Ka Kusaci Allah
Sa’ad da Tsofaffi Za Su Sake Zama Matasa
WANE ne a cikinmu yake jin daɗin sakamakon tsufa, wato, tamoji, rashin gani sosai, daina jin magana, da ƙafafuwa marar ƙwari? Kana iya cewa, ‘Me ya sa Allah zai halicce mu a hanyar da za mu iya jin daɗin kuruciya sai kuma ya ƙyale mu mu ji tsoron sakamakon tsufa?’ Albishirin shi ne, ba nufin Allah ba ne mu yi irin wannan rayuwar. Maimakon haka, ya riga ya ƙudurta cikin ƙauna cewa zai ’yanta mu daga tsufa! Dubi kalmomin da aka furta wa Ayuba, uban iyali, a Ayuba 33:24, 25.
Ka yi la’akari da yanayin da Ayuba ya sami kansa, mutumi mai aminci wanda Jehobah yake ƙauna. Ba da sanin Ayuba ba, Shaiɗan ya ƙalubalanci amincin Ayuba, kuma ya ce yana bauta wa Allah don son kai ne kawai. Jehobah, ya ƙyale Shaiɗan ya jarraba Ayuba saboda tabbacin da yake da shi a Ayuba kuma ya san cewa Yana da ikon kawar da lahani. Sai Shaiɗan ya “buga Ayuba da gyambuna masu-ciwo, tun daga tāfin sawunsa har kan kansa.” (Ayuba 2:7) Tsutsotsi suka rufe jikin Ayuba, kuma fatarsa ta fashe, ta zama baƙi kuma ta sassaɓe. (Ayuba 7:5; 30:17, 30) Ka yi tunanin irin azabar da ya sha. Amma duk da haka, Ayuba ya riƙe amincinsa, yana cewa: “Har in mutu ba ni rabuwa da gaskiyata.”—Ayuba 27:5.
Amma, Ayuba ya yi wani babban kuskure. Sa’ad da yake tunanin cewa zai mutu, sai ya soma damuwa sosai da kunita kansa, “ya maida kansa ya fi Allah gaskiya.” (Ayuba 32:2) Kakakin Allah, Elihu, ya tsauta wa Ayuba. Amma Elihu ya kuma ba Ayuba saƙo mai ƙarfafawa daga Allah: “A cece shi [Ayuba] daga gangarawa cikin rami [kabari], na sami pansa. Namansa za ya komo ya fi na yaro sabontaka; ya komo kwanakin ƙuruciyarsa ke nan.” (Ayuba 33:24, 25) Hakika, waɗannan kalmomin sun sa Ayuba ya kasance da bege sosai. Ba zai ci gaba da shan wahala ba har ya mutu. Idan Ayuba ya tuba, Allah zai yi farin cikin amsar fansa dominsa kuma ya ’yantar da shi daga masifun da yake ciki.a
A cikin tawali’u, Ayuba ya amince da gyarar da aka yi masa, kuma ya tuba. (Ayuba 42:6) Jehobah ya amshi fansa a madadin Ayuba, ya ƙyale fansar ta rufe zunubin Ayuba kuma ta buɗe hanya don Allah ya warkar da shi kuma ya ba shi lada. Jehobah “ya albarkaci ƙarshen Ayuba, har ya fi farkonsa.” (Ayuba 42:12-17) Ɗaya daga cikin albarkar da Ayuba ya samu ita ce, an warkar da muguwar cutar da ke damunsa kuma fatar jikinsa ta “fi na yaro sabontaka,” ka yi tunanin irin murnar da ya yi sa’ad da hakan ya faru!
Fansar da Allah ya amsa a madadin Ayuba tana da iyaka, domin mutumin ya ci gaba da kasancewa ajizi kuma daga baya ya mutu. Muna da fansar da ta fi waccan tamani. Jehobah cikin ƙauna ya ba da Ɗansa, Yesu, a matsayin fansa domin mu. (Matta 20:28; Yohanna 3:16) Dukan waɗanda suka ba da gaskiya da wannan fansar za su sami damar yin rayuwa har abada a cikin aljanna a duniya. A cikin wannan sabuwar duniya mai zuwa, Allah zai ’yantar da ’yan Adam daga tsufa. Me ya sa ba za ka ƙara koya game da yadda za ka rayu a lokacin da tsofaffi za su ga cewa ‘namansu ya fi na yara sabontaka’ ba?
[Hasiya]
a Kalmar nan “pansa” a Ibrananci wadda aka yi amfani da ita a nan tana nufin “rufewa.” Game da Ayuba kuwa, wataƙila yin hadaya da dabba ce fansar, wadda Allah zai karɓa don ya rufe, ko ya gafarta, zunubin Ayuba.—Ayuba 1:5.