Masu Karatu Sun Yi Tambaya
Me Ya Sa Shaidun Jehobah Ba Sa Yin Amfani Da Siffofi A Bautarsu?
A dukan duniya, ’yan Hindu, Buddhism, Katolika da ’yan cocin Orthodox sun ɗauki yin amfani da gumaka, siffofi ko kuma siffofin mutane a matsayin sashe mai muhimmanci na bautarsu. A wasu ɓangarorin ƙasar Afirka, mutane sukan bauta wa itace ko kuma dutse da suka gaskata cewa alla ko kuma ruhun alla yana zaune a cikinta.
Akasin haka, Shaidun Jehobah ba sa amfani da gunki ko sifa a bautarsu. Idan ka halarci wurin da suke yin taro, wato, Majami’un Mulki, ba za ka ga siffofin “waliyai” ko kuma sifar Yesu ko ta Maryamu ba.a Me ya sa? Ka lura da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da wannan batun.
Menene Allah Yake Bukata Daga Isra’ilawa?
Bayan ya ’yantar da Isra’ilawa daga ƙasar Masar, Jehobah Allah ya ba su umurni dalla-dalla game da yadda yake son su bauta masa. Na biyu cikin Dokoki Goma ya ce: “Ba za ka misalta wata ƙira, ko surar abin da ke cikin sama daga bisa, ko abin da ke cikin duniya daga ƙasa, ko kuwa abin da ke cikin ruwa daga ƙarƙashin ƙasa: ba za ka yi sujada garesu ba, ba kuwa za ka bauta musu ba: gama ni Ubangiji Allahnka Allah mai-kishi ne.”—Fitowa 20:4, 5.
A lokacin da Allah yake ba Musa waɗannan dokokin, Isra’ilawa suna cikin yin maraƙi na zinariya, wataƙila ta wajen yin koyi da bautar dabobbi da ’yan Masar suke yi. Basu ƙira gunkin da sunan allolin ’yan Masar ba. Maimakon haka, sun haɗa ta da bautar Jehobah. (Fitowa 32:5, 6) Menene Allah ya yi? Ya yi fushi sosai da waɗanda suka bauta wa gunkin, kuma Musa ya halaka ta.—Fitowa 32:9, 10, 19, 20.
Daga baya, Jehobah Allah ya yi ƙarin bayani game da wannan doka ta biyu. Ta hanyar Musa, ya tuna wa Isra’ilawa cewa kada su yi wa kansu “ƙerarren gumki da kamanin kowace irin halitta ko na namiji ko na tamata, abin da za ya yi kama da kowane dabba da ke a duniya, abin da za ya yi kama da kowane tsuntsu mai-fukafukai da ke tashi a sararin sama, abin da za ya yi kama da kowane mai-rarrafe a ƙasa, abin da za ya yi kama da kowane kifin da ke cikin ruwa ƙalkashin duniya.” (Kubawar Shari’a 4:15-18) Babu shakka, bai kamata Isra’ilawa su yi amfani da kowace irin gumaka a bautarsu ga Allah ba.
Duk da haka, daga baya Isra’ilawa suka soma bauta wa gumaka. Don ya daidaita su, Jehobah ya aika annabawa da suka gargaɗe su a kan hukuncin da ke tafe domin bauta wa gumaka da suke yi. (Irmiya 19:3-5; Amos 2:8) A matsayinta na al’umma, Isra’ila ta yi watsi da gargaɗin Allah. Saboda haka, a shekara ta 607 K.Z., Jehobah ya ƙyale Babiloniyawa su halaka Urushalima kuma suka kai al’ummar zaman bauta.—2 Labarbaru 36:20, 21; Irmiya 25:11, 12.
Menene Kiristoci na Ƙarni ta Farko Suka Gaskata?
Sa’ad da waɗanda ba Yahudawa ba suka zama Kiristoci a ƙarni na farko, ba su ci gaba da yin amfani da gumaka a bautarsu ga Allah ba. Ka lura da abin da Dimitriyus, maƙerin gumaka ta zinariya a Afisa ya ce game da wa’azin manzo Bulus: “Ku mutane, kun sani ta wurin wannan sana’a mu ke samun wadatarmu. Kuna gani, kuma kuna ji, ba cikin Afisus kaɗai ba, amma kaɗan ya rage a cikin Asiya duka, wannan Bulus ya rinjayi mutane dayawa ya juyadda su, yana cewa, waɗannan da hannuwa ke yi ba allohi ba ne.”—Ayyukan Manzanni 19:25, 26.
Kalaman Bulus sun ƙara tabbatar da wannan zargi na Dimitriyus. Sa’ad da yake yin magana ga Helenawa a ƙasar Atina, Bulus ya ce: “Ba ya kamata mu zaci Allantaka tana kama da zinariya, ko azurfa, ko dutse, abin da a kan sassaƙa ta wurin sana’ar mutum da dabarassa. Kwanakin jahilci fa Allah ya yi birin da su; amma yanzu yana umurtan mutane dukansu cikin kowane wuri su tuba.” (Ayyukan Manzanni 17:29, 30) Game da wannan batu, Bulus ya rubuta wa waɗanda suke Tassalunika kuma ya ƙarfafa su da waɗannan kalaman: ‘[Ku] juyo zuwa ga Allah ku bar gumaka.’—1 Tasalunikawa 1:9.
Ba Bulus kaɗai ba ne ya gargaɗi Kiristoci game da yin amfani da gumaka a bautarsu ba, manzo Yohanna ma ya yi hakan. A ƙarshen ƙarni na farko, da gaba gaɗi Yohanna ya gaya musu cewa: “Ku tsare kanku daga gumaka.”—1 Yohanna 5:21.
Shaidun Jehobah suna yin biyayya ga gargaɗin da Allah ya ba da na kada su yi amfani da kowace irin gumaka sa’ad da suke bauta masa. Sun gaskata da kalmar Jehobah Allah sa’ad da ya ce: “Ni ne Ubangiji; wannan ne sunana: ba ni kuwa bada ɗaukakata ga wani, yabona kuma ga sifofi sassaƙaƙu.”—Ishaya 42:8.
[Hasiya]
a Wasu Majami’un Mulki suna ɗauke da zanen mutane na Littafi Mai Tsarki. Amma dai, waɗannan hotunan ado ne kawai ba don bauta ba. Shaidun Jehobah ba sa yin addu’a ga waɗannan hotunan, ko kuma su bauta musu.
[Bayanin da ke shafi na 27]
“Ni ne Ubangiji; wannan ne sunana: ba ni kuwa bada ɗaukakata ga wani, yabona kuma ga sifofi sassaƙaƙu.” —Ishaya 42:8