Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w04 12/1 pp. 18-22
  • Ka Nemi Jehovah, Mai Bincika Zukata

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Nemi Jehovah, Mai Bincika Zukata
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Allah Ya Gwada Isra’ila
  • Isra’ila—Al’ummar da ta Taɓarɓare
  • Wanda Ya Yi Daidai da Wannan a Zamani
  • “Ku Ƙaunaci Nagarta”
  • Jehovah Ya Yi Hukunci
  • Arzurta Duk da Yunwa ta Ruhaniya
  • Ka Faɗi Maganar Allah Da Gaba Gaɗi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Ku Bi Gurbin Annabawa—Amos
    Hidimarmu Ta Mulki—2013
  • Hukuncin Jehovah A Kan Miyagu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Darussa Daga Littattafan Joel da Amos
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
w04 12/1 pp. 18-22

Ka Nemi Jehovah, Mai Bincika Zukata

“Ku zo gare ni, za ku tsira.”—AMOS 5:4.

1, 2. Me ake nufi sa’ad da Nassosi suka ce Jehovah yakan “dubi zuciya”?

JEHOVAH ALLAH ya gaya wa annabi Sama’ila: “Mutum yakan dubi kyan tsari ne kawai, amma Ubangiji yakan dubi zuciya.” (1 Sama’ila 16:7) Ta Yaya Jehovah yakan “dubi zuciya”?

2 A cikin Nassosi, sau da yawa zuciya ta wakilci abin da mutum yake a ciki—muradinsa, tunaninsa, motsin zuciyarsa da kuma soyayya. Saboda haka, sa’ad da Littafi Mai Tsarki ya ce Allah yana duban zuciya, yana nufin cewa yana duba fiye da yadda mutum yake a waje, yana duban ainihin yadda mutum yake a ciki.

Allah Ya Gwada Isra’ila

3, 4. In ji Amos 6:4-6, wane irin yanayi ne ya kasance a masarautar ƙabilu goma na Isra’ila?

3 Sa’ad da Mai Gwada zuciya ya dubi masarautar ƙabilu goma na Isra’ila a zamanin Amos, me ya gani? Amos 6:4-6 sun yi maganar mutane da suke ‘kwance kan gadajen hauren giwa, suna jin daɗin miƙa jiki a dogayen kujerunsu.’ Suna “cin naman maraƙi da na rago.” Irin waɗannan mutane sun “tsara waƙoƙi, kuma suna “shan ruwan inabi.”

4 A ganin ido, kamar yanayi ne na walwala. A cikin sukunin manyan gidajensu masu kyau, masu arziki suna more abinci da abin sha mafi kyau kuma suna cashewa da waƙoƙi masu daɗi. Suna kuma da “gadajen hauren giwa.” Masana tone ƙasa sun samo hauren giwa da aka sassaƙe masu yawa a Samariya babban birnin masarautar Isra’ila. (1 Sarakuna 10:22) Wataƙila, yawancinsu an manna su a jikin kujeru da kuma jikin bangon gidaje.

5. Me ya sa Allah ya ɓata rai ga Isra’ilawa na zamanin Amos?

5 Rayuwar sukuni da Isra’ilawan suke yi, suna cin abinci masu kyau, suna shan ruwan inabi mai zaƙi, kuma suna sauraron waƙoƙi masu daɗi, ya ɓata wa Jehovah Allah rai ne? Bai ɓata masa rai ba. Ballantana ma, ya ba da irin waɗannan abubuwa da yawa domin mutum ya more rayuwa. (1 Timoti 6:17) Abin da ya ɓata wa Jehovah rai shi ne miyagun muradi na mutanen, da kuma muguwar zuciyarsu, da kuma halayensu na ko oho ga Allah na gaskiya da kuma ’yan’uwansu Isra’ilawa.

6. Yaya ruhaniyar Isra’ila take a zamanin Amos?

6 Waɗanda suke son ‘miƙe jikinsu a kan dogayen kujerunsu, suna cin naman rago, suna shan ruwan inabi, suna ƙirƙiro waƙoƙi’ za su ga abin mamaki. Aka tambayi waɗannan mutane: “Kuna ƙoƙari ku kauce wa wannan rana ta masifa?” Da ya kamata yanayin Isra’ila ya dame su, amma ba su ‘yi makoki saboda lalacewar Yusufu ba.’ (Amos 6:3-6) Jehovah ya hangi fiye da arzikinsu, ya ga cewa Yusufu—ko kuma Isra’ila—yana cikin lalataccen yanayi na ruhaniya. Duk da haka, mutanen suka ci gaba da ayyukan su na yau da kullum ba tare da wata damuwa ba. A yau mutane da yawa suna da irin wannan halin. Za su yarda cewa muna cikin lokatai masu wuya, amma domin bai shafe su ba, ba sa damuwa da abin da ke damun wasu kuma ba sa nuna damuwa ga batun ruhaniya.

Isra’ila—Al’ummar da ta Taɓarɓare

7. Menene zai faru idan mutanen Isra’ila suka ƙi su bi gargaɗin Allah?

7 Littafin Amos ya kwatanta al’umma da ta taɓarɓare, duk da yadda ta bayyana cike da arziki. Domin sun ƙi su saurari gargaɗin Allah kuma su gyara tunaninsu, Jehovah zai yashe su wa magabtansu. Sai Assuriyawa su zo su kwashe su daga gadajensu na hauren giwa kuma su kwashe su zuwa bauta. Ba za su sami rayuwa mai sukuni ba!

8. Ta yaya Isra’ila ta kasance a mummunan yanayi na ruhaniya?

8 Ta yaya ne Isra’ilawa suka kasance a wannan yanayi? Yanayin ya fara ne a shekara ta 997 K.Z., sa’ad da ɗan Sarki Sulemanu Yehobowam ya gāje shi, kuma ƙabilu goma na Isra’ila suka raba gari da ƙabilar Yahuza da Biliyaminu. Sarkin fari na masarautar ƙabilu goma na Isra’ila Yerobowam na I ne, “ɗan Nebat.” (1 Sarakuna 11:26) Yerobowam na 1 ya huɗubantar da mutanen da suke ƙarƙashinsa cewa zuwa Urushalima a bauta wa Jehovah ya yi nisa ainu. Amma, ba don ya damu da mutanen ba ne da gaske. Maimakon haka, yana so ya kāre bukatarsa ne. (1 Sarakuna 12:26) Yerobowam na I yana tsoro ne cewa idan Isra’ilawa sun ci gaba da zuwa haikali a Urushalima kowace shekara domin bukukuwan ɗaukaka Jehovah, daga baya za su juya ga masarautar Yahuza. Saboda ya hana wannan, Yerobowam na I ya kafa maruƙa biyu na zinariya, ɗaya a Dan ɗaya kuma a Betel. Saboda haka, bautar maraƙi ta zama addinin ƙasar, a masarautar Isra’ila.—2 Tarihi 11:13-15.

9, 10. (a) Waɗanne bukukuwan addini ne, Sarki Yerobowam na I ya shirya? (b) Yaya Allah ya ɗauki bukukuwa da ake yi a Isra’ila a zamanin Sarki Yerobowam na II?

9 Yerobowam na I ya yi ƙoƙarin ya daraja sabon addinin. Ya shirya bukukuwa masu kama da waɗanda ake yi a Urushalima. Mun karanta a 1 Sarakuna 12:32: “Yerobowam kuma ya sa a yi idin ran goma sha biyar ga wata na takwas kamar yadda ake yi a Yahuza. Ya miƙa hadayu bisa bagade, haka ya yi a Betel.”

10 Jehovah bai yarda da irin waɗannan bukukuwa na addini ba. Hakika ya bayyana sarai fiye da ƙarni guda bayan haka ta bakin Amos a zamanin sarautar Yerobowam na II, wanda ya zama sarkin masarautar ƙabilu goma na Isra’ila a wajen shekara ta 844 K.Z. (Amos 1:1) In ji Amos 5:21-24, Allah ya ce: “Na ƙi bukukuwanku na addini. Ina ƙyamarsu! Sa’ad da kuka kawo mini hadayun ƙonawa da hadayunku na tsaba, ba zan karɓa ba. Ba kuma zan karɓi turkakkun dabbobinku waɗanda kuka miƙa mini hadayun godiya ba. Ku yi shiru da yawan hargowar waƙoƙinku. Ba na so in saurari kaɗe-kaɗenku da bushe-bushenku. Sai ku sa adalci da nagarta su gudano a yalwace kamar kogin da ba ya ƙafewa.”

Wanda Ya Yi Daidai da Wannan a Zamani

11, 12. Wane kamani yake tsakanin bauta a Isra’ila ta dā da kuma wadda ake yi a Kiristendam?

11 A bayyane yake, Jehovah yana gwada zukatan waɗanda suke yin bukukuwa a Isra’ila kuma ya ƙi waɗannan bukukuwa da sadakarsu. Haka nan a yau, Allah ya ƙi bukukuwan arna na Kiristendam, irin su Kirsimati da Ista. Ga masu bauta wa Jehovah, dangantaka ba za ta taɓa kasancewa ba tsakanin adalci da rashin adalci, babu dangantaka tsakanin haske da duhu.—2 Korantiyawa 6:14-16.

12 Da kamani tsakanin bauta da Isra’ilawa masu bauta wa maraƙi da kuma bauta ta Kiristendam. Ko da yake wasu da suke da’awar su Kiristoci ne sun gaskata gaskiyar Kalmar Allah, bautar Kiristendam ba ƙauna ta gaske ga Allah ce ke motsa ta ba. Idan ƙauna ce, da za ta nace a bauta wa Jehovah “a ruhu, da gaskiya kuma” domin irin bauta da ke faranta masa rai ke nan. (Yahaya 4:24) Ban da haka, Kiristendam ba ta ƙyale “adalci da nagarta su gudano a yalwace kamar kogin da ba ya ƙafewa.” Maimako, sai ta ci gaba da rage tamanin farillan ɗabi’a na Allah. Ta amince da fasikanci da wasu zunubai masu tsanani har ta kai ga shafa albarka ga auren ’yan luwaɗi!

“Ku Ƙaunaci Nagarta”

13. Me ya sa muke bukatar mu bi kalmomin Amos 5:15?

13 Ga dukan waɗanda suke so su bauta wa Jehovah a hanyar da ya amince da ita, ya ce: “Ku ƙi mugunta, ku ƙaunaci nagarta.” (Amos 5:15) Ƙauna da ƙiyayya motsin zuciya ne da suke nuna irin mutane da muke a ciki. Tun da zuciya rikici gare ta, dole ne mu yi iyakar ƙoƙarinmu mu kāre ta. (Karin Magana 4:23; Irmiya 17:9) Idan muka ƙyale zuciyarmu ta saƙa muguwar muradi, sai ta sa mu iske muna ƙaunar mugunta muna ƙin nagarta. Idan kuma muka bi zuciya sai mu yi zunubi, ko yaya himmarmu take ba za ta sa mu sami tagomashin Allah ba. Saboda haka mu roƙi taimakon Allah domin mu ‘ƙi mugunta, mu ƙaunaci nagarta.’

14, 15. (a) A Isra’ila, su waye ne suke yin abin da ke nagari, amma yaya ake yi da su? (b) Ta yaya za mu ƙarfafa waɗanda suke cikin hidima ta cikakken lokaci a yau?

14 Ba dukan Isra’ilawa ba ne suke yin mugunta ba a gaban Jehovah. Alal misali, Yusha’u da Amos sun ‘ƙaunaci nagarta’ kuma sun bauta wa Allah cikin aminci suna annabci. Wasu sun yi alkawarin zama Keɓaɓɓu. A dukan lokacin da suke Keɓaɓɓu, suna guje wa dukan ’ya’yan inabi, musamman ma ruwan inabi. (Littafin Ƙidaya 6:1-4) Yaya wasu Isra’ilawa suka ɗauki tafarkin sadaukar da kai na waɗannan mutane masu aikata nagarta? Amsa mai ban mamaki ta wannan tambayar ta bayyana yadda al’ummar ta taɓarɓare a ruhaniya. Amos 2:12 ta ce: “Amma kun sa keɓaɓɓu shan ruwan inabi, kuka kuma umarci annabawa kada su isar da saƙona.”

15 Da ganin misalin aminci na Keɓaɓɓu da annabawa, waɗannan Isra’ilawa da sun ji kunya sun kuma canja hanyoyinsu. Maimakon haka, suka nemi su karya lagon masu aminci daga ɗaukaka Allah. Kada mu aririci ’yan’uwanmu Kiristoci majagaba, masu wa’azi a ƙasashen waje, masu kula masu ziyara, waɗanda suke cikin iyalin Bethel su bar hidimarsu ta cikakken lokaci domin su koma rayuwa irinta yau da kullum. Mu ƙarfafa su su ci gaba da aikinsu nagari!

16. Me ya sa ruhaniya ta Isra’ilawa ta fi kyau a zamanin Musa fiye da zamanin Amos?

16 Ko da yake Isra’ilawa da yawa sun more rayuwa mai gamsarwa a zamanin Amos, ba su da “tanadi a gun Allah.” (Luka 12:13-21) Kakaninsu sun ci manna kawai cikin daji na shekaru 40. Ba su ci naman shanu ba ko kuma su mimmiƙe a dogayen kujeru na hauren giwa don ragwanci. Duk da haka, Musa ya gaya musu: “Ubangiji Allahnku ya sa albarka a kan dukan ayyukan hannuwanku. . . . Ubangiji Allahnku yana tare da ku a shekara arba’in ɗin nan, ba ku rasa kome ba.” (Maimaitawar Shari’a 2:7) Hakika, Isra’ilawa a kullum sun sami abin da suke bukata da gaske a cikin daji. Mafi muhimmanci ma, Allah ya ƙaunace su, ya kāre su, kuma ya saka musu albarka!

17. Me ya sa Jehovah ya fito da Isra’ila da farko ya kai su Ƙasar Alkawari?

17 Jehovah ya tuna wa Isra’ilawan zamanin Amos cewa Shi ya fito da kakaninsu zuwa Ƙasar Alkawari kuma ya taimake su suka kawar da dukan magabtansu. (Amos 2:9, 10) Me ya sa Jehovah ya fito da Isra’ilawa daga ƙasar Masar zuwa ƙasar alkawari? Domin su yi rayuwar sukuni na ragwanci ne kuma su ƙi Mahaliccinsu? A’a! Maimakon haka, domin su zama ’yantattun mutane ne su bauta kuma su kasance da tsabta a ruhaniya. Amma mazauna masarautar ƙabilu goma na Isra’ila ba su ƙi mugunta, su ƙaunaci nagarta ba. Maimakon haka, suna ɗaukaka gumaka, ba Jehovah Allah ba. Dubi abin kunya!

Jehovah Ya Yi Hukunci

18. Me ya sa Jehovah ya ’yantar da mu a ruhaniya?

18 Allah ba zai ƙyale abin kunya na Isra’ila ba. Ya bayyana matsayinsa sarai, sa’ad da ya ce: “Zan hukunta ku saboda zunubinku.” (Amos 3:2) Waɗannan kalmomi ya kamata su sa mu yi tunani game da cetonmu daga bauta a Masar ta zamani, wato, wannan mugun zamani. Jehovah bai ’yantar da mu ba domin mu biɗi makasudan son kai. Maimakon haka, ya yi haka ne domin mu ɗaukaka shi mu mutane ’yantattu mu yi bauta mai tsabta. Kuma kowannenmu dole ya ba da lissafin yadda ya yi amfani da ’yancin da Allah ya ba sa.—Romawa 14:12.

19. In ji Amos 4:4, 5, Menene yawancin Isra’ilawa suka yi ƙaunarsa?

19 Abin baƙin ciki, yawanci a Isra’ila ba su saurari saƙonni masu ƙarfi na Amos ba. Annabin ya fallasa yanayin rashin lafiyarsu ta ruhaniya, da kalmomi da suke rubuce a Amos 4:4, 5: “Jama’ar Isra’ila, ku tafi Betel, tsattsarkan wuri, ku yi ta zunubi! Ku tafi Gilgal ku ƙara zunubi! . . . Gama irin abin da kuke jin daɗin yi ke nan.” Isra’ilawan ba su da sha’awar kirki. Ba su tsare zukatansu ba. Sakamakon wannan shi ne, yawancinsu sun ƙaunaci mugunta kuma suka ƙi nagarta. Waɗannan masu bauta wa maruƙa masu taurin kai ba za su yi canji ba. Jehovah zai yi hukunci kuma za su mutu cikin zunubansu!

20. Ta yaya mutum zai bi tafarkin da ya jitu da Amos 5:4?

20 Lallai ba zai kasance da sauƙi ba ga dukan wanda yake zaune a Isra’ila wannan zamani kuma ya kasance da aminci ga Jehovah. Ba shi da sauƙi a ƙi bin abin da ake yayi, kamar yadda Kiristoci manya da yara suka sani a yau. Duk da haka, ƙauna ga Allah da kuma sha’awar faranta masa ya motsa wasu Isra’ilawa su yi bauta ta gaskiya. Jehovah ya gayyace su kamar yadda yake a rubuce a Amos 5:4: “Ku zo gare ni, za ku tsira.” Hakazalika a yau, Allah yana nuna jinƙai ga waɗanda suka tuba suka zo gare shi ta wajen cikakken sanin Kalmarsa da kuma yin nufinsa. Ba shi da sauƙi a bi wannan tafarkin, amma yin haka yana kai wa ga rai madawwami.—Yahaya 17:3.

Arzurta Duk da Yunwa ta Ruhaniya

21. Wace yunwa ce ta faɗa wa waɗanda suka ƙi bauta ta gaskiya?

21 Me ke jiran waɗanda ba su goyi bayan bauta ta gaskiya ba? Yunwa mafi muni—yunwa ta ruhaniya! “Lokaci yana zuwa da zan aiko da yunwa a ƙasar. Mutane za su ji yunwa, Ba ta abinci ba, za su ji ƙishi, ba na ruwa ba. Za su ji yunwar rashin samun saƙo daga wurin Ubangiji. Ni Ubangiji ne, na faɗa.” (Amos 8:11) Kiristendam tana fama da irin wannan yunwa ta ruhaniya. Amma, masu zuciyar kirki sun ga ni’imar ruhaniya ta mutanen Allah, kuma suna ruga zuwa ƙungiyar Jehovah. An kwatanta bambancin yanayin da ke tsakanin Kiristendam da bayin Jehovah da waɗannan kalmomi: “Waɗanda suke yin sujada gare ni suna kuwa yin mini biyayya, za su sami wadataccen abinci da abin sha, amma ku za ku sha yunwa da ƙishi. Su za su yi murna, amma ku za ku sha kunya.”—Ishaya 65:13.

22. Me ya sa muke da dalilin murna?

22 Mu bayin Jehovah, muna masu godiya kuwa ga tanadi da kuma albarkatu na ruhaniya? Sa’ad da muka yi nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma littattafan Kirista kuma muka halarci taron ikilisiya, manyan taro, da kuma taron gunduma, muna jin kamar mu yi kuka domin yanayi mai kyau na zuciya. Muna farin ciki domin mun fahimci Kalmar Allah sosai, haɗe da huraren annabcin Amos.

23. Menene waɗanda suke ɗaukaka Allah suke morewa?

23 Domin dukan mutane da suke ƙaunar Allah kuma suna so su ɗaukaka shi, annabcin Amos ya ƙunshi saƙon bege. Ko da yaya yanayinmu na tattalin arziki yake, kowane irin gwaji za mu fuskanta a wannan duniyar, mu da muke ƙaunar Allah muna more abinci da abin sha mafi kyau na ruhaniya. (Karin Magana 10:22; Matiyu 24:45-47) Saboda haka, ɗaukaka ta tabbata ga Allah, wanda yake tanadin dukan abubuwa domin amfaninmu. Saboda haka, mu ƙuduri anniyar yabonsa daga zuciya har abada. Wannan zai kasance gatarmu ta farin ciki idan muka nemi Jehovah, Mai Bincika zukata.

Yaya Za Ka Amsa?

• Wane yanayi ya kasance a Isra’ila a zamanin Amos?

• Wane yanayi ne na masarautar ƙabilu goma na Isra’ila yake da kamani a zamaninmu na yau?

• Wace yunwa ce da aka annabta ta kasance a yau, amma su waye ne abin bai shafe su ba?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba