Ku Bi Gurbin Annabawa—Amos
1. Me ya sa misalin annabi Amos zai iya ƙarfafa mu?
1 Shin ka taɓa ji kamar ba ka cancanci ka yi wa’azi ba saboda ba ka da ilimi ko kuma arziki sosai? Idan haka ne, misalin Amos zai iya ƙarfafa ka. Amos mai kiwon tumaki ne kuma yakan yi noman ƙodago a wasu lokatai a shekara. Duk da haka, Jehobah ya ƙarfafa shi ya yi shelar wani saƙo mai muhimmanci. (Amos 1:1; 7:14, 15) Hakazalika, a yau Jehobah yana yin amfani da masu tawali’u. (1 Kor. 1:27-29) Waɗanne darussa ne za mu iya koya daga annabi Amos da za su taimaka mana a wa’azi?
2. Me ya sa za mu iya yin tsayin daka sa’ad da ake hamayya da mu a wa’azi?
2 Ku Ci Gaba da Yin Tsayin Daka Sa’ad da Kuka Fuskanci Hamayya: Sa’ad da Amaziah, wani firist mai bautar gumaka daga masarautar ƙabila goma da ke arewacin Isra’ila ya ji annabcin Amos, sai ya gaya wa Amos cewa: ‘Je ka gida! Ka ƙyale mu! Muna da namu addini!’ (Amos 7:12, 13) Amaziah ya murɗe maganar annabi Amos don ya sa Sarki Yerobowam ya hana shi yin aikinsa. (Amos 7:7-11) Amma Amos bai ji tsoro ba. A yau, wasu limaman addinai dabam-dabam suna neman goyon bayan masu mulki don su tsananta wa bayin Jehobah. Amma, Jehobah ya ba mu tabbaci cewa babu wani maƙamin da aka ƙera da zai yi mana lahani na dindindin.—Ish 54:17.
3. Waɗanne saƙonni biyu ne muke shelarsu a yau?
3 Ku Yi Shelar Hukuncin Allah da Albarka da Zai Kawo Nan Gaba: Ko da yake Amos ya yi annabci cewa za a hukunta ƙabilu goma na Isra’ila, ya kammala rubutun littafin da ake kira da sunansa da alkawarin da Jehobah ya yi cewa zai dawo da mutanensa ƙasarsu kuma ya albarkace su sosai. (Amos 9:13-15) Mu ma muna yin shelar ‘ranar shari’ar’ Allah a yau, amma wannan sashe ɗaya ne kawai na ‘bishara ta mulki’ da muke yaɗawa. (2 Bit. 3:7; Mat. 24:14) Bayan Jehobah ya halaka miyagu a yaƙin Armageddon, duniya za ta zama aljanna.—Zab. 37:34.
4. Me ya sa muke da tabbaci cewa za mu iya yin nufin Jehobah?
4 Yin wa’azin Mulkin Allah a duniya da ke cike da masu hamayya zai gwada ƙudurinmu na yin nufinsa duk rayuwarmu. (Yoh. 15:19) Duk da haka, muna da tabbaci cewa Jehobah zai ci gaba da taimaka mana mu ƙware wajen yin nufinsa kamar yadda ya yi wa Amos.—2 Kor. 3:5.