Hukuncin Jehovah A Kan Miyagu
“Ku yi shirin zuwa gaban Ubangiji.”—AMOS 4:12.
1, 2. Me ya sa za mu kasance da tabbacin cewa Allah zai kawo ƙarshen mugunta?
JEHOVAH zai taɓa kawo ƙarshen mugunta da wahala kuwa a wannan duniya? A farkon ƙarni na 21, tambayar nan ta fi dacewa. Kamar dai duk inda muka juya, sai mu ga tabbacin muguntar mutane. Dubi yadda muke son mu ga duniya da babu mugunta, marar ta’addanci, da kuma marar ɓatanci!
2 Abin farin ciki shi ne za mu iya kasancewa da cikakken tabbaci cewa Jehovah zai kawo ƙarshen mugunta. Halayen Allah sun ba da tabbacin cewa zai ɗauki mataki a kan miyagu. Jehovah mai adalci ne kuma mai gaskiya. A Zabura 33:5, Kalmarsa ta gaya mana: “Yana ƙaunar abin da ke na adalci da gaskiya.” Wata zabura ta ce: “[Jehovah] yana ƙin marar bin doka gaba ɗaya.” (Zabura 11:5) Hakika, Jehovah Allah mai dukan iko mai ƙaunar adalci da gaskiya, ba zai ƙyale abin da ya ƙi ba har abada.
3. Me za a nanata a ƙarin bincika annabcin Amos?
3 Ka yi la’akari da wani dalili kuma da ya sa za mu tabbata cewa Jehovah zai kawar da mugunta. Labarin sha’aninsa na dā ya tabbatar da hakan. Da akwai misalai na musamman na yadda Jehovah yake bi da miyagu cikin littafin Amos a Littafi Mai Tsarki. Ƙara bincika annabcin Amos zai nanata abubuwa uku game da hukuncin Allah. Na farko, ya dace. Na biyu, ba za a iya guje masa ba. Na uku kuma, yana zaɓe, domin Jehovah ya yi wa miyagu hukunci amma kuma yana yi wa waɗanda suka tuba da masu zukatan kirki jinƙai.—Romawa 9:17-26.
Hukuncin Allah Koyaushe Mai Dacewa Ne
4. Ina Jehovah ya aiki Amos, kuma domin menene?
4 A zamanin Amos, al’ummar Isra’ila ta riga ta rabe zuwa masarauta biyu. Ɗayar ta zama masarautar ƙabilu biyu na kudancin Yahuza. Ɗayar kuma ta zama masarautar ƙabilu goma na arewancin Isra’ila. Jehovah ya ba Amos aiki ya zama annabi, ya aike shi daga garinsu Yahuza zuwa Isra’ila. A nan Allah zai yi amfani da Amos wajen yin shelar hukuncinsa.
5. A kan waɗanne al’ummai ne Amos ya fara annabci, kuma domin wane dalili ne guda suka cancanci hukuncin Allah?
5 Amos bai fara aikinsa na shelar hukuncin Jehovah a kan masarautar arewa mai tawaye ba. Maimakon haka, ya fara ne da shelar hukunci a kan al’ummai shida da suke kusa. Waɗannan al’ummai sun haɗa da Suriya, Filistiya, Taya, Edom, Ammon, da kuma Mowab. Amma sun cancanci hukuncin Allah kuwa da gaske? Hakika! Domin tabbatattun magabtan mutanen Jehovah ne.
6. Me ya sa Allah zai kawo masifa bisa Suriya, Filistiya, da kuma Taya?
6 Alal misali, Jehovah ya la’anci Suriyawa domin “sun zalunci mutanen Gileyad.” (Amos 1:3) Suriyawa suka ƙwace yanki daga Gileyad—yanki na Isra’ila na gabas da Kogin Urdun—kuma suka yi wa mutanen Allah rauni ƙwarai a wurin. Filistiya da Taya kuma fa? Filistiya suna da alhakin kwasan Isra’ilawa zuwa bauta, suka sayar da su ga Edomawa, wasu Isra’ilawa kuma suka ƙarasa a hannun mutanen Taya masu cinikin bayi. (Amos 1:6, 9) Dubi—sayar da mutanen Allah zuwa bauta! Ba abin mamaki ba ne da Jehovah zai kawo masifa bisa Suriya, Filistiya, da kuma Taya.
7. Menene Edom, Ammon, da kuma Mowab suke da shi da ya yi daidai da Isra’ila, amma yaya suka yi da Isra’ilawa?
7 Edom, Ammon, da kuma Mowab suna da abu iri ɗaya da Isra’ilawa da kuma junansu. Dukan waɗannan al’ummai uku suna da dangantaka da Isra’ilawa. Edomawa sun fito ne daga Ibrahim ta wurin ɗan tagwayen Yakubu, watau Isuwa. Saboda haka, su ’yan’uwan Isra’ila ne. Ammonawa da Mowabawa sun fito ne daga Lutu, ɗan wan Ibrahim. Amma Edom, Ammon, da kuma Mowab sun yi hulɗa da Isra’ilawa kamar da danginsu suke yi? Ko kaɗan! Edom ya yi amfani da takobi a kan ‘ɗan’uwansa’ babu jinƙai, kuma Ammonawa musamman sun zalunci Isra’ilawa waɗanda aka kama bayi. (Amos 1:11, 13) Ko da yake Amos bai ambata muguntar Mowab kai tsaye a kan mutanen Allah ba, Mowabawa sun daɗe suna hamayya da Isra’ila. Hukunci da zai zo kan waɗannan al’ummai uku da suke dangi zai yi tsanani. Jehovah zai aika musu halaka mai ƙuna.
Ba a Guje wa Hukuncin Allah
8. Me ya sa hukuncin Allah bisa al’ummai shida na kusa da Isra’ila ba abin da za su guje wa ba ne?
8 Babu shakka, al’ummai shida da aka ambata da farko a annabcin Amos sun cancanci hukuncin Allah. Bugu da ƙari, babu wata hanya da za su guje masa. Daga Amos sura 1, aya ta 3, zuwa sura 2, aya ta 1, sau shida Jehovah yake cewa: “Zan hukunta su.” Kamar yadda ya ce, ya hukunta waɗannan al’ummai shida. Tarihi ya tabbatar da cewa waɗannan al’ummai sun sha bala’i. Hakika, huɗu cikinsu—Filistiya, Mowab, Ammon, da kuma Edom—suka daina wanzuwa!
9. Menene mazauna Yahuza suka cancanci a yi musu, kuma me ya sa?
9 Annabcin Amos ya koma kan al’umma ta bakwai, garinsu—Yahuza. Wataƙila waɗanda suke sauraron Amos a masarautar arewaci na Isra’ila sun yi mamakin su ji yana shelar hukunci a kan masarautar Yahuza. Me ya sa mazaunan Yahuza suka cancanci hukunci mai tsanani? Domin ‘sun raina koyarwar [Ubangiji],’ in ji Amos 2:4. Jehovah ba ya ƙyale taka Dokarsa da gangan. A Amos 2:5, ya annabta: “Saboda haka zan aukar da wuta a kan Yahuza ta ƙone kagarar Urushalima.”
10. Me ya sa Yahuza ba za ta guje wa bala’i ba?
10 Yahuza marar aminci ba za ta guje wa wannan bala’i mai zuwa ba. Sau bakwai ke nan Jehovah yake cewa: “Zan hukunta su.” (Amos 2:4) Yahuza ta sha hukunci da aka annabta sa’ad da Babiloniyawa suka halaka ta a shekara ta 607 K.Z. Mun sake ganin cewa miyagu ba za su guje wa hukuncin Allah ba.
11-13. Amos ya yi annabci musamman a kan wace al’umma, kuma wane irin zalunci ya kasance a can?
11 Ba da daɗewa ba annabi Amos ya sanar da hukuncin Jehovah a kan al’ummai bakwai. Duk wanda ya yi tunanin cewa ya gama annabcinsa ke nan ya yi kuskure. Domin Amos yana da sauran annabci! An aike shi ne musamman domin ya yi shelar hukunci mai tsanani a kan masarautar arewacin Isra’ila. Kuma Isra’ila ta cancanci hukuncin domin lalata a ɗabi’a da kuma a ruhaniya na wannan al’ummar.
12 Annabcin Amos ya fallasa zalunci da ya zama ruwan dare a masarautar Isra’ila. Game da wannan, Amos 2:6, 7 suka ce: “Ubangiji ya ce, “Mutanen Isra’ila sun ci gaba da yin zunubi. Hakika, zan hukunta su, don sun sayar da salihai waɗanda suka kāsa biyan bashinsu. Sun kuma sayar da matalauta waɗanda bashinsu bai kai ko kuɗin bi-shanu ba. Sun tattake marasa ƙarfi da kāsassu, suna tunkuɗe matalauta su wuce.”
13 Ana sayar da masu adalci domin azurfa ƙila wannan yana nufin cewa alƙalai da suke karɓan azurfa cin hanci suna hukunta marasa laifi. Waɗanda suka ba da bashi suna sayar da matalauta zuwa bauta a farashin takalmi “bi-shanu,” ƙila don wasu ’yan kuɗi. Waɗannan mutane masu taurin zuciya ‘suna tattake,’ ko kuma sa “kāsassu” su daɗa talaucewa domin waɗannan su zuba ƙura a kansu alamar wahala, ko baƙin ciki, ko kuma wulaƙanci. Ɓatanci ya cika ko’ina da “matalauta” sun fid da rai daga samun shari’ar adalci.
14. Su waye ake zalunta a masarautar ƙabilu goma na Isra’ila?
14 Ka lura da waɗanda ake zalunta. Masu adalci, matalauta, kāsassu na ƙasar. Dokar alkawari ta Jehovah ga Isra’ila ta bukaci a yi juyayin marasa ƙarfi da masu bukata. Irin waɗannan mutane a masarautar ƙabilu goma na Isra’ila yanayinsu yana da muni ƙwarai.
“Ku Yi Shirin Zuwa Gaban Ubangiji”
15, 16. (a) Me ya sa aka yi wa Isra’ilawa gargaɗi, “Ku yi shirin zuwa gaban Ubangiji”? (b) Ta yaya Amos 9:1, 2 suka nuna cewa mugu ba zai tsira daga hukuncin Allah ba? (c) Menene ya faru ga masarautar ƙabilu goma na Isra’ila a shekara ta 740 K.Z.?
15 Tun da lalata da wasu zunubai sun zama ruwan dare a Isra’ila, annabi Amos yana da kyakkyawan dalili na yi wa al’ummar mai tawaye gargaɗi: “Ku yi shirin zuwa gaban Ubangiji.” (Amos 4:12) Isra’ila marar aminci ba za ta guje wa hukuncin Allah da ke zuwa ba, domin sau takwas ke nan Jehovah ya ce: “Zan hukunta su.” (Amos 2:6) Ga miyagu da za su so su ɓuya, Allah ya ce: “Ba wanda zai tsere, ko ɗaya. Ko da za su nutsa zuwa lahira, Zan kama su. Ko sun hau Sama, Zan turo su.”— Amos 9:1, 2.
16 Miyagu ba za su guje wa zartar da hukuncin Jehovah ba bisa kansu ta wajen “nutsa zuwa Lahira” da a alamance yana nufin ƙoƙarin su ɓuya cikin rami. Ba za su tsira daga hukuncin Allah ba kuwa ta wajen ‘hawa sama,’ wato, neman mafaka a kan manyan duwatsu. Gargaɗin Jehovah a bayane yake: Babu inda ba zai iya kai wa ba. Shari’ar Allah ta bukaci masarautar arewa na Isra’ila ta ba da lissafin miyagun ayyukanta. Kuma lokaci kuwa ya cika. A shekara ta 740 K.Z.—kusan shekaru 60 bayan Amos ya yi annabcinsa—Assuriyawa suka ci masarautar arewacin Isra’ila.
Hukuncin Allah Yana Zaɓe
17, 18. Menene Amos sura 9 ta bayyana game da jinƙan Allah?
17 Annabcin Amos ya taimake mu mu ga cewa hukuncin Allah ko da yaushe yana dacewa kuma ba za a iya guje masa ba. Amma littafin Amos ya nuna kuma cewa hukuncin Jehovah yana yin zaɓe. Allah yana iya ganin miyagu kuma ya yi musu hukunci a duk wurin da suka ɓuya. Yana iya gano kuma waɗanda suka tuba masu adalci—waɗanda ya zaɓi ya yi musu jinƙai. An nanata wannan da kyau cikin sura ta ƙarshe na littafin Amos.
18 In ji Amos sura ta 9, aya ta 8, Jehovah ya ce: “Ba zan hallaka dukan jama’ar Yakubu ba.” Kamar yadda aka gani a ayoyi na 13 zuwa 15 Jehovah ya yi alkawari zai ‘dawo da mutanensa ƙasarsu.’ Za a yi musu jinƙai kuma za su samu kwanciyar hankali da ni’ima. Jehovah ya yi alkawarin cewa: “Girbi zai bi bayan huda nan da nan.” Ku yi tunaninsa—za a yi girbi mai yawa har da ba za a iya tattarawa ba har lokacin huɗa ya zagayo!
19. Me ya sami raguwar Isra’ila da kuma Yahuza?
19 Ana iya cewa hukuncin Jehovah a kan miyagu a batun Yahuza da kuma Isra’ila ya yi zaɓe domin waɗanda suka tuba da kuma waɗanda suke da zukatan kirki an yi musu jinƙai. A cikar wannan annabci maidowa da ke Amos sura 9, raguwar da suka tuba daga Isra’ila da kuma Yahuza suka komo daga bautar Babiloniyawa a shekara ta 537 K.Z. Da suka koma ƙasarsu abin ƙauna, sun maido da bauta ta gaskiya. Cikin kwanciyar hankali, suka sake gina gidajensu, kuma suka shuka gonakin inabi da lambuna.
Hukunci Mai Tsanani na Jehovah Zai Zo!
20. Menene bincikenmu na saƙonnin hukunci da Amos ya yi shelarsa ya kamata ya tabbatar mana?
20 Bincikenmu na saƙonnin hukuncin Allah da Amos ya yi shelarsa ya kamata ya tabbatar mana da cewa Jehovah zai kawo ƙarshen mugunta a zamaninmu. Me ya sa za mu gaskata wannan? Na farko, misalai na dā na yadda Allah ya bi da miyagu ya nuna mana yadda zai aikata a zamaninmu. Na biyu, hukuncin Allah a kan masarautar Isra’ila mai ridda ya tabbatar mana cewa Allah zai halaka Kiristendam, sashe mai yawan alhaki na “Babila mai girma,” daular duniya ta addinin ƙarya.—Wahayin Yahaya 18:2.
21. Me ya sa Kiristendam ta cancanci hukuncin Allah?
21 Babu shakkar cewa Kiristendam ta cancanci ta sha hukunci daga Allah. Taɓarɓarewar yanayin addini da na ɗabi’a a cikinta a bayyane suke a fili. Hukuncin Jehovah a kan Kiristendam—da sauran duniyar Shaiɗan—ya dace. Kuma ba wanda za a iya guje masa ba ne domin sa’ad da lokaci ya yi a zartar da hukunci, kalmomin Amos sura 9, aya 1, za su cika: “Ba wanda zai tsere, ko ɗaya.” Hakika, duk inda miyagu suka ɓoye, Jehovah zai same su.
22. Menene aka bayyana sarai game da hukuncin Allah a 2 Tasalonikawa 1:6-8?
22 Hukuncin Allah a kullum mai dacewa ne, ba a kuma guje masa, mai zaɓe ne kuma. Ana iya ganin wannan a kalmomin manzo Bulus: “Allah ya ga adalci ne ya yi sakamakon ƙunci ga waɗanda suke ƙuntata muku, yā kuma ba ku hutu har da mu ma, ku da ake ƙuntata wa ɗin, a ranar bayyanar Ubangiji Yesu daga Sama tare da manyan mala’ikunsa, a cikin wuta mai ruruwa, yana ta saka wa waɗanda suka ƙi sanin Allah, da kuma waɗanda suka ƙi bin bisharar Ubangijinmu Yesu.” (2 Tasalonikawa 1:6-8) “Allah ya ga adalci ne” ya kawo hukuncin mai tsanani a kan waɗanda suke ƙuntata wa bayinsa da ya shafe. Wannan hukunci ba za a guje masa ba, domin miyagu ba za su tsira daga ‘ranar bayyanar Yesu da manyan mala’ikunsa, a cikin wuta mai ruruwa ba.’ Hukuncin Allah zai kasance mai zaɓi domin Yesu zai yi sakamako a kan “waɗanda suka ƙi sanin Allah, da kuma waɗanda suka ƙi bin bishara.” Kuma zartar da hukuncin Allah zai yi jaje ga masu bauta wa Allah waɗanda suka sha ƙunci.
Bege ga Masu Adalci
23. Wane bege ne da ta’aziyya za a samu daga littafin Amos?
23 Annabcin Amos yana ɗauke da saƙon bege da ta’aziyya ga mutane masu zukatan kirki. Kamar yadda aka annabta a cikin littafin Amos, Jehovah bai halaka mutanensa na dā gaba ɗaya ba. Daga baya ya tattaro mutanen Isra’ila da Yahuza daga bauta, ya mai da su ƙasarsu kuma ya albarkace su da ni’ima da kwanciyar hankali. Menene wannan yake nufi ga zamaninmu? Ya ba da tabbaci cewa a lokacin zartar da hukuncin Allah, Jehovah zai sami miyagu ko’ina suka ɓuya kuma zai sami mutanen da ya ga sun cancanci ya yi musu jinƙai ko’ina suke a duniya.
24. A waɗanne hanyoyi ne aka albarkaci bayin Jehovah na zamani?
24 Sa’ad da muke jiran lokacin hukuncin Jehovah ya zo a kan miyagu, menene muka samu mu bayinsa masu aminci? Hakika, Jehovah ya albarkace mu da ni’ima na ruhaniya! Muna morar hanyar bauta da ba ta da ƙarya da yaudara da suka kasance bisa koyarwar ƙarya ta Kiristendam. Jehovah kuma ya albarkace mu da abinci na ruhaniya a yalwace. Ka tuna cewa wannan albarka mai yawa daga Jehovah hakki ne mai girma a gare mu. Allah yana so mu yi wa wasu gargaɗi game da hukuncin da yake zuwa. Muna so mu yi iyaka ƙoƙarinmu mu nemi waɗanda suke ‘da zukatan kirki domin rai madawwami.’ (Ayyukan Manzanni 13:48) Hakika, muna so mu taimaki mutane da yawa su sami wannan ni’ima ta ruhaniya da muke morewa. Kuma muna so su tsira daga zartar da hukuncin Allah da yake zuwa a kan miyagu. Babu shakka, domin mu more waɗannan albarkatai, dole ne mu kasance da zukatan kirki. Kamar yadda za mu gani a talifi na gaba, wannan ma an nanata shi a annabci na Amos.
Yaya Za Ka Amsa?
• Ta yaya annabcin Amos ya nuna cewa hukuncin Jehovah a kullum mai dacewa ne?
• Wane tabbaci ne Amos ya bayar da ya nuna cewa hukuncin Allah ba abin da za a guje masa ba ne?
• Ta yaya littafin Amos ya nuna cewa ana zaɓi wajen zartar da hukuncin Allah?
[Hoto a shafi na 15]
Masarautar Isra’ila ba ta guje wa hukuncin Allah ba
[Hoto a shafi na 16]
A shekara ta 537 K.Z., raguwar Isra’ila da Yahuza suka komo daga bautar Babiloniyawa