Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w09 4/1 pp. 3-4
  • Sake Haifar Mutum—Hanya Ce Ta Samun Ceto?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Sake Haifar Mutum—Hanya Ce Ta Samun Ceto?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Menene Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Mene ne Sake Haifan Mutum Yake Nufi?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Maya Haihuwa—Yaya Muhimmancinsa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Maya Haihuwa—Shawara Ce da Mutum Zai Yanke da Kansa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Maya Haihuwa—Menene Manufarta?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
w09 4/1 pp. 3-4

Sake Haifar Mutum—Hanya Ce Ta Samun Ceto?

YAYA za ka amsa tambayar nan, “An sake haifarka kuwa?” Miliyoyin mutane masu bi a dukan duniya za su amsa wannan tambayar da babbar murya, “E!” Sun yi imani cewa sake haifar mutum ita ce alamar Kiristoci na gaskiya kuma itace kawai hanyar samun ceto. Sun amince da abin da shugabannin addinai irinsu ɗan tauhidi Robert C. Sproul, ya ce: “Idan ba a sake haifar mutum ba, . . . to shi ba Kirista ba ne.”

Kana ɗaya daga cikin waɗanda suka gaskata cewa sake haifar mutum zai kai ka ga ceto? Idan haka ne, babu shakka za ka so ka taimaki danginka da kuma abokananka su bi hanyar ceto. Amma domin su yi haka, hakika, suna bukatar su fahimci bambancin da ke tsakanin mutumin da aka sake haifa da wanda ba a sake haifarsa ba. Saboda haka, ta yaya za ka yi musu bayani game da abin da ake nufi a sake haifar mutum?

Mutane da yawa suna gaskata cewa furcin nan “sake haifar mutum” yana nufin mutumin da ya yi alkawari zai bauta wa Allah da kuma Kristi, saboda haka, yanayinsa ya canja daga wanda yake matacce a ruhaniya zuwa wanda ya sami rai a ruhaniya. Hakika, wata sabuwar ma’anar wannan furci a ƙamus ita ce ‘Kirista wanda ya sabonta naciyarsa ga addini bayan ya fuskanci wani abu.”—Merriam-Webster’s Collegiate Dictionary—Eleventh Edition.

Zai ba ka mamaki ne idan ka fahimci cewa Littafi Mai Tsarki bai amince da wannan ma’anar ba? Za ka so ka san abin da ainihi Kalmar Allah ta koyar game da sake haifar mutum? Hakika za ka amfana daga bincika wannan batu da kyau. Me ya sa? Domin cikakkiyar fahimtar abin da sake haifar mutum take nufi zai shafi rayuwarka da kuma abin da zai faru a rayuwarka a nan gaba.

Menene Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

A cikin dukan littafi Mai Tsarki wannan furci “sake haifar mutum” ya bayyana a Yohanna 3:1-12; LMT, wanda ya bayyana wani hira mai ban sha’awa tsakanin Yesu da wani shugaban addini na Urushalima. Za ka ga inda aka yi ƙaulin wannan labari na Littafi Mai Tsarki a akwatin da yake tare da wannan talifin. Muna gayyatarka ka yi karatun a nitse.

A wannan labarin, Yesu ya nanata ɓangarori dabam dabam na wannan “sabuwar haihuwa.”a Hakika, bayanin Yesu ya taimake mu mu amsa tambayoyi guda biyar masu muhimmanci:

◼ Yaya muhimmancin maya haihuwar?

◼ Ya dangana ne a gare mu mu zaɓi samun maya haihuwa?

◼ Menene manufarta?

◼ Kuma ta yaya take faruwa?

◼ Wane canji ne na dangantaka take kawowa?

Bari mu amsa waɗannan tambayoyi da ɗai-ɗai.

[Hasiya]

a An sami wannan furci “maya haihuwa” a 1 Bitrus 1:3, 23. Wani furci ne na Littafi Mai Tsarki da yake kwatanta “sake haihuwa.” An samo waɗannan furci biyu ne daga fi’ili ta Hellenanci, gen·naʹo.

[Akwati/Hotunan da ke shafi na 4]

“Dole aSāke Haifarku”

“To, akwai wani Bafarisiye, wai shi Nikodimu, wani shugaban Yahudawa. Wannan mutum ya zo wurin Yesu da daddare, ya ce masa, ‘Ya Shugaba, mun sani kai malami ne da ka zo daga wurin Allah, domin ba mai iya yin waɗannan mu’ujizan da kake yi, sai ko Allah na tare da shi.’ Yesu ya amsa masa ya ce, ‘Lalle hakika, ina gaya maka, in ba a sāke haifar mutum ba, ba zai iya ganin Mulkin Allah ba.’ Nikodimu ya ce masa, ‘Ƙaƙa za a haifi mutum bayan ya tsufa? Wato ya iya komawa cikin uwa tasa ta sāke haifo shi?’ Yesu ya amsa masa ya ce, ‘Lalle hakika, ina gaya maka, in ba an haifi mutum ta ruwa da ta Ruhu ba, ba zai iya shiga Mulkin Allah ba. Abin da mutum ya haifa mutum ne, abin kuma da Ruhu ya haifa ruhu ne. Kada ka yi mamaki domin na ce maka, ‘Dole a sāke haifarku.’ Iska na busawa inda ta ga dama. Kakan ji motsinta, amma ba ka san inda ta fito ba, da inda za ta. Haka fa yake ga duk wanda Ruhu ya haifa.’ Sai Nikodimu ya amsa masa ya ce, ‘Ƙaƙa wannan zai yiwu?’ Yesu ya amsa masa ya ce, ‘Ashe, kai ma da kake malamin Isra’ila, ba ka fahimci waɗannan al’amura ba? Lalle hakika, ina gaya maka, abin da muka sani shi muke faɗa, muna kuma shaidar da abin da muka gani, amma kun ƙi yarda da shaidarmu. In na yi muku zancen al’amuran duniya ba ku gaskata ba, yaya za ku gaskata in na yi muku zancen al’amuran sama?’”—Yohanna 3:1-12; LMT.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba