‘Jehobah Ya Sa Fuskarsa Ta Haskaka Wajensu’
DA AKWAI fiye da tsokoki talatin a fuskar ɗan adam. Tsokoki sha huɗu ne suke yin aiki tare don ka yi murmushi! Ka yi tunanin yadda za ka riƙa magana da mutane idan babu waɗannan tsokoki. Zai yi daɗi kuwa? Da kyar. Amma ga kurame tsokoki na fuska suna aiki fiye da sa tattaunawa da mutane ya yi daɗi. Sa’ad da aka haɗa hakan da motsa hannu da fuska, hanya ce mai muhimmanci ta sanar da tunani da ra’ayoyinmu. Mutane da yawa suna mamaki game da yadda ake amfani da yaren kurame a furta bayani mai wuya tare da ba da kowane bayani dalla-dalla.
A kwanan nan, kurame a dukan duniya sun ga fuskar da ta fi kyau wajen furci da launi fiye da kowace fuskar ’yan adam. A alamance, sun ga “fuskar Ubangiji.” (Mak. 2:19) Ba wai hakan ya faru kawai ba ne. Tun da daɗewa Jehobah ya nuna yana ƙaunar kurame sosai. Ya yi hakan tun daga lokacin al’ummar Isra’ila ta dā. (Lev. 19:14) A wannan zamanin, an ga ƙaunarsa ga kurame. “[Allah] wanda yake nufi dukan mutane su tsira, kuma su kawo ga sanin gaskiya.” (1 Tim. 2:4) Ta wajen samun cikakken sani na gaskiya game da Allah, kurame da yawa a alamance sun ga fuskarsa. Ta yaya kurame suka yi hakan tun da yake ba sa jin magana? Kafin mu amsa wannan tambayar, bari mu tattauna abin da ya sa yaren kurame yake da muhimmanci ga kurame.
Gani Ji Ne
Da akwai ra’ayoyi da yawa da ba daidai ba ne game da kurame da kuma yaren kurame. Bari mu taimaka muku ku fahimci wasu gaskiya game da kurame. Kurame suna iya tuƙa mota. Kallon leɓen mutum kuma su fahimci abin da yake nufi yana yi musu wuya sosai. Yaren kurame ya bambanta da rubutun makafi kuma ba motsa hannu kawai ba ne. Babu yaren kurame guda da za a iya yin amfani da shi a dukan duniya. Ƙari ga haka, kurame suna yin yaren kurame da ya bambanta da na wasu kuramen da ke zaune a wasu wurare a cikin ƙasarsu.
Kurame suna iya yin karatu kuwa? Ko da yake wasu sun iya karatu sosai, gaskiyar ita ce, yana yi wa yawancin kurame wuya su yi karatu. Me ya sa? Domin abin da aka rubuta ya fito ne daga yaren da ake furtawa. Ka yi la’akari da yadda yaron da yake iya jin magana yake koyon wani yare. Tun daga lokacin da aka haife shi, yana tare ne da mutanen da suke yaren da ake yi a yankin. Ba da daɗewa ba, zai iya haɗa kalmomi tare kuma su zama jimloli. Hakan yana faruwa ne daga jin yaren. Saboda haka, sa’ad da yaran da ke jin magana suka soma karatu, abin da za su koya kawai shi ne kalmomin da ke rubuce da suka yi daidai da kalaman da suka riga suka sani.
Yanzu ka yi tunanin kana wata ƙasa cikin ɗakin da aka yi da gilashi da ba za ka iya jin ƙara ba. Ba ka taɓa jin yarensu ba. Kowace rana, mutanen sai su zo su yi maka magana ta gilashi. Ba ka jin abin da suke cewa. Leɓunan su ne kawai kake ganin yana motsi. Sa’ad da suka gane cewa ba ka fahimtar su, sai suka rubuta kalaman a kan fallen takarda kuma suka nuna maka abin da suka rubuta ta gilashin. Suna ganin cewa za ka iya fahimtar abin da suka rubuta. Kana ganin hakan zai yiwu? Za ka ga cewa ba za ka iya yin magana da su a wannan yanayin ba. Me ya sa? Domin an rubuta yaren da ba ka taɓa ji ba. Irin yanayin da yawancin kurame suke ciki ke nan.
Yaren kurame hanya ce mafi kyau ta yin magana da kurame. Mutum yana amfani da alamu ya faɗi wani batu da gaɓoɓin jikinsa. Motsa gaɓoɓin jikinsa tare da yin alama da fuskarsa sun yi daidai da dokokin nahawun yaren kurame. Ta hakan aka kafa yaren da ake gani da ya sa ya yiwu a sanar da saƙo ga idanu.
Hakika, kusan kowane motsi da kurma ya yi da hannayensa, jiki, da fuskarsa sa’ad da yake yaren kurame yana da ma’ana. Ba sa amfani da fuskarsu don su yi alamun da zai burge mutane kawai. Suna da muhimmanci a nahawun yaren kurame. Alal misali: Yin tambaya ta wajen ɗaga gira zai iya nuna cewa kana tambayar da ba ka bukatar amsa ko kuma wadda kake bukatar a ba da amsar e ko a’a. Idan ka saukar da gira, hakan na nufin waye, menene, ina, me ya sa, ko kuma yaya. Motsa baki wani lokaci yana nuna girman wani abu ko kuma tsananin wani abu da aka aikata. Yadda kurma yake motsa kansa, ɗaga kafaɗarsa, ko motsa kumatunsa, da kuma ƙifta idanunsa suna da ma’ana ga abin da ake cewa.
Wannan motsa jiki yana taimaka wa mai kallo ya fahimci bayanin da kyau. Ta wajen yin amfani da wannan kyakkyawar hanyar sadarwa, kurame da suka san yaren da kyau suna shirye su sanar da kowane ra’ayi, daga waƙa, soyayya da abubuwan ban dariya, da kuma waɗanda za ka iya gani ko kuma taɓa da kuma abubuwan da ba za mu iya gani ba ko kuma mu taɓa su.
Littattafan Yaren Kurame Sun Taimaka Sosai
Sa’ad da aka furta sani na Jehobah a yaren kurame, kurma zai iya jin saƙon kuma ya “bada gaskiya” ga Mai saƙon. Saboda haka, Shaidun Jehobah suna ƙoƙari sosai su yi wa’azi ga kurame a dukan duniya kuma su yi tanadin littafin da zai amfane su. (Rom. 10:14) A yanzu, akwai rukuni 58 na masu fassara yaren kurame a dukan duniya, kuma akwai littattafan yaren kurame yanzu a faifan DVD a harsuna guda 40 na yaren kurame. Waɗannan ƙoƙarce-ƙoƙarcen sun kawo sakamako mai kyau kuwa?
Jeremy, wanda iyayensa kurame ne, ya ce: “Na tuna yadda babana yake sa’o’i a ɗakinsa yana nazarin sakin layi ƙalilan na talifin Hasumiyar Tsaro, yana ƙoƙarin ya fahimce su. Farat ɗaya, sai ya fito a guje daga ɗakinsa ya yi alama da farin ciki: ‘Na fahimci abin da yake nufi!’ Sai ya bayyana mini abin da sakin layin yake nufi. A lokacin ina ɗan shekara sha biyu ne. Sai na karanta sakin layi da sauri kuma na yi masa alama: ‘Baba, ba na tsammanin cewa abin da yake nufi ke nan. Yana nufin . . . ’ Sai ya gaya mini da alama na tsaya kuma ya koma ɗakinsa don ya fahimci ma’anar abin da aka rubuta da kansa. Ba zan taɓa mance irin baƙin cikin da na gani a fuskarsa ba da kuma irin sha’awar da na ji sa’ad da nake kallonsa yana komawa cikin ɗakinsa. Amma, samun littattafan yaren kurame a faifan DVD yana taimaka masa ya fahimci bayanin da kyau yanzu. Ganin yadda yake farin ciki sa’ad da yake furta yadda yake ji game da Jehobah abu ne da ba na wasa da shi.”
Ka yi la’akari da labarin wasu ma’aurata waɗanda Shaidu ne, da suka yi magana da Jessenia, wata budurwa kurma a ƙasar Chile. Bayan mamarta ta ba su izinin nuna wa Jessenia bidiyon Littafi Na Na Labarun Bible a faifan DVD na yaren kurame na Chile, sun ce: “Sa’ad da Jessenia ta soma kallon bidiyon sai ta soma dariya kuma bayan hakan ta soma kuka. Sa’ad da mamarta ta tambaye ta abin da ya sa take kuka, sai ta ce tana kuka ne domin tana son abin da take kallo. Sai mamarta ta gane cewa ta fahimci dukan abin da ke cikin faifan DVD ɗin.”
Wata mata kurma da take zama a wata karkara a Venezuela tana da ’ya guda, kuma matar ta ɗauki wani cikin. Da ita da mijinta sun ga cewa ba za su iya samun wani yaro ba domin rashin kuɗi, sai suka soma tunanin zubar da cikin. Ba tare da sanin abin da ke faruwa ba, Shaidun Jehobah suka kai wa wannan ma’auratan ziyara, kuma suka nuna musu darasi na goma sha biyu na bidiyon mujallar nan Menene Allah Yake Bukata a Gare Mu? a Yaren Kurame na Venezuela. Wannan darasin ya bayyana ra’ayin Allah game da zubar da ciki da kuma kisan kai. Daga baya, matar ta gaya wa Shaidun cewa ta yi farin ciki sosai domin yin nazarin wannan darasin. Ta ce saboda hakan, sun tsai da shawara cewa ba za su zubar da cikin ba. An ceci ran jariri da taimakon littafin yaren kurame a faifan DVD!
Lorraine, wata Mashaidiya kurma ta ce: “Koyon Littafi Mai Tsarki ya yi mini wuya sosai. A dā ba ni da cikakken fahimi. Amma, sa’ad da aka samu ƙarin koyarwar Littafi Mai Tsarki a yaren kurame, hakan ya taimake ni na samu cikakken fahimi.” George, wanda kurma ne kuma ya zama Mashaidi shekaru talatin da takwas da suka shige, ya ce: “Babu shakka cewa iya fahimtar wani abu da kanka yana sa ka kasance da daraja da kuma gaba gaɗi. Ina jin cewa yaren kurame a faifan DVD ne ya taimaka mini sosai na kyautata dangantaka ta da Jehobah.”
“Taro a Yare Na!”
Ƙari ga littattafan yaren kurame, Shaidun Jehobah sun tsara ikilisiyoyi inda ake gudanar da taro a yaren kurame kawai. A yanzu, akwai ikilisiyoyi fiye da 1,100 na yaren kurame a dukan duniya. Ana yi wa kurame magana da yarensu, kuma ana koyar da Littafi Mai Tsarki a yadda kurma yake tunani, wato, a nasa yaren. Ana gudanar da taron a hanyar da ke nuna daraja ga al’adarsa da kuma hanyar rayuwarsu.
Kafa ikilisiyoyin yaren kurame yana da amfani kuwa? Ka yi la’akari da labarin Cyril wanda aka yi wa baftisma a matsayin Mashaidin Jehobah a shekara ta 1955. Ya yi shekaru da yawa yana nazarin littattafai iyakar yadda ya iya kuma yana halartan taron Kirista a kai a kai. A wasu lokatai akwai masu fassara na yaren kurame, a wasu lokatai kuma babu. Idan babu wanda zai fassara masa, yana dogara ne ga Shaidun da suke ƙoƙarin su taimaka masa ta wajen rubuta masa abin da ake cewa a kan dakalin magana. Sai a shekara ta 1989, sa’ad da ya kai shekara 34 da zama Mashaidi ne aka kafa ikilisiyar yaren kurame na farko a birnin New York, a ƙasar Amirka. A matsayin wanda yake cikin wannan ikilisiyar, yaya Cyril ya ji? “Kamar na fito ne daga kurmi mai duhu zuwa cikin haske. Taro a yare na!”
Ikilisiyoyin yaren kurame na Shaidun Jehobah wurare ne da kurame suke taruwa a kai a kai su koya game da Allah kuma su bauta masa. Wurare ne da mutanen Allah za su ƙulla dangantaka kuma su sami ƙarfafa. A duniyar da kurame ba za su iya magana da mutane ba kuma ana iya ware su daga sauran mutane, waɗannan ikilisiyoyi wuraren sadarwa ne da kuma cuɗanya. A waɗannan ikilisiyoyin, kurame za su iya koya, su yi girma, kuma su ba da kansu a hidimarsu ga Jehobah. Kurame da yawa da Shaidu ne suna hidima na cikakken lokaci. Wasu sun ƙaura zuwa wasu ƙasashe don su taimaka wa kurame su koya game da Jehobah. Kiristoci maza da kurame ne sun zama ƙwararrun malamai, masu tsara abubuwa, da kuma makiyaya, kuma da yawa sun cancanta don su kula da hakkoki a cikin ikilisiya.
A ƙasar Amirka, da akwai fiye da ikilisiyoyin yaren kurame guda 100 da kuma rukunoni 80. A ƙasar Brazil, akwai ikilisiyoyin yaren kurame guda 300 da kuma fiye da rukunoni 400. Da akwai kusan ikilisiyoyin yaren kurame 300 a ƙasar Mexico. Ƙasar Rasha tana da fiye da ikilisiyoyi yaren kurame 30 da rukunoni 113. Waɗannan misalai ne ƙalilan na ƙaruwar da ake samu a dukan duniya.
Shaidun Jehobah suna yin manyan taro da kuma taron gunduma a yaren kurame. A shekarar da ta wuce, an yi fiye da taron gunduma 120 a yaren kurame dabam-dabam a dukan duniya. Waɗannan taron sun taimaki Shaidu kurame su ga cewa suna cikin sashen ’yan’uwanci na dukan duniya da suke amfana daga abinci na ruhaniya a kan kari.
Leonard kurma ne kuma shi Mashaidin Jehobah ne fiye da shekara 25. Ya ce: “Na san cewa Jehobah Allah ne na gaskiya. Duk da haka, ban fahimci abin da ya sa ya ƙyale mutane suke shan wahala ba. A wani lokaci, hakan na sa na yi fushi da shi. Amma sa’ad da ake ba da wani jawabi a taron gunduma na yaren kurame, na fahimci abin da ya sa ya ƙyale wahala. Sa’ad da aka gama jawabin, matata ta taɓa ni ta ce, ‘Ka gamsu?’ Da dukan zuciyata na ce e! Bayan shekara 25, na yi farin cikin cewa ban bar Jehobah ba. Ina ƙaunarsa amma ban fahimce shi sosai ba. A yau, na fahimce shi!”
Godiya da Dukan Zuciya
Menene kurame suke gani a fuskar Jehobah sa’ad da suka koya game da shi? Suna ganin ƙauna, juyayi, adalci, aminci, ƙauna ta alheri da sauransu.
Dukan kurame da Shaidu ne a dukan duniya suna ganin fuskar Jehobah kuma za su ci gaba da yin haka sosai. Da yake yana ƙaunar kurame a zuciyarsa, ‘Jehobah ya sa fuskarsa ta haskaka a wajensu.’ (Lit. Lis. 6:25) Irin waɗannan kurame suna godiya da yake sun san Jehobah!
[Hotunan da ke shafi na 25]
Da akwai fiye da ikilisiyoyin yaren kurame guda 1,100 a dukan duniya
[Hotunan da ke shafi na 26]
Fuskar Jehobah ta haskaka sosai a yankin kurame