Su Waye Ne Makiyaya Bakwai Da Shugabanni Takwas A Yau?
“Sa’annan za mu tayar masa da makiyaya bakwai, da shugabannai takwas.”—MI. 5:5.
1. Me ya sa Sarkin Suriya da na Isra’ila ba su yi nasara a mugun ƙullin da suka yi ba?
SARKIN Isra’ila da Sarkin Suriya sun soma yaƙan Sarkin Yahuda a ƙarni na takwas kafin zamaninmu, wato a tsakanin shekara ta 762 da 759. Mene ne manufarsu? Suna so ne su ci ƙasar Urushalima kuma su cire Sarki Ahaz daga kan kursiyin kuma su naɗa wataƙila wani da ba zuriyar Dauda ba. (Isha. 7:5, 6) Amma ba su yi nasara ba. Me ya sa? Domin Jehobah ya riga ya alkawarta cewa zuriyar Dauda za ta mallaki kursiyin har abada, kuma maganar Allah ba ta faɗi a ƙasa a banza ba.—Josh. 23:14; 2 Sam. 7:16.
2-4. Ka bayyana yadda Ishaya 7:14, 16 suka cika (a) a ƙarni na takwas kafin zamaninmu (b) a ƙarni na farko a zamaninmu.
2 Da farko, an ɗauka cewa Sarkin Suriya da na Isra’ila za su yi nasara a yaƙin amma a yaƙi ɗaya kawai, an kashe sojojin Sarki Ahaz guda 120,000! “Ɗan sarki” mai suna Maaseiah ma ya mutu a yaƙin. (2 Laba. 28:6, 7) Amma Jehobah yana kallon abin da yake faruwa, ya tuna da alkawarin da ya yi wa Dauda, sai ya aika annabi Ishaya da wani saƙo mai ban ƙarfafa.
3 Ishaya ya ce: “Wata budurwa wadda take da ciki, za ta haifi ɗa, za a raɗa masa suna Immanuwel. Kafin lokacin ya yi, ƙasashen sarakunan nan biyu waɗanda suka firgita ku [Suriya da Isra’ila] za su zama kango.” (Isha. 7:14, 16, Littafi Mai Tsarki) Sashen farko na wannan annabcin ya shafi haihuwar Almasihu. (Mat. 1:23) Amma, Sarkin Suriya da na Isra’ila ba su yaƙi Yahuda a zamanin Yesu ba, saboda haka, annabci game da Immanuwel ya sami cikarsa na farko a zamanin Ishaya.
4 Jim kaɗan bayan Ishaya ya yi wannan annabcin, sai matarsa ta yi ciki kuma ta haifi ɗa da aka ba shi suna Maher-shalal-hash-baz. Wataƙila wannan ɗan shi ne wanda Ishaya ya kira “Immanuwel.”a A dā, ana ba jariri suna sa’ad da aka haife shi, wataƙila bisa ga wani abin da ya faru a lokacin, sa’an nan daga baya iyayensa da danginsa su ba shi wani suna. (2 Sam. 12:24, 25) Babu wani tabbacin da ya nuna cewa an kira Yesu da wannan suna Immanuwel.—Karanta Ishaya 7:14; 8:3, 4.
5. Wace shawara marar kyau ce Sarki Ahaz ya yanke?
5 Yayin da Isra’ila da kuma Suriya suka ƙulla su ci Yahuda, al’ummar Assuriya ma sun so su ci Yahuda. Assuriya wata muguwar al’umma ce da take da iko sosai a lokacin. Littafin Ishaya 8:3, 4 sun ce Assuriya za ta ci Suriya da kuma Isra’ila a yaƙi kafin ta kai wa Yahuda hari. Maimakon Ahaz Sarkin Yahuda ya yi imani da abin da annabin Allah, wato Ishaya ya faɗa, sai ya yi yarjejeniya da Assuriyawa. A sakamakon haka, Assuriyawa suka riƙa wulaƙanta Yahudawa. (2 Sar. 16:7-10) Sarki Ahaz bai yi nasara ba a matsayinsa na shugaban Yahuda. Za mu iya tambayar kanmu, ‘Sa’ad da nake so in yanke shawarwari masu muhimmanci, shin ina dogara ga Jehobah ne ko kuma mutane?’—Mis. 3:5, 6.
WANI SABON MAKIYAYI MAI HALI DABAM
6. Ta yaya sarautar Hezekiya ta yi dabam da na Ahaz?
6 Sa’ad da Ahaz ya mutu a shekara ta 746 kafin zamaninmu, sai ɗansa Hezekiya ya soma sarauta. A lokacin, mutanen ƙasar suna cikin talauci kuma sun daina bauta wa Jehobah. Wane gyara ne Sarki Hezekiya zai yi da farko? Shin zai sa al’ummar ta yi arziki ne? A’a. Hezekiya yana ƙaunar Jehobah kuma shi shugaba mai kirki ne. Abu na farko da ya yi shi ne, ya sa mutanen su soma bauta wa Jehobah. Sa’ad da ya fahimci nufin Allah a gare shi, sai ya yi biyayya. Wannan misali ne mai kyau, ko ba haka ba?—2 Laba. 29:1-19.
7. Me ya sa sabon Sarkin yake bukatar ya tallafa wa Lawiyawan?
7 Lawiyawa suna da babban hakki na taimaka wa mutanen su sake soma bauta wa Jehobah. Saboda haka, Hezekiya ya haɗu da Lawiyawan kuma ya yi alkawarin tallafa musu. Wataƙila Lawiyawan sun yi farin ciki sosai sa’ad da suka ji sarkin ya ce: “Ubangiji ya zaɓe ku domin ku tsaya a gabansa, ku yi masa hidima.” (2 Laba. 29:11) Hakika, Lawiyawan sun sami umurni kai tsaye cewa su taimaka wa mutanen su bauta wa Jehobah.
8. Mene ne Hezekiya ya sake yi don ya taimaka wa mutanen su soma bauta wa Jehobah, kuma da wane sakamako?
8 Hezekiya ya gayyaci dukan Yahudawa da Isra’ilawa zuwa babban Idin Ƙetarewa. Bayan Idin, sai mutanen suka yi Idin Gurasa Marar-Yisti har kwanaki bakwai. Sun ji daɗin idin sosai har suka ƙara kwanaki bakwai. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Aka yi farinciki ƙwarai fa cikin Urushalima: gama tun cikin zamanin Solomon ɗan Dauda sarkin Isra’ila ba a yi irin wannan ba a cikin Urushalima.” (2 Laba. 30:25, 26) Babu shakka, idin ya ƙarfafa dukansu. 2 Labarbaru 31:1, ta ce: “Ananan sa’anda aka gama dukan wannan, . . . suka farfashe umudai, suka sassare Asherim suka rurrushe masujadai, da bagadai.” Al’ummar ta sake soma bauta wa Jehobah. Hakan ya taimaka musu su kasance a shirye don matsalolin da suke dab da fuskanta.
SARKIN YA SHIRYA DON FAƊA
9. (a) Ta yaya aka ɓata shirin da Isra’ilawa suke yi? (b) Wane nasara ne Sennakerib ya soma yi a Yahuda?
9 Kamar yadda Ishaya ya annabta, Assuriyawa sun ci Isra’ilawa a yaƙi kuma sun kai mazaunan bauta a ƙasarsu. Hakan ya ɓata shirin da Isra’ilawa suke yi na naɗa sarki a Yahuda da ba daga zuriyar Dauda ba. Amma, mene ne Assuriyawa suke shiryawa? Sun zo su halaka Yahuda. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ananan a cikin shekara ta goma sha huɗu ta sarki Hezekiah, Sennacherib sarkin Assyria ya tasa wa yaƙin dukan birane masu-ganuwa na Yahuda, ya ci su.” Sennacherib ya ci birane 46 na Yahuda. Ka yi tunani yadda za ka ji da a ce kana Urushalima a lokacin. Kana ganin yadda Assuriyawa suke cin biranen Yahuda kuma suna daɗa kusantar inda kake da zama!—2 Sar. 18:13.
10. Me ya sa annabcin Mikah ya ƙarfafa Hezekiya?
10 Hakika, Hezekiya ya san cewa matsala tana tafe, amma hakan bai birkita shi ba ko kuma ya sa ya nemi taimako daga sarakan arna kamar yadda mahaifinsa Ahaz marar aminci ya yi. Hezekiya ya dogara ga Jehobah. (2 Laba. 28:20, 21) Babu shakka, ya san da wannan furucin da annabi Mikah ya yi game da Assuriyawa cewa: “Za mu tayar masa da makiyaya bakwai, da shugabannai takwas. . . . Za ya cece mu daga Ba-asshure, lokacinda ya zo ƙasarmu, sa’anda ya taka cikin iyakarmu.” (Mi. 5:5, 6) Hakika, wannan furucin ya ƙarfafa Hezekiya. Furucin ya nuna cewa Jehobah zai yi amfani da wasu irin mayaƙa don ya ci Assuriyawa a yaƙi.
11. A wane lokaci ne annabcin nan na makiyaya bakwai da shugabannai takwas zai samu cikarsa mafi muhimmanci?
11 Annabcin da aka yi game da makiyaya bakwai da shugabannai takwas zai cika a hanya mafi muhimmanci bayan an haifi Yesu, “wanda za ya zama mai-mulki cikin Isra’ila; mafitansa tun daga zamanin dā.” (Karanta Mikah 5:1, 2.) Babu shakka, hakan zai faru a nan gaba sa’ad da ‘Assuriyawa’ na zamaninmu za su kai wa bayin Jehobah hari. Jehobah zai sa Yesu ya ja-goranci wasu mayaƙa don su halaka maƙiyan. Waɗanne mayaƙa ke nan? Za mu amsa wannan tambayar a talifi na gaba. Amma bari mu fara tattauna darasin da za mu iya koya daga matakin da Hezekiya ya ɗauka sa’ad da Assuriyawa suka kai musu hari.
HEZEKIYA YA ƊAUKI MATAKAN DA SUKA DACE
12. Mene ne Hezekiya da mutanen da ke tare da shi suka yi don su kāre bayin Allah?
12 Sa’ad da muka ji cewa ba za mu iya magance wata matsala da kanmu ba, Jehobah yana a shirye ya taimaka mana. Amma yana so mu yi iya ƙoƙarinmu game da matsalar kuma abin da Hezekiya ya yi ke nan. Littafi Mai Tsarki ya ce ya nemi shawara daga wurin “hakimansa da jarumawansa,” kuma ya yanke shawara ya ‘toshe ruwayen maɓulɓulan da ke bayan birnin.’ Bugu da ƙari, Hezekiya “ya yi ƙarfin hali, ya gina dukan inda gānuwa ta rushe, ya ƙara tsawon hasumiyan birni, ya gina wani garu kuma daga waje, . . . ya yi kayan yaƙi, da garkuwa dayawa.” (2 Laba. 32:3-5) A wannan lokacin, Jehobah ya yi amfani da Hezekiya da hakimansa da kuma annabawa masu aminci su kāre da kuma ƙarfafa bayinsa.
13. Wane mataki mafi muhimmanci ne Hezekiya ya ɗauka don ya sa mutanensa su kasance a faɗake don harin Assuriyawa da ke tafe? Ka bayyana.
13 Abin da Hezekiya ya yi bayan haka, ya fi toshe ruwaye da kuma gina ganuwar birnin muhimmanci. Domin shi makiyayi ne mai kyau, ya tattara mutanen kuma ya ƙarfafa su da kalmomi na gaba. Ya ce: “Kada ku ji tsoro, kada ku yi fargaba domin sarkin Assyria, . . . gama tare da mu akwai wanda ya fi nasa: Tare da shi akwai iko na jiki, amma a garemu akwai Ubangiji, Allahnmu, mai-taimakonmu, wanda za ya yi yaƙi dominmu.” Hezekiya ya tuna wa mutanen cewa Jehobah zai yi yaƙi domin su. Hakan ya taimaka musu su kasance da bangaskiya da kuma gaba gaɗi. Hezekiya da dukan hakimansa da jarumai da kuma annabi Mikah da Ishaya sun nuna cewa su makiyaya ne masu kyau, kamar yadda Jehobah ya annabta ta bakin annabawa.—2 Laba. 32:7, 8; karanta Mikah 5:5, 6.
14. Mene ne Rabshakeh ya ce, kuma me mutanen suka yi?
14 Sarkin Assuriya da mayaƙansa sun kafa sansani a birnin Lachish da ke kudu matso yamma na birnin Urushalima. Daga wurin, sai ya aiki mutane uku su je su gaya wa mazaunan Urushalima cewa su ba da kai. Ainihin mai aiken mai suna Rabshakeh ya yi wa mazaunan Urushalima magana da Ibrananci. Da farko, ya yi ƙoƙari ya rinjaye su don kada su saurari Hezekiya, amma su yi biyayya ga Assuriyawa. Sai ya yi ƙarya cewa zai kai su ƙasar da za su ji daɗi sosai. (Karanta 2 Sarakuna 18:31, 32.) Rabshakeh ya kuma gaya musu cewa allolin ƙasarsu da kuma Jehobah ba za su iya kāre su ba. Mutanen sun kasance da hikima kuma sun ƙi su gaskata da ƙaryar da kuma zargin da ya yi. A yau ma, bayin Jehobah sun yin koyi da misalinsu.—Karanta 2 Sarakuna 18:35, 36.
15. Mene ne mazaunan Urushalima suke bukatar su yi, kuma ta yaya Jehobah ya ceci birnin?
15 Babu shakka, Hezekiya ya yi fushi sosai amma maimakon ya nemi taimako daga wata ƙasa, ya aika a kirawo annabi Ishaya. Ishaya ya gaya wa Hezekiya cewa: “[Sennakerib] ba za ya iso wannan birni ba, ba kuwa za ya halba mata kibiya ba.” (2 Sar. 19:32) Abin da mazaunan Urushalima suke bukatar yi kawai shi ne su yi tsayin daka, gama Jehobah zai yi yaƙi domin su. Hakika, Jehobah ya cika alkawarinsa! Littafi Mai Tsarki ya ce: “A daren nan fa ya zama mala’ikan Ubangiji ya fita, ya buga mutum [dubu] ɗari da tamanin da biyar cikin sansanin Assyriyawa.” (2 Sar. 19:35) Ba matakin da Hezekiya ya ɗauka na toshe ruwaye da kuma gina ganuwa ba ne ya kāre su ba, amma Jehobah ne.
DARUSSAN DA ZA MU KOYA A YAU
16. Su waye ne a yau suke wakiltar (a) mazaunan Urushalima (b) ‘Assuriyawa’ (c) makiyaya bakwai da shugabannai takwas?
16 Annabcin nan na makiyaya bakwai da shugabannai takwas yana cika sosai a zamaninmu. A zamanin dā, Assuriyawa sun kai wa mazaunan Urushalima hari. Nan ba da daɗewa ba, maƙiya da ke kamar ‘Assuriyawa’ za su so su halaka bayin Jehobah. Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da harin nan da na ‘Gog na ƙasar Magog’ da na “sarkin arewa” da kuma na “sarakunan duniya.” (Ezek. 38:2, 10-13; Dan. 11:40, 44, 45; R. Yoh. 17:14; 19:19) Shin wannan hari dabam-dabam ne? Ba mu san amsar wannan tambayar ba. Wataƙila Littafi Mai Tsarki ya yi amfani da furuci dabam-dabam don ya ambata yaƙi ɗaya. Waɗanne mayaƙa ne Mikah ya annabta cewa Jehobah zai yi amfani da su don ya halaka waɗannan ‘Assuriyawa’ masu mugunta? Jehobah zai yi amfani da wata hanya da ba a saba ba. Littafi Mai Tsarki ya ce Jehobah zai yi amfani da ‘makiyaya bakwai da shugabannai takwas.’ (Mi. 5:5) Su waye ne waɗannan mutanen? Dattawan ikilisiya ne. (1 Bit. 5:2) A yau, Jehobah yana yin amfani da amintattun dattawa masu yawa domin ya kula da kuma ƙarfafa bayinsa don harin ‘Assuriyawa’ na zamaninmu da ke tafe.b Annabcin Mikah ya ce za su “lalatar da ƙasar Assyria da takobi.” (Mi. 5:6) Ɗaya cikin makaman da suke amfani da shi don yaƙan maƙiyan shi ne “takobin Ruhu, wato maganar Allah.”—2 Kor. 10:4; Afis. 6:17.
17. Waɗanne darussa huɗu ne dattawa za su iya koya daga abin da muka tattauna a wannan talifin?
17 Dattawan da suke karanta wannan talifin za su koyi darussa masu amfani daga abin da muka tattauna: (1) Hanya mafi muhimmanci na yin shiri don wannan harin ‘Assuriya,’ ita ce ta ƙarfafa bangaskiyarsu ga Allah kuma ta taimaka wa ’yan’uwa ma su yi hakan. (2) Sa’ad da ‘Assuriyawa’ suka kawo hari, wajibi ne dattawa su kasance da tabbaci cewa Jehobah zai cece mu. (3) A lokacin, za mu ji kamar umurnin da ƙungiyar Jehobah za ta ba mu ba zai yiwu ba. Amma, ya wajaba dukanmu mu kasance a shirye don mu yi biyayya ga kowane umurnin da aka ba mu, ko da mun amince da su ko a’a. Me ya sa? Domin yin biyayya ga umurnin zai sa mu samu ceto. (4) Idan akwai kowane mutum da ke dogara ga ilimin duniyar nan ko wadata ko ƙungiyoyin ’yan Adam, ya kamata su sake tunani nan da nan. Wajibi ne dattawa su taimaki kowane ɗan’uwa da ya ƙi dogara ga Jehobah baki ɗaya.
18. Ta yaya yin bimbini a kan wannan batun zai taimaka mana a nan gaba?
18 Lokaci zai zo da mutane za su ga kamar bayin Jehobah ba su da mai taimako, kamar yadda ya faru da mazaunan Urushalima a zamanin Hezekiya. Sa’ad da hakan ya faru, kalmomin Hezekiya za su iya ƙarfafa mu. Bari dukanmu mu tuna cewa magabtanmu suna da “iko na jiki, amma a garemu akwai [Jehobah], Allahnmu, mai-taimakonmu, wanda za ya yi yaƙi dominmu.”—2 Laba. 32:8.
a A Ibrananci, kalmar nan “budurwa” da ke Ishaya 7:14 tana nufin mace mai aure ko kuma wadda ba ta taɓa sanin namiji ba. Saboda haka, za a iya yin amfani da kalmar nan wa matar Ishaya da kuma Maryamu wadda budurwa ce Bayahudiya.
b A yawancin lokaci, lambar nan bakwai a Littafi Mai Tsarki tana wakiltar cikakken abu. Lambar nan takwas kuma da ta ɗara bakwai yana wakiltar abu mai yawa.