Jimrewa Da Gwaji Ya Ƙarfafa Dogararmu Ga Jehobah
Ada Dello Stritto Ce Ta Ba Da Labarin
Yanzu na gama kofe Nassosin Yini cikin littafin rubutu na. Shekaruna talatin da shida, amma rubuta waɗannan ’yan kalmomi sun ɗauke ni sa’o’i biyu. Menene ya sa ya daɗe haka? Mahaifiyata za ta bayyana.—Joel
MAI gidana da ni mun yi baftisma a matsayin Shaidun Jehobah a shekara ta 1968. Bayan na haifi ’ya’ya lafiyayyu biyu, David da Marc, na haifi ɗanmu na uku, Joel. An haife shi bakwaini a shekara ta 1973 a asibitin da ke garin Binche a ƙasar Belgium, kusan mil arba’in kudu daga Brussels. Nauyinsa laba uku da oza sha biyu. Sa’ad da na bar asibitin, an bukaci Joel ya kasance a asibitin don ya daɗa nauyi.
Bayan ’yan makonni muka ga cewa ɗanmu bai samu sauƙi ba, mai gidana Luigi da ni, muka kai shi wurin likitan yara. Bayan ya gama gwada Joel, likitan ya ce: “Ku yi mini haƙuri. Kamar Joel yana da dukan matsalolin da ’yan’uwansa ba su da shi.” Muka yi shiru na dogon lokaci. A wannan lokacin, na gane cewa ɗanmu yana da rashin lafiya mai tsanani. Sai likitan ya kai mai gidana gefe guda ya gaya masa: “Ɗanku na da ciwon trisomy 21,” wanda ake kuma kira Down syndrome.a
Mun yi baƙin ciki saboda abin da likitan ya faɗa, sai muka shawarta mu ga wani likita. Ya gwada Joel a hankali na kusan sa’a ɗaya ba tare da yin wata magana ba. Ga Luigi da ni, ya zama kamar ba shi da iyaka. Daga baya, likitan ya daga kai ya ce, “Ɗanku zai dogara a gareku sosai.” Da kirki sai ya daɗa, “Amma Joel zai yi farin ciki domin iyayensa suna ƙaunarsa!” Da baƙin ciki, na ɗauki Joel a hankali, sai muka tafi da shi gida. A lokacin, yana watanni biyu.
Tarurrukan Kirista da Hidima Sun Ƙarfafa Mu
Ƙarin gwaji ya nuna cewa Joel yana da ciwon kirji mai tsanani da kuma cuta mai tsanani na rashin bitamin D. Domin zuciyarsa tana da faɗi sosai, tana matse huhunsa kuma hakan na sa shi yawan ciwo. Ba da jimawa ba, lokacin da yake da wata huɗu, Joel ya kamu da cutar namoniya kuma yana bukata ya koma asibiti, inda aka ware shi. Mun yi azaba da muka gan shi yana fama. Mun ji kamar mu riƙe shi a hannunmu kuma mu yi masa sumba, amma a makonni goma na azaba, ba a yarda mu taɓa shi ba ko kaɗan. Luigi da ni ba mu yi komi ba sai dai kallo, da kuma riƙe kanmu, muna addu’a.
A lokacin wannan gwaji, mun ci gaba da halartan tarurruka na ikilisiya tare da David da Marc, a lokacin suna da shekara shida da uku. A gare mu, kasancewa a Majami’ar Mulki yana kamar muna riƙe da hannun Jehobah mai kula. A sa’o’in da muke wurin, kewaye da ’yan’uwanmu Kiristoci, mun ji cewa mun iya zuba nawayarmu a kan Jehobah, kuma mun samu natsuwa a zuci. (Zab. 55:22) Har ma nas da suke lura da Joel sun yi kalami cewa sun lura da yadda halartar tarurrukanmu na Kirista ta taimaka mana mu tsaya da ƙarfi.
A wannan lokaci, na kuma roƙi Jehobah domin ƙarfi na ci gaba da fita hidimar fage. Maimakon zama a gida ina yin kuka, na so yi wa wasu magana kuma in gaya musu dalilin da ya sa dogara ga alkawuran Allah na duniyar da babu ciwo ya ƙarfafa ni. A kowanne lokaci da na samu damar fita hidimar fage, ina jin cewa Jehobah ya amsa addu’o’ina.
“Wannan Abin Mamaki Ne!”
Rana ce mai ban farin ciki yayin da muka samu kawo Joel gida daga asibiti! Amma kashegari, farin cikinmu ta juya zuwa baƙin ciki. Yanayin Joel ya yi tsanani da sauri, sai muka sake komo da shi asibitin. Bayan gwaji da aka yi masa, likitocin suka gaya mana: “Joel yana da aƙalla watanni shida da zai rayu.” Bayan watanni biyu, sa’ad da yake misalin wata takwas, kamar tsinkayan likitocin zai zama gaskiya domin yanayin Joel ya daɗa taɓarɓarewa. Wani likita ya zauna tare da mu ya ce: “Ku yi mini haƙuri. Babu wani ƙarin abu da za mu iya yi masa.” Sai ya daɗa da cewa: “A wannan lokacin, sai Jehobah ne kaɗai zai iya taimake shi.”
Na koma ɗakin da Joel yake a asibitin. Ko da yake ina baƙin ciki kuma na gaji, na ƙudura ba zan taɓa barin gefen gadonsa ba. ’Yan’uwa Kiristoci mata sun yi ta yin canji domin su zauna da ni yayin da Luigi yake lura da yaranmu biyu manyan. Mako ɗaya ya wuce. Sai farat ɗaya, Joel ya samu ciwon zuciya. Nas ɗin suka ruga zuwa cikin ɗakin amma babu abin da za su iya yi domin su taimake shi. Bayan ’yan wasu mintoci, sai ɗaya daga cikinsu ya ce a hankali, “Ya mutu.” A gajiye, na fashe da kuka na kuma bar ɗakin. Na yi ƙoƙari na yi wa Jehobah addu’a amma na rasa kalmomin da zan yi amfani da su don nuna zafi da nake ji. Mintoci sha biyar sun wuce, sai kuma wani nas ya kira ni, “Joel ya soma jin sauƙi!” Ta riƙe ni a hannu ta ce, “Ki zo, yanzu za ki iya ganin shi.” Sa’ad da na komo wurin Joel, zuciyarsa ta soma bugawa kuma! Da sauri sai labarin farfaɗowarsa ta yaɗu ko’ina. Nas da kuma likitoci suka zo su gan shi, da yawa kuma suka ce, “Wannan abin mamaki ne!”
Ƙarin Ci Gaba Mai Ban Mamaki a Shekararsa ta Huɗu
A shekara ta farko na rayuwar Joel, likitan yara ya yi ta maimaita mana cewa, “Joel yana bukatar ƙauna sosai.” Tun da Luigi da ni mun ga kula na ƙauna daga Jehobah bayan haihuwar Joel, mun so mu kewaye ɗanmu da kula na ƙauna ma. Muna da zarafi da yawa na yin haka domin yana bukatar taimakonmu a cikin dukan abubuwa da yake yi.
Kowacce shekara a farkon shekaru bakwai na rayuwar Joel, mun yi fama da jerin aukuwa iri ɗaya. Tsakanin watan Oktoba da Maris, ya yi fama da cututtuka da yawa, kuma muna bukata komar da shi asibitin. Amma kuma, na yi ƙoƙari na keɓe lokaci da yawa don ’ya’yanmu David da Marc. Da haka, suka shaƙu sosai a taimakon Joel ya samu ci gaba, kuma da sakamako mai ban mamaki. Alal misali, likitoci da yawa sun gaya mana cewa Joel ba zai taɓa iya yin tafiya ba. Amma wata rana sa’ad da Joel yake shekara huɗu, ɗan mu Marc ya ce, “Ka zo nan, Joel, ka nuna wa mama cewa za ka iya yi!” Abin mamaki, Joel ya fara yin tafiya! Mun yi farin ciki, kuma mun yi addu’a tare a matsayin iyali don yi wa Jehobah godiya daga zukatanmu. A wasu lokatai, ko da Joel ya yi ’yan ci gaba a wasu hanyoyi, muna yaba masa da farin ciki.
Horar da Shi Game da Allah Daga Jariri ya Kawo Sakamako Mai Kyau
Sau da yawa, muna ɗaukan Joel tare da mu zuwa Majami’ar Mulki. Don tsare shi daga ƙwayoyin cuta da za su iya sa shi yin ciwo da wuri, muna saka shi a cikin keken yara da aka rufe da madubin roba. Duk da zama da yake yi a cikin wannan murfin, yana more kasancewa tare da ikilisiya.
’Yan’uwanmu Kiristoci sun zama abin ƙarfafa a garemu, sun kewaye mu da ƙauna kuma sun ba mu taimako da muke bukata. Wani ɗan’uwa sau da yawa yakan tuna mana kalmomin da ke Ishaya 59:1: “Duba, hannun Ubangiji ba ya yi gajarta ba, har da ba ya iya ceto ba; kunnensa kuwa ba ya yi nauyi ba, har da ba za ya iya ji ba.” Waɗannan kalmomi masu tabbaci sun taimaka mana mu dogara ga Jehobah.
Yayin da Joel yake girma, mun yi ƙoƙari mu sa bautar Jehobah ta zama abu na musamman a rayuwarsa. A kowacce zarafi, muna yi masa magana game da Jehobah a hanyar da za ta sa Joel ya gina dangantaka na ƙauna da Ubansa na samaniya. Mun roƙi Jehobah ya albarkaci ƙoƙarce-ƙoƙarcenmu don horon ya ba da ’ya’ya masu amfani.
Da ya shiga farkon shekarunsa na goma sha, mun yi farin cikin lura cewa Joel yana son gaya wa waɗanda ya sadu da su gaskiyar Littafi Mai Tsarki. Sa’ad da yake samun sauƙi daga wata fiɗa mai tsanani a shekararsa ta sha huɗu, na yi farin ciki matuƙa sa’ad da Joel ya tambaye ni, “Mama, zan iya ba likita littafin nan Kana Iya Rayuwa Har Abada Cikin Aljanna A Duniya?” Bayan ’yan shekaru, aka sake yi wa Joel fiɗa. Mun sani sosai cewa wataƙila ba zai rayu ba. Kafin fiɗar, Joel ya ba wa likitocinsa wasiƙa da muka rubuta tare da shi. Ta bayana matsayinsa a kan yin amfani da jini. Likitan ya tambayi Joel, “Ka kuma amince?” Joel da ƙarfi ya amsa, “E, Likita.” Mun yi alfahari sosai don dogara da ɗanmu ya yi ga mahaliccinsa da kuma ƙudurinsa na faranta masa rai. Ma’aikatan asibitin sun tallafa mana sosai, kuma mun yi godiya sosai.
Ci Gaban Joel a Ruhaniya
Da yake shekara sha bakwai, Joel ya keɓe kansa ga Allah ta wurin yin baftisma. Rana ce da ba za mu taɓa mantawa ba! Ganin ci gabansa ta ruhaniya ta cika mu da farin ciki mai zurfi. Tun daga lokacin ƙaunarsa ga Jehobah da ƙwazonsa ga gaskiya ba ta yi sanyi ba. A gaskiya, ga kowanne da Joel ya sadu da shi, yana faɗan cewa, “Gaskiyar ita ce rayuwata!”
Da yake ƙarshen shekararsa ta goma sha, Joel ya koya yin rubutu da karatu. Ya ɗauki babban ƙoƙari. Kowanne kalma da ya yi ƙoƙarin iya rubutawa nasara ce. Tun daga lokacin, yana soma kowacce rana da yin nazarin nassi na yini daga littafin Examining the Scriptures Daily. Bayan haka, sai ya kofa nassin cikin ɗaya daga cikin littattafan rubutunsa a hankali, wanda war haka ya yi yawa sosai!
A ranakun taro, Joel zai tabbata mun je Majami’ar Mulki da wuri domin yana son ya yi sammako don ya marabci waɗanda suke shigowa cikin majami’ar. Yayin da ake yin taruwai, yana farin cikin yin kalami da kuma yin gwadi. Yana taimaka da kula da makarufo da kuma yin wasu ayyuka. Kowacce mako, idan lafiyar jikinsa ya bar shi, yana raka mu zuwa aikin wa’azi. A shekara ta 2007 aka sanar wa ikilisiya cewa an naɗa Joel a matsayin bawa mai hidima. Mun zubar da hawaye na farin ciki. Wannan albarka ce daga Jehobah!
Mun Shaida Taimakon Jehobah
A shekara ta 1999 mun fuskanci wata jaraba. Wani magagacin direba ya buga motar mu, kuma Luigi ya ji ciwo mai tsanani. An yanke daya daga cikin ƙafafunsa, kuma ya yi fiɗa da yawa a kashinsa na baya. Har yanzu, ta wurin dogara ga Jehobah, mun ji ƙarfafa da yake ba wa bayinsa da suke da bukata. (Filib. 4:13) Ko da shike Luigi ya zama gurgu, mun yi ƙoƙari mu dubi gefensa mai kyau. Domin ba zai iya yin aiki na jiki ba, ya samu lokaci mai yawa na lura da Joel. Wannan ya sa na nemi lokaci sosai ga ayyuka na ruhaniya. Luigi kuma zai iya mai da hankali sosai ga bukatu na ruhaniyar iyalinmu da kuma na waɗanda suke ikilisiyar mu, inda ya ci gaba da yin bauta a matsayin mai tsara ayyukan rukunin dattawa.
Domin yanayin mu, mun yi amfani da yawan lokacin mu tare kamar iyali. Da shigewar lokaci, mun koya zama da labshin hali don kada mu zaci fiye da abin da muke da shi. A kwanakin da muka ji sanyin gwiwa, muna furta damuwanmu ga Jehobah a cikin addu’a. Abin baƙin ciki, yayin da ’ya’yanmu David da kuma Marc suka manyanta kuma suka bar gida, a hankali suka daina bauta wa Jehobah. Muna sa zuciya wata rana za su dawo ga Jehobah.— Luk 15:17-24.
A cikin waɗannan shekaru, mun iya jin taimakon Jehobah da kuma koya yadda za mu dogara a gareshi a dukan kalubale da muka fuskanta. Kalmomin da ke cikin Ishaya 41:13 suna da ƙarfafa a garemu: “Ni Ubangiji Allahnka zan riƙe hannun damanka, in ce maka, Kada ka ji tsoro, ni taimake ka.” Sanin cewa Jehobah yana riƙe da hannun mu da ƙarfi tushen ƙarfafa ne. Hakika, da gaske za mu iya cewa jure da jarabobbi ya ƙarfafa dogararmu a kan Ubanmu mahalicci, Jehobah.
[Hasiya]
a Trisomy 21 lahani ne da ake haifar mutum da shi kuma yana sa girma na hankali ta yi jinkiri. Zanen halitta, wato chromosomes suna zuwa a biyu-biyu, amma yara da ake haifa da trisomy suna da ƙarin zanen halitta a ɗaya cikinsu. Trisomy 21 yana ɓata chromosome 21.
[Hotuna da ke shafi na 16, 17]
Joel tare da mamarsa, Ada
[Hoton da ke shafi na 18]
Ada, Joel, da kuma Luigi
[Hoton da ke shafi na 19]
Joel yana jin daɗin marabtar ’yan’uwa maza da mata a Majami’ar Mulki