Ka Kusaci Allah
Yana Daraja Mu da ’Yancin Yin Zaɓi
2 SARAKUNA 18:1-7
YA KAMATA iyaye su kafa wa yaransu misali mai kyau. Tasiri mai kyau na iyaye zai iya taimaka wa yaro ya samu halaye masu kyau kuma ya tsai da shawarwari masu kyau a rayuwarsa. Abin baƙin ciki, iyaye da yawa suna kafa wa yaransu mummunar misali. Shin waɗannan yaran za su iya yin nasara a rayuwarsu kuwa? Mun samu amsar a cikin wata gaskiya mafi ba da tabbaci, wato cewa, Jehobah Allah ya daraja kowannenmu da ’yancin yin zaɓi. Ka yi la’akari da misalin Hezekiya, a cikin 2 Sarakuna 18:1-7.
Hezekiya “ɗan Ahaz sarkin Yahuda” ne. (Aya ta 1) Ahaz ya sa talakawansa su daina yin tsarkakkar bauta ta Jehobah. Wannan mugun sarkin ya bauta wa Baal, tare da bukukuwanta na yin hadaya da mutane. Ya sa an kashe ’yan’uwan Hezekiya ɗaya ko fiye da hakan. Ahaz ya sa an rufe ƙofofin haikalin kuma “ya yi wa kansa bagadai cikin kowace kusurwar Urushalima.” Ya “cakuni Ubangiji.” (2 Labarbaru 28:3, 24, 25) Hakika, mahaifin Hezekiya mugu ne sosai. Amma Hezekiya zai iya ƙin yin irin kurakuren mahaifinsa kuwa?
Ba da daɗewa ba bayan Hezekiya ya zama sarki, ya nuna cewa ba zai ƙyale misali marar kyau na mahaifinsa ya rinjaye shi ba. Hezekiya ya ci gaba da “aikata nagarta a gaban Ubangiji.” (Aya ta 3) Hezekiya ya dogara ga Jehobah, kuma “ba a yi wani kamarsa a cikin sarakunan Yahudawa duka” ba. (Aya ta 5) A cikin shekara ta farko ta sarautarsa, matashin sarkin ya soma gabatar da bauta ta gaskiya da ta kai ga kawar da masujadai, inda ake bauta wa gumakan arna. An sake buɗe haikalin, kuma an dawo da bauta ta gaskiya. (Aya ta 4; 2 Labarbaru 29:1-3, 27-31) Hezekiya “ya [ci gaba da] manne wa Ubangiji . . . , Ubangiji kuwa yana tare da shi.”—Ayoyi ta 6, 7.
Mene ne ya taimaki Hezekiya ya guji mummunar misalin mahaifinsa? Shin mahaifiyarsa Abijah ce wadda ba a yi magana game da ita sosai ba ce ta nuna wa ɗanta misali mai kyau? Shin Hezekiya sarki matashi ya yi koyi ne da misali mai kyau na Ishaya wanda ya soma hidimarsa ta annabci kafin a haifi Hezekiya?a Littafi Mai Tsarki bai ambata hakan ba. Ko yaya dai ya faru, mun tabbata da abu ɗaya: Hezekiah ya zaɓi ya bi hali da ya bambanta da na mahaifinsa.
Misalin Hezekiya abin ƙarfafa ne ga duk waɗanda iyayensu suka kafa musu mummunar misali sa’ad da suke yara. Ba za mu iya kawar da abubuwan da suka faru mana a dā ba. Amma irin waɗannan abubuwan ba sa nufin cewa ba za mu yi nasara ba. Zaɓin da muka yi yanzu zai iya kai mu ga samun farin ciki a nan gaba. Kamar Hezekiya, za mu iya zaɓa mu yi ƙauna da kuma bauta wa Allahn gaskiya, Jehobah. Irin wannan tafarkin zai sa mu yi rayuwa mai gamsarwa yanzu kuma zai kai ga rai na har abada a cikin sabuwar duniya ta Allah. (2 Bitrus 3:13; Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4) Muna da dalilin yin godiya ga Allah mai ƙauna wanda ya daraja kowannenmu da kyauta mafi girma, wato, ’yancin yin zaɓi!
[Hasiya]
a Ishaya ya soma annabcinsa daga shekara ta 778 K.Z. zuwa bayan shekara ta 732 K.Z. Hezekiya ya soma sarauta a shekara ta 745 K.Z., sa’ad da yake ɗan shekara ashirin da biyar.