Maganar Jehobah Rayayya Ce
Darussa Daga Littattafan Joel da Amos
ABIN da kawai ya faɗa game da kansa shi ne sunansa, wato, “Joel ɗan Pethuel.” (Joel 1:1) A cikin littafin da ke ɗauke da sunansa, Joel ya mai da hankali ne kawai a kan saƙonsa, shi ya sa aka ƙiyasta cewa annabcinsa bai wuce shekara ta 820 K.Z. ba, wato, shekaru tara bayan Uzziah ya zama sarkin Yahuda. Me ya sa Joel bai ce kome ba game da kansa? Wataƙila yana son ya mai da hankali ne a kan saƙon ba ɗan saƙon ba.
A zamanin Uzziah, an naɗa wani da ke zama a Yahuda mai suna Amos wanda “makiyayi ne: mai-gyaran itatuwan [ɓaure],” ya zama annabi. (Amos 7:14) Ba kamar Joel ba wanda annabcinsa a Yahuda ne, an aiki Amos zuwa arewa, wato, masarautar ƙabilu goma na Isra’ila. An kammala littafin Amos kusan shekara ta 804 K.Z., bayan da annabin ya koma Yahuda, kuma an rubuta littafin Amos ne a hanyar da ta fita sarai kuma mai sauƙin fahimta.
ME YA SA AKA YI “KAITON RANAN”?
(Joel 1:1–3:21)
A cikin wahayi, Joel ya ga tsutsa, fara, da kyankyaso da suka kai hari. An kira maharan “al’umma babba, mai-ƙarfi” da kuma “ƙarfafan mazaje.” (Joel 1:4; 2:2-7) Joel ya ce cikin baƙin ciki: “Kaiton ranan!, gama ranar Ubangiji ta kusa, misalin hallaka fa za ta abko daga wurin Mai-iko duka.” (Joel 1:15) Jehobah ya shawarci mazaunan Sihiyona: “Ku juyo mani da dukan zuciyarku.” Idan suka yi haka, Jehobah zai “yi juyayin mutanensa” kuma zai kawar da “na arewa,” wato, ƙwarin da za su kai hari. Kafin zuwan babban ranarsa, Jehobah zai “zuba [ruhunsa] a bisa dukan masu-rai” kuma zai “nuna al’ajabai cikin sammai, da cikin duniya.”—Joel 2:12, 18-20, 28-31.
An ƙalubalanci al’ummai: ‘Su bubbuga garmunansu a yi takuba da su; lauzunansu kuma su yi māsu da su’ kuma su shirya yin yaƙi. An umurce su su zo “kwarin Jehoshaphat,” inda za a yi masu shari’a kuma a halakar da su. “Amma Yahuda za ya tabbata har abada.”—Joel 3:10, 12, 20.
Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:
1:15; 2:1, 11, 31; 3:14—Mecece “ranar Ubangiji”? Ranar Jehobah ita ce ranar da zai hukunta maƙiyansa, wanda hakan zai sa a halaka su kuma a ceci masu bauta ta gaskiya. Alal misali, irin wannan ranar ta faɗa kan Babila ta dā a shekara ta 539 K.Z., sa’ad da Midiya da Farisa suka kame ta. (Ishaya 13:1, 6) Wata “ranar Ubangiji” tana nan tafe, a lokacin da zai hukunta “Babila Babba,” daular duniya na addinin ƙarya.—Ru’ya ta Yohanna 18:1-4, 21.
2:1-10, 28—Ta yaya aka cika annabcin ƙwarin da suka kai hari? Babu wani labari a cikin Littafi Mai Tsarki da ya ambata cewa ƙwari masu yawa da aka kwatanta a cikin littafin Joel sun kai wa ƙasar Ka’ana hari. Saboda haka, annabci ne na abin da ya faru a shekara ta 33 A.Z., sa’ad da Jehobah ya soma zuba ruhunsa a kan mabiyan Kristi kuma suka soma sanar da saƙon da ke baƙanta ran shugabannin addinin ƙarya. (Ayukan Manzanni 2:1, 14-21; 5:27-33) Gata ne mu saka hannu a cikin irin wannan aikin a yau.
2:32—Menene ma’anar ‘kiran sunan Jehobah’? Kiran sunan Allah yana nufin sanin sunan, daraja shi sosai, dogara ga mai sunan, da kuma amincewa da shi.—Romawa 10:13, 14.
3:14—Menene “kwarin yankan shari’a”? Wuri ne na alama inda Jehobah yake yin hukunci. A zamanin Jehoshaphat Sarkin Yahuda, wanda sunansa ke nufin “Jehobah Shi ne Mai Hukunci,” Allah ya ceci Yahuda daga al’ummai da suka kewaye ta ta wajen ruɗar da sojojin. Shi ya sa aka kira wurin “kwarin Jehoshaphat.” (Joel 3:2, 12) A zamaninmu, kwarin yana wakiltar wani wurin da za a tattake al’ummai kamar yadda ake matse ruwan anab.—Ru’ya ta Yohanna 19:15.
Darussa Dominmu:
1:13, 14. Idan muna so mu samu ceto, muna bukatar mu tuba da gaske kuma mu yarda cewa Jehobah ne Allah na gaskiya.
2:12, 13. Tuba na gaskiya zai fito ne daga zuciya. Ya ƙunshi ‘tsaga zuciya” ba yaga ‘tufafi ba’ a zahiri.
2:28-32. A “babbar rana mai-ban razana ta Ubangiji,” wanda “ya kira bisa sunan Ubangiji [ne] za ya tsira.” Muna godiya sosai cewa Jehobah yana ba mutane daga ko’ina ruhunsa, kuma ya sa tsofaffi da yara, maza da mata, su saka hannu a aikin yin annabci, wato, sanar da “ayyuka masu-girma na Allah”! (Ayukan Manzanni 2:11) Yayin da ranar Jehobah take kusatowa, ya kamata mu kasance da “tasarrufi mai-tsarki da ibada”?—2 Bitrus 3:10-12.
3:4-8, 19. Joel ya annabta cewa za a hukunta al’umman da suka kewaye Yahuda domin sun zalunci zaɓaɓɓun mutanen Allah. Don tabbatar da waɗannan kalaman na annabci, Nebuchadnezzar Sarkin Babila ya halaka birnin Tyre. Bayan haka, Alexander mai Girma ya kame ɓangaren ƙasar da ke kewaye da ruwa, kuma an kashe dubban sojojinta da kuma manyan mutane, kuma an sayar da mutane 30,000 zuwa bauta. Filistiyawa sun fuskanci irin wannan yanayin a hannun Alexander da kuma waɗanda suka gaje shi. An halakar da Edom a ƙarni na huɗu K.Z. (Malachi 1:3) Waɗannan annabce-annabcen da suka cika sun ƙarfafa bangaskiyarmu ga Jehobah a matsayin Mai Cika alkawuransa. Kuma sun nuna yadda Jehobah zai bi da al’ummai da suke tsananta wa masu bauta masa a yau.
3:16-21. “Sammai da duniya za su yi rawa,” kuma al’ummai za su fuskanci hukuncin Jehobah. “Amma Ubangiji za ya zama mafaka ga mutanensa,” kuma zai ba su rai a cikin aljanna. Bai kamata ba ne mu ƙudurta cewa za mu manne wa Jehobah yayin da ranarsa ta hukunta wannan muguwar duniyar take kusatowa?
“KA YI SHIRI KA GAMU DA ALLAHNKA”
(Amos 1:1–9:15)
Amos yana da saƙo ga al’ummai maƙiyan Isra’ila da suka kewaye ta, yana kuma da saƙo ga Yahuda da Isra’ila. Za a halaka Suriya, Filistiya, Tyre, Edom, da Mowab domin yadda suka zalunci mutanen Allah. Za a halaka mazauna Yahuda “saboda sun ƙi shari’ar Ubangiji.” (Amos 2:4) Masarautar ƙabilu goma ta Isra’ila fa? Zunubanta sun haɗa da cutar da talakawa, lalata, da kuma rashin daraja annabawan Allah. Amos ya yi gargaɗi cewa Jehobah zai halakar da “bagadan Beth-el” kuma zai “buga gidan damana da gidan rani.”—Amos 3:14, 15.
Duk da hukunci iri-iri da aka yi musu, Isra’ilawa da suke bauta wa gunki sun ci gaba da yin taurin kai. Amos ya ce masu: ‘Ku yi shiri ku gamu da Allahnku.’ (Amos 4:12) Ga Isra’ilawa kuwa, ranar Jehobah tana nufin cewa za su “tafi cikin bauta gaba da Dimashka,” wato, Assuriya. (Amos 5:27) Amos ya fuskanci hamayya daga firist ɗin Bethel amma hakan bai tsoratar da shi ba. Jehobah ya gaya wa Amos cewa: “Matuƙa ta abko ma mutanena Isra’ila ba ni ƙara gafarta masu ba daɗai.” (Amos 8:2) Sheol ko manyan duwatsu ba za su iya kāre su daga hukuncin Allah ba. (Amos 9:2, 3) Duk da haka, akwai alkawarin maidowa. “Zan dawo da mutanena Isra’ila daga bauta,” in ji Jehobah, “za su gina biranen da ke kangaye, su zauna a ciki; za su dasa gonakin anab, su sha ruwansu; za su yi lambuna kuma, su ci anfaninsu.”—Amos 9:14.
Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:
4:1—Su wanene suke wakiltar “shanu na Bashan”? Tudun Bashan, a gabashin Tekun Galili, sanannen wurin kiwon dabbobi ne, har da shanu. Ƙasa mai albarka da suke da ita tana ɗaya daga cikin abubuwan da suka sa hakan. Amos ya kwatanta matan Samariya masu son jin daɗi da shanun Bashan. Waɗannan matan babu shakka suna matsa wa ‘iyayengijinsu,’ ko mazansu, su cuci talakawa don su cika bukatunsu na yin arziki.
5:5—Ta yaya ne Isra’ila ba za ta ‘biɗi Bethel ba’? Yerobowam ya kafa bautar gunki a Bethel. Tun daga wannan lokacin, wannan birnin ya zama cibiyar bautar ƙarya. Gilgal da Beer-sheba suna cikin wuraren da ake bautar ƙarya. Don ta tsira daga bala’in da aka annabta, Isra’ila tana bukatar ta daina zuwa bauta a wuraren nan kuma ta soma biɗar Jehobah.
7:1—Menene “girbe [ciyawa] na sarki” yake nufi? Wataƙila harajin da sarki ya ce a dinga biya ne domin kula da masu hawan dawakinsa da kuma dabbobinsa. Za a biya wannan harajin ne “a loton farkon tsirawan amfanin damana.” Bayan haka, mutane za su iya girbe hatsinsu. Amma kafin su yi haka, sai fari suka taru kuma suka cinye hatsinsu da sauran shuke-shukensu.
8:1, 2—Menene “kwando cike da anfanin damana” ke nufi? Hakan na nufin cewa ranar Jehobah ta kusa. Ana samun amfanin gona ne a ƙarshen damina. Sa’ad da Jehobah ya sa Amos ya ga “kwando cike da anfanin damana,” hakan yana nufin cewa ƙarshen Isra’ila ya kusa. Saboda haka, Allah ya gaya wa Amos: “Matuƙa ta abko ma mutanena Isra’ila; ba ni ƙara gafarta masu ba daɗai.”
Darussa Dominmu:
1:1:3, 6, 9, 11, 13; 2:1, 4, 6. Domin fushin da ya yi da Isra’ila, Yahuda, da kuma al’ummai shida da suka kewaye su ne ya sa Jehobah ya ce: “Ba zan juyadda hukuncinta ba.” Ba za a iya guje wa hukuncin Jehobah ba.—Amos 9:2-5.
2:12. Kada mu sa majagaba, masu kula masu ziyara, masu wa’azi a ƙasashen waje, ko waɗanda suke Bethel da suke aiki tuƙuru su yi sanyin gwiwa ta wajen ariritarsu su bar hidimarsu na cikakken lokaci don su zo su soma rayuwar da yawancin mutane suka ɗauka cewa rayuwar jin daɗi ce. Akasin haka, muna bukatar mu ƙarfafa su su ci gaba da aiki mai kyau da suke yi.
3:8. Kamar yadda mutum zai ji tsoro sa’ad da ya ji rurin zaki, Amos ya ji cewa yana bukatar ya yi wa’azi sa’ad da Jehobah ya ce masa: “Je ka, ka yi ma mutanena . . . annabci.” (Amos 7:15) Ya kamata tsoron Allah ya motsa mu mu zama masu wa’azin saƙon Mulki da kuzari.
3:13-15; 5:11. Da taimakon Jehobah, Amos makiyayi ya ba da “shaida” ga manyan mutane da ba sa damuwa. Hakazalika, Jehobah yana iya shirya mu don mu sanar da saƙon Mulki ko da ƙalubalen yankinmu suna da yawa.
4:6-11; 5:4, 6, 14. Duk da cewa Isra’ilawa sun ci gaba da ƙin ‘komowa’ wurin Jehobah, an aririce su su ‘biɗi Ubangiji, za su rayu kuma.’ Muddin Jehobah cikin haƙuri ya ƙyale wannan muguwar duniyar ta ci gaba da kasancewa, dole ne mu ƙarfafa mutanen da ke cikinta su biɗi Allah.
5:18, 19. Yin “muradin ranar Ubangiji” ba tare da an shirya mata ba sosai wawanci ne. Yanayin mutumin da ya yi haka yana kama ne da mutumin da ya guji zaki kuma ya gamu da wani mugun naman daji, kuma ya sake guduwa sai maciji ya sare shi. Abin hikima ne mu “yi tsaro” a ruhaniyance kuma mu kasance da shiri.—Luka 21:36.
7:12-17. Muna bukatar mu kasance marasa tsoro kuma masu gaba gaɗi wajen sanar da saƙon Allah.
9:7-10. Kasancewa zuriyar ubannin iyalai masu aminci da kuma na waɗanda aka cece su daga ƙasar Masar a matsayin zaɓaɓɓun mutanen Allah, bai hana Isra’ilawa marar aminci su sami rashin amincewar Allah kamar Kushawa ba. Samun amincewar Allah marar son kai, ya dangana ne a kan ‘jin tsoronsa, da kuma aikata adalci,’ ba zuriya ba.—Ayukan Manzanni 10:34, 35.
Abin da Ya Kamata Mu Yi
Ranar da Allah zai hukunta duniyar Shaiɗan ta kusa. Allah ya ba masu bauta masa ruhunsa, kuma ya shirya su don su gargaɗi mutane game da ranarsa da ke zuwa. Bai kamata ba ne mu saka hannu sosai wajen taimaka wa mutane su san Jehobah kuma su ‘kira sunansa’ ba?—Joel 2:31, 32.
“Ku ƙi mugunta,” in ji Amos, “ku ƙaunaci nagarta, ku kafa shari’a a cikin ƙofa.” (Amos 5:15) Yayin da ranar Jehobah take kusatowa, zai zama abin hikima mu kusanci Allah kuma mu keɓe kanmu daga wannan muguwar duniya da kuma tarayyarta marar kyau. Don cim ma haka, akwai darussa na kan kari masu yawa da za mu iya koya daga littattafan Littafi Mai Tsarki na Joel da Amos!—Ibraniyawa 4:12.
[Hoto a shafi na 28]
Joel ya annabta: “Ranar Ubangiji ta kusa”
[Hotuna a shafi na 31]
Kamar Amos, muna bukatar mu kasance masu sanar da saƙon Allah da gaba gaɗi babu tsoro