Maza, Kuna Miƙa Kai Ga Shugabancin Kristi Kuwa?
“Kan kowane namiji Kristi ne.” —1 KOR. 11:3.
1. Menene ya nuna cewa Jehobah, Allah ne mai tsari?
“KAI ne mai-isa ka karɓi ɗaukaka da daraja da iko, ya Ubangijinmu da Allahnmu,” in ji Ru’ya ta Yohanna 4:11, “gama kai ka halicci dukan abu, saboda nufinka kuma suka kasance, saboda nufinka aka halicce su.” Domin Shi ne Mahalicci, Jehobah Allah ne Mamallakin dukan sararin samaniya kuma yana da iko bisa dukan halittunsa. An ga cewa Jehobah “ba Allah na yamutsai ba ne, amma na kwanciyar rai ne” a hanyar da ya tsara iyalinsa na mala’iku.—1 Kor. 14:33; Isha. 6:1-3; Ibran. 12:22, 23.
2, 3. (a) Wanene halittar Jehobah na fari? (b) Wane matsayi ne Ɗan fari yake da shi game da Uban?
2 Kafin ya halicci wani abu, Allah ya wanzu shi kaɗai na shekaru marar iyaka. Halittarsa ta fari shi ne halittar ruhu da aka kira “kalma” domin shi ne Kakakin Jehobah. Ta hanyar Kalman ne aka halicci sauran dukan abubuwa. Daga baya, ya zo duniya a matsayin mutum kamiltacce kuma ya zama Yesu Kristi.—Karanta Yohanna 1:1-3, 14.
3 Menene Nassosi ya faɗa game da matsayin Allah da kuma na Ɗansa na fari? A ƙarƙashin ja-gorancin ruhu mai tsarki, manzo Bulus ya gaya mana: “Ina so ku sani, kan kowane namiji Kristi ne; kan mace kuma namiji ne; kan Kristi kuma Allah ne.” (1 Kor. 11:3) Kristi yana ƙarƙashin shugabancin Ubansa. Shugabanci da kuma miƙa kai suna da muhimmanci don salama da haɗin kai su kasance tsakanin halittu masu basira. Har ma wanda, ‘a cikinsa aka halicci dukan abu,’ yana bukatan ya miƙa kansa ga shugabancin Allah.—Kol. 1:16.
4, 5. Yaya Yesu ya ji game da matsayinsa a wurin Jehobah?
4 Yaya Yesu ya ji game da miƙa kansa ga shugabancin Jehobah da kuma zuwa duniya? Nassosi ya ce: “Kristi Yesu kuma: shi da ya ke cikin surar Allah, ba ya maida kasancewarsa daidai da Allah abin raini ba, amma ya wofinta kansa da ya ɗauki surar bawa, yana kasancewa da sifar mutane; da aka iske shi cikin kamanin mutum, ya ƙasƙantar da kansa, ya zama yana biyayya har da mutuwa, i, har mutuwa ta giciye.”—Filib. 2:5-8.
5 A kowane lokaci, Yesu yana yin nufin Ubansa cikin tawali’u. Ya ce: “Ni bisa ga kaina ban iya kome ba . . . shari’ata mai-adalci ce; domin ba na bin nufin kaina ba, amma nufin wanda ya aiko ni.” (Yoh. 5:30) “Kullum ina aika abin da ya gamshe [Ubana],” in ji shi. (Yoh. 8:29) A kusan ƙarshen rayuwarsa a duniya, Yesu ya ce a addu’arsa ga Ubansa: “Na ɗaukaka ka a duniya, yayinda na cika aikin da ka ba ni in yi.” (Yoh. 17:4) Babu shakka, fahimta da kuma amincewa da shugabancin Allah a kansa bai yi wa Yesu wuya ba.
Miƙa Kai ga Uban Yana Kawo Amfani ga Ɗan
6. Waɗanne halaye masu kyau ne Yesu ya nuna?
6 Sa’ad da yake duniya, Yesu ya nuna halaye masu ban al’ajabi. Ɗaya daga cikinsu ita ce ƙauna mai girma da ya nuna ga Ubansa. “Ina ƙaunar Uba,” in ji shi. (Yoh. 14:31) Ya kuma nuna ƙauna mai girma ga mutane. (Karanta Matta 22:35-40.) Yesu mai alheri ne da kuma sanin ya kamata, ba mai zafin hali ko tilasta wa mutane ba ne. “Ku zo gareni, dukanku da ku ke wahala, masu-nauyin kaya kuma,” in ji shi, “ni kuwa in ba ku hutawa. Ku ɗaukar wa kanku karkiyata, ku koya daga wurina; gama ni mai-tawali’u ne, mai-ƙasƙantar zuciya: za ku sami hutawa ga rayukanku. Gama karkiyata mai-sauƙi ce, kayana kuma mara-nauyi.” (Mat. 11:28-30) Masu kama da tumaki manya da ƙanana, musamman waɗanda ake zalunta, sun sami ta’aziya sosai a hali mai kyau na Yesu da kuma saƙonsa mai ƙarfafawa.
7, 8. A ƙarƙashin Doka, wane irin hani ne ke kan mace mai zubar jini, amma yaya Yesu ya bi da ita?
7 Yi la’akari da yadda Yesu ya bi da mata. A tarihi, maza da yawa sun wulakanta mata. Abin da malaman addinai na Isra’ila ta dā suka yi ke nan. Amma Yesu ya bi da mata cikin daraja. Hakan ya bayyana a yadda ya bi da matar da ta yi ciwon zubar jini na shekaru sha biyu. “Ta sha wahala dayawa” a wurin masu magani kuma ta kashe dukan abin da take da shi don ta warke. Duk da ƙoƙarce-ƙoƙarcenta, cutarta ta “daɗu.” A ƙarƙashin Doka, ana ɗaukanta marar tsarki. Duk wanda ya taɓa ta zai zama marar tsarki.—Lev. 15:19, 25.
8 Lokacin da matar ta ji cewa Yesu yana warkar da masu ciwo, ta shiga cikin taron da suka kewaye shi, tana cewa: “Idan na taɓa ko tufafinsa kaɗai, zan sami lafiya.” Ta taɓa Yesu, kuma nan da nan ta sami lafiya. Yesu ya san cewa bai kamata ta taɓa tufafinsa ba. Duk da haka, Yesu bai tsawata mata ba. Akasin haka, ya bi da ita da hankali. Ya fahimci yadda take ji a cikin waɗannan shekaru da ta yi tana rashin lafiya kuma ya san cewa tana neman taimako sosai. Da juyayi, Yesu ya gaya mata: “Ɗiya, bangaskiyarki ta warkar da ke; ki tafi lafiya, ki rabu da azabarki.”—Mar. 5:25-34.
9. Sa’ad da almajiran Yesu suka yi ƙoƙarin hana yara zuwa wajensa, me ya ce?
9 Har yara ma sun saki jiki a wurin Yesu. Akwai lokacin da mutane suka kawo masa yara, almajiransa suka kwaɓe su, wataƙila suna tunanin cewa ba zai so yara su dame shi ba. Amma Yesu bai ji hakan ba. Labarin da ke cikin Littafi Mai Tsarki ya ce: “Sa’anda Yesu ya ga wannan, hankalinsa ya tashi da haushi [ga almajiransa], ya ce masu, Ku bar yara ƙanƙanana su zo gareni; kada ku hana su: gama na irin waɗannan mulkin Allah ya ke.” Sai “ya rungume su, ya sa masu albarka, ya ɗibiya masu hannuwa.” Yesu ya jimre da yara kuma ya marabce su.—Mar. 10:13-16.
10. Ta yaya Yesu ya koyi halayen da yake da su?
10 Ta yaya Yesu ya koyi halayen da ya nuna sa’ad da yake duniya? Kafin ya zo duniya, ya lura da Ubansa na sama shekaru aru-aru kuma ya koyi halayensa. (Karanta Misalai 8:22, 23, 30.) A sama, ya ga yadda Jehobah yake nuna shugabanci cikin ƙauna bisa dukan halittunsa kuma ya sa hakan ya zama jikinsa. Yesu zai iya yin hakan da a ce ba ya yin biyayya? Abin farin ciki ne a gare shi ya miƙa kai ga Ubansa, kuma Jehobah yana farin cikin samun irin wannan Ɗa. Sa’ad da yake duniya, Yesu ya nuna sarai halaye masu kyau na Ubansa na samaniya. Gata ne a gare mu mu miƙa kai ga Kristi, Sarkin Mulki na sama da Allah ya naɗa.
Ka Yi Koyi da Halayen Kristi
11. (a) Wanene ya kamata mu yi aiki tuƙuru mu yi koyi da shi? (b) Me ya sa maza a cikin ikilisiya musamman za su yi ƙoƙari su yi koyi da Yesu?
11 Dukan mutanen da suke cikin ikilisiyar Kirista, musamman maza, suna bukatan su ci gaba da yin aiki tuƙuru don su yi koyi da halayen Kristi. Kamar yadda aka ambata ɗazu, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kan kowane namiji Kristi ne.” Kamar yadda Kristi ya yi koyi da Shugabansa, Allah na gaskiya, ya kamata maza Kiristoci su yi ƙoƙari su yi koyi da shugabansu, Kristi. Sa’ad da ya zama Kirista, manzo Bulus ya yi hakan. Ya ƙarfafa ’yan’uwa Kiristoci: “Ku zama masu-koyi da ni, kamar yadda ni kuma na Kristi ne.” (1 Kor. 11:1) Kuma manzo Bitrus ya ce: “Zuwa wannan aka kiraye ku: gama Kristi kuma ya sha azaba dominku, yana bar maku gurbi, domin ku bi sawunsa.” (1 Bit. 2:21) Umurnin yin koyi da Kristi yana da muhimmanci ga maza don wani dalili kuma. Sune suke zama dattawa da bayi masu hidima. Kamar yadda Yesu ya yi farin ciki wajen yin koyi da Jehobah, ya kamata maza Kirista su yi farin ciki wajen yin koyi da Kristi da halayensa.
12, 13. Yaya ya kamata dattawa su bi da tumakin da ke ƙarƙashin kulawarsu?
12 Wajibi ne dattawa cikin ikilisiyar Kirista su koyi kasancewa kamar Kristi. Bitrus ya ba dattawa wannan umurnin: “Ku yi kiwon garken Allah wanda ke wurinku, kuna yin shugabanci, ba kamar na tilas ba, amma da yardan rai, bisa ga nufin Allah; ba kuwa domin riba mai-ƙazanta ba, amma da karsashin zuciya; ba kuwa kamar masu-nuna sarauta bisa abin kiwo da aka sanya a hannunku ba, amma kuna nuna kanku gurbi ne ga garken.” (1 Bit. 5:1-3) Bai kamata dattawa Kiristoci su yi watsi, su zalunci ko kuma matsa wa tumaki ba. Ta wajen yin koyi da misalin Kristi, suna yin ƙoƙari su zama masu nuna ƙauna, masu sanin ya kamata, masu tawali’u, kuma masu kirki wajen bi da tumakin da ke ƙarƙashin kulawarsu.
13 Waɗanda suke yin ja-gora a cikin ikilisiya maza ne ajizai, kuma ya kamata su riƙa tunawa da wannan kasawa a koyaushe. (Rom. 3:23) Saboda haka, ya kamata su yi ɗokin koya game da Yesu kuma su yi koyi da ƙaunarsa. Suna bukatan su yi bimbini game da yadda Allah da kuma Kristi suka bi da mutane kuma su yi ƙoƙari su yi koyi da su. Bitrus ya aririce mu: “Dukanku kuwa ku ɗaura kanku da tawali’u, da za ku bauta ma juna: gama Allah yana tsayayya da masu-girman kai, amma yana ba da alheri ga masu-tawali’u.”—1 Bit. 5:5.
14. Yaya yawan girmamawa da ya kamata dattawa su yi wa wasu?
14 Sa’ad da suke sha’ani da tumakin Allah, ya kamata mazan da aka naɗa a cikin ikilisiya su nuna halaye masu kyau. Romawa 12:10 ta ce: “Ku yi zaman daɗin soyayya da junanku cikin ƙaunar ’yan’uwa; kuna gabatar da juna cikin bangirma.” Dattawa da bayi masu hidima suna girmama mutane. Kamar Kiristoci gabaki ɗaya, bai kamata waɗannan maza su ‘yi kome domin tsaguwa, ko girman kai amma a cikin tawali’u za su mai da wani ya fi su.’ (Filib. 2:3) Ya kamata waɗanda suke yin ja-gora su ɗauki mutane kamar sun fi su. Ta wajen yin hakan, mazan da aka naɗa suna bin shawarar Bulus: “Mu fa da ke ƙarfafa ya wajaba mu ɗauki kasawar raunana, kada mu yi son kai. Bari kowanen mu ya gami ɗan’uwansa wajen abin da ke nagari, zuwa ginawa. Gama Kristi kuma bai yi son kai ba.”—Rom. 15:1-3.
‘Ba da Girma ga Mata’
15. Yaya ya kamata magidanta su bi da matansu?
15 Ka yi la’akari yanzu da shawarar da Bitrus ya ba maza masu aure. Ya rubuta: “Ku mazaje, ku zauna da matayenku bisa ga sani, kuna ba da girma ga mace, kamar ga wadda ta fi rashin ƙarfi.” (1 Bit. 3:7) Girmama mutum yana nufin a ɗaukaka shi sosai. Da haka, za ka yi la’akari da ra’ayi, bukatu, da abin da mutumin yake so kuma ka yi abin da ya faɗa idan babu wani dalili mai muhimmanci na ƙin yin hakan. Haka ne ya kamata miji ya bi da matarsa.
16. Wane gargaɗi ne Kalmar Allah ta ba magidanta game da girmama matansu?
16 Sa’ad da yake gaya wa magidanta su girmama matansu, Bitrus ya daɗa wannan kashedin: “Domin kada addu’o’inku su hanu.” (1 Bit. 3:7) Hakan ya nuna sarai yadda Jehobah yake ɗaukan yadda miji yake bi da matarsa. Idan bai girmama ta ba, Jehobah ba zai ji addu’o’insa ba. Ƙari ga haka, mata suna ba da haɗin kai idan mazansu suka girmama su, ko ba haka ba?
17. Menene yawan ƙaunar da maigida zai nuna wa matarsa?
17 A kan batun mutum ya ƙaunaci matarsa, Kalmar Allah ta ba da wannan shawarar: “Ya kamata mazaje kuma su yi ƙaunar matayensu kamar jikunansu. . . . gama babu mutum wanda ya taɓa ƙin jiki nasa; amma yakan ciyar da shi ya kuma kiyaye shi, kamar yadda Kristi kuma ya kan yi da ikilisiya . . . Kowane ɗayanku shi yi ƙaunar matatasa kamar kansa.” (Afis. 5:28, 29, 33) Menene yawan ƙaunar da magidanta za su nuna wa matansu? “Ku mazaje” in ji Bulus, “ku ƙaunaci matanku, kamar yadda Kristi kuma ya ƙaunaci ikilisiya, ya bada kansa dominta.” (Afis. 5:25) Hakika, ya kamata maigida ya kasance a shirye ya mutu domin matarsa, kamar yadda Kristi ya yi domin mutane. Sa’ad da maigida Kirista ya bi da matarsa cikin ƙauna, sanin ya kamata, yana sauraronta, ba ya son kai, yana da sauƙi matarsa ta miƙa kai ga shugabancinsa.
18. Wane taimako ne maza suke da shi wajen kula da hakkinsu a cikin aure?
18 Daraja mata a wannan hanyar wani aiki ne mai girma da ake bukata daga magidanta? A’a, Jehobah ba zai taɓa gaya musu su yi abin da ya fi ƙarfinsu ba. Ballantana ma, masu bauta wa Jehobah suna iya samun iko mafi ƙarfi a sararin samaniya, wato, ruhu mai tsarki na Allah. Yesu ya ce: “Idan ku fa da ku ke miyagu, kun san yadda za ku ba ’ya’yanku alherai, balle fa Ubanku na sama za ya bada ruhu mai-tsarki ga waɗanda su ke roƙonsa?” (Luk 11:13) A cikin addu’o’insu, magidanta suna iya roƙon cewa ta hanyar ruhunsa, Jehobah ya taimaka musu a sha’aninsu da wasu, har da matansu.—Karanta Ayyukan Manzanni 5:32.
19. Menene talifinmu na gaba zai tattauna?
19 Hakika, maza suna da hakki mai girma na koyon yadda za su miƙa kai ga Kristi kuma su yi koyi da shugabancinsa. Mata kuma fa, musamman matan aure? Talifi na gaba zai tattauna yadda ya kamata su ɗauki matsayinsu a tsarin Jehobah.
Ka Tuna?
• Waɗanne halaye na Yesu ne ya kamata mu yi koyi da su?
• Yaya ya kamata dattawa su bi da tumaki?
• Yaya ya kamata maigida ya bi da matarsa?
[Hotuna da ke shafi na 10]
Ka yi koyi da Yesu ta wajen girmama mutane