Yesu Ne Musa Mafi Girma
“Ubangiji Allah za ya tayas maku da wani annabi daga cikin ’yan’uwanku kamar ni; a gareshi za ku kasa kunne.”—A. M. 3:22.
1. Yaya Yesu Kristi ya shafe tarihi?
SHEKARU dubu biyu da suka shige, haihuwar wani ɗa ta sa rundunar mala’iku a sama su yabi Allah a gaban wasu makiyaya. (Luk. 2:8-14) Shekaru talatin bayan wannan aukuwar, wannan ɗan ya soma hidimarsa ta shekara uku da rabi wadda ta canja tarihin ’yan Adam. Wani sanannen masanin tarihi na ƙarni ta 19 mai suna Philip Schaff ya ce game da wannan mutumin: “Ko da yake bai rubuta littafi ba, amma ya jawo rubutu da yawa, rubutu game da wa’azi, jawabi, tattaunawa, littattafan ilimi, littattafan fasaha, da waƙoƙin yabo fiye da duk waɗanda ake rubutawa game da manyan mutane a dā da na zamaninmu.” Wannan fitaccen matashin shi ne, Yesu Kristi.
2. Menene manzo Yohanna ya ce game da Yesu da hidimarsa?
2 Manzo Yohanna ya rubuta labari a kan hidimar Yesu kuma ya kammala da cewa: “Akwai kuma waɗansu abu dayawa da Yesu ya yi; ina tsammani da a ce za a rubuta su kowane ɗaya, da duniya da kanta ba za ta ɗauki littattafai waɗanda za a rubuta ba.” (Yoh. 21:25) Yohanna ya san cewa ba zai iya rubuta duk abubuwan da Yesu ya ce da kuma yi a shekara uku da rabi wadda ya yi wa’azi a duniya. Duk da haka, tarihi mai muhimmanci da Yohanna ya rubuta a Linjilarsa suna da tamani sosai.
3. Yaya za mu zurfafa saninmu game da matsayin Yesu a nufin Allah?
3 Ban da Linjila guda huɗu, wasu littattafai a cikin Littafi Mai Tsarki sun ba da bayanai masu ƙarfafawa game da rayuwar Yesu. Alal misali, labaran da ke cikin Littafi Mai Tsarki na wasu mutane masu aminci da suka rayu kafin Yesu, suna ɗauke da bayanai da suke zurfafa saninmu game da matsayin Yesu a nufin Allah. Bari mu tattauna wasu daga cikinsu.
Maza Amintattu da Suka Wakilci Kristi
4, 5. Wanene ya wakilci Yesu, kuma a waɗanne hanyoyi?
4 Yohanna da sauran mutane uku da suka rubuta Linjila sun ambata Musa, Dauda, da Sulemanu a matsayin mazan da suka wakilci Yesu a matsayin Shafaffe da Sarki mai jiran gado. A wace hanya ce mutanen nan na dā suka wakilci Yesu, kuma menene za mu iya koya daga waɗannan labaran?
5 A taƙaice, Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa Musa annabi ne, matsakanci ne, da kuma mai ceto. Yesu ma haka. Dauda makiyayi ne da kuma sarki wanda ya halaka maƙiyan Isra’ila. Yesu ma makiyayi ne domin yana yi wa mutanen Allah ja-gora kuma sarki ne mai nasara. (Eze. 37:24, 25) A lokacin da yake da aminci, Sulemanu sarki ne mai hikima, kuma a lokacin sarautarsa Isra’ila sun more salama. (1 Sar. 4:25, 29) Yesu ma mai hikima ne sosai kuma ana kiransa “Sarkin Salama.” (Ish. 9:6) Babu shakka, matsayin Yesu Kristi ya yi kama da na mutanen nan na dā, amma matsayin Yesu a nufin Allah mai girma ne. Na farko, bari mu kwatanta Yesu da Musa don mu ga yadda hakan zai taimaka mana mu ƙara fahimtar cikakken matsayin Yesu a nufin Allah.
Musa, Ya Gabaci Yesu
6. Yaya manzo Bitrus ya bayyana muhimmancin saurarar Yesu?
6 Ba da daɗewa ba da yin Fentakos na shekara ta 33 A.Z., manzo Bitrus ya yi ƙaulin annabcin da Musa ya yi wanda ya samu cikawa a Yesu Kristi. Bitrus yana tsaye a gaban taron jama’a masu bauta a haikali. Mutanen sun yi “mamaki dayawa” sa’ad da Bitrus da Yohanna suka warkar da wani maroƙi wanda gurgu ne tun daga haihuwa, kuma dukansu suka ruga don su gani. Bitrus ya bayyana cewa wannan aiki mai ban mamaki ya yiwu ne a sakamakon ruhu mai tsarki na Jehobah da ke aiki ta hanyar Yesu Kristi. Bayan haka, ya yi ƙaulin Nassosin Ibrananci, kuma ya ce: “Musa dai ya ce, Ubangiji Allah za ya tayas maku da wani annabi daga cikin ’yan’uwanku kamar ni; a gareshi za ku kasa kunne cikin iyakacin abin da za shi faɗa maku duka.”—A. M. 3:11, 22, 23; karanta Kubawar Shari’a 18:15, 18, 19.
7. Menene ya sa masu sauraron Bitrus suka fahimci kalamansa game da annabin da ya fi Musa girma?
7 Wataƙila waɗannan kalaman na Musa, sanannu ne ga masu sauraron Bitrus. A matsayinsu na Yahudawa, suna daraja Musa sosai. (K. Sh 34:10) Cike da ɗoki, suna sa ran ganin zuwan annabin da ya fi Musa girma. Wannan annabin ba zai zama shafaffe kawai na Allah kamar Musa ba, amma zai zama Almasihu, “Kristi na Allah ne, zaɓaɓensa.”—Luk. 23:35; Ibran. 11:26.
Kamannin da ke Tsakanin Yesu da Musa
8. Waɗanne kamanni ne ke tsakanin rayuwar Musa da Yesu?
8 Sa’ad da yake duniya, Yesu ya yi kama da Musa a wasu ɓangarori. Alal misali, sa’ad da yake jariri, Musa da Yesu sun tsira daga hannun mugun sarkin da ya so ya kashe su. (Fit. 1:22–2:10; Mat. 2:7-14) Ƙari ga hakan, an ‘kirawo su daga cikin Masar.’ Annabi Hosea ya ce: “Sa’anda Isra’ila yana yaro, sa’annan na ƙaunatace shi, na kuwa kirawo ɗana daga cikin Masar.” (Hos. 11:1) Kalaman Hosea tana nuni ga lokacin da aka fitar da al’ummar Isra’ila daga ƙasar Masar, a ƙarƙashin shugabansu Musa, wanda Allah ya naɗa. (Fit. 4:22, 23; 12:29-37) Amma dai, kalaman Hosea suna nuni ne ga abubuwan da suka faru, da kuma abubuwan da za su faru a nan gaba. Kalamansa sun cika a lokacin da Yusufu da Maryamu suka dawo daga ƙasar Masar tare da Yesu bayan mutuwar Sarki Hiridus.—Mat. 2:15, 19-23.
9. (a) Waɗanne mu’ujizai ne Musa da Yesu suka yi? (b) Ka ba da wasu kamani da ke tsakanin Yesu da Musa. (Ka duba akwatin nan “Ƙarin Hanyoyi da Yesu Ya yi Kama da Musa,” da ke shafi na 26.)
9 Musa da Yesu sun yi mu’ujizai, kuma hakan ya nuna cewa suna da goyon bayan Jehobah. Hakika, Musa ne ɗan adam na farko da aka rubuta cewa ya yi mu’ujizai. (Fit. 4:1-9) Alal misali, Musa ya yi mu’ujizai da suka ƙunshi mai da ruwan kogin Masar da kuma rafukansu jini, ya kuma raba ruwan Jar Teku, kuma ruwa ya fito daga dutse a hamada. (Fit. 7:19-21; 14:21; 17:5-7) Yesu ma ya yi mu’ujizai da ruwa. Mu’ujizarsa ta farko ita ce wadda ya mai da ruwa zuwa ruwan inabi a bikin da ya halarta. (Yoh. 2:1-11) Bayan haka, ya kwantar da rakumin ruwa a Tekun Galili. Akwai lokacin da ma ya yi tafiya a kan ruwa! (Mat. 8:23-27; 14:23-25) Za ka iya ganin wasu ƙarin kamanni da ke tsakanin Musa da Musa Mafi girma, Yesu, a akwatin da ke shafi na 26.
Kristi Annabi Ne
10. Menene ayyukan annabi na gaskiya, kuma menene ya sa Musa ya zama ɗaya?
10 Yawancin mutane suna ɗaukan annabi a matsayin wanda yake faɗin abin da zai faru a gaba, amma wannan sashe ne kawai na aikin annabin. Annabi na gaskiya hurarren kakaki ne ga Jehobah, wanda ke shelar “ayyuka masu-girma na Allah.” (A. M. 2:11, 16, 17) Ban da wannan, annabcinsa zai iya ya ƙunshi sanar da abubuwan da za su faru a gaba, bayyana ɓangarori dabam-dabam na nufin Jehobah, ko kuma sanar da hukuncin Allah. Musa irin wannan annabi ne. Ya annabta dukan Annoba Goma da suka faɗa wa ƙasar Masar. Ya sanar da Isra’ilawa dokokin da ke cikin Dokar alkawari a Sinai. Kuma ya koyar da al’ummar daidai da nufin Allah. Duk da haka, annabin da ya fi Musa girma zai zo daga baya.
11. Ta yaya Yesu ya yi ayyuka na annabi da ya fi na Musa girma?
11 Daga baya, a ƙarni na farko, Zakariya ya yi annabci sa’ad da ya sanar da nufin Allah game da ɗansa, Yohanna. (Luk. 1:76) Wannan ɗan shi ne Yohanna mai yin Baftisma, wanda ya sanar da zuwan annabin da ya fi Musa girma wanda ake jira tun da daɗewa, wato, Yesu Kristi. (Yoh. 1:23-36) A matsayinsa na annabi, Yesu ya annabta abubuwa da yawa. Alal misali, ya yi magana game da mutuwarsa, yadda zai mutu, inda zai mutu, da kuma waɗanda za su kashe shi. (Mat. 20:17-19) Wani abin mamaki ga masu sauraronsa shi ne, Yesu ya annabta cewa za a halaka Urushalima da kuma haikalinsa. (Mar. 13:1, 2) Annabce-annabcensa suna cika a lokacinmu.—Mat. 24:3-41.
12. (a) Wane misali ne Yesu ya kafa don yin wa’azi a dukan duniya? (b) Ta yaya za mu bi misalin Yesu a yau?
12 Ƙari ga zama annabi, Yesu mai wa’azi ne da kuma malami. Ya yi wa’azin bishara ta Mulkin Allah, kuma babu wanda ya taɓa yin magana da gaba gaɗi kamar shi. (Luk. 4:16-21, 43) A matsayinsa na malami, babu na biyunsa. “Babu mutumin da ya taɓa yin magana haka,” in ji wasu da suka saurare shi. (Yoh. 7:46) Yesu yana da ƙwazo sosai game da yaɗa bishara, kuma ya koya wa mabiyinsa su kasance da irin wannan ƙwazon ga Mulki. Da haka, ya kafa gurbi na yin wa’azi da koyarwa a dukan duniya wanda har yanzu ana cikinsa. (Mat. 28:18-20; A. M. 5:42) A shekarar da ta shige, mabiyan Kristi miliyan bakwai sun yi awoyi 1,500,000,000 wajen yin wa’azin bishara ta Mulki da kuma koya wa masu son gaskiya Littafi Mai Tsarki. Ka saka hannu yadda ya kamata a wannan hidimar?
13. Menene zai taimake mu “mu zauna a faɗake”?
13 Babu shakka, Jehobah ya cika annabcin da ya yi na ta da annabi kamar Musa. Yaya sanin hakan ya shafe ka? Hakan yana ba ka ƙarin tabbaci a cikar hurarrun annabce-annabce da suka shafi nan gaba? Hakika, yin tunani sosai game da misalin Musa Mafi Girma, yana motsa mu “mu zauna a faɗake, da natsuwa” game da abin da Allah zai yi ba da daɗewa ba.—1 Tas. 5:2, 6, Littafi Mai Tsarki.
Ka Daraja Kristi a Matsayin Matsakanci
14. Yaya Musa ya zama matsakanci tsakanin Isra’ilawa da Allah?
14 Kamar Musa, Yesu matsakanci ne. Jehobah ya yi amfani da Musa sa’ad da ya kafa Dokar alkawari a tsakaninsa da Isra’ilawa. Idan ’ya’yan Yakubu suka yi biyayya ga dokokin Allah, za su ci gaba da zama mutanen Allah na musamman, wato, ikilisiyarsa. (Fit. 19:3-8) An ci gaba da bin wannan alkawarin daga shekara ta 1513 K.Z., har ƙarni na farko A.Z.
15. Yaya Yesu ya zama matsakanci mafi kyau?
15 A shekara ta 33 A.Z., Jehobah ya kafa alkawari mafi kyau da sabuwar Isra’ila, wato, “Isra’ila na Allah,” wadda ta zama ikilisiya na dukan duniya na shafaffu Kiristoci. (Gal. 6:16) Ko da yake alkawarin da Musa ya zama matsakancinsa ya ƙunshi dokoki da Allah ya rubuta a kan dutse, alkawari da Yesu ya zama matsakancinsa ya fi kyau. Allah ya rubuta dokokin alkawarin a zuciyar ’yan adam. (Karanta 1 Timothawus 2:5; Ibraniyawa 8:10.) Saboda haka, “Isra’ila na Allah” a yanzu ita ce keɓaɓɓiyar taska ga Allah, ‘al’umma mai-fitowa da ’ya’ya’ na Mulkin Almasihu. (Mat. 21:43) Waɗanda suke cikin wannan al’umma na ruhaniya su ne ke cikin sabon alkawari. Duk da haka, ba su kaɗai ba ne za su amfana daga sabon alkawarin. Mutane da yawa, har da waɗanda suka mutu za su samu albarka na har abada domin wannan alkawari na musamman.
Ka Daraja Kristi a Matsayin Mai Ceto
16. (a) A waɗanne hanyoyi ne Jehobah ya yi amfani da Musa ya ceci Isra’ila? (b) In ji Fitowa 14:13, wanene Tushen ceto?
16 A darensu na ƙarshe kafin su bar Masar, wasu cikin ’ya’yan Isra’ila suna cikin mugun haɗari. Ba da daɗewa ba, mala’ikan Allah zai wuce ta ƙasar Masar ya kashe dukan ’ya’yan fari. Jehobah ya gaya wa Musa cewa za a ceci ɗan fari na Isra’ilawa idan Isra’ilawa suka ɗauki jinin ɗan rago na Idin Ƙetarewa kuma suka yayyafa shi a kan dogaran ƙofa da kuma bisa dokin ƙofofinsu. (Fit. 12:1-13, 21-23) Hakan abin ya faru. Daga baya, dukan al’ummar ta shiga cikin mugun haɗari. Sun shiga cikin tarko tsakanin Jan Teku da kuma karusan yaƙi na Masarawa da ke bin su. Jehobah kuma ya yi tanadin ceto ta wurin Musa wanda ta mu’ujiza ya raba ruwan tekun.—Fit. 14:13, 21.
17, 18. A waɗanne hanyoyi ne Yesu ya zama mai ceto da ya fi Musa?
17 Ko da yake waɗannan ayyukan ceto suna da girma, ceton da Jehobah ya yi ta wurin Yesu ya fi girma. Ta wurin Yesu ne aka ’yantar da masu biyayya daga bauta wa zunubi. (Rom. 5:12, 18) Kuma wannan ceton shi ne “fansa ta har abada.” (Ibran. 9:11, 12) Sunan nan Yesu, yana nufin “Jehobah Ne Ceto.” Yesu a matsayin Mai Cetonmu, ya cece mu daga zunubanmu na dā kuma ya buɗe mana hanyar more rayuwa mafi kyau a nan gaba. Ta wajen cetonsu daga bauta wa zunubi, Yesu ya ceci mabiyansa daga fushin Allah kuma ya sa sun ƙulla dangantaka mai kyau da Jehobah.—Mat. 1:21.
18 Da shigewar lokaci, ceto daga zunubi da Yesu ya yi tanadinsa zai ƙunshi ’yanci daga mugun sakamakonsa, wato, ciwo da mutuwa. Don mu zana hoton yadda hakan zai kasance a zuciyarmu, yi la’akari da abin da ya faru sa’ad da Yesu ya tafi gidan wani mutum mai suna Yariyus, wanda ɗiyarsa ’yar shekara goma sha biyu ta mutu. Yesu ya tabbatar da Yariyus cewa: “Kada ka ji tsoro, sai dai ka bada gaskiya, za a maishe ta lafiyayya.” (Luk. 8:41, 42, 49, 50) Kamar yadda ya faɗa, yarinyar ta tashi daga matattu! Ka yi tunani irin farin cikin da iyayenta za su yi! Sa’an nan za ka fahimci irin farin cikin da za mu yi sa’ad da “waɗanda suna cikin kabarbaru za su ji muryatasa, [Yesu] su fito” a tashin matattu. (Yoh. 5:28, 29) Hakika, Yesu Mai Cetonmu ne!—Karanta Ayukan Manzanni 5:31; Tit. 1:4; R. Yoh. 7:10.
19, 20. (a) Ta yaya yin bimbini a kan matsayin Yesu na Musa Mafi Girma ya shafe mu? (b) Menene za a tattauna a talifi na gaba?
19 Sanin cewa za mu iya taimaka wa mutane su amfana daga ayyukan Yesu na ceto zai motsa mu mu sa hannu a aikin wa’azi da kuma koyarwa. (Isha. 61:1-3) Ƙari ga haka, yin bimbini a kan matsayin Yesu na Musa mafi Girma zai sa mu kasance da tabbaci sosai cewa zai ceci mabiyansa sa’ad da ya zo ya zartar da hukunci a kan miyagu.—Mat. 25:31-34, 41, 46; R. Yoh. 7:9, 14.
20 Hakika, Yesu ne Musa mafi Girma. Ya yi abubuwa da yawa masu ban al’ajabi da Musa ba zai taɓa iya yi ba. Kalmomin Yesu a matsayin annabi da kuma ayyukansa na matsakanci sun shafi dukan iyalin ’yan adam. A matsayin Mai Ceto, Yesu ya kawo ceto na har abada ga dukan ’yan adam da za su sami ceto na har abada. Duk da haka, da ƙarin abubuwa da za a mu iya koya game da Yesu daga mutane masu aminci na dā. Talifi na gaba zai nuna yadda ya zama Dauda Mafi Girma da kuma Sulemanu Mafi Girma.
Za Ka Iya Bayyanawa?
Ta yaya ne Yesu ya fi Musa girma a matsayin
• Annabi?
• Matsakanci?
• Mai ceto?
[Akwati/Hotunan da ke shafi na]
Ƙarin Hanyoyi da Yesu Ya yi Kama da Musa
◻ Su biyun sun bar matsayi mai girma don su yi wa Jehobah da mutanensa hidima.—2 Kor. 8:9; Filib. 2:5-8; Ibran. 11:24-26.
◻ Su biyun sun yi hidima a matsayin shafaffu ko kuma ‘waɗanda Jehobah ya zaɓa.’—Mar. 14:61, 62; Yoh. 4:25, 26; Ibran. 11:26.
◻ Su biyun sun shaida sunan Jehobah, wato, wakilansa ne.—Fit. 3:13-16; Yoh. 5:43; 17:4, 6, 26.
◻ Su biyun sun kasance da tawali’u.—Lit. Lis. 12:3; Mat. 11:28-30.
◻ Su biyun sun ciyar da mutane masu yawa. —Fit. 16:12; Yoh. 6:48-51.
◻ Su biyun sun yi hidima a matsayin alƙali da kuma mai ba da doka.—Fit. 18:13; Mal. 4:4; Yoh. 5:22, 23; 15:10.
◻ An ba su biyun shugabanci bisa gidan Allah. —Lit. Lis. 12:7; Ibran. 3:2-6.
◻ An bayyana su biyun Shaidun Jehobah masu-aminci.—Ibran. 11:24-29; 12:1; R. Yoh. 1:5.
◻ Bayan mutuwar Musa da Yesu, Allah ya ɓoye gawawwakinsu.—K. Sha 34:5, 6; Luk 24:1-3; A. M. 2:31; 1 Kor. 15:50; Yahu. 9.