Kasancewa da Amincewar Allah Duk da Canje-Canje na Rayuwa
KANA fuskantar canje-canje a rayuwarka? Yana yi maka wuya ka amince da waɗannan canje-canje? Yawancinmu mun kasance ko kuma za mu kasance cikin irin wannan yanayi. Wasu misalai na abubuwa da suka faru a dā suna iya taimaka mana mu san halaye da za su kasance da amfani.
Alal misali, ka yi la’akari da Dauda da kuma canje-canje masu yawa da ya fuskanta. Shi yaro ne makiyayi sa’ad da Sama’ila ya naɗa shi sarki mai jiran gado. Sa’ad da yake matashi, ya ba da kansa ya yi faɗa da Goliyat, katon nan ɗan Filistiya. (1 Sam. 17:26-32, 42) Daga baya, aka gaya wa Dauda matashi ya je ya zauna a fadan Sarki Saul, kuma aka naɗa shi shugaban rundunar sojoji. Dauda bai taɓa tunanin cewa zai fuskanci dukan waɗannan canje-canje a rayuwarsa ba; balle ya hangi abin da zai faru a nan gaba ba.
Dangantakar Dauda da Saul ta ɓace sosai. (1 Sam. 18:8, 9; 19:9, 10) Don ya ceci ransa, Dauda ya yi zaman gudun hijira na shekaru da yawa. Sa’ad da yake sarautar Isra’ila, yanayinsa ya canja sosai, musamman bayan da ya yi zina, kuma ta wajen yin ƙoƙarin ya ɓoye wannan zunubi, ya yi kisa. Domin zunuban da ya yi, ya fuskanci masifu a cikin iyalinsa. Alal misali, Dauda ya fuskanci tawaye daga wajen ɗansa Absalom. (2 Sam. 12:10-12; 15:1-14) Har ila, bayan da Dauda ya tuba daga zunubansa na zina da kisa, Jehobah ya gafarta masa kuma ya sake samun amincewar Allah.
Yanayinka yana iya canjawa. Rashin lafiya, talauci, ko kuma matsaloli na iyali, har ma ayyukanmu suna iya canja rayuwarmu. Waɗanne halaye ne za su taimaka mana mu jimre da irin waɗannan ƙalubalen?
Sauƙin Kai Yana Taimaka Mana
Sauƙin kai ya ƙunshi halin miƙa kai. Sauƙin kai na gaske yana taimaka mana mu ga kanmu yadda muke da gaske da kuma yadda wasu suke. Ta wajen guje wa raina halaye da kuma nasarorin wasu, za mu so su da kuma abin da suke yi sosai. Hakazalika, sauƙin kai zai taimaka mana mu fahimci dalilin da ya sa wani abu ya faru da mu da kuma yadda za mu bi da yanayin.
Jonatan, ɗan Saul, misali ne mai kyau a gare mu. Aukuwa da suka fi ƙarfinsa sun canja yanayinsa. Sa’ad da Sama’ila ya gaya wa Saul cewa Jehobah zai tsige shi daga mulkin, bai ce Jonatan ba ne zai zama sarki ba. (1 Sam. 15:28; 16:1, 12, 13) Allah ya zaɓi Dauda a matsayin sarkin Isra’ila maimakon Jonatan. A wasu hanyoyi, rashin biyayyar Saul ta shafi Jonatan. Ko da yake ba ruwansa da abin da Saul ya yi, Jonatan ba zai gaji matsayin ubansa ba. (1 Sam. 20:30, 31) Yaya Jonatan ya aikata game da wannan yanayin? Ya riƙe Dauda ne a zuciya domin rasa wannan gatan da ya yi, kuma ya soma kishinsa? A’a. Ko da ya girmi Dauda kuma ya fi shi wayo, Jonatan ya ɗaukaka shi cikin aminci. (1 Sam. 23:16-18) Sauƙin kai ya taimaka masa ya fahimci wanda yake da albarkar Allah, kuma bai “aza kansa gaba da inda ya kamata” ba. (Rom. 12:3) Jonatan ya fahimci abin da Jehobah yake bukata a gare shi kuma ya amince da shawarar da Ya yanke a kan batun.
Hakika, canje-canje da yawa suna kawo wasu matsaloli. A wani lokaci, Jonatan ya yi sha’ani da maza biyu da suka yi kusa da shi. Na ɗaya shi ne abokinsa Dauda, sarki mai jiran gado, wanda Jehobah ya zaɓa. Na biyun kuma shi ne Saul, mahaifinsa, wanda Jehobah ya ƙi amma har ila yana sarauta. Babu shakka, wannan yanayin ya dami Jonatan sosai, yayin da ya yi ƙoƙarin ya kasance cikin amincewar Jehobah. Canje-canje da muke fuskanta suna iya damunmu kuma su sa mu tsoro. Amma idan muka ƙoƙarta muka fahimci ra’ayin Jehobah, za mu iya ci gaba da bauta masa da aminci yayin da muke jimrewa da canje-canjen.
Muhimmancin Filako
Filako ya ƙunshi mutum ya san kasawarsa. Filako da sauƙin kai ba sa nufin abu ɗaya. Mai yiwuwa mutum mai sauƙin kai ba zai san kasawarsa ba.
Dauda mai filako ne. Ko da yake Jehobah ya zaɓe shi ya zama sarki, shekaru da yawa Dauda bai hau karagar mulkin ba. Littafi Mai Tsarki bai ce Jehobah ya bayyana wa Dauda dalilin wannan jinkirin ba. Duk da haka, ko da yake wannan yanayin yana iya gajiyarwa, hakan bai dame shi ba. Ya san kasawarsa, kuma ya fahimci cewa Jehobah wanda ya ƙyale wannan yanayin zai bi da al’amura yadda ya kamata. Saboda haka, Dauda bai kashe Saul ba don ya ceci ransa, kuma ya hana abokin tafiyarsa, Abishai yin hakan.—1 Sam. 26:6-9.
A wani lokaci, wani yanayi zai iya tasowa a cikin ikilisiyarmu da ba mu fahimta ba ko kuma muna ganin ba a bi da yanayin ba a hanya da ta fi dacewa. Shin cikin filako za mu fahimci cewa Yesu ne Shugaban ikilisiya kuma yana aiki ta wurin rukunin dattawa da aka naɗa su yi shugabanci? Za mu nuna filako ne, mu san cewa don mu ci gaba da kasancewa cikin amincewar Jehobah muna bukatan mu jira Shi ya yi ja-gora ta wurin Yesu Kristi? Za mu jira cikin filako ne ko da yake yin hakan ba shi da sauƙi?—Mis. 11:2.
Tawali’u Yana Taimaka Mana Mu Kasance da Hali Mai Kyau
Tawali’u sauƙin hali ne. Yana taimaka mana mu jimre mugunta cikin haƙuri ba tare da ƙyama, ƙiyayya, da ɗaukan fansa ba. Yana da wuya a kasance da tawali’u. Yana da kyau a lura cewa cikin wata ayar Littafi Mai Tsarki an gayyaci “masu-tawali’u na duniya” su ‘biɗi tawali’u.’ (Zeph. 2:3) Tawali’u yana da nasaba da sauƙin kai da filako, amma ya ƙunshi wasu halaye, kamar nagarta da sauƙin hali. Mai tawali’u zai iya samun ci gaba na ruhaniya domin yana amincewa da koyarwa da umurni.
Ta yaya tawali’u zai taimaka mana mu bi da canje-canje a rayuwarmu? Wataƙila ka lura cewa mutane da yawa suna ɗaukan canje-canje a matsayin abin da ba shi da kyau. Hakika, suna iya zama zarafin da Jehobah zai ƙara koyar da mu. Rayuwar Musa ta nuna hakan.
Sa’ad da yake ɗan shekara arba’in, Musa ya riga ya samu halaye mafi kyau. Ya san bukatun mutanen Allah kuma ya nuna halin sadaukar da kansa. (Ibran. 11:24-26) Duk da haka, kafin Jehobah ya gaya masa ya fito da Isra’ila daga Masar, Musa ya fuskanci canje-canje da suka kyautata tawali’unsa. Ya gudu daga Masar kuma ya zauna a ƙasar Midiya har tsawon shekaru arba’in, yana aikin makiyayi, kuma shi ba sananne ba ne. Menene sakamakon? Wannan canjin ya sa ya zama mutumin kirki. (Lit. Lis. 12:3) Ya koyi saka al’amura na ruhaniya kan gaba da nasa.
Don mu ga misalin tawali’un Musa, bari mu yi la’akari da abin da ya faru sa’ad da Jehobah ya ce yana son ya ƙi al’ummar da ta yi rashin biyayya kuma ya sa zuriyar Musa ta zama al’umma mai girma. (Lit. Lis. 14:11-20) Musa ya yi roƙo a madadin al’ummar. Kalamansa sun nuna cewa ya damu da sunan Allah da zaman lafiyar ’yan’uwansa, ba son kansa ba. Mutum yana bukatan ya kasance mai tawali’u kafin ya samu irin hakkin da Musa yake da shi a matsayin shugaba da kuma matsakaici na al’ummar. Maryamu da Haruna sun yi gunaguni game da shi, duk da haka Littafi Mai Tsarki ya ce Musa “mai-tawali’u ne ƙwarai, gaba da kowane mutum.” (Lit. Lis. 12:1-3, 9-15) Kamar dai Musa ya jimre da zage-zagensu cikin tawali’u. Yaya abubuwa za su kasance da a ce Musa ba mai tawali’u ba ne?
A wani lokaci, ruhun Jehobah ya shiga cikin wasu maza, kuma ya sa su yin annabci. Joshua, bawan Musa ya yi tunanin cewa waɗannan Isra’ilawan suna yin abin da bai dace ba. Musa kuma, cikin tawali’u ya ɗauki abubuwa bisa ra’ayin Jehobah kuma bai damu ba game da yin rashin ikonsa. (Lit. Lis. 11:26-29) Da a ce Musa ba mai tawali’u ba ne, da ba zai amince da wannan canjin a tsarin Jehobah ba.
Tawali’u ya taimaka wa Musa ya yi amfani da iko mai girma da kuma hakkin da Allah ya ɗanka masa da kyau. Jehobah ya gaya masa ya hau Dutsen Horeb kuma ya tsaya a gaban mutanen. Allah ya yi wa Musa magana ta wurin mala’ika kuma ya naɗa shi a matsayin matsakanci na alkawari. Tawali’un Musa ya taimaka masa ya yi na’am da wannan canji mai girma na iko kuma har ila ya kasance cikin amincewar Allah.
Mu kuma fa? Muna bukatan mu kasance da tawali’u idan muna son mu yi girma. Dukan waɗanda aka ɗanka wa gata da iko a cikin mutanen Allah suna bukatan su zama masu tawali’u. Hakan yana hana mu nuna fahariya sa’ad da muka fuskanci canje-canje kuma yana taimaka mana mu bi da yanayin da halin da ya dace. Yadda muka aikata yana da muhimmanci. Za mu amince da canjin ne? Za mu ɗauka cewa zarafin yin gyara ne? Yana iya zama zarafi na musamman na koyan kasancewa da tawali’u!
A koyaushe za mu samu kanmu muna fuskantar canje-canje a rayuwarmu. A wani lokaci ba shi da sauƙi mu fahimci dalilin da ya sa abubuwa suke faruwa. Kasawa da kuma damuwa suna iya sa ya yi mana wuya mu ci gaba da ɗaukan abubuwa yadda Jehobah yake ɗaukan su. Duk da haka, halaye kamar sauƙin kai, filako, da tawali’u za su taimaka mana mu amince da canje-canjen kuma mu kasance da amincewar Allah.
[Bayanin da ke shafi na 4]
Sauƙin kai na gaske yana taimaka mana mu ga kanmu yadda muke da gaske
[Bayanin da ke shafi na 5]
Tawali’u yana da muhimmanci don ci gabanmu
[Hoton da ke shafi na 5]
Musa ya fuskanci ƙalubale da suka kyautata tawali’unsa