An Sake Gano Begen Rai Na Har Abada A Duniya
“Ya Daniyel, ka kulle zantattukan, . . . har kwanakin ƙarshe; mutane da yawa za su kai da kawo a guje, ilimi kuma za ya ƙaru.”—DAN. 12:4.
1, 2. Waɗanne tambayoyi ne za a tattauna a wannan talifin?
MILIYOYIN mutane a yau sun fahimci ainihin tushen Nassi na begen yin rayuwa a cikin aljanna a duniya har abada. (R. Yoh. 7:9, 17) A farkon tarihin ’yan adam, Allah ya bayyana cewa ya halicci ’yan adam su yi rayuwa ba na ’yan shekaru ba kuma su mutu, amma su rayu har abada.—Far. 1:26-28.
2 Mutanen Isra’ila suna da begen cewa ’yan adam za su sake zama kamiltattu kamar yadda Adamu yake a dā. Nassosin Kirista na Helenanci sun bayyana yadda Allah zai sa ya yiwu ’yan adam su samu rai na har abada a cikin Aljanna a duniya. To, me ya sa ake bukatan a sake gano begen ’yan adam? Yaya aka bayyana begen ga miliyoyin mutane?
An Ɓoye Bege
3. Me ya sa ba abin mamaki ba ne ba cewa an ɓoye begen rai na har abada a duniya?
3 Yesu ya annabta cewa annabawan ƙarya za su ɓata koyarwarsa kuma za a yaudari yawancin mutane. (Mat. 24:11) Manzo Bitrus ya gargaɗi Kiristoci: “Masu-ƙaryan malanta za su kasance kuma a cikinku.” (2 Bit. 2:1) Manzo Bulus ya ce “kwanaki za su zo inda [mutane] ba za su daure da koyarwa mai-lafiya ba; amma bisa ga ƙaiƙayin kunnuwa za su tattara wa kansu masu-koyarwa bisa ga sha’awoyinsu.” (2 Tim. 4:3, 4) Shaiɗan yana sa hannu wajen yaudarar mutane kuma ya yi amfani da Kiristoci ’yan ridda don ya ɓoye gaskiya mai daɗaɗa zuciya game da nufin Allah ga ’yan adam da kuma duniya.—Karanta 2 Korintiyawa 4:3, 4.
4. Wane bege ne ga ’yan adam shugabannin addinai ’yan ridda suka ƙi amincewa da shi?
4 Nassosi ya bayyana cewa Mulkin Allah gwamnati ce a sama da za ta farfashe kuma ta kawo ƙarshen dukan mulkoki na ’yan adam. (Dan. 2:44) A lokacin sarautar Kristi na shekara dubu, za a kulle Shaiɗan a cikin rami marar matuƙa, za a ta da matattu, kuma za a mai da ’yan adam zuwa kamiltattu a duniya. (R. Yoh. 20:1-3, 6, 12; 21:1-4) Amma, shugabannin addinai ’yan ridda na Kiristendam sun yi na’am da wasu ra’ayoyi dabam kuma sun soma koyar da su. Alal misali, Shugaban Cocin Origen na Iskandiriya na ƙarni na uku ya la’anci waɗanda suka yi imani cewa sarauta ta shekara dubu za ta kawo albarka a duniya. Ɗan tauhidi na Katolika, Augustine ɗan birnin Hippo (shekara ta 354-430 A.Z.) “ya goyi bayan ra’ayin cewa ba za a yi sarauta ta shekara dubu ba,” in ji littafin nan The Catholic Encyclopedia.a
5, 6. Me ya sa Origen da Augustine suke hamayya da sarauta ta shekara dubu a duniya?
5 Me ya sa Origen da Augustine suke hamayya da sarauta ta shekara dubu? Origen ɗalibin Clement ne na Iskandiriya, wanda ya amince da koyarwar Helenanci wadda ta ce kurwa ba ta mutuwa. Da yake ra’ayin Plato game da kurwa ya rinjaye shi sosai, Origen ya haɗa ra’ayin Plato na kurwa da kuma abin da ke faruwa da ita cikin koyarwar Kirista,” in ji ɗan tauhidi Werner Jaeger. Saboda haka, Origen ya koyar da cewa kowace albarka da sarauta ta shekara dubu za ta kawo, ba za ta kasance a duniya ba amma a duniya ta ruhu.
6 Kafin ya soma bin Kiristanci na ridda sa’ad da yake ɗan shekara 33, Augustine ya zama mai bin sashe na falsafa na Plato da Plotinus ya kafa a ƙarni na uku. Bayan ya soma bin Kiristanci na ridda, ya ci gaba da bin ra’ayin Plato. Augustine “yana da tasiri sosai wajen haɗa koyarwa na Sabon Alkawari da koyarwar Plato na falsafa na Helenanci,” in ji littafin nan The New Encyclopædia Britannica. Littafin nan The Catholic Encyclopedia ya ce, Augustine ya bayyana cewa Sarauta ta Shekara Dubu da ke cikin Ru’ya ta Yohanna sura ta 20 “tatsuniya ce kawai.” Ya daɗa: “Kiristoci ’yan ridda waɗanda ’yan tauhidi ne . . . sun ɗauki matsayinsa kuma suka soma bin wannan ra’ayin, kuma aka daina bin imani na asali na sarauta ta shekara dubu a duniya.”
7. Wane imanin ƙarya ne ya yi wa begen ’yan adam na rai na har abada a duniya zagon ƙasa, kuma ta yaya?
7 Ra’ayin da ya kasance a Babila na dā kuma aka yaɗa a dukan duniya ne ya yi wa begen ’yan adam game da rai na har abada zagon ƙasa, ra’ayin shi ne cewa ’yan adam suna da kurwa ko kuma ruhu da ba ya mutuwa, suna zama ne kawai cikin jiki na zahiri. Sa’ad da ’yan Kiristendam suka yi na’am da wannan ra’ayin, ’yan tauhidi sun murguɗe Nassosi don su sa ayoyin da suka kwatanta bege na samaniya su zama kamar suna koyar da cewa dukan mutanen kirki za su tafi sama. Bisa wannan ra’ayin, suna nuna cewa mutum zai yi rayuwa na ɗan lokaci ne kawai a duniya, don a gwada ko ya cancanci yin rayuwa a sama. Irin wannan abin ya faru da ainihin begen da Yahudawa suke da shi na yin rayuwa har abada a duniya. Yayin da Yahudawa suka soma yin na’am da ra’ayin Helenanci game da kurwa marar mutuwa, suka daina kasancewa da ainihin begensu na yin rayuwa a duniya. Hakan ya bambanta da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da ’yan adam. Mutum halitta ne na zahiri ba ruhu ba ne. Jehobah ya gaya wa ɗan adam na farko: “Turɓaya ne kai.” (Far. 3:19) Duniya ce gidan ’yan adam har abada, ba sama ba.—Karanta Zabura 104:5; 115:16.
Gaskiya ta Haskaka a Cikin Duhu
8. Menene wasu masana na alif da ɗari shidda suka faɗa game da begen ’yan adam?
8 Ko da yake yawancin addinan da suke da’awar cewa su Kiristoci ne ba sa koyar da begen rai na har abada a duniya, ba a koyaushe ba ne Shaiɗan yake nasara wajen ɓoye gaskiya. Cikin shekaru da suka shige, wasu mutane ƙalilan da suke karanta Littafi Mai Tsarki da kyau sun ga hasken gaskiya yayin da suka fahimci wasu fannoni na yadda Allah zai mai da ’yan adam kamiltattu. (Zab. 97:11; Mat. 7:13, 14; 13:37-39) A shekara ta alif da ɗari shidda, fassarar Littafi Mai Tsarki da kuma wallafa shi ya sa Nassosi Masu Tsarki su wanzu a ko’ina. A shekara ta alif da dari shidda da hamsin da ɗaya, wani masani ya rubuta cewa tun da yake ta wurin Adamu ne mutane “suka yi hasarar Aljanna, da Rai Madawwami a Duniya,” saboda haka, ta wurin Kristi “za a sa dukan ’yan adam su yi rayuwa a Duniya; idan ba haka ba, kamannin ba zai yi daidai ba.” (Karanta 1 Korintiyawa 15:21, 22.) Wani marubucin waƙar Turanci wanda sananne ne a duniya, John Milton (1608-1674), ya rubuta littafin nan Paradise Lost da kuma littafi na biyu Paradise Regained. A cikin littattafansa, Milton ya yi nuni ga ladar da masu aminci za su samu a aljanna ta duniya. Ko da yake Milton ya ba da yawancin lokacinsa a rayuwa ga nazarin Littafi Mai Tsarki, ya gane cewa ba za a fahimci gaskiya na Nassi sosai ba har sai bayyanuwar Kristi.
9, 10. (a) Menene Isaac ya rubuta game da begen ’yan adam? (b) Me ya sa Newton yake ganin cewa lokacin bayyanuwar Kristi yana da nisa sosai?
9 Sanannen ɗan lissafi Sir Isaac Newton (1642-1727) yana son Littafi Mai Tsarki sosai. Ya fahimci cewa za a ta da tsarkakku zuwa rayuwa a sama kuma za su yi sarauta da Kristi ba tare da an gan su ba. (R. Yoh. 5:9, 10) Game da talakawan Mulkin, ya rubuta: “Mutane za su ci gaba da zama a duniya bayan ranar hukunci ba shekara dubu kawai ba amma har abada.”
10 Newton ya gaskata cewa Kristi zai bayyana ne ƙarnuka da yawa a gaba. “Dalili ɗaya da ya sa Newton yake ganin cewa Mulkin Allah zai kasance ne a nan gaba shi ne, yana da tabbaci cewa wani mugun abu zai faru domin ’yan ridda da suke koyar da Allah Uku Cikin Ɗaya,” in ji ɗan tarihi Stephen Snobelen. Har ila ba a sanar da bisharar ba. Kuma Newton bai ga rukunin da ke da’awar cewa su Kiristoci ne da za su iya yin wa’azin bisharar ba. Ya rubuta: “Waɗannan annabce-annabcen Daniyel da kuma Yohanna [wanda aka rubuta a cikin littafin Ru’ya ta Yohanna] bai kamata a fahimce su ba har sai kwanaki na ƙarshe.” Newton ya ba da bayani: “‘Daniyel ya ce ‘mutane da yawa za su yi ta kai da kawo a guje, kuma ilimi zai ƙaru.’ Dole ne a yi wa’azin Linjila a dukan al’ummai kafin ƙunci mai girma, da kuma ƙarshen duniya. Ba zai yiwu ba a samu mutane masu yawa daga dukan al’ummai da ba za a iya ƙirgawa ba da ke riƙe da ganyayen dabino da suka fito daga wannan ƙunci mai girma, sai dai ko ta wurin wa’azin Linjila kafin ƙuncin ya zo.”—Dan. 12:4; Mat. 24:14; R. Yoh. 7:9, 10.
11. Me ya sa aka ɓoye begen ’yan adam ga yawancin mutane a kwanakin Milton da Newton?
11 A kwanakin Milton da Newton, yana da haɗari mutum ya furta ra’ayin da ya saɓa wa koyarwar coci. Saboda haka, ba a wallafa yawancin rubuce-rubuce game da binciken da suka yi a kan Littafi Mai Tsarki ba har sai bayan mutuwarsu. Gyaran da aka yi wa coci a ƙarni na goma sha shidda bai kawar da koyarwar ƙarya game da kurwa marar mutuwa ba, kuma cocin Farostanta da aka amince da su sun ci gaba da koyar da ra’ayin Augustine cewa Sarauta ta Shekara Dubu ta riga ta wuce. Ilimi ya ƙaru kuwa a kwanaki na ƙarshe?
“Ilimi [na Gaskiya] Kuma Za Ya Ƙaru”
12. A wane lokaci ne ilimi na gaskiya ya ƙaru?
12 Daniyel ya faɗi abubuwa masu kyau da za su faru a “kwanakin ƙarshe.” (Karanta Daniyel 12:3, 4, 9, 10.) “Sa’annan masu-adalci za su haskaka kamar rana,” in ji Yesu. (Mat. 13:43) Ta yaya ilimi na gaskiya ya ƙaru a kwanakin ƙarshe? Ka yi la’akari da wasu abubuwan da suka faru shekaru da yawa kafin shekara ta 1914, shekarar da kwanakin ƙarshe ya soma.
13. Menene Charles Taze Russell ya rubuta bayan ya bincika batun maidowa?
13 A ƙarshen shekarun alif da ɗari takwas, sahihan mutane da yawa suna neman su fahimci “kwatancin sahihiyan kalmomi.” (2 Tim. 1:13) Charles Taze Russell yana cikin irin waɗannan mutanen. A shekara ta 1870, shi da wasu mutane ƙalilan masu neman gaskiya sun kafa ajin nazarin Littafi Mai Tsarki. A shekara ta 1872 sun bincika batun mai da ’yan adam kamiltattun mutane kamar yadda Adamu yake a dā. Daga baya Russell ya rubuta: “Har zuwa wannan lokacin ba mu fahimci bambancin da ke tsakanin ladar mutanen coci da ake gwada su yanzu da kuma ladar masu aminci a duniya gabaki ɗaya ba.” Ladar da masu aminci za su samu shi ne “maido da yanayin kamilta da Adamu, wanda shi ne shugaba da kuma kakan ’yan adam, ya more a dā a Adnin.” Russell ya yarda cewa wasu sun taimake shi a nazarinsa na Littafi Mai Tsarki. Su waye ne waɗannan?
14. (a) Yaya Henry Dunn ya fahimci A. M. 3:21? (b) Su waye ne Dunn ya ce za su zauna a duniya har abada?
14 Henry Dunn yana cikinsu. Ya rubuta game da “mayar da kowane abu, abin da Allah ya ambata ta bakin annabawansa masu-tsarki waɗanda ke tun farkon duniya.” (A. M. 3:21) Dunn ya san cewa maidowar za ta haɗa da mayar da ’yan adam kamiltattu a duniya a lokacin Sarautar Kristi ta Shekara Dubu. Dunn ya kuma bincika tambayar da mutane da yawa suke tunani a kai, Su waye ne za su rayu har abada a duniya? Ya bayyana cewa za a ta da miliyoyi daga matattu, a koya musu gaskiya, kuma za su sami zarafin ba da gaskiya ga Kristi.
15. Menene George Storrs ya fahimta game da tashin matattu?
15 A shekara ta 1870, George Storrs da kansa ya kammala cewa za a ta da marasa adalci daga matattu don su sami zarafin yin rayuwa har abada. Daga Nassosi, ya fahimci cewa wanda aka ta da daga mutuwa kuma ya kasa amincewa da wannan zarafin “zai mutu, ko da mai zunubin yana da shekara ɗari.” (Isha. 65:20) Storrs ya zauna a Brooklyn, New York, kuma ya harhaɗa wata mujalla mai suna Bible Examiner.
16. Menene ya sa Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka bambanta da Kiristendam?
16 Daga Littafi Mai Tsarki, Russell ya fahimci cewa lokaci ya yi da za a sanar da bishara a ko’ina. Saboda haka, a shekara ta 1879, ya soma wallafa Zion’s Watch Tower and Herald of Christ’s Presence da yanzu ake kira Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah. A dā, mutane ƙalilan ne kawai suka fahimci gaskiya game da begen ’yan adam, amma a yanzu, rukunin Ɗaliban Littafi Mai Tsarki a ƙasashe da yawa ne suke samun Hasumyar Tsaro kuma suke nazarinta. Imanin da suke da ita cewa mutane ƙalilan ne kawai za su tafi sama amma miliyoyi za su samu kamiltaccen rai a duniya ne ya bambanta Ɗaliban Littafi Mai Tsarki daga yawancin mutanen Kiristendam.
17. Ta yaya ilimi na gaskiya ya kasance a yalwace?
17 “Kwanakin ƙarshe” da aka annabta ya soma a shekara ta 1914. Ilimi na gaskiya game da begen ’yan adam ya yaɗu kuwa? (Dan. 12:4) A shekara ta 1913, ana buga huɗubar Russell a jaridu dubu biyu da adadin masu karatu miliyan goma sha biyar. A ƙarshen shekara ta 1914, mutane fiye da miliyan tara a manyan ɓangarori guda uku a duniya sun riga sun kalli “Photo-Drama of Creation” (Hoton Wasan Kwaikwayo na Halitta) wanda ya haɗa da hotunan da suka bayyana Sarautar Kristi ta Shekara Dubu. Daga shekara ta 1918 har zuwa 1925, an ba da jawabin nan “Millions Now Living Will Never Die,” (Miliyoyin Mutane da Suke Rayuwa Yanzu Ba Za Su Taɓa Mutuwa Ba) a cikin harsuna fiye da 30 a dukan duniya kuma ya bayyana begen rai na har abada a duniya. A shekara ta 1934, Shaidun Jehobah sun fahimci cewa ya kamata a yi wa waɗanda suke da begen yin rayuwa a duniya har abada baftisma. Wannan fahimin ya sa suka sake kasancewa da himma sosai don yin wa’azin bisharar Mulki. A yau, begen yin rayuwa a duniya har abada ya sa mutane da yawa su nuna godiya ga Jehobah.
“’Yancin Daraja” a Nan Gaba
18, 19. Wace irin rayuwa ce aka annabta a Ishaya 65:21-25?
18 An hure annabi Ishaya ya rubuta game da irin rayuwar da mutanen Allah za su more a duniya. (Karanta Ishaya 65:21-25) Wasu itatuwan da ke da rai shekaru 2,700 da suka shige sa’ad da Ishaya ya rubuta waɗannan kalmomi suna nan har yanzu. Kana ganin kanka a aljanna kana rayuwa wadda za ta daɗe kamar itatuwan nan a cikin koshin lafiya da ƙarfi?
19 Maimakon a haifi mutum kuma bayan wani ɗan lokaci ya mutu, rayuwa za ta sa mu sami zarafi na dindindin na yin gini, shuka, da kuma koyan abubuwa. Ka yi tunanin abokantaka da za ka ƙulla. Waɗannan dangantakar za su ci gaba har abada. Lallai “’ya’yan Allah” za su more “’yancin daraja” a duniya!—Rom. 8:21.
[Hasiya]
a Augustine ya yi da’awar cewa Sarauta ta Shekara Dubu ta Mulkin Allah ba a nan gaba ba ne, amma an riga an soma ta sa’ad da aka kafa coci.
Za Ka Iya Bayyanawa?
• Yaya aka ɓoye begen ’yan adam game da rayuwa a duniya?
Wane fahimi ne wasu masu karatun Littafi Mai Tsarki suka samu a shekarun alif da ɗari shida?
• Yaya aka fahimci bege na gaskiya na ’yan adam sosai yayin da shekara ta 1914 take kusa?
• Yaya ilimi na gaskiya game da bege na duniya ya ƙaru?
[Hotunan da ke shafi na 13]
Marubucin waƙa John Milton (hagu) da ɗan lissafi Isaac Newton (dama) sun fahimci begen rai na har abada a duniya
[Hotunan da ke shafi na 15]
Ɗaliban Littafi Mai Tsarki na farko sun fahimci daga Nassosi cewa lokaci ya yi da za a sanar da bege na gaske na ’yan adam a dukan duniya