Ku Bi Gurbin Annabawa—Joel
1. Ta yaya za mu bi misalin Joel a nuna tawali’u sa’ad da muke yin wa’azi?
1 Wane ne annabi Joel? Abin da ya bayyana game da kansa kawai shi ne cewa shi “ɗan Pethuel” ne. (Joel 1:1) Wannan annabi mai tawali’u bai ɗaukaka kansa a matsayin mai idar da saƙo ba, amma ya mai da hankali ga saƙon da Jehobah ya ba shi. Hakazalika, sa’ad da muke wa’azi ya kamata mu riƙa taimaka wa mutane su daraja Littafi Mai Tsarki kuma su ɗaukaka Jehobah, amma ba wai su yabe mu ba. (1 Kor. 9:16; 2 Kor. 3:5) Ƙari ga haka, muna samun ƙarfafa daga saƙon da muke ba wa mutane. Wane fannin annabcin Joel ne zai taimaka mana mu kasance da himma da kuma bege a yau?
2. Sanin cewa ranar Jehobah ta yi kusa zai motsa mu mu yi mene ne?
2 “Ranar Ubangiji ta Kusa” (Joel 1:15): Ko da yake an rubuta waɗannan kalmomin shekaru aru-aru da suka shige, a yanzu muna ganin cikar su dalla-dalla. Yadda abubuwa suke taɓarɓarewa a duniya da kuma halin ko-in-kula da mutane a yankinmu suke nuna mana a wa’azi suna tabbatar mana cewa muna gab da ƙarshen wannan yanayin da duniya take ciki. (2 Tim. 3:1-5; 2 Bit. 3:3, 4) Ya kamata sanin cewa ƙarshen ya kusa ya motsa mu mu sa yin wa’azin bishara kan gaba a rayuwarmu, ko ba haka ba?—2 Bit. 3:11, 12.
3. Me ya sa yin wa’azi yake da muhimmanci sosai yayin da muke gab da ƙunci mai girma?
3 “Ubangiji Za Ya Zama Mafaka ga Mutanensa” (Joel 3:16): Wannan girgizawa da aka ambata a ayar nan tana nufin hukuncin Jehobah a lokacin ƙunci mai girma. Muna samun ƙarfafa sosai daga sanin cewa Jehobah zai ceci bayinsa masu aminci a lokacin. (R. Yoh. 7:9, 14) Yayin da muke ganin yadda Jehobah yake taimaka mana da kuma ƙarfafa mu sa’ad da muke wa’azi, hakan yana sa mu kasance da bangaskiya da za ta sa mu jimre a lokacin ƙunci mai girma da ke zuwa.
4. Me ya sa za mu iya yin farin ciki kuma mu kasance da gaba gaɗi game da gaba?
4 Ko da yake wasu mutane sun ɗauka cewa annabcin Joel na hukunci ne kawai, annabcin yana ɗauke da bege ga mutanen Allah cewa za su sami ceto. (Joel 2:32) Bari mu kasance da gaba gaɗi game da gaba kuma mu ci gaba da yin wa’azin Mulkin Allah da himma yayin da muke bin abin da aka rubuta a Joel 2:23 da ta ce: “Ku yi murna fa, . . . ku yi farin zuciya cikin Ubangiji Allahnku.”