Ku Ba da Cikakken “Shaida”
1. Wane misali mai kyau ne manzo Bulus ya kafa a yin wa’azi?
1 “Ka cika hidimarka.” (2 Tim. 4:5) Kafin Bulus ya yi wannan gargaɗin ya riga ya yi tafiye-tafiye don aikin wa’azi a wasu ƙasashe sau uku a cikin shekara tara, wato, a tsakanin shekara ta 47 da 56 a zamaninmu. Shi ya sa ya yi wa Timotawus wannan maganar da gaba gaɗi. Littafin Ayyukan Manzanni ya sha ambata cewa Bulus ya ba da cikakken “shaida.” (A. M. 23:11; 28:23) Ta yaya mu ma za mu iya yin hakan a yau?
2. Waɗanne matakai ne za mu ɗauka don mu ba da cikakken shaida sa’ad da muke wa’azi gida gida?
2 Wa’azi Gida Gida: A wasu lokatai magidanta da yawa suna kasancewa a gida a ƙarshen mako ko kuma da yammar kowace rana. Saboda haka, zai dace mu ziyarce mutane a lokatai da ba mu saɓa yin hakan ba domin mu sami damar yin wa’azi ga waɗanda ba su taɓa jin bishara ba. Kuma za mu iya yin hakan sau da yawa har sai mun cim ma burinmu na yin wa’azi a kowane gida. Mene ne za ku yi idan duk ƙoƙarinku na yi wa wani wa’azi ya ci tura? Mai yiwuwa idan kun aika masa wasiƙa ko kuma kun tuntuɓe shi ta waya za ku iya samunsa.
3. Wane dama ne muke da shi na yin wa’azi cikin jama’a ko kuma a duk inda muka sami zarafi?
3 Wa’azi Cikin Jama’a da Kuma a Duk Inda Aka Sami Zarafi: A yau, bayin Jehobah suna koya wa mutanen da suka kasa kunne yadda za su kasance da “hikima.” A wani lokaci, suna hakan ne a kan “tituna” ko kuma a “kasuwoyi.” (Mis. 1:20, 21, Littafi Mai Tsarki) Shin, muna mai da hankali ga mutane don mu yi musu wa’azi sa’ad da muke harkokinmu na yau da kullum? Muna “dukufa kan yin wa’azi” kuwa? (A. M. 18:5, LMT) Idan amsar mu e ce, to hakan ya nuna cewa muna cika aikinmu na ba da cikakken “shaida.”—A. M. 10:42; 17:17; 20:20, 21, 24.
4. Ta yaya addu’a da bimbini za su taimaka mana mu ba da cikakken shaida?
4 A wani lokaci, kunya ko kuma wata kasawa tana iya hana mu ba da shaida. Amma mun tabbata cewa Jehobah ya san yanayinmu. (Zab. 103:14) Duk da haka, idan mun sami kanmu a irin wannan yanayin, zai dace mu yi addu’a Allah ya taimake mu don mu kasance da gaba gaɗin yin wa’azi. (A. M. 4:29, 31) Yayin da muke nazari da kuma bimbini a kan Kalmar Allah, za mu ƙara kasancewa da godiya domin yawan amfanin da ake samu daga bishara. (Filib. 3:8) Hakan zai sa mu yi wa’azi da himma!
5. Ta yaya za mu saka hannu a cikar annabcin Joel?
5 Joel ya annabta cewa kafin babban ranar Jehobah mai ban tsoro ta zo, mutanen Allah za su ci gaba da yin wa’azi kuma ba za a “iya tsai da” su ba. (Joel 2:2, 7-9, LMT) Saboda haka, bari mu yi iya ƙoƙarinmu a yin wannan wa’azin da ba za a sake yi ba!