Mutumin da Yake da Imani da Alkawuran Allah
Umurni: Ka yi wannan aikin a inda za ka mai da hankalinka wuri ɗaya. Sa’ad da kake karanta Nassosi ka sa kanka cikin yanayin. Ka yi tunanin yanayin a zuciyarka. Ka ji muryoyin mutanen. Ka ji yadda ainihin mutanen da ke ciki suke ji.
KA YI TUNANI A KAN YANAYIN NAN.—KARANTA FARAWA 12:1-4; 18:1-15; 21:1-5; 22:15-18.
Ka bayyana yadda Ibrahim ya ji sa’ad da Allah ya yi masa alkawari cewa zai zama kakan “zuriya” da zai albarkaci dukan duniya.
․․․․․
A ganin ka, menene kamannin baƙi ukun da aka kwatanta a Farawa 18:2?
․․․․․
Yaya kake ganin ayyukan da aka kwatanta a Farawa 18:6-8? (Ka tuna cewa Ibrahim ya kusa shekaru 100 a lokacin.)
․․․․․
KA BINCIKE SOSAI.
Shekaru nawa ne ke tsakanin lokacin da Jehobah ya yi wa Ibrahim alkawarin ɗa da kuma lokacin da aka haifi Ishaku? (Sake karanta Farawa 12:4 da 21:5.)
․․․․․
Waɗanne tabbaci ne Jehobah ya ba Ibrahim a lokacin da yake jiran cikar alkawarin? (Karanta Farawa 12:7; 13:14-17; 15:1-5, 12-21; 17:1, 2, 7, 8, 15, 16.)
․․․․․
Menene Jehobah ya yi sa’ad da Ibrahim bai tabbata ba sosai game da samun ɗa? (Sake karanta Farawa 15:3-5, 12-21.)
․․․․․
Ta yaya Jehobah ya ba da bayani game da ‘zuriyar’ da sannu-sannu?
․․․․․
KA YI AMFANI DA ABIN DA KA KOYA. KA RUBUTA ABIN DA KA KOYA GAME DA . . .
Amfanin ba da gaskiya ga alkawuran Allah.
․․․․․
Yadda Jehobah ya bayyana nufinsa da sannu-sannu.
․․․․․
WANE ƁANGAREN WANNAN LABARI NE YA FI MA’ANA A GARE KA, KUMA ME YA SA?
․․․․․