Ka Daraja ’Yan’uwanka Kurame Maza da Mata!
MUTANEN Allah a yau iyali ce babba ta ’yan’uwa maza da mata masu ruhaniya, waɗanda za a iya bin diddigen gādonsu zuwa maza da mata na zamanin dā. Waɗannan sun haɗa da Sama’ila, Dauda, Samson, Rahab, Musa, Ibrahim, Saratu, Nuhu, da Habila. Kurame da yawa suna cikin bayin Jehobah masu aminci. Alal misali, mutane biyu na farko da suka zama Shaidun Jehobah a ƙasar Mongolia, ma’aurata ne kurame. Kuma nagartar ’yan’uwanmu kurame masu bi a Rasha ne ya sa muka samu ’yanci a Kotun Turai na ’Yancin ’Yan Adam.
A zamani, “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” ya yi tanadin littattafai na yaren kurame kuma ya tsara ikilisiyoyi da kuma manyan tarurruka da tarurrukan gunduma a yaren kurame. (Mat. 24:45) Waɗannan sun amfani kurame sosai.a Amma ka taɓa yin tunani game da yadda kurame suke koya game da Allah na gaskiya kuma su samu ci gaba a cikin gaskiya ba tare da waɗannan tanadin ba? Ka taɓa tunanin abin da za ka iya yi don ka taimaka wa kuramen da suke yankinku?
Kafin Tanadi na Zamani
Idan kuma fa aka ce ka yi wa wasu kurame tsofaffi tambaya game da yadda suka ji sa’ad da suka san Allah? Suna iya gaya maka yadda suka ji sa’ad da suka fara koyan cewa Allah yana da suna, yadda wannan gaskiya ta canja rayuwarsu kuma hakan ya kiyaye su shekaru da yawa kafin a yi tanadin bidiyo ko kuma faifan DVD na yaren kurame da zai taimaka musu su koya gaskiya masu wuya da ke cikin Nassi. Suna iya bayyana yadda yake a lokacin da ba a yin taro ko kuma fassara shi a yaren kurame. Maimakon haka, wani zai zauna kusa da su kuma ya riƙa rubuta musu abin da ake faɗa a fallen takarda don ya taimaka musu su fahimci abin da ake cewa. Wani ɗan’uwa kurma ya koyi gaskiyar Littafi Mai Tsarki ta wannan hanyar shekaru bakwai kafin a sami wanda zai riƙa fassara taro zuwa yaren kurame.
Shaidu kurame tsofaffi sun tuna yadda yake a yi wa mutane masu jin magana wa’azi tare da waɗanda suke cikin ikilisiya. A hannu ɗaya, suna riƙe da katin da ke ɗauke da gabatarwa mai sauƙi na hidimar ƙofa ƙofa. Sai su riƙe sabon fitowa na jaridun Hasumiyar Tsaro da Awake! a ɗayan hannun. Yana da wuya sosai a yi nazarin Littafi Mai Tsari da wani kurma ta wajen yin amfani da littattafai da babu wani cikinsu wanda ya fahimci sosai. Wataƙila, kurame tsofaffi masu shela sun tuna baƙin ciki da suka fuskanta sa’ad da babu wanda ya fahimce su kuma saboda haka ba su iya ci gaba da yin magana game da gaskiya ta ruhaniya ba. Sun kuma san yadda yake mutum ya ƙaunaci Jehobah sosai duk da haka ba su da gaba gaɗin yin amfani da shi ko kuma su aikata bisa abin da suka koya. Me ya sa? Don ba su tabbata ba ko fahiminsu game da wani batu daidai ne.
Duk da waɗannan tangarɗa, ’yan’uwanmu kurame maza da mata sun ci gaba da riƙe amincinsu. (Ayu. 2:3) Sun yi haƙuri suna sauraron Jehobah. (Zab. 37:7) Kuma yanzu yana yi musu albarka fiye da yadda yawancinsu suka taɓa tsammani.
Ka yi la’akari da ƙoƙarce-ƙoƙarcen da wani ɗan’uwa kurma ya yi, shi miji ne da kuma uba. Kafin a fito da bidiyon yaren kurame, da aminci yana ja-gora wajen gudanar da nazari na iyali. Ɗansa ya tuna: “Nazari na iyali a koyaushe yana yi wa babana wuya, tun da yake dukan abin da yake koyar da mu daga cikin littattafai ne. Sau da yawa, ba ya fahimtar abin da aka rubuta sosai. Mu yara ma mun sa nazarin ya yi masa wuya. Muna saurin sa ya san sa’ad da bai bayyana abubuwa daidai ba. Duk da haka, yana gudanar da nazari na iyali a koyaushe. Ya ji cewa idan muka koya wani abu game da Jehobah ya fi muhimmanci da kunya da yake sha a wani lokacin domin bai fahimci Turanci sosai ba.”
Da akwai kuma misalin Richard, wani ɗan’uwa a shekarunsa na saba’in wanda kurma ne da kuma makaho da ke da zama a birnin Brooklyn, New York, a Amirka. An san Richard da halartar taron Kirista a kai a kai. Don ya halarci taro, yana shiga jirgin ƙasa da kansa, yana ƙirga inda jirgin yake tsayawa don ya san sa’ad da zai sauka. A wani lokacin ɗari, ƙanƙara ta yi yawa sosai har aka fasa taro. An sanar da dukan waɗanda suke cikin ikilisiya, amma an manta a gaya wa Richard. Sa’ad da ’yan’uwan suka fahimci abin da ya faru kuma suka neme shi, suka same Richard yana tsaye a gaban Majami’ar Mulki, yana jira da haƙuri a buɗe ƙofar. Sa’ad da aka tambaye shi abin da ya sa ya fita cikin sanyi, ya amsa, “Ina ƙaunar Jehobah.”
Menene Za Ka Iya Yi?
Da akwai kurame a yankinku? Za ka iya koyan yaren kurame domin ka yi magana da su? Kurame masu fara’a ne da haƙuri sa’ad da suke koya wa mutane yarensu. Kana iya saduwa da kurma babu shiri ko kuma sa’ad da kake hidima. Menene za ka iya yi? Ka yi ƙoƙari ka yi magana da shi. Ka yi amfani da alama, ’yar wasiƙa, zane, hotuna, ko kuma ka haɗa waɗannan abubuwa. Ko idan mutumin ya nuna ba ya son gaskiya, ka gaya wa Mashaidi kurma ko kuma wanda ya san yaren kurame game da ziyararka. Wataƙila kurman zai fi son saƙon sa’ad da aka gabatar da shi a yaren kurame.
Wataƙila kana koyon yaren kurame kuma kana halartan ikilisiyar yaren kurame. Ta yaya za ka zama ƙwararre a yin alama da kuma fahimtar yaren? Ko da yake akwai masu shela da ba kurame ba ne a ikilisiyarku, me ya sa ba za ka yi musu magana da yaren kurame ba? Wannan zai taimake ka ka riƙa yin tunani a yaren kurame. A wani lokaci, kana iya fuskantar gwajin ka yi magana maimakon yin amfani da yaren kurame, tun da yake zai fi maka sauƙi. Sa’ad da kake koyon kowane yare, dole ne ka nace idan kana so ka ƙware.
Yin iyakar ƙoƙarinmu don yin amfani da yaren kurame yana nuna ƙauna da ladabi ga ’yan’uwanmu kurame. Ka yi tunanin taƙaici da kurame suke fuskanta a kowace rana domin ba sa fahimtar mutane a wajen aiki ko kuma a makaranta. “Kowace rana, mutane da suke kusa da ni suna magana,” in ji wani ɗan’uwa kurma. “Sau da yawa, ina jin na kaɗaita kuma an bar ni a baya kuma sai na yi baƙin ciki ƙwarai, har da fushi. Kalmomi ba za su iya kwatanta yadda nake ji a wani lokaci ba.” Ya kamata taronmu ya zama wurin da ’yan’uwanmu kurame za su samu abinci na ruhaniya kuma su more sadarwa da abuta mai daɗaɗawa.—Yoh. 13:34, 35.
Ba za a manta da ƙananan rukuni na kurame da suke taruwa a ikilisiyoyi inda mutane suke jin magana ba. Ana fassara musu jawaban. Don su fahimci abin da ake gabatarwa, kurame suna zama a gaban Majami’ar Mulkin. Hakan na taimaka musu su riƙa ganin mai fassarar da mai ba da jawabin a layi guda ba mai tare su. An ga cewa sauran mutane da suke cikin ikilisiyar suna sabawa da hakan nan da nan, ba tare da janye hankalinsu ba. Ana amfani da wannan tsarin a manyan taro da taron gunduma inda ake fassara zuwa yaren kurame. Waɗanda suke cikin ikilisiya masu aiki tuƙuru sun cancanci a yaba musu sosai don fassarawa yadda kurma zai furta bayanin da ma’ana da kuma yadda ya dace.
Wataƙila kana cikin ikilisiya da ke kula da rukunin yaren kurame ko kuma ikilisiyar da ke da kurame kaɗan da ake fassara wa taron. Menene za ka yi don ka nuna kana kula da su? Ka gayyace su zuwa gidanka. Idan zai yiwu, ka koyi wasu alamu a yaren kuramen. Kada ka ji kunya don ba ka iya yaren kurame ba. Za ka nemi hanyar yin magana da su, kuma nuna irin wannan ƙaunar zai kawo farin ciki da ba za ka manta ba. (1 Yoh. 4:8) Shaidu kurame masu bi suna da abubuwa da yawa da za su koya mana. Su masu hira ne sosai, suna da basira, kuma suna da ban dariya. Wani ɗan’uwa da iyayensa kurame ne ya ce: “Dukan rayuwata ina tare da kurame, kuma sun koya mini abubuwa fiye da yadda zan iya biya. Muna iya koyan abubuwa da yawa daga ’yan’uwanmu kurame.”
Jehobah yana ƙaunar bayinsa masu aminci, har da kurame. Misalinsu na bangaskiya da jimiri yana azurta ƙungiyar Jehobah. Saboda haka, bari mu daraja ’yan’uwanmu kurame!
[Hasiya]
a Ka duba talifin nan “Jehobah Ya Sa Fuskarsa Ta Haskaka Wajensu,” a cikin fitowar Hasumiyar Tsaro na 15 ga Agusta, 2009.
[Hotunan da ke shafi na 31]
Kurma zai fi yin sha’awar saƙon Mulki idan aka gabatar masa da shi a yaren kurame
[Hotunan da ke shafi na 32]
Ya kamata taronmu ya zama wurin da ’yan’uwanmu kurame maza da mata suke samun ƙarfafa na ruhaniya