Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 1/15 pp. 28-32
  • An Ɗaukaka Yadda Jehobah Yake Sarauta!

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • An Ɗaukaka Yadda Jehobah Yake Sarauta!
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Sarautar Allah Bisa Isra’ila
  • Sakamakon Sarautar ’Yan Adam
  • Sabuwar Al’umma a Ƙarƙashin Sarautar Allah
  • Yadda Jehobah Yake Sarauta a Yau
  • Sarautar Jehobah ta Yi Nasara
  • Sarautar Shaiɗan Ba Za Ta Yi Nasara ba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Mulkin Allah—Sabuwar Sarauta Ta Duniya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Mene ne Mulkin Allah?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Me Ya Sa Muke Bukatar Mulkin Allah?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2020
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 1/15 pp. 28-32

An Ɗaukaka Yadda Jehobah Yake Sarauta!

“Maɗaukaki yana riƙe da sarauta a cikin mulkin mutane.”—DAN. 4:17.

1, 2. Waɗanne dalilai ne suka sa sarautar ’yan Adam ta faɗi ras?

BABU shakka, sarautar ’yan Adam ba ta yi nasara ba! Ainihin dalilin da ya jawo hakan shi ne, mutane ba su da hikimar yin sarauta da kyau. Kasawar sarautar ’yan Adam a bayyane take musamman a yau da masu sarauta da yawa ‘sun zama masu-son kansu, masu-son kuɗi, masu-ruba, masu-girman kai, marasa-tsarki, masu-baƙar zuciya, masu-tsegumi, marasa-kamewa, masu-zafin hali, marasa-son nagarta, masu-cin amana, masu-kumbura.’—2 Tim. 3:2-4.

2 Tun da daɗewa, iyayenmu na farko sun ƙi sarautar Allah. Ta yin haka, wataƙila sun yi tunanin cewa suna zaɓan ’yancin kai. Amma gaskiyar ita ce, suna miƙa kansu ne ga sarautar Shaiɗan. Shekaru dubu shida ta gurguwar gudanarwa na ’yan Adam, wadda take ƙarƙashin tasirin Shaiɗan “mai-mulkin wannan duniya,” ta jefa mu cikin yanayi mafi muni a tarihin ’yan Adam. (Yoh. 12:31) Sa’ad da yake kalami a kan yanayin ’yan Adam a yau, littafin nan The Oxford History of the twentieth Century ya ce “neman duniya mai kyau” ba shi da amfani. Ya bayyana: “Ba wai kawai ba za ta taɓa samuwa ba ne, amma yin ƙoƙarin ƙafa ta zai kai ga bala’i, mulkin kama karya, da kuma yaƙi.” Wannan ya nuna sarai cewa sarautar ’yan Adam ta faɗi ras!

3. Me za mu ce game da yadda Allah zai yi sarauta da a ce Adamu da Hauwa’u ba su yi zunubi ba?

3 Abin baƙin ciki, iyayenmu na farko sun ƙi sarautar Allah wadda ita kawai za ta yi nasara! Hakika, ba mu san yadda Jehobah zai tsara sarautarsa a duniya ba da a ce Adamu da Hauwa’u sun kasance da aminci a gare shi. Amma dai, za mu kasance da tabbaci cewa sarautar Allah da ’yan Adam suka amince da ita za ta kasance na ƙauna da rashin son kai. (A. M. 10:34; 1 Yoh. 4:8) Domin hikimar Allah da babu kamarta, za mu kuma kasance da tabbaci cewa da ’yan Adam sun kasance a ƙarƙashin sarautar Jehobah, da an guje wa dukan kurakuran da sarautar ’yan Adam ta jawo. Da sarautar Allah ta yi nasara wajen “biya wa kowane mai-rai muradinsa.” (Zab. 145:16) A taƙaice, da za ta zama kamiltacciyar sarauta. (K. Sha 32:4) Abin baƙin ciki shi ne, ’yan Adam sun ƙi ta!

4. Yaya yawan yadda aka ƙyale Shaiɗan ya yi sarauta?

4 Har ila, yana da kyau mu tuna cewa ko da yake Jehobah ya ƙyale ’yan Adam su yi sarautar kansu, ba wai ya yi watsi da ikonsa na yin sarauta bisa halittunsa ba. An tilasta wa har Sarkin Babila mai iko ya gane cewa, “Maɗaukaki yana riƙe da sarauta a cikin mulkin mutane.” (Dan. 4:17) A ƙarshe, Mulkin Allah zai sa a yi nufinsa. (Mat. 6:10) Hakika, a wannan ɗan lokaci, Jehobah ya ƙyale Shaiɗan ya aikata a matsayin “allah na wannan zamani” domin ya ba da tabbatacciyar amsa ga batutuwa da wannan mai hamayya ya ta da. (2 Kor. 4:4; 1 Yoh. 5:19) Duk da haka, Shaiɗan bai taɓa aikata fiye da abin da Jehobah ya ƙyale ba. (2 Laba. 20:6; gwada Ayuba 1:11, 12; 2:3-6.) Da akwai wasu mutane da suka zaɓi su miƙa kansu ga Allah a kowane lokaci, ko da yake suna zama a duniyar da babban Maƙiyin Allah yake sarauta.

Sarautar Allah Bisa Isra’ila

5. Wane alkawari ne Isra’ila ta yi ga Allah?

5 Daga zamanin Habila har zuwa lokacin da aka kafa al’ummar Isra’ila, mutane da yawa masu aminci sun bauta wa Jehobah kuma sun yi biyayya ga umurninsa. (Ibran. 11:4-22) A zamanin Musa, Jehobah ya ɗauki alkawari da zuriyar Yakubu, kuma suka zama al’ummar Isra’ila. A shekara ta 1513 K.Z., Isra’ilawa suka miƙa kansu da zuriyarsu ga amincewa da Jehobah a matsayin Sarki, suna cewa: “Abin da Ubangiji ya faɗi duka mu a yi.”—Fit. 19:8.

6, 7. Menene ya bayyana sarautar Allah bisa Isra’ila?

6 Jehobah yana da manufa da ta sa ya zaɓi Isra’ilawa su zama mutanensa. (Karanta Kubawar Shari’a 7:7, 8.) Wannan zaɓin ya shafi fiye da lafiyar Isra’ilawa. Ya shafi sunan Allah da ikon mallakarsa, kuma sune suka fi muhimmanci. Isra’ila za ta ba da shaida ga gaskiyar cewa Jehobah ne Allah makaɗaici na gaskiya. (Isha. 43:10; 44:6-8) Shi ya sa Jehobah ya gaya wa al’ummar: “Kai al’umma mai-tsarki ne ga Ubangiji Allahnka, Ubangiji kuma ya zaɓe ka ka zama al’umma keɓaɓiya gareshi daga cikin dukan al’umman da ke bisa fuskar duniya.”—K. Sha 14:2.

7 Yadda Allah ya yi wa Isra’ilawa ja-gora ya nuna cewa ya yi la’akari da ajizancinsu. Duk da haka, dokokinsa cikakku ne kuma sun nuna halayen wanda Ya ba da su. Dokokin Jehobah da aka ba da ta hanyar Musa sun nuna cewa Allah mai tsarki ne, yana son adalci, yana a shirye ya gafarta, kuma shi mai haƙuri ne. Daga baya, a zamanin Joshua da tsaransa, al’ummar ta yi biyayya ga dokokin Jehobah kuma ta more salama da albarka ta ruhaniya. (Josh. 24:21, 22, 31) Wannan lokacin a tarihin Isra’ila ya nuna cewa sarautar Jehobah ta yi nasara.

Sakamakon Sarautar ’Yan Adam

8, 9. Wane roƙo ne da bai dace ba Isra’ilawa suka yi, da wane sakamako?

8 Amma, da shigewar lokaci Isra’ilawa suka riƙa juya wa sarautar Allah baya kuma suka yi rashin kāriyarsa. Daga baya, ta hanyar annabi Sama’ila, Isra’ila ta ce tana son sarki ɗan Adam. Jehobah ya gaya wa Samai’ila ya ba su abin da suke so. Amma, Jehobah ya daɗa: “Ba kai suka ƙi ba, ni ne suka ƙi, kada in yi sarki a bisansu.” (1 Sam. 8:7) Ko da yake Jehobah ya ƙyale Isra’ila ta samu sarki da ake gani, ya gargaɗe su cewa sarautar mutum za ta kawo mugun sakamako.—Karanta 1 Sama’ila 8:9-18.

9 Tarihi ya nuna gaskiyar gargaɗin Jehobah. Sarautar mutum ta jawo wa Isra’ila matsaloli masu tsanani, musamman idan sarkin ya kasance marar aminci. Da wannan misalin na Isra’ila, ba abin mamaki ba ne cewa a dukan tarihi, sarautar ’yan Adam da ba su san Jehobah ba ta kasa kawo sakamako mai kyau na dindindin ba. Hakika, wasu ’yan siyasa sun roƙi albarkar Allah a kan ƙoƙarce-ƙoƙarcensu don su cim ma salama da kwanciyar hankali, amma yaya Allah zai albarkaci waɗanda suka ƙi miƙa kai ga sarautarsa?—Zab. 2:10-12.

Sabuwar Al’umma a Ƙarƙashin Sarautar Allah

10. Me ya sa aka canja Isra’ila a matsayin al’ummar da Allah ya zaɓa?

10 Al’ummar Isra’ila ta nuna cewa ba ta son ta bauta wa Jehobah da aminci. Daga baya, sun ƙi Almasihun da Allah ya naɗa, kuma Jehobah ya ƙi su kuma ya faɗi cewa zai canja su da rukunin mutanen da suke cikin sabuwar al’umma. Saboda haka, a shekara ta 33 A.Z., an kafa ikilisiyar Kirista na shafaffu masu bauta wa Jehobah. Wannan ikilisiya, ita ce sabuwar al’umma da ke ƙarƙashin ikon Jehobah na sarauta. Bulus ya kira ta “Isra’ila na Allah.”—Gal. 6:16.

11, 12. Waɗanne kamani ne na kula yake tsakanin Isra’ila da kuma “Isra’ila na Allah”?

11 Da akwai bambanci da kuma kamanni tsakanin al’ummar Isra’ila na asali da sabuwar “Isra’ila na Allah.” Ba kamar Isra’ila ta dā ba, ikilisiyar Kirista ba ta da sarki ɗan Adam, kuma ba ta bukatan ta miƙa hadayu na dabbobi a madadin masu zunubai. Kamani ɗaya da yake tsakanin al’ummar Isra’ila da ikilisiyar Kirista shi ne tsarin dattawa. (Fit. 19:3-8) Irin waɗannan dattawa Kirista ba sa sarauta bisa garken. Maimakon haka, suna kula da ikilisiya ne kuma suna ba da kansu sosai wajen yi wa ayyukan ikilisiya ja-gora. Suna bi da kowane mutum a cikin ikilisiya da ƙauna, kuma suna daraja kowa.—2 Kor. 1:24; 1 Bit. 5:2, 3.

12 Ta wajen yin bimbini a kan sha’anin da Allah ya yi da Isra’ila, waɗanda suke cikin “Isra’ila na Allah” da kuma ‘waɗansu tumakinsu’ suna godiya sosai ga Jehobah da kuma sarautarsa. (Yoh. 10:16) Alal misali, tarihi ya nuna cewa sarakunan Isra’ila sun rinjayi talakawansu sosai a hanyoyi masu kyau ko marar kyau. Wannan ya nuna cewa ko da yake waɗanda suke ja-gora tsakanin Kiristoci ba sarakuna ba ne kamar waɗannan sarakuna na dā, dole ne a koyaushe su riƙa kafa misali mai kyau na bangaskiya.—Ibran. 13:7.

Yadda Jehobah Yake Sarauta a Yau

13. Wane abu mafi muhimmanci ne aka cim ma a shekara ta 1914?

13 Kiristoci a yau suna yin shela ga duniya cewa sarautar ’yan Adam ta kusa kai ƙarshenta. A shekara ta 1914, Jehobah ya kafa Mulkinsa a sama a ƙarƙashin Sarkin da ya naɗa, Yesu Kristi. A wannan lokacin, ya ba Yesu iko “a kan nasara ya fita, garin yin nasara kuma.” (R. Yoh. 6:2) An gaya wa sabon Sarki da aka naɗa cewa: “Ka ci sarauta a tsakiyar maƙiyanka.” (Zab. 110:2) Abin baƙin ciki, al’ummai a kai a kai sun ƙi su miƙa kai ga sarautar Jehobah. Sun ci gaba da aikatawa kamar ‘babu Jehobah.’—Zab. 14:1.

14, 15. (a) Ta yaya Mulkin Allah take sarauta a kanmu a yau, kuma domin hakan, waɗanne tambayoyi ne ya kamata mu yi wa kanmu? (b) Ta yaya ake ganin cewa sarautar Allah ta fi kyau har a yau?

14 Har ila da sauran shafaffu ƙalilan na “Isra’ila na Allah,” kuma a matsayin ’yan’uwan Yesu sun ci gaba da aikata a matsayin “manzanni . . . madadin Kristi.” (2 Kor. 5:20) An naɗa su a matsayin rukunin bawan nan mai aminci da hikima don su kula kuma su yi tanadin abinci na ruhaniya ga shafaffu da kuma taron Kiristoci da suke ƙaruwa da yanzu sun ƙunshi miliyoyi da suke da begen yin rayuwa a duniya har abada. (Mat. 24:45-47; R. Yoh. 7:9-15) Ana ganin albarkar Jehobah a kan wannan shirin ta wajen ni’ima na ruhaniya da masu bauta ta gaskiya suke morewa a yau.

15 Ya kamata kowanenmu ya tambayi kansa: ‘Na fahimci hakkoki da ya kamata na ɗauka a cikin ikilisiyar Kirista? Ina tallafa wa yadda Jehobah yake sarauta da kyau kuwa? Ina alfaharin zama talakan sarautar Mulkin Jehobah? Na ƙuduri aniya na ci gaba da gaya wa mutane game da Mulkin Allah daidai ƙarfi na kuwa?’ A matsayin rukuni, muna ba da kanmu da yardan rai mu bi ja-gorar da Hukumar Mulki take ba da wa kuma mu ba da haɗin kai ga dattawa da aka naɗa a cikin ikilisiyoyi. A irin waɗannan hanyoyi, mun nuna cewa muna amincewa da sarautar Allah. (Karanta Ibraniyawa 13:17.) Miƙa kai da yardan rai yana kawo haɗin kai na musamman a wannan duniya da take rabe. Yana kawo salama da adalci kuma yana jawo yabo ga Jehobah, hakan na nuna cewa sarautarsa ta fi kyau.

Sarautar Jehobah ta Yi Nasara

16. Ya kamata kowannenmu a yau ya tsai da wace shawara?

16 Lokaci yana gabatowa sosai da za a magance batutuwa da aka ta da a gonar Adnin. Saboda haka, yanzu ne lokacin da mutane za su tsai da shawara. Kowanne mutum zai tsai da shawara ko zai yi na’am da sarautar Jehobah ko kuma ya manne wa sarautar ’yan Adam. Gata ce a gare mu mu taimaka wa masu tawali’u su tsai da shawara mai kyau. Ba da daɗewa ba a Armageddon, sarautar Jehobah za ta sake gwamnatocin ’yan Adam da take ƙarƙashin rinjayar Shaiɗan gaba ɗaya. (Dan. 2:44; R. Yoh. 16:16) Sarautar ’yan Adam za ta zo ƙarshenta, kuma Mulkin Allah zai yi sarauta bisa dukan duniya. A cikakkiyar ma’anar wannan kalmar, za a ɗaukaka sarautar Jehobah.—Karanta Ru’ya ta Yohanna 21:3-5.

17. Waɗanne abubuwa ne suka taimaka wa masu tawali’u su tsai da shawara mai kyau game da sarauta?

17 Ya kamata waɗanda har yanzu ba su tsai da shawarar bin Jehobah ba, cikin addu’a su yi la’akari da amfanin da hanyar sarauta ta Allah za ta kawo ga ’yan Adam. Sarautar ’yan Adam ta kasa magance matsalolin aikata laifi, har da ta’addanci. Sarautar Allah za ta cire dukan mugaye daga duniya. (Zab. 37:1, 2, 9) Sarautar ɗan Adam ta ci gaba da jawo yaƙe-yaƙe, amma sarautar Allah za ta sa “yaƙoƙi su ƙare har iyakar duniya.” (Zab. 46:9) Sarautar Allah za ta mai do da salama tsakanin mutane da dabbobi! (Isha. 11:6-9) Talauci da kuma yunwa abubuwa ne da ake gani sosai a ƙarƙashin sarautar ’yan Adam, amma sarautar Allah za ta kawar da su. (Isha. 65:21) Ko ’yan Adam masu sarauta da suke da nufin kirki ba su iya kawar da cuta da mutuwa ba, amma a ƙarƙashin sarautar Allah, tsofaffi da masu ciwo za su yi farin cikin komowa cikin ƙuruciyarsu. (Ayu. 33:25; Isha. 35:5, 6) Hakika, duniya za ta zama aljanna inda za a yi tashin matattu.—Luk 23:43; A. M. 24:15.

18. Ta yaya za mu nuna cewa mun gaskata cewa yadda Allah yake sarauta ya fi kyau?

18 Hakika, sarautar Allah za ta kawo ƙarshen dukan lahani da Shaiɗan ya jawo sa’ad da ya rinjayi iyayenmu na farko su juya wa Mahaliccinsu baya. Kuma ka yi tunani, shekaru dubu shida ke nan da Shaiɗan yake ta yin ɓarna, amma ta wurin Kristi, Allah zai kawar da dukan wannan ɓarnar cikin shekara dubu ɗaya! Wannan tabbaci ne sosai cewa sarautar Allah ta fi kyau! A matsayin Shaidun Allahnmu, mun amince da shi a matsayin Sarkinmu. Saboda haka, bari mu nuna a kowace rana, hakika kowane sa’a na rayuwarmu cewa mu masu bauta wa Jehobah ne, talakawan Mulkinsa ne, kuma muna alfaharin zama Shaidunsa. Bari mu yi amfani da kowane zarafi mu gaya wa dukan mutane da za su saurara cewa sarautar Jehobah ce ta fi kyau.

Game da Sarautar Allah, Menene Muka Koya Daga Karanta . . .

• Kubawar Shari’a 7:7, 8?

• 1 Sama’ila 8:9-18?

• Ibraniyawa 13:17?

• Ru’ya ta Yohanna 21:3-5?

[Hotuna da ke shafi na 29]

Jehobah a koyaushe ya ci gaba da sarautarsa

[Hoton da ke shafi na 31]

Miƙa kai da yardan rai ga yadda Jehobah yake sarauta na kawo haɗin kai a dukan duniya

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba