Maya Haihuwa—Yaya Muhimmancinsa?
A DUKAN tattaunawarsa da Nikodimu, Yesu ya nanata cewa maya haihuwa, ko kuma sake haihuwa yana da muhimmanci sosai. Ta yaya ya fito da wannan dalla-dalla?
Ka lura yadda Yesu a tattaunawarsa da Nikodimu ya nanata muhimmancin sake haihuwar. Ya ce: “In ba a sāke haifar mutum ba, ba zai iya ganin Mulkin Allah ba.” (Yohanna 3:3) Kalmomin nan “in ba” da kuma “ba zai” sun nanata wajibin sake haihuwar. Alal misali: Idan mutum ya ce, “in ba rana, gari ba zai yi haske ba,” yana nufin cewa hasken gari ya dangana ga rana. Hakazalika, Yesu ya nuna cewa sake haifar mutum tilas ce in za a ga Mulkin Allah.
A ƙarshe, don ya kawar da shakka game da batun, Yesu ya ce: “Dole a sāke haifarku.” (Yohanna 3:7) A bayyane yake, in ji Yesu, sake haifar mutum wajibi ne, tilas ne, domin mutum ya “shiga Mulkin Allah.”—Yohanna 3:5.
Tun da Yesu ya ɗauki wannan sabuwar haihuwa da muhimmanci, ya kamata Kiristoci su tabbata cewa sun fahimci wannan batun da kyau. Alal misali, kana tsammanin Kirista zai iya zaɓa a sake haifarsa ne?
[Bayanin da ke shafi na 5]
“In ba rana, gari ba zai yi haske ba”