Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w09 1/1 pp. 9-10
  • Matsayin Maryamu a Nufin Allah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Matsayin Maryamu a Nufin Allah
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “Mai-Samun Alheri,” “Mai-albarka . . . Cikin Mata”
  • Ɗaya Daga Cikin Masu Sarauta
  • An Ba da Albarkatai Masu Girma
  • “Ga ni, Baiwar Ubangiji”
    Ka Yi Koyi Da Bangaskiyarsu
  • “Ga ni, Baiwar Ubangiji”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Abin da Misalin Maryamu Ya Koya Mana
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Mala’ika Jibra’ilu Ya Ziyarci Maryamu
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
w09 1/1 pp. 9-10

Matsayin Maryamu a Nufin Allah

ALOKACIN hidimar Yesu, wata mata ta yi magana da babbar murya a cikin jama’a ta ce: “Cikin da ya haife ka mai-albarka ne, da kuma māman da ka sha.” Idan da Yesu yana sun a bauta wa mahaifiyarsa, a wannan lokaci ya sami zarafin da zai ce a bauta mata. Maimakon haka, ya ce: “Gwamma dai waɗannan da suna jin maganar Allah, suna kiyaye ta kuma.”—Luka 11:27, 28.

Yesu bai ba mahaifiyarsa wani girma na musamman ba; kuma bai ce mabiyansa su yi hakan ba. Ta yaya wannan ya jitu da bauta da yawancin sahihan masu bi suke yi wa Maryamu? Bari mu tattauna abin Littafi Mai Tsarki ya ce game da wasu koyarwa da suka zama gama gari game da uwar.

“Mai-Samun Alheri,” “Mai-albarka . . . Cikin Mata”

Mala’ika Jibrailu ya sanar wa Maryamu abin da matsayinta a nufin Allah zai zama. A wannan lokaci, ya gaishe ta, yana cewa: “A gaishe ki, ke da ki ke mai-samun alheri, Ubangiji yana tare da ke.” (Luka 1:28) Wani fassarar ya ce “Salama alaikun, ya ke zaɓaɓɓiya, Ubangiji yana tare da ke!” Bayan haka, Elizabeth ta gaida Maryamu da waɗannan kalaman: “Mai-albarka ki ke cikin mata, abin haihuwa na cikinki kuma mai-albarka ne.” (Luka 1:42) Waɗannan kalaman sun nuna cewa ya kamata a bauta wa Maryamu ne?

A’a. Ko da yake an haɗa waɗannan kalaman a cikin addu’a da Katolika suke yi wa Maryamu, Littafi Mai Tsarki bai ce a riƙa yin addu’a gare ta ba. Jibra’lu da Elizabeth sun daraja gata na musamman da aka ba Maryamu, wato, a matsayin wadda za ta haifi Almasihu, amma yin addu’a gare ta ba ya cikin Nassosi. Akasin haka, sa’ad da almajiran Yesu suka tambaye shi ya koya musu yadda za su yi addu’a, ya ce su riƙa yin addu’a ga Ubansu. Hakika, sanannen addu’ar Yesu ta soma da waɗannan kalaman: “Ubanmu wanda ke cikin sama”—Matta 6:9.

Ɗaya Daga Cikin Masu Sarauta

Wani koyarwa game da Maryamu shi ne yanzu ita ce “Sarauniyar Sama.” Littafi Mai Tsarki bai taɓa ba ta irin wannan laƙabi ba. Hakan ya nuna cewa tana da wuri na musamman a tsarin Allah a samaniya. Wane wuri ne wannan?

Wasu daga cikin amintattun almajiran Yesu za su yi sarauta tare da shi a Mulkinsa. (Luka 22:28-30) Yesu zai ba waɗanda aka zaɓa iko su zama “priests ga Allahnmu; suna kuwa mulki bisa duniya.” (Ru’ya ta Yohanna 5:10) Littafi Mai Tsarki ya nuna mana cewa Maryamu tana ɗaya daga cikin waɗanda aka ba wannan gata mai girma. Yaya muka san haka?

Za ka tuna cewa bayan da Yesu ya mutu, Maryamu ta “lizima cikin addu’a” tare da almajiran Yesu da ’yan’uwansa. Wasu mutane 120 sun haɗu har da “waɗansu mata.” (Ayukan Manzanni 1:12-15) Sa’ad da “ranar Fentekos ta yi” in ji Littafi Mai Tsarki ya ce, “dukansu suna tare wuri ɗaya” sa’ad da ruhu mai tsarki na Allah ya zauna bisa kowannen su, ya ba su gatar yin magana a harshen da ba na su ba.—Ayukan Manzanni 2:1-4.

Da yake Maryamu tana cikin waɗanda aka albarkace su ta wannan hanya ya nuna cewa an zaɓe ta da sauran matan da suka karɓi ruhu mai tsarki su kasance a cikin Mulkin Yesu na Samaniya. Wannan tabbacin ya nuna cewa yanzu Maryamu tana zaune da Yesu a samaniya. (Romawa 8:14-17) Yi la’akari da wasu gata da ita da abokan sarauta na Yesu za su samu a wajen cika nufin Allah.

An Ba da Albarkatai Masu Girma

Littafin Ru’ya ta Yohanna ya ce za a tada mutane 144,000 daga matattu zuwa sama su yi sarauta tare da Yesu a matsayin firistoci, alkalai, da kuma sarakuna. (Ru’ya ta Yohanna 14:1, 4; 20:4, 6) A matsayinsu na firistoci, za su kasance a yin amfani da hadayar Yesu ga dukan ’yan adam da suka yi biyayya, za su sa su kamilta a ruhaniya, ɗabi’a, da kuma zahiri. (Ru’ya ta Yohanna 21:1-4) Gata ne dukan masu bauta wa Jehobah su ga wannan lokaci!a

Har yanzu Maryamu tana da aiki a cikawar nufin Jehobah. Don tawali’unta, bangaskiya, biyayya, da kuma ruhaniyarta a matsayin mama, ban da ma jimrewarta, ta cancanci a yi koyi da ita. Ana darajata sosai saboda ita ce ta haifi Almasihu da kuma yadda ta kasance a cikin waɗanda za su ba da albarka fansar Yesu ga ’yan adam.

Amma, wani darassi mai muhimmanci da muka koya daga Maryamu shi ne ita da sauran amintattun bayin Allah sun bauta wa Jehobah ne kawai ba wani allah ba. Tare da abokan sarautar Yesu da ke sama, Maryamu ta tayar da muryarta ta ce: “Ga wanda ya ke zaune bisa kursiyin, ga Ɗan rago kuma, albarka, da daraja, da ɗaukaka, da mulki, har zuwa zamanun zamanai.”—Ru’ya ta Yohanna 5:13; 19:10.

[Hasiya]

a Don ƙarin bayani game da waɗannan albarkatai, ka duba babi na 8 a littafin nan Menene Ainihin Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Shaidun Jehobah ne suka wallafa.

[Bayanin da ke shafi na 10]

Saboda tawali’un Maryamu, bangaskiyarta, da kuma biyayyarta ta cancanta a yi koyi da ita

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba