Ka Kasance Mai Biyayya Da Kuma Gaba Gaɗi Kamar Kristi
“Ku yi farinciki, na yi nasara da duniya.”—YOH. 16:33.
1. Yaya yawan biyayyar Yesu take ga Allah?
YESU KRISTI a koyaushe yana yin nufin Allah. Bai taɓa tunanin yi wa Ubansa na samaniya rashin biyayya ba. (Yoh. 4:34; Ibran. 7:26) Amma abin da ya fuskanci a duniya ya sa yin biyayya ya yi masa wuya. Daga somawar aikinsa na wa’azi, magabtan Yesu, har da Shaiɗan sun yi ƙoƙari su rinjaye Yesu, su tilasta masa, ko kuma su ruɗe shi ya bar tafarkinsa na kasancewa da aminci. (Mat. 4:1-11; Luk 20:20-25) Waɗannan abokan gaba sun sa Yesu azaba na hankali, na motsin zuciya da kuma na zahiri. Daga baya, suka yi nasarar kashe shi a kan gungumen azaba. (Mat. 26:37, 38; Luk 22:44; Yoh. 19:1, 17, 18) Duk da abin da ya faru masa, da kuma wahala mai tsanani da ya sha, Yesu ya yi “biyayya har da mutuwa.”—Karanta Filibiyawa 2:8.
2, 3. Menene za mu iya koya daga Yesu da yake ya kasance da aminci duk da wahala da ya sha?
2 Abin da Yesu ya fuskanta sa’ad da yake duniya ya koya masa sababbin ɓangarori na biyayya. (Ibran. 5:8) Zai iya zama kamar babu abin da Yesu zai ƙara koya gama da bauta wa Jehobah. Balle ma, ya more dangantaka na kud da kud da Jehobah na shekaru aru aru kuma ya zama “gwanin mai-aiki” na Allah a lokacin halitta. (Mis. 8:30) Duk da haka, jimrewa cikin bangaskiya duk da wahala da ya sha ya nuna cewa yana da cikakken aminci. Yesu, Ɗan Allah, ya daɗa ruhaniyarsa. Menene za mu iya koya daga abin da ya faru masa?
3 Ko da yake shi kamili ne, Yesu bai yi ƙoƙari ya yi cikakkiyar biyayya da kansa ba. Ya yi addu’a Allah ya taimake shi ya ci gaba da yin biyayya. (Karanta Ibraniyawa 5:7.) Don mu ci gaba da yin biyayya, mu ma muna bukatar mu kasance da tawali’u, kuma mu yi addu’a don taimakon Allah a kai a kai. Don wannan dalilin, manzo Bulus ya gargaɗi Kiristoci: “Ku kasance da wannan hali a cikinku wanda ke cikin Kristi Yesu,” wanda ya “ƙasƙantar da kansa, ya zama yana biyayya har da mutuwa.” (Filib. 2:5-8) Tafarkin da Yesu ya bi ya tabbatar da cewa ’yan adam suna iya yin biyayya har a tsakanin miyagu mutane ma. Hakika, Yesu kamili ne, amma ’yan adam ajizai kamar mu kuma fa?
Za Mu Iya Yin Biyayya Duk da Ajizancinmu
4. Menene yake nufin cewa an halicce mu da ’yancin zaɓe?
4 Allah ya halicce Adamu da Hauwa’u a matsayin halittu masu basira da suke da ’yancin zaɓe. A matsayin ’ya’yansu, mu ma muna da ’yancin zaɓe. Menene hakan yake nufi? Yana nufin cewa muna iya tsai da shawara mu yi abin da ke da kyau ko kuma marar kyau. A wata sassa, Allah ya ba mu ’yancin zaɓan mu yi masa biyayya ko kuma rashin biyayya. Wannan ’yancin zaɓe yana kawo hakki sosai. Hakika, shawara da muka tsai da game da ɗabi’armu za ta nuna ko za mu samu rai ko kuwa mutuwa. Suna kuma shafan waɗanda suke kusa da mu.
5. Wace kokawa ce dukanmu za mu yi, kuma yaya za mu iya yin nasara?
5 Domin ajizancin da muka gada, yin biyayya ba za ta yi mana sauƙi ba. Ba a koyaushe yake da sauƙi a yi biyayya ga dokokin Allah ba. Bulus ya yi fama don ya yi biyayya. Ya rubuta: “Ina ganin wata shari’a dabam a cikin gaɓaɓuwana, tana yaƙi da shari’ar hankalina, tana saka ni bauta ƙarƙashin shari’ar zunubin nan da ke cikin gaɓaɓuwana.” (Rom. 7:23) Hakika, sa’ad da ya kasance babu sadaukar da kai, azaba, ko damuwa, biyayya tana da sauƙi. Amma yaya muke aikatawa sa’ad da biyayya ta saɓa da “kwaɗayin jiki, da sha’awar idanu”? Waɗannan sha’awoyi marasa kyau suna tasowa daga ajizancinmu da kuma tasirin “ruhun duniya” da ya kewaye mu, kuma suna da iko sosai. (1 Yoh. 2:16; 1 Kor. 2:12) Don mu ƙi su, dole ne mu ‘shirya zuciyarmu’ kafin mu fuskanci gwaji ko jaraba kuma mu ƙuduri aniya cewa za mu yi biyayya ga Jehobah, ko da menene zai faru. (Zab. 78:8) Muna da misalan mutane da yawa a cikin Littafi Mai Tsarki da suka yi nasara domin sun shirya zuciyarsu.—Ezra 7:10; Dan. 1:8.
6, 7. Ka ba da misalin yadda nazari na kanmu zai iya taimaka mana mu tsai da shawarwari masu kyau.
6 Hanya ɗaya da za mu shirya zuciyarmu ita ce ta wajen sa ƙwazo a yin nazarin Nassosi da kuma littattafai da ke bisa Littafi Mai Tsarki. Ka yi tunanin cewa kana cikin wannan yanayin. A ce yamma ce da kake yin nazari na kanka. Ka riga ka yi addu’a ruhun Jehobah ya taimake ka ka yi amfani da abin da ka koya daga Kalmarsa. Ka shirya za ka kalli wani fim a talabijin washegari da yamma. Ka ji cewa wannan fim yana da kyau, amma ka kuma san ya ƙunshi lalata da mugunta.
7 Ka yi bimbini bisa gargaɗin Bulus a Afisawa 5:3: “Amma fasikanci, da dukan ƙazanta, ko sha’awa, kada a ko ambata a cikinku, gama haka ya kamata ga tsarkaka.” Ka kuma tuna shawarar Bulus da ke Filibiyawa 4:8. (Karanta.) Sa’ad da kake yin bimbini a kan wannan hurarren gargaɗi, ka tambayi kanka, ‘Idan da ganga na ba da zuciyata ga irin wannan fim, ina bin misalin Yesu ne na cikakkiyar biyayya ga Allah?’ Menene za ka yi? Za ka kalli wannan fim ɗin har ila?
8. Me ya sa dole ne mu kasance da mizanai masu girma na ɗabi’a da na ruhaniya?
8 Zai zama abin kuskure mu sauƙaƙa ƙudurinmu na manne wa mizanan Jehobah, wataƙila mu yi tunani cewa muna da ƙarfi sosai mu yi tsayayya da sakamakon muguwar tarayya, har lokacin da wannan tarayya ta ƙunshi mugun nishaɗi na lalata. Maimakon haka, dole ne mu kāre kanmu da yaranmu daga lalatattun tasiri na halin Shaiɗan. Masu kiwon dabbobin suna aiki tuƙuru don su kāre dabbobinsu sa’ad da cuta ta ɓarke a wurin da suke zaune, wadda za ta hallaka dabbobinsu, har ma ta sa dabbobin su watse zuwa wasu wurare, ta hakan su yaɗa wannan cuta mai kisa. Ya kamata mu fi kasancewa a faɗake don mu tsare kanmu daga “dabarun Shaiɗan.”—Afis. 6:11.
9. Me ya sa za mu ƙuduri aniya kowace rana mu yi biyayya ga Jehobah?
9 Kusan kowace rana, muna zaɓan ko za mu yi abubuwa yadda Jehobah yake so ko kuma ba za mu yi ba. Domin mu samu ceto, dole ne mu yi biyayya ga Allah kuma mu yi rayuwa bisa mizanansa na adalci. Ta wajen bin misalin Kristi na biyayya “har mutuwa,” muna nuna cewa bangaskiyarmu ta gaske ce. Jehobah zai albarkace mu domin tafarkinmu na bangaskiya. Yesu ya yi alkawari: “Wanda ya jimre har matuƙa shi ne za ya tsira.” (Mat. 24:13) Hakika, hakan na bukatar mu koya nuna gaba gaɗin da ya dace, irin wanda Yesu ya nuna.—Zab. 31:24.
Yesu Ya Nuna Misali Mafi Kyau na Gaba Gaɗi
10. Waɗanne irin matsi ne za mu iya fuskanta, kuma yaya ya kamata mu aikata?
10 Da yake halayen wannan duniya sun kewaye mu, muna bukatar gaba gaɗi don mu ƙi su. Kiristoci suna fuskantar matsi na ɗabi’a, na mutane, na kuɗi, da na addini da za su iya sa su bijire daga hanyoyin adalci na Jehobah. Mutane da yawa suna fuskantar hamayya daga iyali. A wasu ƙasashe, makarantu sun nace wajen koyar da ra’ayin bayyanau, kuma mutane suna amince da koyarwa cewa babu Allah. Ba za mu yi banza da waɗannan matsi ba. Dole ne mu aikata domin mu yi tsayayya da su kuma ta haka mu kāre kanmu. Misalin Yesu ya nuna mana yadda za mu yi nasara.
11. Ta yaya yin tunani game da misalin Yesu zai sa mu ƙara kasancewa da gaba gaɗi?
11 Yesu ya gaya wa almajiransa: “A cikin duniya kuna da wahala; amma ku yi farin ciki, na yi nasara da duniya.” (Yoh. 16:33) Bai taɓa faɗa wa rinjaya ta wannan duniya ba. Bai taɓa ƙyale duniya ta hana shi cika aikin wa’azi da aka ba shi ba ko kuma ta sa ya bar mizanansa na bauta ta gaskiya da kuma halin da ya dace; mu ma za mu yi hakan. Sa’ad da yake addu’a, Yesu ya faɗa game da almajiransa: “Ba na duniya su ke ba, kamar yadda ni ba na duniya ba ne.” (Yoh. 17:16) Koya game da misalin gaba gaɗi na Kristi da kuma yin tunani game da hakan zai sa mu kasance da gaba gaɗin da ake bukata don mu kasance a ware daga duniya.
Ka Koyi Gaba Gaɗi Daga Wajen Yesu
12-14. Ka ba da misalan gaba gaɗin da Yesu ya nuna.
12 Yesu ya nuna gaba gaɗi ƙwarai a hidimarsa gabaki ɗaya. Ta wajen yin amfani da ikonsa na Ɗan Allah, da gaba gaɗi ya “shiga cikin haikali na Allah, ya fitarda dukan masu-sayarwa da masu-saye cikin haikali, ya jirkitadda tabura na masu-musanyar kuɗi, da kujerun masu-sayarda kurciyoyi.” (Mat. 21:12) Sa’ad da sojoji suka zo su kama Yesu a darensa na ƙarshe a duniya, da gaba gaɗi ya zo gaba don ya kāre almajiransa, yana cewa: “Idan . . . ni kuke nema, ku bar waɗannan su tafi abinsu.” (Yoh. 18:8) Ba da daɗewa ba, ya gaya wa Bitrus ya ajiye takobinsa, hakan ya nuna cewa Yesu bai dogara da makamai na duniya ba, amma ya dogara ga Jehobah.—Yoh. 18:11.
13 Yesu da gaba gaɗi ya fallasa malaman ƙarya na zamaninsa marasa ƙauna da kuma koyarwarsu na ƙarya. Yesu ya gaya musu: “Kaitonku, ku marubuta da Farisawa, munafukai! gama ku kan rufe wa mutane mulkin sama . . . kun ƙyale matsaloli mafiya girma na Attaurat, shari’a, da jinƙai da bangaskiya . . . ku kan gyara bayan tasa da ƙwarya, amma daga ciki cike su ke da zalumci da zarcewa.” (Mat. 23:13, 23, 25) Almajiran Yesu za su bukaci irin wannan gaba gaɗi domin shugabannin addinan ƙarya za su tsananta musu kuma su kashe wasu cikinsu.—Mat. 23:34; 24:9.
14 Yesu ya nuna gaba gaɗi har wajen tsayayya wa aljanu. A wani lokaci, wani mutumi mai aljanu sosai da babu wanda zai iya riƙe shi da sarƙa ya fuskance shi. Yesu bai ji tsoro ba, ya fitar da aljannu masu yawa da sun riƙe mutumin. (Mar. 5:1-13) A wannan zamanin, Allah bai ba Kiristoci ikon yin irin waɗannan mu’ujizoji ba. Har ila, a aikinmu na wa’azi da koyarwa, mu ma muna yaƙi na ruhaniya da Shaiɗan, wanda ya “makantar da hankulan marasa-bada gaskiya.” (2 Kor. 4:4) Kamar yadda yake da Yesu, makamanmu “ba na jiki ba ne, amma masu-iko ne gaban Allah da za su rushe wurare masu-ƙarfi” wato, ra’ayin ƙarya na addini da suka yi jijiya sosai a cikinsu. (2 Kor. 10:4) Sa’ad da muke amfani da waɗannan makamai na ruhaniya, muna koyon abubuwa da yawa daga misalin Yesu.
15. Gaba gaɗin Yesu ya dangana ne a kan menene?
15 Gaba gaɗin Yesu ya dangana a kan bangaskiya ba a kan jarumtaka ba. Haka ya kamata namu ya kasance. (Mar. 4:40) Ta yaya za mu samu bangaskiya ta gaske? Misalin Yesu yana yi mana ja-gora. Ya nuna cewa ya san Nassosi sosai kuma yana da cikakken tabbaci a gare su. A matsayin makami, Yesu bai yi amfani da takobi na zahiri ba, amma da takobi na ruhu, wato, Kalmar Allah. Ya goyi bayan koyarwarsa a kai a kai ta wajen yin nuni ga Nassosi. Sau da yawa yana soma kalamansa da wannan furci: “An rubuta,” wato, a cikin Kalmar Allah.a
16. Ta yaya za mu samu bangaskiya mai girma?
16 Don mu kasance da bangaskiya da za ta iya jimre wa gwaji da ake fuskanta ta wajen almajiranci, dole ne mu karanta kuma mu yi nazarin Littafi Mai Tsarki kullum kuma mu halarci taron Kirista, mu riƙa kafa koyarwa da ita ce tushen bangaskiya a cikin zuciyarmu. (Rom. 10:17) Dole ne mu yi bimbini sosai, a kan abin da muka koya, mu ƙyale shi ya shiga cikin zuciyarmu. Bangaskiya ce kaɗai tare da ayyukan da suke nuna cewa muna da ita ne za su motsa mu mu ɗauki mataki na gaba gaɗi. (Yaƙ. 2:17) Dole ne mu yi addu’a don mu sami ruhu mai tsarki domin bangaskiya tana cikin ’ya’yan ruhu.—Gal. 5:22.
17, 18. Ta yaya wata ’yar’uwa matashiya ta nuna gaba gaɗi a makaranta?
17 Wata ’yar’uwa matashiya mai suna Kitty ta shaida yadda bangaskiya ta gaske take sa a kasance da gaba gaɗi. Tun tana ƙarama, ta san cewa bai kamata ta ji “kunya” yin bishara a makaranta ba, kuma tana son ta ba da shaida mai kyau ga abokan ajinta. (Rom. 1:16) Kowace shekara tana ƙuduri aniya ta yi wa mutane wa’azin bishara, amma tana ɗan jinkiri domin rashin gaba gaɗi. Sa’ad da ta kusan shekara ashirin, sai ta canja makaranta. Ta ce, “A wannan lokacin, zan biya dukan zarafin da na yi hasararsa.” Kitty ta yi addu’a don ta kasance da gaba gaɗi da kuma basira irin ta Kristi, kuma ta samu zarafin da ya dace.
18 A rana na farko a makaranta, an gaya wa ɗaliban su gabatar da kansu ɗaɗɗaya. Yawancinsu sun ambata addininsu, kuma suka daɗa cewa ba sa bauta a kai a kai. Kitty ta fahimci cewa wannan ne zarafin da ta yi addu’a ta samu. Sa’ad da aka zo kanta, sai ta faɗa da gaba gaɗi, “Ni Mashaidiyar Jehobah ce, kuma tushen ja-gora ta a al’amuran bauta da halin kirki shi ne Littafi Mai Tsarki. Sa’ad da ta ci gaba da magana, wasu ɗalibai suka nuna ta fuskarsu cewa addininta ba sananne ba ne. Amma wasu sun saurara kuma daga baya suka yi tambayoyi. Har malamin ya yi amfani da Kitty don ya nuna misali mai kyau na wadda take goyon bayan imaninta. Kitty ta yi farin ciki sosai da ta koya daga misalin Yesu na gaba gaɗi.
Ka Nuna Bangaskiya da Gaba Gaɗi Irin ta Kristi
19. (a) Menene kasancewa da bangaskiya ta gaske ya ƙunsa? (b) Ta yaya za mu sa Jehobah farin ciki?
19 Manzannin ma sun fahimci cewa dole ne ayyukansu na gaba gaɗi ya kasance bisa bangaskiya. Sun roƙi Yesu: “Ka ƙara mana bangaskiya.” (Karanta Luka 17:5, 6.) Kasancewa da bangaskiya ta gaske ya ƙunshi fiye da gaskatawa kawai cewa akwai Allah. Ta ƙunshi ƙulla dangantaka na kud da kud da Jehobah, irin dangantaka da ke tsakanin yaro da uba mai kirki da kuma ƙauna. An hure Sulemanu ya rubuta: “Ɗana, idan zuciyarka ta yi hikima, har ni ma zuciyata za ta yi fari. I, cikina za ya yi murna, lokacin da leɓunanka suna faɗin al’amuran da ke daidai.” (Mis. 23:15, 16) Hakanan ma, bin mizanan adalci da gaba gaɗi yana sa Jehobah farin ciki, kuma sanin hakan yana ƙara sa mu kasance da gaba gaɗi. Saboda haka, bari a koyaushe mu yi koyi da misalin Yesu, muna kasancewa da gaba gaɗi don adalci!
[Hasiya]
a Alal misali, ka duba Matta 4:4, 7, 10; 11:10; 21:13; 26:31; Markus 9:13; 14:27; Luka 24:46; Yohanna 6:45; 8:17.
Za Ka Iya Bayyanawa?
• Menene zai taimaka mana mu yi biyayya duk da cewa mu ajizai ne?
• Bangaskiya ta gaske ta dangana a kan menene, kuma ta yaya hakan zai sa mu kasance da gaba gaɗi?
• Menene sakamakon yin biyayya da kuma kasancewa da gaba gaɗi irin ta Kristi?
[Hotunan da ke shafi na 13]
Kana ‘shirya zuciyarka’ ka tsayayya wa gwaji?
[Hotunan da ke shafi na 15]
Kamar Yesu, muna iya nuna gaba gaɗi da ke bisa bangaskiya, yadda Yesu ya yi