Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 4/1 p. 20
  • ‘Mulkinka Zai Tabbata’

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • ‘Mulkinka Zai Tabbata’
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Dogara Ga Ruhun Allah Sa’ad Da Kake Fuskantar Canji A Yanayin Rayuwa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Darussa Daga Littafin Sama’ila na Biyu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Zunubin Sarki Dauda
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • ‘Ka Koya Mini Na Aikata Nufinka’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 4/1 p. 20

Ka Kusaci Allah

‘Mulkinka Zai Tabbata’

2 SAMA’ILA 7:1-16

ACIKIN tarihi, an cire mutane da yawa da suke mulki daga kan karagarsu. An cire wasu bayan an yi zaɓe, wasu kuma an cire su ƙarfi da yaji. Yesu Kristi kuma fa, Sarkin Mulkin Allah na samaniya? Akwai abin da zai iya hana shi yin mulki a matsayin Sarkin da Allah ya naɗa? Za a iya samun amsar a cikin kalaman da Jehobah ya yi wa Sarki Dauda na Isra’ila ta dā, kamar yadda yake rubuce a cikin 2 Sama’ila sura ta 7.

A farkon surar, mun karanta cewa Dauda ya ji kunya, domin shi sarki ɗan Adam, yana zaune a fada mai kyau, yayin da akwatin Allah yana cikin madaidaicin tanti.a Dauda ya furta muradinsa na gina gida mai kyau, ko haikali ga Jehobah. (Aya ta 2) Amma ba Dauda ba ne zai gina gidan. Ta bakin annabi Natan, Jehobah ya gaya wa Dauda cewa ɗansa ne zai gina haikalin.—Ayoyi ta 4, 5, 12.

Muradin da Dauda yake da shi ya faranta wa Jehobah rai. Domin son ibadar da yake yi kuma bisa ga annabci, Allah ya yi alkawari da Dauda cewa zai ta da wani daga zuriyar sarauta na Dauda wanda zai yi mulki har abada. Natan ya gaya wa Dauda cikakken alkawarin da Allah ya yi masa: “Gidanka fa da mulkinka za su tabbata har abada a gabanka: kursiyinka za ya tsaya har abada.” (Aya ta 16) Wanene wannan Magaji na dindindin na wannan alkawarin, Wanda zai yi mulki har abada?— Zabura 89:20, 29, 34-36.

Yesu Ba-nazarat ya fito ne daga zuriyar Dauda. Sa’ad da yake sanar da haihuwar Yesu, mala’ikan ya ce: “Ubangiji Allah kuma za ya ba shi kursiyi na ubansa Dawuda: za shi yi mulki kuma bisa gidan Yakubu har abada; mulkinsa kuwa ba shi da matuƙa.” (Luka 1:32, 33) Saboda haka alkawarin da aka yi da Dauda ya samu cikawa a kan Yesu Kristi. Saboda haka, yana mulki ne, ba don zaɓin ’yan Adam ba, amma don alkawarin da Allah ya yi wanda ya ba shi damar yin sarauta har abada. Bari mu tuna cewa alkawuran da Allah ya yi suna cika koyaushe.—Ishaya 55:10, 11.

Akwai darussa masu tamani guda biyu da za mu koya daga 2 Sama’ila sura 7. Na farko, muna da tabbaci cewa babu wani abu ko wani mutum da zai iya hana Yesu Kristi yin mulki. Saboda haka, muna da tabbaci cewa zai cika ainihin manufar mulkinsa, wato, ya cika nufin Allah gaba ɗaya a duniya yadda ake yi a sama.—Matta 6:9, 10.

Na biyu, wannan labarin ya koya mana darassi mai daɗaɗa zuciya game da Jehobah. Ka tuna cewa Jehobah ya ga kuma ya daraja muradin da ke zuciyar Dauda. Hakan na ƙarfafa mu mu san cewa Jehobah yana daraja ibadar da muke masa. A wasu lokatai, yanayin da suka fi ƙarfinmu, kamar rashin lafiya ko tsufa, suna iya hana mu cika dukan abin da zuciyarmu ta motsamu mu yi don bauta wa Allah. Idan haka ne, bari mu samu ƙarfafa daga sanin cewa Jehobah yana ganin muradin zuciyar da take cike da son bauta masa.

[Hasiya]

a Akwatin alkawari, akwati ne mai tsarki da aka gina bisa umurni da fasalin da Jehobah ya bayar. Yana wakiltar bayyanuwar Jehobah a Isra’ila ta dā.—Fitowa 25:22.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba