Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w09 10/1 p. 16
  • Jehobah Yana Ɗaukan Tawali’u da Tamani

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Jehobah Yana Ɗaukan Tawali’u da Tamani
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Makamantan Littattafai
  • Musa—Mutumi Ne Mai Ƙauna
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Ku Zama Masu Tawali’u Don Ku Faranta Ran Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
  • Taƙaici Daga Littafin Ƙidaya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Alƙalin da ke Manne wa Abin da ya Dace
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
w09 10/1 p. 16

Ka Kusaci Allah

Jehobah Yana Ɗaukan Tawali’u da Tamani

Littafin Lissafi 12:1-15

GIRMAN KAI, kishi, dogon buri. Irin waɗannan halayen sun zama ruwan dare a tsakanin mutanen da suke son su yi nasara a wannan duniyar. Amma irin waɗannan halayen suna jawo mu kusa da Allah kuwa? Akasin hakan, Jehobah yana ɗaukan masu bauta masa cikin tawali’u da tamani. Hakan ya yi daidai da labarin da ke Littafin Lissafi sura 12. Abin ya faru ne a jejin Sinai, bayan an ceci Isra’ilawa daga ƙasar Masar.

Yayyen Musa, Maryamu da Haruna, ‘suka soma yin zargin’ ƙaninsu. (Aya ta 1) Maimakon su yi wa Musa magana, sai suka soma yin gunaguni game da shi, wataƙila suna yaɗa gunagunin a cikin zangon. Wataƙila Maryamu wadda aka fara yin ƙaulinta ce ta ja-goranci wannan gunagunin. Gunaguninsu na farko shi ne cewa Musa ya auri Bakushiya. Shin Maryamu tana kishi ne don wataƙila za a fi sanin wannan matar da ba Ba’isra’ila ba ce fiye da ita?

Dalilan yin gunaguninsu ya wuce hakan. Maryamu da Haruna sun ci gaba da cewa: “Ubangiji ya yi magana da Musa kaɗai ne? ba ya yi magana kuma da mu ba?” (Aya ta 2) Shin sun yi wannan gunagunin ne don su samu ƙarin iko ko kuwa a san su sosai?

A cikin labarin, Musa bai amsa wannan gunagunin ba da kansa. Amma, ya haƙura ne da zage-zagen. Haƙurinsa ya tabbatar da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce wato shi “mai-tawali’u ne ƙwarai” fiye da kowane mutum a duniya.a (Aya ta 3) Musa ba ya bukatan ya kāre kansa. Jehobah yana sauraro kuma ya kāre Musa.

Jehobah ya ɗauki gunagunin a matsayin shi suke yi ma wa. Balle ma, shi ne ya naɗa Musa. Sa’ad da yake yi wa masu yin gunagunin faɗa, Allah ya tuna masu cewa yana da dangataka na musamman da Musa: ‘Ina yin magana da shi baki da baki.’ Sai Jehobah ya tambayi Maryamu da Haruna: “Don mi fa ba ku ji tsoro ku yi zargin . . . Musa ba?” (Aya ta 8) Ta wajen yin zargin Musa, sun yi laifin yin zargin Allah. Domin wannan rashin kunya mai tsanani, za su fuskanci fushin Allah.

Maryamu, wadda ita ce ta ta da batun, ta kamu da ciwon kuturta. Nan da nan Haruna ya gaya wa Musa ya yi roƙo a madadinta. Ka yi tunani, samun lafiyar Maryamu yana hannun wanda ta yi wa laifi! Musa ya aikata yadda aka roƙe shi cikin tawali’u. Magana na farko da Musa ya yi a wannan zancen shi ne cewa, Jehobah ya yafe wa ’yar’uwansa. An warkar da Maryamu, amma ta ci gaba da shan kunyar zama a bayan gari har kwanaki bakwai.

Wannan labarin ya ba mu ƙarin haske game da irin halayen da Jehobah yake darajawa da kuma waɗanda ya ƙi jini. Idan muna son mu kusaci Allah, wajibi ne mu watsar da girman kai, kishi, da dogon buri da muke da su. Masu tawali’u ne Jehobah yake ƙauna. Ya yi alkawari: “Masu-tawali’u za su gāji ƙasan; Za su faranta zuciyarsu kuma cikin yalwar salama.”—Zabura 37:11; Yaƙub 4:6.

[Hasiya]

a Tawali’u hali ne mai ƙarfi da ke sa mutum ya jimre wa rashin adalci ba tare da ramuwa ba.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba