“Wanene Ya Gane Nufin Ubangiji?”
“Wanene ya gane nufin Ubangiji, da zai koya masa? Amma nufin Kristi yana wurinmu.”—1 KOR. 2:16.
1, 2. (a) Wace matsala ce mutane da yawa suke fuskanta? (b) Mene ne muke bukatan mu tuna game da tunaninmu da na Jehobah?
YA TAƁA yi maka wuya ka fahimci tunanin wani? Wataƙila ba ka daɗe da aure ba, kuma kana ganin ba ka san yadda za ka fahimci tunanin abokiyar aurenka ba. Hakika, yadda maza da mata suke tunani da kuma yin magana ya bambanta. A wasu al’adu, yadda mace za ta yi magana da namiji ya bambanta, kuma yadda namiji zai yi magana da tamace ya bambanta ko da yake yarensu ɗaya ne! Ƙari ga hakan, bambancin al’ada da yare zai iya sa mutane su riƙa tunani dabam kuma su kasance da hali dabam. Amma, yayin da kake daɗa sanin mutane, za ka daɗa samun zarafi na soma fahimtar yadda suke tunani.
2 Saboda haka, bai kamata mu yi mamaki ba cewa yadda muke tunani ya yi dabam da na Jehobah. Ta wurin annabi Ishaya, Jehobah ya gaya wa Isra’ilawa: “Tunanina ba tunaninku ba ne; al’amuranku kuma ba al’amurana ba ne.” Don ya nuna gaskiyar hakan, Jehobah ya ci gaba da cewa: “Kamar yadda sammai suna da nisa da duniya, haka nan kuma al’amurana sun fi naku tsawo, tunanina kuma sun fi naku.”—Isha. 55:8, 9.
3. A waɗanne hanyoyi biyu ne za mu iya yin ƙoƙari mu san “asirin Jehobah”?
3 Amma, hakan yana nufi ne cewa ba za mu yi ƙoƙari mu fahimci tunanin Jehobah ba? A’a. Ko da yake ba za mu iya taɓa fahimtar dukan nufin Jehobah ba, duk da hakan, Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa mu mu san “asirin Ubangiji.” (Karanta Zabura 25:14; Misalai 3:32.) Hanya ɗaya da za mu kusaci Jehobah ita ce ta wajen kula da kuma mai da hankali ga ayyukansa kamar yadda yake rubuce a cikin Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki. (Zab. 28:5) Wata hanya ita ce ta wajen sanin “nufin Kristi,” wanda shi ne “surar Allah marar-ganuwa.” (1 Kor. 2:16; Kol. 1:15) Ta wajen ba da lokaci sosai mu yi nazarin labaran Littafi Mai Tsarki da kuma yin bimbini a kansu, za mu soma fahimtar halayen Jehobah da kuma tunaninsa.
Ka Guji Mugun Hali
4, 5. (a) Wane mugun hali ne muke bukatan mu guji? Ka bayyana. (b) Wane mugun tunani ne Isra’ilawa suka yi?
4 Yayin da muke yin bimbini a kan ayyukan Jehobah, muna bukatar mu guji halin shari’anta Allah da mizanan ’yan Adam. An ambata wannan halin a kalaman Jehobah da ke rubuce a Zabura 50:21: “Kana tsammani ni kamarka ne sosai.” Kamar yadda wani masanin Littafi Mai Tsarki ya faɗa ne fiye da shekaru 175 da suka shige: “Mutane sukan shari’anta Allah bisa nasu mizanai kuma su yi tunani cewa dokokin da ya kamata mutane su bi ya shafi Allah.”
5 Muna bukatan mu mai da hankali kada mu ƙyale mizananmu da sha’awoyinmu su ja-goranci yadda muke ɗaukan Jehobah. Me ya sa hakan yake da muhimmanci? Yayin da muke nazarin Nassosi, muna iya ganin cewa wasu ayyukan Jehobah ba su dace ba a namu ra’ayin ajizanci. Isra’ilawa na dā sun yi irin wannan tunanin kuma suka kammala yadda bai dace ba game da yadda Jehobah ya yi sha’ani da su. Ka lura da abin da Jehobah ya gaya musu: “Kun ce, Hanyar Ubangiji ba ta yi daidai ba. Ku ji, ya gidan Isra’ila: Hanyata ba daidai ba ce? ba naku hanya ba ce ta yi rashin gaskiya?”—Ezek. 18:25.
6. Wane darasi ne Ayuba ya koya, kuma yaya za mu amfana daga abin da ya fuskanta?
6 Abu ɗaya da zai taimaka mana mu guji kuskuren shari’anta Jehobah da namu mizanai shi ne mu fahimci cewa ra’ayinmu yana da iyaka kuma wani lokaci mukan yi kuskure sosai. Ayuba ya bukaci ya koyi wannan darasin. A lokacin da yake shan wahala, Ayuba ya yi fama da baƙin ciki kuma ya riƙa tunanin kansa kawai. Ya mance da batutuwa masu muhimmanci. Amma Jehobah cikin ƙauna ya taimaka masa ya faɗaɗa ra’ayinsa. Ta wajen yi wa Ayuba tambayoyi fiye da 70, da Ayuba bai iya amsa ko ɗaya ba, Jehobah ya nanata kasawar fahimin Ayuba. Ayuba ya aikata cikin tawali’u kuma ya daidaita ra’ayinsa.—Karanta Ayuba 42:1-6.
Yadda Za Mu San “Nufin Kristi”
7. Yaya za mu samu taimako wajen fahimtar tunanin Jehobah, idan mun bincika ayyukan Yesu?
7 Yesu ya yi koyi sosai da Ubansa a dukan abubuwan da ya yi da kuma faɗa. (Yoh. 14:9) Saboda haka, bincika ayyukan Yesu zai taimaka mana mu fahimci yadda Jehobah yake tunani. (Rom. 15:5; Filib. 2:5) Bari mu bincika labarai biyu na Linjila.
8, 9. Kamar yadda yake rubuce a Yohanna 6:1-5, wane yanayi ne ya sa Yesu ya yi wa Filibus tambaya, kuma me ya sa Yesu ya yi hakan?
8 Ka yi tunanin yanayin nan. Ya faru ne kafin Idin Ƙetarewa na shekara ta 32 A.Z. Bai daɗe ba da manzannin Yesu suka dawo daga tafiye-tafiyen wa’azi a dukan ƙasar Galili. Tun da yake sun gaji daga dukan waɗannan ayyuka, Yesu ya kai su wani wurin da babu kowa a gaɓar arewa maso gabashin Tekun Galili. Amma, mutane dubbai suka bi su zuwa wajen. Bayan da Yesu ya warkar da kuma koya wa wannan jama’ar abubuwa da yawa, wata matsalar game da yadda za a yi wani abu ta taso. Yaya dukan waɗannan mutanen za su samu abinci a wannan wurin da babu kowa? Da ya ga bukatan, Yesu ya tambayi Filibus wanda ɗan yankin ne: “Daga ina za mu sayo abinci, domin waɗannan su ci?”—Yoh. 6:1-5.
9 Me ya sa Yesu ya yi wa Filibus wannan tambayar? Shin Yesu ya damu ne da abin da zai yi? A’a. Mene ne ainihi tunaninsa? Manzo Yohanna, wanda yake wajen ya bayyana: “[Yesu] ya faɗi ne domin ya gwada shi; gama shi da kansa ya san abin da zai yi.” (Yoh. 6:6) A nan, Yesu ya gwada ci gaba da almajiransa suka yi a ruhaniya. Ta wurin yin wannan tambayar, ya jawo hankalinsu kuma ya ba su zarafin furta bangaskiyarsu ga abin da zai iya yi. Amma sun yi hasarar wannan zarafin kuma sun nuna cewa ra’ayinsu yana da iyaka ainun. (Karanta Yohanna 6:7-9.) Sai Yesu ya nuna cewa zai iya yin wani abu da ba su taɓa tsammani ba. Ya ciyar da waɗannan mutane dubbai masu jin yunwa ta mu’ujiza.—Yoh. 6:10-13.
10-12. (a) Me ya sa Yesu bai yi abin da mata Ba-heleniya ta roƙa nan da nan ba? Ka bayyana. (b) Mene ne za mu bincika yanzu?
10 Wannan labarin zai iya taimaka mana mu fahimci tunanin Yesu a wani lokaci. Ba da daɗewa ba bayan ya ciyar da wannan rukunin mutane masu yawa, Yesu da manzaninsa suka yi tafiya zuwa arewa, sun wuce iyakar Isra’ila, zuwa yankin Tyre da Sidon. Sa’ad da suke wajen, sun sadu da wata mata Ba-heleniya wadda ta roƙi Yesu ya warkar da ’yarta. Da farko, Yesu ya ƙi ya saurare matar. Amma sa’ad da ta ci gaba da nacewa, Yesu ya gaya mata: “Bari ’ya’yan gida su ƙoshi tukuna: gama ba ya yi kyau ba a ɗauki abincin ’ya’ya a jefa wa [“’ya’yan,” NW] karnuka.”—Mar. 7:24-27.
11 Me ya sa da farko Yesu ya ƙi ya taimaka wa wannan matar? Shin Yesu yana gwada ta ne, kamar yadda ya gwada Filibus, ya ga yadda za ta aikata, yana ba ta zarafin nuna bangaskiyarta? Yadda ya yi maganar bai sa ta yi sanyin gwiwa ba, ko da yake ba a bayyana hakan a cikin ayar ba. Ya sauƙaƙa kwatancin ta wajen yin amfani da kalmar nan “’ya’yan karnuka.” Saboda haka, wataƙila Yesu yana aikatawa ne kamar mahaifi wanda yake son ya ba ɗansa abin da yake so ba tare da nuna masa niyyarsa ba domin ya gwada ƙudurin ɗan. Ko mene ne dai, muddin matar ta furta bangaskiyarta, Yesu da yardan rai ya ba ta abin da ta roƙa.—Karanta Markus 7:28-30.
12 Waɗannan labaran Linjila biyu sun ba mu fahimi mai tamani game da “nufin Kristi.” Bari yanzu mu ga yadda waɗannan labaran za su taimaka mana mu fahimci nufin Jehobah da kyau.
Yadda Jehobah Ya Yi Sha’ani da Musa
13. Ta yaya sanin tunanin Yesu yake taimaka mana?
13 Sanin tunanin Yesu yana taimaka mana mu fahimci ayoyin Nassosi da suke da wuyar fahimta. Alal misali, ka yi la’akari da kalaman Jehobah ga Musa bayan da Isra’ilawa suka yi maraƙi na zinariya don bauta. Allah ya ce: “Na ga wannan mutane, kuma, ga shi, mutane masu-taurin kai ne: sai fa ka bar ni, domin fushina shi yi ƙuna a kansu, in kakkashe su: ni kuwa in yi babbar al’umma da kai.”—Fit. 32:9, 10.
14. Yaya Musa ya aikata ga kalaman Jehobah?
14 Labarin ya ci gaba da cewa: “Musa kuwa ya roƙi Ubangiji Allahnsa, ya ce, Ya Ubangiji, don me fushinka ya yi ƙuna a kan mutanenka, waɗanda ka fishe su daga ƙasar Masar da babban iko da hannu mai-ƙarfi? Don me Masarawa za su yi magana, su ce, Don ƙeta ya fishe su, domin shi kashe su cikin duwatsu, shi share su daga fuskar duniya? Ka juyo ga barin zafin fushinka, ka tuba ga barin wannan mugunta bisa mutanenka. Ka tuna da Ibrahim, da Ishaƙu, da Isra’ila, bayinka, waɗanda ka rantse masu bisa ga kanka, ka ce masu, Zan riɓanɓanya irinku kamar tamrarin sama, kuma dukan wannan ƙasa wadda na ambata zan bayas da ita ga irinku, za su kuwa gāje ta har abada. Ubangiji kuwa ya tuba ga barin mugunta da ya ce za ya yi ga mutanensa.”—Fit. 32:11-14.a
15, 16. (a) Wane zarafi ne Musa ya samu domin abin da Jehobah ya faɗa? (b) A wane azanci ne Jehobah “ya tuba”?
15 Musa yana bukatan ya gyara tunanin Jehobah ne? Ko kaɗan! Ko da yake Jehobah ya faɗa abin da yake da niyyar yi, wannan ba hukuncinsa na ƙarshe ba ne. Jehobah yana gwada Musa ne, kamar yadda Yesu ya yi wa Filibus da mata Ba-heleniya. An ba Musa zarafin furta ra’ayinsa.b Jehobah ya naɗa Musa a matsayin matsakanci tsakaninsa da Isra’ila, kuma Jehobah yana daraja yadda ya naɗa Musa a wannan matsayin. Musa zai ƙyale baƙin ciki da yake yi ya shafi ayyukansa ne? Zai yi amfani da wannan zarafin ne don ya ƙarfafa Jehobah ya mance da Isra’ila kuma ya sa zuriyar Musa ta zama babbar al’umma ne?
16 Amsar da Musa ya ba da ya nuna bangaskiyarsa da kuma dogararsa ga adalcin Jehobah. Yadda ya aikata ya nuna ba shi da son kai, amma ya damu da sunan Jehobah. Ba ya son a ɓata sunan. Ta hakan Musa ya nuna cewa ya fahimci “nufin Ubangiji” game da wannan batun. (1 Kor. 2:16) Mene ne sakamakon? Domin Jehobah ba ya nace wa yin wani abu, hurarren labarin ya ce “ya tuba.” A Ibrananci, wannan furcin yana nufin cewa Jehobah bai kawo bala’in da yake da niyyar jawo wa al’ummar gabaki ɗaya ba.
Yadda Jehobah Ya Yi Sha’ani da Ibrahim
17. Yaya Jehobah ya yi haƙuri sosai sa’ad da yake bi da damuwar Ibrahim?
17 Wani misali na yadda Jehobah yake ba bayinsa zarafin furta bangaskiyarsu da kuma amincinsu ya ƙunshi roƙon da Ibrahim ya yi game da Saduma. A wannan labarin, Jehobah ya yi haƙuri sosai ta wajen ƙyale Ibrahim ya yi tambayoyi guda takwas. A wani lokaci, Ibrahim ya yi wannan roƙo da dukan zuciyarsa: “Wannan ya yi nisa da kai ka yi irin wannan, a kashe masu-adalci tare da miyagu, har kuma masu-adalci za su zama ɗaya da miyagu; wannan ya yi nisa da kai: Mai-shari’an dukan duniya ba za ya yi daidai ba?”—Far. 18:22-33.
18. Mene ne muka koya daga yadda Jehobah ya yi sha’ani da Ibrahim?
18 Daga wannan labarin, mene ne muka koya game da tunanin Jehobah? Shin Jehobah yana bukatan Ibrahim ya ba shi shawara ne kafin ya tsai da shawara da ta dace? A’a. Da Jehobah ya faɗa masa dalilan shawararsa da farko. Amma ta wajen waɗannan tambayoyin, Jehobah ya ba Ibrahim zarafin amincewa da shawarar kuma ya fahimci tunaninsa. Ya kuma ba wa Ibrahim zarafi ya fahimci zurfin juyayin Jehobah da shari’arsa. Hakika, Jehobah ya yi sha’ani da Ibrahim a matsayin aboki.—Isha. 41:8; Yaƙ. 2:23.
Darussa Dominmu
19. Ta yaya za mu yi koyi da Ayuba?
19 Me muka koya game da “nufin Ubangiji”? Muna bukatan mu ƙyale Kalmar Allah ta gyara fahiminmu na nufin Jehobah. Bai kamata mu ɗora wa Jehobah kasawarmu da kuma shari’anta shi da mizananmu da kuma tunaninmu ba. Ayuba ya ce: “[Allah] ba mutum ba ne kamana, da zan amsa masa, Mu zo a yi mana shari’a tare.” (Ayu. 9:32) Kamar Ayuba, yayin da muka fara fahimtar nufin Jehobah, za mu motsa mu ce: “Ga shi, waɗannan gefen al’amuran ikonsa ne kawai, ƙanƙanuwar raɗar labarinsa kuwa mu ke ji. Amma tsawar ikonsa, wa ke da iko ya gane?”—Ayu. 26:14.
20. Mene ne ya dace mu yi idan muka sami aya na nassi da ya yi mana wuyan fahimta?
20 Mene ne ya kamata mu yi sa’ad da muka karanta wani wuri a Littafi Mai Tsarki da ke da wuyar fahimta, musamman game da nufin Jehobah? Bayan mun yi bincike a kan batun, kuma har ila ba mu samu amsar dalla-dalla ba, za mu iya ɗaukan wannan a matsayin gwaji na dogararmu ga Jehobah. Ka tuna, a wasu lokatai wasu wurare da ke da wuyar fahimta suna ba mu zarafin nuna bangaskiyarmu ga halayen Jehobah. Ya kamata mu yarda cikin tawali’u cewa ba mu fahimci kowane abu da yake yi ba. (M. Wa. 11:5) Ta hakan, za mu motsa mu yarda da waɗannan kalmomi na manzo Bulus: “Oh! zurfin wadata na hikimar Allah duk da na saninsa! ina misalin wuyan binciken shari’unsa, al’amuransa kuma sun fi gaban a bincika su duka! Gama wanene ya san nufin Ubangiji? wanene kuwa ya taɓa zama abokin shawaransa? wanene kuwa ya fara ba shi, har da za a saka masa kuma? Gama dukan abu daga gare shi ne, ta wurinsa kuma, zuwa gare shi kuma. A gare shi ɗaukaka har abada. Amin.”—Rom. 11:33-36.
[Hasiya]
a Akwai irin wannan labarin a cikin Littafin Lissafi 14:11-20.
b Wasu masana sun faɗa cewa ana iya ɗaukan maganar fasaha na asali na Ibrananci da aka fassara “ka bar ni” da ke Fitowa 32:10 a matsayin gayyata, shawara cewa za a bar Musa ya yi roƙo ko kuma ya “tsaya” tsakanin Jehobah da al’ummar. (Zab. 106:23; Ezek. 22:30) Ko yaya dai, Musa ya saki jiki ya furta ra’ayinsa ga Jehobah.
Ka Tuna?
• Mene ne zai taimake mu mu guji halin shari’anta Jehobah da mizananmu?
• Ta yaya fahimtar yadda Yesu ya aikata zai taimaka mana mu san “asirin Jehobah”?
• Waɗanne darussa ne ka koya daga hirar Jehobah da Musa da kuma Ibrahim?
[Hotuna da ke shafi na 5]
Mene ne muka koya game da tunanin Jehobah a hanya da ya yi sha’ani da Musa da kuma Ibrahim?