?

7 Ta wajen wa’azin da Bulus ya yi a wuraren da jama’a suke da kuma gida-gida, mutane da yawa sun ji saƙonsa. Kana tunanin cewa dukan waɗanda suka ji saƙonsa suna zaune ne kawai a Afisa, babu mai zuwa wani wuri ya yi kasuwanci, ya je ya ziyarci danginsa, ko ya nemi inda babu hayaniya ya zauna? Da kyar. Mutane da yawa a yau sun ƙaura domin irin waɗannan dalilan; wataƙila kai ma haka. A lokacin, mutane daga wasu wurare sun je Afisa don su ziyarci ’yan’uwansu ko su yi kasuwanci. A lokacin da suke wurin, wataƙila sun sadu da Bulus ko kuwa sun ji shi yana wa’azi. Menene zai faru sa’ad da suka koma gida? Waɗanda suka karɓi gaskiya za su ba da shaida. Wasu ƙila ba su zama masu bi ba, duk da haka, wataƙila sun faɗi abubuwan da suka ji sa’ad da suke Afisa. Da haka, wataƙila ’yan’uwansu, maƙwabtansu, ko kuwa masu aiki a ƙarƙashinsu sun ji gaskiya, kuma sun karɓe ta. (Gwada Markus 5:14) Menene hakan ya nuna game da yadda shaidar da kake yi sosai zai iya shafan wasu?

8. Ta yaya ne mutanen da suke dukan yankin Asiya suka ji gaskiya?

8 Game da hidimarsa a Afisa, Bulus ya rubuta cewa ‘kofa mai-faɗi mai-yalwar aiki tana buɗe a gare shi.’ (1 Kor. 16:8, 9) Wace kofa ce wannan, kuma ta yaya aka buɗe masa ita? Hidimar da Bulus ya ci gaba da yi a Afisa ta kai ga yaɗa wa’azin bishara. Ka yi la’akari da abin da ya faru a Kolosi, Lawudikiya, da Hiyarabolis, birane uku da ke nesa da teku daga Afisa. Bulus bai taɓa zuwa wurin ba, amma sun ji wa’azin bishara. Abafras ya fito ne daga wannan yankin. (Kol. 2:1; 4:12, 13) Abafras ya saurari Bulus sa’ad da yake wa’azi a Afisa ne kuma ya zama Kirista? Littafi Mai Tsarki bai ambata hakan ba. Wataƙila Abafras ya wakilci Bulus wajen yaɗa gaskiya a garinsu. (Kol. 1:7) Ƙila saƙon Kirista ya isa birane kamar Filadalfiya, Sardisu, da Thyatira ne a shekarar da Bulus yake wa’azi a Afisa.

9. (a) Wace sha’awa ce Bulus yake da ita? (b) Menene zai zama jigon shekara ta 2009?

9 Saboda haka, dattawan Afisa suna da dalili mai kyau na amincewa da abin da Bulus ya ce: “Ban maida raina wani abu ba, kamar abin tamani a gareni, bisa ga in cika tafiyata, da hidima kuma wadda na karɓa daga wurin Ubangiji Yesu, in shaida bishara ta alherin Allah ke nan.” Wannan ayar tana ɗauke da jigon shekara ta 2009 mai ban ƙarfafa: “Shaida bishara” sosai. —A. M. 20:24.

Yin Bishara Sosai a Yau

10. Ta yaya muka sani cewa za mu ba da shaida sosai?

10 Umurnin “yi ma jama’a wa’azi, [da] shaida kuma,” ya haɗa da wasu mutane ba manzanni kaɗai ba. Sa’ad da Yesu da aka ta da daga matattu ya yi wa almajirai da suka taru a Galili magana, mai yiwuwa mutane 500, ya ba da wannan umurni: “Ku tafi fa, ku almajirtadda dukan al’ummai, kuna yi musu baftisma zuwa cikin sunan Uba da na Ɗa da na Ruhu Mai-tsarki: kuna koya musu su kiyaye dukan iyakar abin da na umurce ku.” Wannan umurnin ya shafi dukan Kiristoci na gaskiya a yau, kamar yadda kalaman Yesu suka nuna: “Ga shi kuwa ina tare da ku kullayaumi har matuƙar zamani.”—Mat. 28:19, 20.

11. Wane aiki mai muhimmanci ne aka san Shaidun Jehobah da shi?

11 Kiristoci masu ƙwazo sun ci gaba da yin biyayya ga wannan umurnin, suna ƙoƙartawa su “shaida bishara” sosai. Ainihin hanyar yin hakan ita ce abin da Bulus ya ambata wa dattawan Afisa, wato, wa’azi na gida-gida. A cikin wani littafi na shekara ta 2007 game da yin aikin wa’azi na ƙasar waje da kyau, David G. Stewart Ƙarami, ya ce: “Salon da Shaidun Jehobah suke amfani da shi na koya wa mutane su faɗi imaninsu ya fi kyau [da umurni daga kan dakali kawai]. Shaidun Jehobah da yawa suna ɗaukan aikin gaya wa mutane game da imaninsu abin farin ciki.” Menene sakamakon? “A shekara ta 1999, a cikin bincike da na yi a babban birane biyu na Gabashin Turai, mutane kashi biyu zuwa huɗu ne kawai suka ce masu wa’azi ’yan cocin ‘Mormon’ sun taɓa zuwa wajensu. Amma, mutane fiye da kashi saba’in ne suka faɗi cewa Shaidun Jehobah sun yi musu wa’azi sau da yawa.”

12. (a) Me ya sa muke zuwa wajen mutane “sau da yawa” a yankinmu? (b) Za ka iya ba da labarin wani da ya canja halinsa game da saƙonmu?

12 Mutane da yawa a unguwarku su ma sun shaida hakan. Wataƙila kai ma kana wannan aikin. Sa’ad da kake zuwa wajen mutane a hidimarka na gida-gida, ka yi wa’azi ga maza, da mata, da kuma matasa. Wataƙila wasu ba su saurare ka ba duk da cewa ka je wajensu “sau da yawa.” Wasu kuma sun ɗan saurare ka sa’ad da kake tattauna wata aya cikin Littafi Mai Tsarki ko wani jigo na Nassi da su. Ga wasu kuma, ka ba da shaida mai kyau, kuma sun amince da abin da ka faɗa. Dukan waɗannan abubuwa suna iya faruwa sa’ad da muka yi ‘shaidar bishara’ sosai. Wataƙila kamar yadda ka sani, akwai misalai da yawa na mutanen da muka sha zuwa wajen su da suka ƙi saurarawa sosai, amma daga baya suka canja halinsu. Wataƙila wani abu ya faru da su ko wani da suke ƙauna, kuma hakan ya taɓa zuciyarsu kuma suka saurari gaskiya. A yanzu sun zama ’yan’uwanmu. Saboda haka, kada ka yi sanyin gwiwa ko da mutane da yawa ba su saurare ka ba kwanan nan. Ba dukan mutane ba ne za su san gaskiya. Amma abin da Allah yake bukata shi ne mu ci gaba da yin wa’azi da himma.

Sakamakon da Wataƙila ba Mu Sani Ba

13. Ta yaya wa’azi da muke yi zai iya kawo sakamakon da wataƙila ba mu sani ba?

13 Ba waɗanda Bulus ya taimaka musu kai tsaye su zama Kiristoci ba ne ba kawai hidimarsa ta shafa. Mu ma haka. Muna iya ƙoƙarinmu mu ga cewa mun yi wa’azi na gida-gida a kai a kai, kuma mu yi wa mutane da yawa wa’azi. Muna wa’azin bishara ga maƙwabtanmu, abokan aiki, abokan makaranta da danginmu. Mun san dukan sakamakon ne? Ga wasu, za a iya samun sakamako mai kyau nan da nan. A wasu yanayi kuwa, iri na gaskiya ba zai ba da amfani ba nan da nan, amma daga baya sai ya yi jijiya a zuciyar mutumin kuma ya girma. Ko da hakan bai faru ba, mutane da muke yi wa magana suna iya gaya wa wasu abin da muka faɗa, abin da muka gaskata, da yadda muka aikata. Hakika, wataƙila ba da saninsu ba sun taimaki wannan iri ya faɗi a ƙasa mai kyau a wani waje.

14, 15. Menene sakamakon wa’azin da wani ɗan’uwa ya yi?

14 Alal misali, ka yi la’akari da Ryan da matarsa, Mandi, da suke zaune a birnin Florida na Amirka. A wajen aikinsa, Ryan ya yi wa wani abokin aikinsa wa’azi. Wannan mutum mai bin addinin Hindu, yana son yadda Ryan yake yin ado da yadda yake yin magana. Sa’ad da suke tattaunawa, Ryan ya yi magana a kan tashin matattu da yanayin matattu. Wata rana da yamma na wani watan Janairu, mutumin ya tambayi matarsa, Jodi, abin da ta sani game da Shaidun Jehobah. Ita ’yar Katolika ce, kuma ta ce abin da ta sani game da Shaidu shi ne suna “wa’azi na kofa-kofa.” Sai Jodi ta rubuta “Shaidun Jehobah” a na’urar bincike na Intane, wannan ya buɗe mata dandalinmu a cikin Duniyar Gizo www.watchtower.org. Jodi ta karanta littattafai a wannan dandali har kusan wata uku, har da Littafi Mai Tsarki da kuma talifofin da suka ba ta sha’awa.

15 Da shigewar lokaci, Jodi ta sadu da Mandi, da yake su biyun nas ne. Mandi ta yi farin cikin amsa tambayoyin Jodi. Bayan wani lokaci, sun yi abin da Jodi ta kira “tattaunawa daga Adamu zuwa Armageddon.” Jodi ta yarda a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ita. Ba da daɗewa ba ta soma zuwa taro a Majami’ar Mulki. A watan Oktoba, Jodi ta zama mai shela da ba ta yi baftisma ba, kuma ta yi baftisma a watan Fabrairu. Ta rubuta: “Yanzu da na san gaskiya, na sami farin ciki da gamsuwa a rayuwata.”

16. Menene labarin ɗan’uwa da ke birnin Florida ya nuna game da ƙoƙarinmu na ba da shaida sosai?

16 Ryan bai san cewa wa’azin da ya yi wa wani mutum zai sa wani dabam ya shigo cikin gaskiya ba. Amma ya fahimci yadda ƙudurinsa na ba da “shaidar bishara” sosai zai iya shafar wasu. Wataƙila, ka yi wa’azi a gida, a wajen aiki, a makaranta, ko kuma a wurin da ka sami zarafin yin haka, kuma ba da saninka ba hakan ya zama hanyar da wasu suka ji wa’azin bishara. Kamar yadda Bulus bai san dukan abin da wa’azinsa ya cim ma ba a yankin “Asiya,” wataƙila ba za ka san dukan sakamako masu kyau na shaidar da ka yi sosai ba. (Karanta A. M. 23:11; 28:23.) Amma yana da muhimmanci ka ci gaba da yin hakan!

17. Menene ka ƙuduri aniyar yi a shekara ta 2009?

17 A shekara ta 2009, bari mu ɗauki aikinmu na yin wa’azi gida-gida da kuma sauran hanyoyi da muhimmanci. Ta yin hakan, za mu iya furta kalamai irin ta Bulus: “Ban maida raina wani abu ba, kamar abin tamani a gareni, bisa ga in cika tafiyata, da hidima kuma wadda na karɓa daga wurin Ubangiji Yesu, in shaida bishara ta alherin Allah ke nan.”

Yaya Za Ka Amsa?

• Ta yaya manzanni Bitrus da Bulus da kuma wasu a ƙarni na farko suka ba da shaida sosai?

• Me ya sa wa’azinmu zai shafi mutane sosai fiye da yadda muka sani?

• Menene jigon shekara ta 2009, kuma me ya sa kake ganin ya dace?

[Bayanin da ke shafi na 19]

Jigon shekara ta 2009 zai zama: “Shaida bishara” Sosai.—A. M. 20:24.

[Hoto a shafi na 17]

Dattawa na Afisa sun san cewa Bulus ya saba yin wa’azi na gida-gida

[Hoto a shafi na 18]

Ta yaya ne shaidar da ka bayar sosai za ta iya shafan mutane?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba