Magidanta, Ku Yi Koyi Da Ƙaunar Kristi!
A DARENSA na ƙarshe a duniya, Yesu ya gaya wa manzanninsa masu aminci: “Sabuwar doka ni ke ba ku, ku yi ƙaunar juna; kamar yadda ni na ƙaunace ku, ku ma ku yi ƙaunar juna. Bisa ga wannan mutane duka za su fahimta ku ne almajiraina, idan kuna da ƙauna ga junanku.” (Yoh. 13:34, 35) Hakika, Kiristoci na gaskiya suna bukatar su ƙaunaci juna.
Da yake magana kai tsaye ga magidanta mabiyan Kristi, manzo Bulus ya rubuta: “Ku mazaje, ku ƙaunaci matanku, kamar yadda Kristi kuma ya ƙaunaci ikilisiya, ya bada kansa dominta.” (Afis. 5:25) Ta yaya mai gida Kirista zai yi amfani da wannan umurni na Nassi a aurensa, musamman idan matarsa mai bauta wa Jehobah ce da ta keɓe kanta?
Kristi Yana Ƙaunar Ikilisiyar
Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ya kamata mazaje kuma su yi ƙaunar matayensu kamar jikunansu. Wanda ya ke ƙaunar matatasa kansa ya ke ƙauna: gama babu mutum wanda ya taɓa ƙin jiki nasa; amma ya kan ciyarda shi ya kan kiyaye shi, kamar yadda Kristi kuma ya kan yi da ikilisiya.” (Afis. 5:28, 29) Yesu ya ƙaunaci almajiransa kuma suna da tamani a gare shi. Yana kuma tattalinsu. Ko da yake su ajizai ne, ya bi da su a hankali kuma ya kyautata musu. Da yake yana son ya “miƙo ma kansa ikilisiya, ikilisiya mai-daraja,” yana mai da hankali a kan halaye masu kyau na almajiransa.—Afis. 5:27.
Kamar yadda Kristi yake ƙaunar ikilisiya, dole ne miji ya ƙaunaci matarsa ta kalmominsa da kuma ayyukansa. Matar da mijinta ke nuna mata ƙauna a kullum tana ji ana daraja ta kuma tana farin ciki. A wata sassa, matar da take da dukan abubuwan biyan bukatar rayuwa a gida amma mijinta ya yi watsi da ita ba za ta yi farin ciki ba.
Ta yaya maigida zai nuna cewa yana ƙaunar matarsa? A fili, yana gabatar da ita ga mutane cikin daraja kuma yana yabonta don yadda take taimakonsa. Idan matarsa ta taimaka wajen cim ma wani abu mai muhimmanci a iyalin, ba ya jinkirin sa mutane su san hakan. Sa’ad da suke su kaɗai, ta fahimci cewa yana ƙaunarta. Riƙe hannu, yin murmushi, runguma da kuma yabo kamar dai abubuwa ne marar muhimmanci sosai, amma abu ne da mace za ta daɗe tana tunawa.
“Ba Wani Abin Kunya ba Ne ShiCe da Su ‘Yan’Uwa’”
Yesu Kristi bai ji “kunya . . . shi ce da [mabiyansa shafaffu] ’yan’uwa” ba. (Ibran. 2:11, 12, 17) Idan kai miji ne Kirista, ka tuna cewa matarka ma ’yar’uwar ka ce Kirista. Keɓe kanta da ta yi ga Jehobah ya fi wa’adin da ta ɗauka na aure muhimmanci, ko da ta yi baftisma ne kafin ka aure ta ko kuma bayan kun yi aure. Sa’ad da yake kiran matarka ta yi kalami, ɗan’uwan da yake gudanar da nazari a ikilisiya yana kiranta “’Yar’uwa”. ’Yar’uwarka ce, ba kawai a Majami’ar Mulki ba amma har da gida. Yana da muhimmanci ka bi da ita a hankali kuma ka nuna mata halin kirki a gida kamar yadda za ka yi a Majami’ar Mulki.
Idan kana da ƙarin hakki na hidima a ikilisiya, a wasu lokatai zai yi maka wuya ka daidaita ayyukan ikilisiya da hakkokinka na iyali. Haɗin kai tsakanin dattawa da bayi masu hidima da kuma koyar da wasu su ɗauki wasu hakkoki na ikilisiya zai ba ka ƙarin lokacin mai da hankali ga ’yar’uwar da ta fi bukatarka, wato, matarka. Ka tuna cewa ’yan’uwa maza da yawa za su iya yin ayyukan ikilisiya da aka ba ka, amma kai kaɗai ne ɗan’uwan da ya auri matarka.
Ƙari ga haka, kai ne shugaban matarka. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kan kowane namiji Kristi ne; kan mace kuma namiji ne; kan Kristi kuma Allah ne.” (1 Kor. 11:3) Yaya ya kamata ka nuna wannan shugabancin? Za ka yi hakan ne cikin ƙauna, ba ta wurin kaulin ayar da aka ambata a baya ba a kullum da kuma son a yi maka ladabi. Abin da zai taimake ka ka nuna shugabanci mai kyau shi ne yin koyi da Yesu Kristi a yadda kake bi da matarka.—1 Bit. 2:21.
“Ku Ne Abokaina”
Yesu ya kira almajiransa abokansa. Ya gaya musu: “Ba ni ƙara ce da ku bayi ba; gama bawa ba ya san abin da ubangijinsa ke yi ba: amma na ce da ku abokai; gama dukan abin da na ji daga wurin Ubana, na sanar muku da su.” (Yoh. 15:14, 15) Yesu da almajiransa suna tattaunawa sosai. Kuma suna yin abubuwa tare. An gayyaci ‘Yesu da almajiransa’ bikin aure a Kana. (Yoh. 2:2) Suna da wurare masu kyau da suke son zuwa, kamar lambun Jathsaimani. Littafi Mai Tsarki ya ce “Yesu kullum ya kan tafi can tare da almajiransa.”—Yoh. 18:2.
Mata tana bukatar ta ji cewa ita ce abokiya mafi kusa na mijinta. Yana da muhimmanci mata da miji su more rayuwa tare! Ku bauta wa Allah tare. Ku ji daɗin yin nazarin Littafi Mai Tsarki tare. Ku riƙa tafiya, magana, da cin abinci tare. Ku zama aminai ba ma’aurata kawai ba.
“Ya Ƙaunace Su Har Matuƙa”
Yesu ya ‘ƙaunaci almajiransa har matuƙa.’ (Yoh. 13:1) Wasu magidanta ba sa yin koyi da Kristi a wannan batun. Suna iya ma barin ‘matarsu ta ƙuruciya,’ wataƙila don su auri matashiya.—Mal. 2:14, 15.
Wasu, kamar Willi, sun yi koyi da Kristi. Domin rashin lafiya, matar Willi tana bukatar a kula da ita koyaushe har shekaru da yawa. Yaya Willi ya ji game da wannan? Ya ce: “Ina ɗaukan matata a matsayin kyauta daga Allah kuma hakan na ɗauke ta. Ban da haka, shekara sattin da ta shige na ɗauki alkawari cewa zan kula da ita a lokatai masu daɗi da marar daɗi. Ban zan taɓa manta wannan alkawarin ba.”
Magidanta Kiristoci, ku yi koyi da ƙaunar Kristi. Ku daraja matarku mai jin tsoron Allah don ita ’yar’uwarka ce kuma abokiyarka.
[Hotunan da ke shafi na 20]
Matarka ce aminiyarka?
[Hotunan da ke shafi na 20]
‘Ka Ci Gaba da ƙaunar Matarka’