Kafin Ku Soma Wa’azi, Kuna Bukata Ku Yi Bincike
1. Me ya sa ake tsara ikilisiyoyi bisa ga yaruka da ake yi a yankin da ake harsuna da dama?
1 Bayan almajiran Yesu suka karɓi ruhu mai tsarki a Fentakos 33 A.Z., sai suka soma yi wa mutanen da suka halarci taron “zance da waɗansu harsuna.” (A. M. 2:4) A sakamakon haka, mutane kusan 3,000 suka yi baftisma. Wani abin sha’awa shi ne, mai yiwuwa yawancin baƙin suna jin Ibrananci ko Helenanci. Duk da haka, Jehobah ya sa aka yi musu wa’azin Mulki a yarensu. Hakika, ɗaya daga cikin dalilan da ya sa shi ne, a yawancin lokatai mutane suna karɓan bishara sosai idan an yi musu wa’azi a yarensu. Shi ya sa a yau ake tsara ikilisiyoyi bisa ga yare a yankin da ake harsuna da dama. (Ku duba littafin nan Organized to Do Jehovah’s Will, shafi na 107, sakin layi na 2-3.) Ba a ba wa rukunonin da ke wani yare yankin da za su yi wa’azi, amma suna yi wa mutane wa’azi a yankin ikilisiyar da suke ƙarƙashinta da kuma yankunan wasu ikilisiyoyi da ke garin.
2. (a) Me ake nufi da aikin nema kuma a ina ne yake da muhimmanci a yi hakan? (b) Ta yaya ikilisiyoyi za su taimaka wa juna sa’ad da suke yin wa’azi a yankin da ake harsuna dabam-dabam? (c) Mene ne ya kamata mu yi idan muka samu wani da yake son saƙonmu amma yana wani yare dabam?
2 Idan kuna zaune ne a inda mutane suna yare ɗaya, za ku iya yin wa’azi gida-gida babu wata matsala. Amma wannan yanayin yana iya canjawa idan kuna zama a birnin da ake harsuna da dama. Wataƙila, kuna wa’azi a yanki ɗaya da wasu ikilisiyoyin da suke harsuna dabam. Ko da yake ikilisiyoyin nan za su iya ba ku adireshin mutanen da suka haɗu da su, wato, waɗanda suke yin yaren ikilisiyarku, ikilisiyarku ko rukuninku ne yake da hakkin neman waɗannan mutanen. (Ku duba akwati mai jigon nan “Ku Taimaka wa Juna.”) Saboda haka, kuna bukata ku yi bincike don ku san inda mutanen da suke yarenku suke da zama. Ta yaya za a nemi waɗannan mutane?
3. Mene ne zai taimaka wa ikilisiya ko rukuni ya san inda zai nemi mutane da kuma tsawon lokaci da zai yi amfani da shi wajen yin hakan?
3 Yadda Za A Tsara Aikin Neman Waɗanda Suke Wani Yare: Tsawon lokaci da za ku yi kuna neman mutane a yankin da ake harsuna da dama ya dangana ne da yanayin yankin. Alal misali, mutane nawa ne suke yaren a yankin? Masu shela nawa ne suke yankin? Adireshin mutane guda nawa ne ikilisiyar ko rukunin yake da shi a yanzu? Ba wajibi ba ne ikilisiya ta bi tsari guda wajen neman mutanen da suke wani yare a dukan yankunan ba, amma suna iya mai da hankali sosai ga sassa na yankunan da mutanen da ke yaren suka fi yawa da kuma wuraren da babu nisa sosai daga yankin. Saboda haka, kasancewa da tsari mai kyau yana da muhimmanci sosai don mutane da yawa su samu damar kira bisa sunan Jehobah.—Rom. 10:13, 14.
4. (a) Yaya za a tsara wannan aikin neman mutane? (b) Ta yaya za ku nemi mutanen da suke yarenku?
4 Rukunin dattawa, musamman mai kula da hidima, zai tsara ya kuma ja-goranci yadda za a yi wannan aikin, saboda aikin ya kasance bisa tsari. (1 Kor. 9:26) A rukunin da ake yin wani yare dabam, rukunin dattawa na ikilisiyar zai iya zaɓan wani ɗan’uwa da ya cancanta, mai yiwuwa dattijo ko bawa mai hidima don ya ja-gorance wannan aikin. Idan zai yiwu, rukunin dattawa na ikilisiyar da ke tura ’yan’uwa yin wannan aikin suna iya yin shiri saboda dukan masu shela da ke cikin ikilisiyar su saka hannu wajen yin aikin a lokaci-lokaci.—Ku duba akwatin nan mai jigo “Yadda Za Ku Nemi Waɗanda Suke Yin Yaren Ikilisiyarku.”
5. (a) Waɗanne shawarwari ne masu shela za su iya bi sa’ad da suke neman mutane? (b) Mene ne za mu iya faɗa sa’ad da muke neman mutane?
5 Duk sa’ad da muka fita neman waɗanda suke yin wani yare, ya kamata mu san cewa wa’azi ne muke yi. Saboda haka, ya kamata mu yi irin adon da muke yi sa’ad da muke fita wa’azi. ’Yan’uwa da yawa sun ga cewa gwada gabatarwa da suke so su yi amfani da shi da kuma yin magana da yaren sa’ad da suke neman yana taimaka musu su kasance da himma kuma su ƙware wajen yin yaren. Za mu iya ba da rahoton awoyin da muka yi muna neman mutane amma ba za mu ba da rahoton awoyin da muka yi muna shirya katin da ke ɗauke da taswirar unguwa da kuma jerin adireshi ba. Sa’ad da muka samu wani da yake yaren, ya kamata mu yi ƙoƙari don mu gaya masa saƙon Mulkin, sa’an nan mu gaya wa mai kula da hidima ko kuma wanda shi ya naɗa don ya saka adireshin a cikin katin da ke ɗauke da taswirar unguwa. Ya kamata a ɗauki wannan matakin ko da mutumin ya nuna yana son saƙonmu ko a’a. Ko da yake aikin neman mutane yana da muhimmanci, muna bukata mu daidaita aikin da wasu fannonin wa’azi.—Ku duba akwatin nan mai jigo “Abin da Za Ku Faɗa Sa’ad da Kuke Neman Mutane.”
6. Waɗanne ƙalubale na musamman ne ke tattare da neman kurame?
6 Yadda Za A Nemi Kurame: Neman kurame yana tattare da ƙalubale kuma yana bukatar ƙwazo da naciya. Ba a gane ko waye ne kurma daga ganin sunansa, ko siffarsa ko kuma adonsa. Ƙari ga haka, iyalinsa da abokansa za su iya yin sanyin jiki wajen ba da wani bayani game da shi ga masu shela saboda tsoro ko kuma kunya. Waɗannan shawarwari da ke gaba game da neman kurame za su iya taimakawa sa’ad da ake neman waɗanda suke wani yare dabam.
7. (a) Yaya za a iya neman kurame a unguwoyin da ke da manyan gidaje? (b) Me za mu yi don mutane su daina shakkar mu?
7 Ikilisiyoyi da rukunonin da suke yaren kurame sun yi nasara a neman mutane a cikin unguwoyi. Kuna iya samun wani a yankin wanda zai gaya muku cewa maƙwabcinsa ko abokin aikinsa ko kuma abokin makarantarsa yana yaren kurame. Mai yiwuwa ya taɓa ganin wata alama a titi wadda ta nuna cewa akwai yara kurame a yankin. Ko kuma wataƙila yana da wani dangi da kurma ne. Ku tuna cewa tambayoyin da kuke yi za su iya sa mutane su yi shakkar ku. Amma za ku iya kwantar da hankalin mai gidan ta wurin kasancewa da fara’a da ladabi da kuma yin taƙaitaccen bayani. Wasu sun yi nasara ta wajen nuna wa mutumin bidiyon Littafi Mai Tsarki ko kuma wasu dibidi da aka yi a yaren kurame yayin da suke tambayarsa game da kurame. Bayan haka, sai su bayyana cewa suna so su ba waɗannan kuramen saƙon bishara daga Littafi Mai Tsarki. Idan mai gidan yana shakkar ba da bayani game da kuramen, wataƙila zai iya karɓan adireshinku ko kuma takardar gayyata zuwa taron ikilisiya don ya ba danginsa ko abokinsa wanda kurma ne.
8. Ta yaya ikilisiya da ke kusa za ta iya taimaka wa ikilisiyar da ke yaren kurame?
8 Ikilisiyar da ke yaren kurame tana iya ɗaukan kwana ɗaya ko biyu a shekara ta gayyaci wata ikilisiya da ke kusa da take yare dabam don ta taimaka mata wajen neman mutane a unguwoyin ko garuruwa da ke yankinsu. Ana iya yin gwaji da kuma ba da umurni a kan yadda za a yi neman sa’ad da ikilisiyar yaren kurame suke gudanar da taron da ake yi kafin a fita wa’azi. Ikilisiyar da ke yaren kurame tana iya tura wa kowane rukuni na masu wa’azi na ikilisiyar da ke wani yare dabam aƙalla mai shela ɗaya, sai kuma a ba wa masu shelan kati da ke ɗauke da taswirar unguwar da za su je neman mutane a yankin.
9. Ta yaya za a nemi kurame a inda suke taro da kuma nishaɗi ko kuma inda suke karɓan agaji?
9 Za a iya neman kurame a inda aka san cewa kurame suna zuwa don taro ko nishaɗi da kuma inda suke zuwa don su karɓi agaji. Ya kamata masu shela su sa kayan da ya dace da wannan yanayin. Zai fi dacewa su tattauna da mutum ɗaya ko biyu kuma su yi hakan cikin hikima maimakon yi wa jama’ar gaba ɗaya wa’azi a lokaci ɗaya. Idan an samu waɗanda suke son saƙonmu, masu shelan za su iya karɓan adireshin mutanen kuma su ba da nasu.
10. Ta yaya masu shela za su iya neman kurame a wuraren kasuwanci da ke yankinsu?
10 A wasu wuraren kasuwanci, muna iya tambaya kawai ko akwai ma’aikata ko kuma ’yan ciniki waɗanda suka iya yaren kurame da suka saba zuwa wurin. Idan akwai makarantar kurame a yankin, za mu iya ba su wasu littattafanmu da aka sa a dibidi don su yi amfani da su a laburarensu.
11. Me ya sa neman mutanen da ke wani yare dabam sashe ne mai muhimmanci a hidimarmu?
11 Aiki Mai Muhimmanci: Neman kurame ko kuma mutanen da suke yarenku aiki ne mai wuya. Bugu da ƙari, yaruka da ake yi a wasu unguwoyi suna iya canjawa a cikin ƙanƙanin lokaci yayin da mutane suna ƙaura daga yankin, wasu kuma suna shigowa. Hakan yana sa ya yi wuya a kasance da cikakken adireshin mutane. Duk da haka, a wurare da dama, wannan aikin neman mutane muhimmin sashe ne na aikin wa’azi. Jehobah ne ya ba mu wannan aikin yin wa’azi kuma shi ba mai tāra ba ne. (A. M. 10:34) Nufinsa shi ne cewa “dukan mutane su tsira, kuma su kawo ga sanin gaskiya.” (1 Tim. 2:3, 4) Saboda haka, bari mu haɗa kai da Jehobah da kuma ’yan’uwa wajen neman mutanen da ke da “zuciya mai-gaskiya mai-kyau,” waɗanda ke yin yare dabam-dabam.—Luk 8:15.
[Akwati a shafi na 5]
Ku Taimaka wa Juna
Idan ikilisiya ko rukuni za su so a taimaka musu a neman waɗanda suke yarensu don su yi musu wa’azi, mai kula da hidima zai iya tuntuɓar dattawan ikilisiyar da ke wani yare dabam wadda ke kusa. Zai fi dacewa ku tuntuɓi ikilisiyoyin da ba su da nisa sosai kaɗai ko kuma ikilisiyoyin da suke da masu shela da dama waɗanda suka iya yaren. Waɗannan ikilisiyoyin kuma za su iya sanar da masu shelarsu cewa idan suka samu waɗanda suke yin wannan yaren, su rubuta sunansu da kuma adireshinsu don su ba wa mai kula da hidima, shi kuma ya ba wa ikilisiya ko kuma rukunin da ke neman waɗannan mutanen. Masu kula da hidima na ikilisiyoyin da ke neman mutane za su iya tsara yadda za a yi wa’azi a yankunan da ake yaruka da dama, kuma za su iya kwatanta wa waɗanda suke son saƙonmu ikilisiya ko rukunin da ke yin yarensu.
Idan masu shela sun samu wani da yake yare dabam (ko kuma kurma) kuma ya nuna cewa lallai yana son saƙonmu, su cika fom na Please Follow Up (S-43) ba tare da ɓata lokaci ba kuma su ba wa sakataren ikilisiya. Wannan zai sa mutumin ya samu taimako wajen kyautata dangantakarsa da Allah da sauri.—Ku duba km 5/11 shafi na 3.
[Akwati a shafi na 6]
Yadda Za Ku Nemi Waɗanda Suke Yin Yaren Ikilisiyarku
• Ku tambayi waɗanda kuke nazarin Littafi Mai Tsarki da su da iyalinku da abokan aiki da dai sauran su.
• A cikin hikima, ku tambayi mutane a wuraren da jama’a suke taruwa, kamar su laburare da ofisoshi da kuma manyan makarantu.
• Ku bincika jaridu don samun bayanai game da abubuwan da waɗanda suke yin wani yare dabam suka shirya don jama’arsu.
• Ku ziyarci shaguna da wuraren kasuwanci da mutanen da suke yin wani yare dabam suke yawan zuwa.
• Ku nemi izini daga ma’aikata ko kuma masu kula da wuraren kasuwanci ko makarantun jami’a ko kuma tashoshi, wato, wuraren da mutanen da ke yaren suke yawan zuwa kuma ku samu teburi ku jera littattafanmu a kai.
[Akwati a shafi na 7]
Abin da Za Ku Faɗa Sa’ad da Kuke Neman Mutane
Nuna fara’a da kuma yin magana kai tsaye zai iya sa mutane su sake jiki sa’ad da muke yi musu tambaya. Kafin mu soma tambayar zai dace mu nuna littattafan da muke da su a yaren.
Bayan gaisuwa, za ku iya ce: “Muna neman mutanen da suke yin yaren ․․․․․ don mu tattauna saƙo mai daɗi da ke cikin Littafi Mai Tsarki tare da su. Ko ka san wani da yake yaren?”
Sa’ad da kuke neman kurame, za ku iya ce: “Sannu. Don Allah bari in nuna maka wani abu. [Ku nuna wa mutumin bidiyon wani nassi daga New World Translation a yaren kurame ta yin amfani da ƙaramin dibidi tafi da gidanka.] Wannan wata ayar Littafi Mai Tsarki ce a yaren kurame na Amirka. Ban da Littafi Mai Tsarki, muna da wasu fayafayan bidiyo da dama da ake ba wa kurame babu farashi don taimaka musu su ƙulla dangantaka mai kyau da Allah. Ka san wani kurma ko wani da ba ya ji sosai kuma ya iya yaren kurame?” Idan mutumin ya ce bai san wani kurma ba, za mu iya tambayarsa ko ya taɓa ganin kurma a wajen aiki ko a makaranta ko kuma a unguwarsu.