Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 11/15 pp. 17-19
  • Jehobah Yana Sauraron Kukan Mai Tawali’u

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Jehobah Yana Sauraron Kukan Mai Tawali’u
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “Magana a Kan Kari”
  • Taimako ta Wurin Taron Kirista
  • ‘Ka Yi Addu’a ba Fasawa’
  • Jehovah ‘Mai Kiyaye Mu A Lokatan Wahala’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Ka Dogara Ga Jehobah, “Allah Na Dukan Ta’aziyya”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • An Ƙarfafa Mu Mu Sha Kan Kowane Gwaji
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • ”Ku Yi Kuka Tare da Masu-Kuka”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 11/15 pp. 17-19

Jehobah Yana Sauraron Kukan Mai Tawali’u

MAI hikima Sarki Sulemanu na Isra’ila ta dā ya lura cewa, “sa’a da tsautsayi sukan sami kowannen[mu].” (M. Wa. 9:11, Littafi Mai Tsarki) Aukuwa mai ban tausayi da kuma gwaji mai tsanani suna iya ɓata rayuwarmu sosai. Alal misali, mutuwar farat ɗaya na wani da ke cikin iyali za ta iya kawo baƙin ciki ƙwarai. A cikin makonni da watanni nan gaba, baƙin ciki da fid da rai za su iya shawo kan waɗanda suke cikin iyalin. Mutum yana iya rikicewa har ya ji bai cancanci yin addu’a ga Jehobah ba domin yadda yake ji.

A irin wannan yanayin, mutum yana bukatan a ƙarfafa shi, a yi la’akari da shi kuma a nuna masa ƙauna. Yana da ban ƙarfafa da mai zabura Dauda ya rera: “Ubangiji yana talafan dukan waɗanda su ke faɗuwa, yana tada dukan tanƙwararru.” (Zab. 145:14) Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa “idanun Ubangiji suna kai da kawowa a cikin dukan duniya, domin ya bayyana kansa mai ƙarfi sabili da waɗanda zuciyarsu ta kamalta gareshi.” (2 Laba. 16:9) Yana ‘tare da wanda ya ke da karyayyen ruhu mai-tawali’u, domin ya wartsakar da ruhun masu-tawali’u, ya wartsakar da masu-karyayyen zuciya.’ (Isha. 57:15) Ta yaya Jehobah yake tallafa da kuma ƙarfafa wanda yake da karyayyen ruhu mai tawali’u?

“Magana a Kan Kari”

Ɗaya cikin hanyoyi da Jehobah yake ba da taimako a lokacin da ya dace shi ne ta wurin ’yan’uwanci na Kirista. An ƙarfafa Kiristoci su “ƙarfafa masu-raunanan zukata.” (1 Tas. 5:14) Furcin da ke nuna cewa mun damu kuma muna ƙaunar ’yan’uwanmu masu bi za su taimaka wajen ƙarfafa mutum a lokacin da yake baƙin ciki da makoki. Kalaman ta’aziyya da aka furta a lokacin ɗan tattaunawa zai taimaka sosai wajen ƙarfafa wanda ya yi sanyin gwiwa. Wanda ya jimre irin wannan baƙin ciki yana iya furta irin waɗannan kalamai masu ma’ana. Ko kuma suna iya zama abin da aboki da ya fuskanci irin waɗannan yanayi ya lura da shi. Ta wurin waɗannan hanyoyin, Jehobah zai iya ƙarfafa ruhun mai tawali’u.

Ka yi la’akari da yanayin wani dattijo Kirista mai suna Alex, wanda ya rasa matarsa sanadiyyar ciwon ajali ba da daɗewa ba bayan aurensu. Wani mai kula mai ziyara mai juyayi ya furta kalaman ta’aziyya ga Alex. Shi ma ya rasa matarsa amma ya sake aure da daɗewa. Mai kula mai ziyaran ya kwatanta cewa yadda ya ji ya sha kansa. Yana jin daɗi sa’ad da yake tare da wasu mutane a hidima da kuma a tarurrukan ikilisiya. Amma, sa’ad da ya shiga cikin ɗakinsa kuma ya rufe ƙofa, sai ya ji ya kaɗaita. “Na samu sauƙi sa’ad da na san cewa ba ni kaɗai ba ne nake ji hakan kuma cewa wasu sun fuskanci hakan,” in ji Alex. Hakika, “magana a kan kari” za ta iya zama abin ƙarfafa a lokacin baƙin ciki.—Mis. 15:23.

Wani dattijo Kirista da ya san mutane da yawa da suka rasa abokan aurensu, ya yi wa Alex wasu kalaman ban ƙarfafa. Cikin tausayi, ya furta cewa Jehobah ya san yadda muke ji da abin da muke bukata. “Idan a watanni da shekaru nan gaba, ka ji cewa kana bukatar abokiyar aure,” in ji ɗan’uwan, “tanadi na ƙauna daga Jehobah a yanzu shi ne sake yin aure.” Hakika, ba dukan waɗanda suka rasa abokan aurensu da suke so su sake yin aure suke iya yin hakan kuma ba. Amma da yake tunani game da kalaman ɗan’uwan, Alex ya ce, “Tuna maka cewa wannan tanadin Jehobah ne yana sauƙaƙa duk laifin da kake ji cewa za ka yi rashin aminci ga abokiyar aurenka ko kuma tsarin aure na Jehobah ta wajen sake yin aure nan gaba.”—1 Kor. 7:8, 9, 39.

Marubucin wannan zabura Dauda wanda ya fuskanci gwaji da matsaloli da yawa, ya faɗa: “Idanun Ubangiji suna fuskanta wajen masu-adalci; kunnuwansa kuma a buɗe su ke ga jin ƙarassu.” (Zab. 34:15) Hakika, Jehobah yana iya amsa kukan masu tawali’u a lokacin da ya dace ta wurin furcin ’yan’uwa Kiristoci masu juyayi da suka manyanta. Irin wannan tanadin yana da tamani da amfani kuma.

Taimako ta Wurin Taron Kirista

Mutumin da ya karaya yana iya yin tunani marar kyau da zai sa ya ware kansa. Amma, Misalai 18:1 ta ba da gargaɗi: “Wanda ya ware kansa dabam, muradin kansa ya ke biɗa, yana kuwa hauka gāba da sahihiyar hikima duka.” Alex ya ce: “Idan mutum ya rasa abokiyar aure, zai riƙa mugun tunani.” Ya tuna, yana tambayar kansa: “‘Da akwai wani abu dabam da ya kamata na yi ne? Da na daɗa zama mai yin la’akari da fahimi ne?’ Ba na son na kaɗaita. Ba na son na zama marar aure. Yana da wuya na daina yin irin wannan tunanin domin a kowace rana ina nan ni kaɗai.”

Fiye da dā, wanda ya karaya yana bukatan cuɗanya mai kyau. Ana samun wannan a tarurrukan ikilisiya. A irin wannan yanayin, muna buɗe zukatanmu ga koyarwar Allah mai kyau da mai ban ƙarfafa.

Tarurrukan Kirista za su taimaka mana mu daidaita ra’ayinmu game da yanayinmu. Yayin da muke saurara da kuma yin bimbini a kan ayoyin Littafi Mai Tsarki, muna mai da hankalinmu ga batutuwa biyu da suka fi muhimmanci, wato, kunita ikon mallakar Jehobah da kuma tsarkake sunansa ba ga wahalar da muke sha ba kaɗai. Bugu da ƙari, sa’ad da ake koya mana game da Jehobah a taron Kirista, muna samun ƙarfafa ta sanin cewa ko da wasu ba su san baƙin ciki da muke yi ba ko kuma ba su fahimci yadda muke ji ba, Jehobah ya san da hakan. Ya san hakan domin “ta wurin ɓacin zuciya ruhu ya kan karai.” (Mis. 15:13) Allah na gaskiya yana son ya taimaka mana, kuma hakan yana sa mu kasance da ƙwazo da kuma ƙarfi mu ci gaba.—Zab. 27:14.

Sa’ad da magabtansa suka matsa masa sosai, Sarki Dauda ya yi kuka ga Allah: “Ruhuna ya yi suwu daga cikina: zuciyata a cikina tana zaman kaɗaici.” (Zab. 143:4) Sau da yawa wahala tana gajiyar da mutum a zahiri da sosuwar rai, har ta matar da zuciyarsa. Muna iya fuskantar wahala na rashin lafiya na dogon lokaci. Muna da tabbaci cewa Jehobah zai taimaka mana mu jimre. (Zab. 41:1-3) Ko da yake Allah ba ya warkar da kowanne mutum ta mu’ujiza a yanzu, yana ba mai rashin lafiya hikima da ƙarfi da yake bukata don ya jimre da yanayinsa. Ka tuna cewa sa’ad da gwaji ya nauyaya shi, Dauda ya dogara ga Jehobah. Ya rera: “Ina tuna da kwanakin dā; ina tunani da dukan al’amuranka: ina bimbini a kan ayyukan hannuwanka.”—Zab. 143:5.

Da yake an rubuta waɗannan hurarrun kalamai cikin Kalmar Allah ya nuna cewa Jehobah ya fahimci yadda muke ji. Irin waɗannan kalamai tabbaci ne cewa yana saurara roƙe-roƙenmu. Idan mun amince da taimakon Jehobah, ‘zai taimake mu.’—Zab. 55:22.

‘Ka Yi Addu’a ba Fasawa’

Yaƙub 4:8 ya ce: “Ku kusato ga Allah, shi kuwa za ya kusato gare ku.” Hanya ɗaya da za mu kusaci Allah ita ce ta wurin addu’a. Manzo Bulus ya umurce mu mu “yi addu’a ba fasawa.” (1 Tas. 5:17) Ko idan ya yi mana wuya mu faɗa yadda muke ji, “ruhu da kansa yana roƙo dominmu da nishenishe waɗanda ba su furtuwa.” (Rom. 8:26, 27) Babu shakka, Jehobah ya fahimci yadda muke ji.

Monika, wadda take more irin wannan dangantaka da Jehobah ta ce: “Ta wurin addu’a da karatun Littafi Mai Tsarki da kuma nazari na kaina, na ji cewa Jehobah ya zama aminina. Ya zama aboki na gaske a gare ni har na fahimci yadda yake taimako na a kai a kai. Abin ban ƙarfafa ne na san cewa ko a lokacin da ba zan iya bayyana yadda nake ji ba, ya fahimce ni. Na san cewa alherinsa da albarkarsa ba su da iyaka.”

Saboda haka, bari mu amince da furci na ƙauna da ƙarfafa na ’yan’uwa Kiristoci, mu yi amfani da shawara mai kyau da tunasarwa masu ƙarfafa bangaskiya da muke ji a tarurrukan Kirista, kuma mu gaya wa Jehobah kome da ke zuciyarmu ta wurin addu’a. Ta wurin waɗannan tanadi na kan lokaci ne Jehobah yake nuna mana cewa yana damuwa da mu. Bisa ga abin da Alex ya fuskanta ya ce, “Idan muka yi iyakar ƙoƙarinmu muka yi amfani da dukan abubuwa da Jehobah Allah yake mana tanadinsu don mu kasance da ƙarfi a ruhaniya, za mu samu “mafificin girman iko” don mu jimre wa kowane gwaji da muke fuskanta.—2 Kor. 4:7.

[Akwati/Hoton da ke shafi na 18]

Ta’aziyya ga Mai Tawali’u

Zabura tana cike da kalaman sosuwar zuciya na ’yan Adam haɗe da tabbaci da Jehobah ya furta a kai a kai cewa yana sauraron kukan mai tawali’u da baƙin ciki ya sha kansa. Ka yi la’akari da waɗannan baitoci:

“A cikin ƙuncina na yi kira ga Ubangiji, na tada murya zuwa ga Allahna: Ya ji muryata daga cikin haikalinsa, kukana kuma da na yi a gabansa ya shiga kunnuwansa.”—Zab. 18:6.

“Ubangiji yana kusa da masu-karyayyar zuciya, yana ceton irin waɗanda su ke da ruhu mai-tuba.” —Zab. 34:18.

“[Jehobah] yana warkar da masu-karyayyar zuciya, yana ɗaure raunukan su.”—Zab. 147:3.

[Hoton da ke shafi na 17]

“Magana a kan kari” za ta iya kasancewa da ban ƙarfafa a ranar baƙin ciki!

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba