Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w09 10/15 pp. 26-28
  • Kai ‘Dasashe ne Kafaffe Kuma Cikin Tushen’?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kai ‘Dasashe ne Kafaffe Kuma Cikin Tushen’?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “Faɗin da Ratar da Tsawon da Zurfin”
  • Ka Gwada Fahiminka
  • An Ƙaddara Su “Kafin Kafawar Duniya”
  • “Gwargwadon Wadatar Alherinsa”
  • Asirin Nufin Allah
  • “Ga Azanci . . . Ku Zama Cikakkun Mutane”
  • Wakilci Na Cika Nufin Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Ka Yi Wa’azi Game da Alherin Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • Ka Kara Fahimtar Kalmar Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
  • Jehobah Yana Tattara Iyalinsa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
w09 10/15 pp. 26-28

Kai ‘Dasashe ne Kafaffe Kuma Cikin Tushen’?

KA TAƁA ganin babban itacen da iska mai ƙarfi yake kaɗawa? Itacen yana fuskantar matsi mai girma, duk da haka, ya jimre. Me ya sa? Domin yana da tushe mai ƙarfi da ya kafu a cikin ƙasa. Muna iya zama kamar wannan itacen. Sa’ad da muke fama da gwaje-gwaje masu wuya a rayuwarmu, mu ma za mu iya jimrewa idan mu “dasassu ne kafaffu kuma cikin tushen.” (Afis. 3:14-17; NW) Menene wannan tushen?

Kalmar Allah ta ce “Kristi Yesu da kansa babban dutse na ƙusurwa” ne na ikilisiyar Kirista. (Afis. 2:20; 1 Kor. 3:11) An ƙarfafa mu Kiristoci mu “yi tafiya a cikinsa hakanan, dasassu, ginannu kuma cikinsa, kafaffu cikin bangaskiya.” Idan muka yi hakan, za mu iya jimre dukan farmakin da ake kai wa bangaskiyarmu, har da waɗanda ake yi ta hanyar “magana mai-rinjayarwa” da ke bisa ‘ruɗi na banza’ na mutane.—Kol. 2:4-8.

“Faɗin da Ratar da Tsawon da Zurfin”

Ta yaya, za mu zama “dasassu” da kuma ‘kafaffu cikin bangaskiya’? Hanya ɗaya mai muhimmanci da za mu iya kafa saiwoyinmu a cikin ƙasa, a alamance, ita ce ta yin nazarin hurarriyar Kalmar Allah sosai. Jehobah yana son mu “ruska, tare da dukan tsarkaka, ko menene fāɗin da ratar da tsawon da zurfin” gaskiya. (Afis. 3:18) Saboda haka, babu Kirista da ya kamata ya gamsu da fahimi na sama-sama kawai, ta wajen sanin “farkon zantattukan” da ke cikin Kalmar Allah kaɗai. (Ibran. 5:12; 6:1) Akasin haka, ya kamata kowannenmu ya yi ɗokin zurfafa fahiminsa na gaskiyar Littafi Mai Tsarki.—Mis. 2:1-5.

Amma, hakan ba ya nufin cewa muna bukatan mu sami ilimi sosai don mu zama ‘dasassu da ƙafaffu’ cikin gaskiya. Balle ma, Shaiɗan ma ya san abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Muna bukatan wani abu kuma. Muna bukatan mu san “ƙaunar Almasihu . . . wadda ta fi gaban sani.” (Afis. 3:19) Duk da haka, sa’ad da muka yi nazari domin muna ƙaunar Jehobah da kuma gaskiya, samun ƙarin cikakken sani game da Kalmar Allah zai ƙarfafa bangaskiyarmu.—Kol. 2:2.

Ka Gwada Fahiminka

A yanzu, me ya sa ba za ka gwada fahiminka ba game da wasu koyarwa masu muhimmanci da ke cikin Littafi Mai Tsarki? Yin hakan zai ƙarfafa ka ka riƙa yin nazarin Littafi Mai Tsarki na kanka sosai. Alal misali, ka karanta ayoyi na farko na wasiƙar Bulus ga Afisawa. (Ka duba akwatin nan “Zuwa ga Afisawa.”) Bayan ka karanta waɗannan ayoyin, ka tambayi kanka, ‘Na fahimci ma’anar furcin da ke waɗannan ayoyin Littafi Mai Tsarki da aka yi da rubutun tafiyar tsutsa a cikin akwatin?’ Bari mu bincika su ɗaya bayan ɗaya.

An Ƙaddara Su “Kafin Kafawar Duniya”

Bulus ya rubuta zuwa ga ’yan’uwa masu bi: “[Allah] ya rigaya ya ƙadara mu da zaman ’ya’yansa ta wurin Yesu Kristi.” Hakika, Jehobah ya ƙudurta cewa zai kai wasu cikin ’yan Adam zuwa kamiltacciya iyalinsa a samaniya. Waɗannan ’ya’ya na Allah za su zama sarakuna da firistoci tare da Kristi. (Rom. 8:19-23; R. Yoh. 5:9, 10) A lokacin da ya fara ƙalubalantar ikon mallakar Jehobah, Shaiɗan ya yi da’awar cewa ’yan adam suna da laifi. Saboda haka, ya dace da Jehobah ya zaɓi waɗannan ’yan adam ɗin su saka hannu wajen kawar da dukan mugunta daga duniya, har da tushen mugunta, Shaiɗan Iblis! Amma, ba wai Jehobah ya ƙaddara tuntuni ba ne ba cewa mutane kaza da kaza ne za su zama ’ya’yansa ba. Maimakon haka, Allah ya ƙudurta cewa za a samu rukunin ’yan adam da za su yi sarauta tare da Kristi a sama.—R. Yoh. 14:3, 4.

Wace “duniya” ce Bulus yake nufi sa’ad da ya rubuta wasiƙa zuwa ga Kiristoci masu bi cewa a matsayin rukuni, an zaɓe su ne “kafin kafawar duniya”? Ba ya nuni ga lokacin da Allah bai halicce duniya ko ’yan adam ba. Hakan zai ƙaryata ƙa’idar mai muhimmanci na adalci. Me zai sa a ɗaura wa Adamu da Hauwa’u laifin abubuwan da suka yi inda Allah ya riga ya ƙaddara tun kafin a halicce su cewa za su yi tawaye? Saboda haka, a wane lokaci ne Allah ya tsai da shawarar yadda zai magance yanayin da Adamu da Hauwa’u suka haddasa sa’ad da suka bi Shaiɗan wajen yin tawaye ga ikon mallakar Allah? Jehobah ya yi hakan bayan iyayenmu na asali sun yi tawaye, amma kafin a samu duniyar mutane ajizai da za a ’yanta.

“Gwargwadon Wadatar Alherinsa”

Me ya sa Bulus ya faɗi cewa an yi shirin da ke ayoyi na farko na Afisawa ne bisa “gwargwadon wadatar alherin [Allah]”? Ya faɗi hakan ne domin ya nanata cewa ba a tilasta wa Jehobah ya ’yantar da ’yan adam masu zunubi ba.

Babu wani a cikinmu da ya cancanci a ’yantar da shi. Amma, domin ƙauna mai girma da yake yi wa ’yan adam, Jehobah ya yi shirye-shirye na musamman don ya cece mu. Hakika, idan aka yi la’akari da ajizancinmu da zunubinmu, ’yantar da mu da aka yi, alheri ne na gaske, kamar yadda Bulus ya faɗa.

Asirin Nufin Allah

A dā, Allah bai bayyana yadda zai gyara ɓarnar da Shaiɗan ya yi ba. “Asiri” ne. (Afis. 3:4, 5) Daga baya, sa’ad da aka kafa ikilisiyar Kirista, Jehobah ya bayyana dalla-dalla yadda zai cim ma nufinsa na asali ga ’yan adam da kuma duniya. A “cikar wokatai” in ji Bulus, Allah ya kafa “wakilci,” wato, tsarin ja-gorar al’amura da zai kai ga haɗa kan dukan halittunsa masu basira.

Sashe na farko na wannan haɗin kan ya soma a Fentakos na shekara ta 33 A.Z., sa’ad da Jehobah ya soma tattara waɗanda za su yi sarauta da Kristi a sama. (A. M. 1:13-15; 2:1-4) Sashe na biyu zai zama tattara waɗanda za su zauna a cikin aljanna a duniya a ƙarƙashin Mulkin Almasihu na Kristi. (R. Yoh. 7:14-17; 21:1-5) Furcin nan “wakilci” ba ya nuni ga Mulkin Almasihu, domin an kafa wannan Mulkin ne a shekara ta 1914. Maimakon haka, wannan kalmar tana nuni ne ga yadda Allah yake bi da harkoki don ya cim ma nufinsa na mai do da haɗin kai a dukan duniya.

“Ga Azanci . . . Ku Zama Cikakkun Mutane”

Babu shakka, yin nazari mai kyau zai taimaka maka ka fahimci “fāɗin da ratar da tsawon da zurfin” gaskiya sosai. Amma, babu shakka cewa harkokin rayuwa na yau da kullum zai iya sa Shaiɗan ya raunana ko kuma halaka halinmu mai kyau na yin nazari cikin sauƙi. Kada ka ƙyale shi ya yi maka hakan. Ka yi amfani da ‘fahimi’ da Allah ya ba ka ka ‘zama cikakken mutum ga azanci. (1 Yoh. 5:20; 1 Kor. 14:20) Ka tabbata cewa ka fahimci dalilin da ya sa ka gaskata abin da ka yi imani da shi, kuma a koyaushe za ka iya ba da ‘dalilin begen da ke cikinka.’—1 Bit. 3:15.

A ce kana Afisa sa’ad da aka karanta wasiƙar Bulus da farko. Kalamansa za su ƙarfafa ka ka so ka ƙara kasancewa da “imani da sanin Ɗan Allah,” ko ba haka ba? (Afis. 4:13, 14) Babu shakka! Saboda haka, bari hurarrun kalaman Bulus su motsa ka ka yi hakan a yau. Idan kana da cikakkiyar ƙauna ga Jehobah da kuma cikakken sani na Kalmarsa, hakan zai taimake ka ka zama ‘dasashe da kafaffe cikin tushen’ Kristi. Ta hakan, za ka iya jimre duk wani gwajin da Shaiɗan zai iya sa ka fuskanta kafin ƙarshen wannan muguwar duniya.—Zab. 1:1-3; Irm. 17:7, 8.

[Akwati/Hotunan da ke shafi na 27]

“Zuwa ga Afisawa”

‘Albarka ga Allah da Uba na Ubangijinmu Yesu Kristi, wanda ya albarkace mu da kowace albarkan ruhaniya cikin sammai cikin Kristi: kamar yadda ya zaɓe mu a cikinsa tun kafin kafawar duniya, domin mu kasance masu-tsarki marasa-aibi a gabansa cikin ƙauna: bayan da ya rigaya ya ƙadara mu da zaman ’ya’yansa ta wurin Yesu Kristi, bisa ga yardan nufinsa, zuwa yabon darajar alherinsa, wanda ya kyautar mana a lokacin da ya mai da mu karbabbu cikin Ƙaunatacen: wanda muna da fansarmu a cikinsa ta wurin jininsa, gafarar laifofinmu, gwargwadon wadatar alherinsa, wanda ya yawaita shi zuwa gare mu cikin dukan hikima da kaifin hankali, da ya sanar mana da asirin nufinsa, bisa ga yardansa da ya nufa a cikinsa zuwa wakilci na cikar wokatai, shi tattara dukan abu cikin Kristi, abubuwan da ke cikin sammai, da abubuwan da ke bisa duniya; a cikinsa, na ke cewa.’—Afis. 1:3-10.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba