Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w11 7/15 pp. 28-32
  • Ka Shiga Cikin Hutun Allah Kuwa?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Shiga Cikin Hutun Allah Kuwa?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Sa’ad da Muke Bukatar Yin Canje-Canje
  • Ka Ci Gaba da Yin Tafiya Tare da Ƙungiyar Jehobah
  • Sa’ad da Wani da Muke Ƙauna Ya Bar Jehobah
  • “Maganar Allah Mai-Rai Ce”
  • Abin da Za Ka Yi Idan Wani a Iyalinku Ya Bar Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
  • Yadda Za a Bi da Wanda Aka Yi wa Yankan Zumunci
    “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah”
  • Mene Ne Hutun Allah?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
w11 7/15 pp. 28-32

Ka Shiga Cikin Hutun Allah Kuwa?

“Maganar Allah mai-rai ce, mai-aikatawa.”—IBRAN. 4:12.

1. Ta yaya za mu shiga cikin hutun Allah a yau, amma me ya sa hakan zai yi mana wuya?

A TALIFIN da ya gabata, mun fahimci cewa za mu iya shiga cikin hutun Allah a yau idan muka yi biyayya ga Jehobah da kuma ƙungiyarsa. Yadda muke yin biyayya zai nuna cewa muna son nufinsa ya cika. Amma wani lokaci yakan kasance da wuya mu yi biyayya. Alal misali, sa’ad da muka koya cewa Jehobah yana son mu daina yin wani abin da muke son yi, zai kasance mana da wuya mu yi masa biyayya nan da nan. Idan hakan ya faru mana, muna bukatar mu koya yadda za mu kasance a “shirye mu yi biyayya.” (Yaƙ. 3:17, NW) A cikin wannan talifin, za mu tattauna wasu yanayi da za su ba mu zarafin nunawa ko muna a shirye mu yi biyayya a dukan lokaci.

2, 3. Mene ne za mu ci gaba da yi don mu faranta wa Jehobah rai?

2 Sa’ad da ka koya daga cikin Littafi Mai Tsarki cewa kana bukatar ka yi canje-canje a rayuwarka, kana a shirye ka yi biyayya? Littafi Mai Tsarki ya ce Allah zai tara wa kansa “muradin dukan dangogi.” (Hag. 2:7) Hakan yana nufin cewa Allah yana zaɓar mutanen da suke da tamani a gare shi domin suna ƙaunar nagarta. Gaskiya ce cewa sa’ad da muka soma nazarin Littafi Mai Tsarki, yawancinmu muna yin abubuwan da ba su da kyau. Amma domin muna ƙaunar Allah da kuma Ɗansa kuma muna son mu faranta ma Allah rai, mun yi farin cikin yin canje-canje a yadda muke tunani da aikatawa. Mun roƙi Jehobah a addu’a don taimako kuma mun yi ƙoƙari mu yi wasu canje-canje da ake bukata. A ƙarshe mun yi baftisma kuma mun samu amincewar Jehobah.—Karanta Kolosiyawa 1:9, 10.

3 Amma har ila mu ajizai ne. Kuma har ila muna bukatar mu yi canje-canje a rayuwarmu don mu yi abin da ya dace. Amma Jehobah ya yi alkawari zai taimake mu idan muka ci gaba da yin iya ƙoƙarinmu don mu faranta masa rai.

Sa’ad da Muke Bukatar Yin Canje-Canje

4. A waɗanne hanyoyi uku ne Jehobah yake nuna mana cewa muna bukatar yin canje-canje?

4 Kafin mu soma yin canje-canje a rayuwarmu, muna bukatar mu san irin canje-canjen da za mu yi. Jehobah zai iya yin amfani da jawabi a Majami’ar Mulki ko kuma wani talifi a cikin mujallunmu da zai sa mu fahimci inda muke yin kuskure. A wasu lokatai ba za mu fahimta ba cewa muna bukatar yin wasu canje-canje ko bayan mun ji jawabin ko kuma karanta wata mujalla, saboda haka Jehobah zai iya yin amfani da ’yan’uwa a cikin ikilisiya don su yi mana gyara.—Karanta Galatiyawa 6:1.

5. A waɗanne hanyoyi ne mukan iya aikata idan wani ya yi mana gargaɗi, kuma me ya sa dattawa za su ci gaba da taimakonmu?

5 Idan ɗan’uwa ajizi ya yi mana gyara, zai iya kasance da wuya mu karɓi abin da ya faɗa ko da ya yi mana magana cikin tawali’u. Amma kamar yadda Galatiyawa 6:1 ta nuna, Jehobah ya ba dattawa umurni cewa su “komo” da mu “cikin ruhun tawali’u.” Idan mun karɓi gargaɗinsu, za mu kasance da tamani a gaban Jehobah. Hakika, a cikin addu’o’inmu muna yawan gaya wa Jehobah cewa mu ajizai ne kuma muna kurakurai da yawa. Amma sa’ad da dattijo ya gaya mana cewa mun yi wani kuskure, a wasu lokatai muna ƙoƙarin ba da dalilan yin hakan, ko kuma mu yi ƙoƙarin sauƙaƙa laifin. Wataƙila mun ce mutumin da ya yi mana gargaɗin ba ya son mu ko kuma bai yi mana magana cikin alheri ba. (2 Sar. 5:11) Ko kuma mun yi fushi sosai ko kuma mu aikata yadda bai dace ba domin dattijo ya yi wa wani cikin iyalinmu gargaɗi a kan wani abu da yake yi da ba shi da kyau ko kuma ya yi mana gargaɗi a kan adon da muke yi da bai dace ba ko cewa muna bukatar mu kasance da tsabta ko kuma Jehobah ba ya son irin nishaɗin da muke yi. Amma bayan mun huce, muna iya amince cewa abin da ya faɗa yana da amfani a gare mu.

6. Ta yaya kalmar Allah take bayyana “tunanin zuciya da nufe-nufenta”?

6 Ayar Nassi na wannan talifin ta gaya mana cewa Kalmar Allah “mai-aikawa” ce. Wannan yana nufin cewa Kalmar Allah, tana da ikon taimakon mutane su canja rayukansu. Kalmarsa ta taimaka mana mu yi wasu canje-canjen da muke bukata kafin mu yi baftisma da kuma bayan mun yi hakan. A cikin wasiƙarsa ga Ibraniyawa Kiristoci, Bulus ya sake rubuta cewa Kalmar Allah tana “hudawa har zuwa mararrabar rai da ruhu da gaɓaɓuwa da ɓargo kuma, tana kuwa da hanzari ga ganewar tunanin zuciya da nufe-nufenta.” (Ibran. 4:12) A wata sassa, sa’ad da muka fahimci nufin Allah sarai a gare mu, ayyukanmu za su nuna irin mutane da muke a ciki. Shin da akwai bambanci tsakanin abin da mutane suke gani (“rai”) da irin mutane da ainihi muke a ciki (“ruhu”)? (Karanta Matta 23:27, 28.) Ka yi tunanin abin da za ka yi a yanayi da za mu yi magana a kai yanzu.

Ka Ci Gaba da Yin Tafiya Tare da Ƙungiyar Jehobah

7, 8. (a) Me ya sa wasu Ibraniyawa Kiristoci suke son su ci gaba da bin wasu sashe na Doka da Aka Ba da ta Hannun Musa? (b) Me ya sa za mu ce suna gāba da nufin Jehobah?

7 Da yawa a cikinmu mun san waɗannan kalaman da ke Misalai 4:18 da kyau: “Tafarkin mai-adalci yana kama da haske na ketowar alfijir, wanda ya ke haskakawa gaba gaba har zuwa cikakkiyar rana.” Hakan yana nufin cewa za mu kyautata halinmu kuma mu ƙara fahimtar nufe-nufen Allah da shigewar lokaci.

8 Mun riga mun koyi cewa bayan mutuwar Yesu, Kiristoci Ibraniyawa da yawa sun so su ci gaba da bin Dokar da Aka Ba da ta Hannun Musa. (A. M. 21:20) Bulus ya bayyana sarai cewa Kiristoci ba sa bukatar su bi Dokar da Aka Ba da ta Hannun Musa, amma wasu har ila ba su amince da abin da Jehobah yake bukata a gare su ba. (Kol. 2:13-15) Wataƙila sun ji cewa idan sun ci gaba da bin wasu sashen na Dokar, ba za a tsananta musu ba. Amma Bulus ya bayyana wa Ibraniyawa Kiristoci dalla-dalla cewa idan suka ci gaba da saɓa wa nufin Allah, ba za su shiga cikin hutun Allah ba.a (Ibran. 4:1, 2, 6; karanta Ibraniyawa 4:11.) Don su samu amincewar Jehobah, suna bukatar su yarda cewa Jehobah yana son mutanensa su bauta masa a wata hanya yanzu.

9. Wane hali ne ya kamata mu kasance da shi sa’ad da aka yi wasu gyare-gyare game da fahiminmu na batutuwa na Nassi?

9 A kwanan nan, an yi gyare-gyare a fahiminmu na wasu koyarwar Littafi Mai Tsarki. Ya kamata mu yi farin ciki game da waɗannan canje-canjen domin Jehobah yana amfani da bawan nan mai aminci mai hikima don ya koya mana gaskiya. A wasu lokatai Hukumar Mulki, wadda ke wakiltar bawan nan mai aminci, mai hikima, tana bitar fahiminmu game da wasu koyarwar. Idan waɗannan ’yan’uwa maza suka ga cewa ana bukatar a yi canje-canje, ba sa jin tsoron gyara yadda suka bayyana wasu koyarwa a dā ko kuma ƙara bayyana batun sarai. Sun san cewa wasu za su faɗa mummunan abubuwa game da bawan nan mai aminci, mai hikima domin waɗannan canje-canje, amma hakan bai dame su ba. Abin da ya fi muhimmanci a gare su shi ne su ba da haɗin kai ga nufin Allah. Yaya kake ji sa’ad da aka yi wani gyara a yadda muka fahimci wata koyarwa ta Littafi Mai Tsarki?—Karanta Luka 5:39.

10, 11. Mene ne wasu ’yan’uwa suka yi sa’ad da suka ji cewa an tsara sababbin hanyoyin yin wa’azi?

10 Bari mu yi la’akari da wani misali. A misalin shekaru ɗari da suka shige, wasu cikin Ɗaliban Littafi Mai Tsarki da suke ba da jawabai masu kyau ga jama’a suna ganin cewa ba da jawabai ita ce hanya mafi kyau da za su yi wa’azi. Suna son yin magana a gaban mutane. Wasu cikinsu suna farin ciki sosai sa’ad da mutane suka yabe su don jawabansu. Amma daga baya, ya kasance a bayane cewa Jehobah yana son mutanensa su shagala a hanyoyi dabam dabam na yin wa’azi, har da wa’azi gida zuwa gida. Wasu cikin waɗannan masu ba da jawabai da kyau ba sa son yin hakan. Jawabansu ya sa mutane su riƙa tunani cewa suna ƙaunar Jehobah kuma suna masa biyayya, amma ayyukansu a wannan yanayin sun nuna cewa ba sa hakan. Mun san cewa Jehobah bai yi farin ciki da ayyukansu ba. Sun bar ƙungiyarsa.—Mat. 10:1-6; A. M. 5:42; 20:20.

11 Ya kuma yi wa ’yan’uwa da yawa wuya su yi wa’azi gida zuwa gida, musamman da farko. Amma sun yi biyayya kuma sun kasance da aminci ga ƙungiyar Jehobah. Da shigewar lokaci, ya yi musu sauƙi su yi wa’azi gida zuwa gida. Jehobah ya albarkace su sosai. Mene ne za ka yi sa’ad da bawan nan mai aminci mai hikima ya gaya maka ka yi ƙoƙari ka gwada wata hanyar wa’azi da ba ka taɓa yi a dā ba? Kana yin biyayya ko idan wannan hanyar yin wa’azi kamar yana da wuya sosai a gare ka?

Sa’ad da Wani da Muke Ƙauna Ya Bar Jehobah

12, 13. (a) Me ya sa Jehobah ya gaya mana mu kori mugun nan daga cikinmu? (b) Mene ne zai iya kasance yanayi mai wuya ga iyaye Kiristoci?

12 Babu shakka mun yarda cewa don mu faranta wa Jehobah rai, dole ne mu yi biyayya ga umurni na mu kasance da tsabta a kowace hanya. (Karanta Titus 2:14.) Amma da akwai yanayi da zai iya sa ya yi mana wuya mu yi biyayya ga wannan umurnin. Alal misali, ka yi tunanin wannan yanayin: Ma’aurata Kirista masu aminci suna da ɗa guda kaɗai kuma ɗan ya bar gaskiya. Ya fi son “nishatsin zunubi domin ’yan kwanaki” maimakon abotarsa da Jehobah da kuma iyayensa. Domin ayyukansa, ba zai kasance sashen ƙungiyar kuma ba. Saboda hakan, ikilisiyar ta yi masa yankan zumunci.—Ibran. 11:25.

13 Iyayen sun yi baƙin ciki sosai! Sun san cewa Littafi Mai Tsarki ya ce ‘Kada ku yi cuɗanya da duk wanda ake kira ɗan’uwa, mai bi, in yana fasiki, ko makwaɗaici, ko matsafi, ko mai zage-zage, ko mashayi, ko mazambaci, kada ku ko ci abinci da irin waɗannan.’ Ya kuma ce: “Ku kori mugun nan daga cikinku.” (1 Kor. 5:11, 13, Littafi Mai Tsarki) Sun fahimci cewa kalmar nan “duk wanda” ta ƙunshi waɗanda suke cikin iyalin da ba sa zama cikin gida ɗaya. Amma domin suna ƙaunar ɗansu sosai, suna iya yin tunani: ‘Muna bukatar mu riƙa magana da ɗanmu sosai. Ba za mu iya taimaka wa ɗanmu ya dawo ga Jehobah, idan ba za mu iya yin magana da shi ba.”b

14, 15. Mene ne ya wajaba iyaye su tuna da shi sa’ad da suke tsai da shawara ko za su yi magana da ɗansu da aka yi wa yankan zumunci?

14 Muna baƙin cikin ganin cewa waɗannan iyaye suna wahala. Ɗansu yana iya zaɓa ya daina bin salon rayuwa marar kyau. Amma ya ci gaba da yin abu marar kyau fiye da yadda yake yin cuɗanya da iyayensa da kuma ikilisiyar. Iyayen suna son su taimaki ɗansu, amma ba za su iya hana shi yin abin da ya tsai da shawara cewa zai yi ba. Shi ya sa suke baƙin ciki sosai!

15 Amma mene ne waɗannan iyaye ƙaunatattu za su yi? Shin za su yi biyayya ga umurnin Jehobah da ke a bayane? Gaskiya ce cewa da akwai wasu lokatai da za su bukaci su yi wa ɗansu magana game da “batutuwan da suka dace na iyali.” Sa’ad da suke tsai da shawara game da wannan, dole ne su tuna abin da Jehobah yake son su yi. Nufinsa shi ne ƙungiyar ta kasance da tsabta, kuma masu laifi su dawo hankalinsu idan zai yiwu. Ta yaya iyaye Kiristoci za su goyi bayan wannan nufin?

16, 17. Mene ne za mu iya koya ta yin bimbini a kan misalin Haruna?

16 Ɗan’uwan Musa, Haruna ya fuskanci wani yanayi mai wuya game da abin da ’ya’yansa biyu suka yi. ’Ya’yansa Nadab da Abihu sun miƙa hadaya a hanyar da Jehobah bai amince ba kuma Jehobah ya halaka su. Hakika, wannan ya kawo ƙarshe ga cuɗanya da suka yi da iyayensu. Amma, ba shi ke nan ba. Jehobah ya umurci Haruna da ’ya’yansa masu aminci: “Kada ku saki gashin kanku, kada kuwa ku tsatsage tufafinku [da sassafe]; domin kada ku mutu, kada kuma [Jehobah] ya yi fushi da dukan jama’a.” (Lev. 10:1-6) Saƙon a bayane yake. Dole ne mu ƙaunaci Jehobah sosai fiye da marasa aminci da suke cikin iyalinmu.

17 A yau, Jehobah ba ya halaka waɗanda suke ƙin bin dokokinsa nan da nan. Yana ba su zarafi cikin ƙauna don su tuba daga yin ayyukan da ba su da kyau. Ta yaya Jehobah zai ji, idan iyaye suka yi rashin biyayya da umurninsa kuma suna tunanin cewa suna da dalilai na ci gaba da yin cuɗanya da ɗansu ko ’yarsu da aka yi wa yakan zumunci?

18, 19. Waɗanne albarka ne waɗanda suke cikin iyali za su samu idan suka ci gaba da kasancewa da aminci ga Jehobah?

18 Yawanci da aka yi musu yakan zumunci a yanzu sun amince cewa mataki mai ƙarfi da abokansu da mutanen iyalinsu suka ɗauka ya taimaka musu su dawo cikin hankalinsu. Alal misali, wata matashiya ta gaya wa dattawa cewa abu ɗaya da ya sa ta canja hanyar rayuwarta shi ne yadda wanta ya bi da ita. Ya kasance da aminci ga Jehobah kuma ya yi biyayya ga umurninsa sa’ad da aka yi mata yankan zumunci. Hakan ya sa ta so ta dawo cikin ƙungiyar Jehobah.

19 Mene ne muke bukatar yi? Muna bukatar mu yi biyayya ga Jehobah a dukan yanayi a rayuwa. Domin mu ajizai ne, hakan zai yi mana wuya a wasu lokatai. Amma, ya kamata mu gaskata cewa hanyar da Allah yake bi da matsalolinmu shi ya fi kyau.

“Maganar Allah Mai-Rai Ce”

20. A waɗanne hanyoyi biyu ne za mu iya fahimtar Ibraniyawa 4:12? (Duba hasiya.)

20 Sa’ad da Bulus ya rubuta a littafin Ibraniyawa 4:12 cewa: “Maganar Allah mai-rai ce” ba ya magana game da Littafi Mai Tsarki.c Sauran ayoyi a wannan surar sun nuna cewa yana magana game da alkawuran Allah. Bulus yana magana cewa alkawuran Allah suna cikawa a koyaushe. Jehobah ya ce game da kalmarsa: “Ba za ta koma wurina wofi ba.” Kuma ya ce: “Za ta cika abin da na nufa, za ta yi albarka kuma a cikin saƙona.” (Isha. 55:11) Saboda haka, dole ne mu yi haƙuri idan Allah bai cika alkawuransa ba sa’ad da muke son ya yi hakan. Muna da tabbaci cewa Jehobah yana aiki don ya cika nufinsa.—Yoh. 5:17.

21. Ta yaya Ibraniyawa 4:12 zai iya taimaka wa tsofaffi su ci gaba da bauta wa Jehobah?

21 Waɗanda suke cikin “taro mai-girma” da yawa sun bauta wa Jehobah cikin shekaru da yawa. (R. Yoh. 7:9) Ba su yi tsammani ba cewa za su yi tsufa a wannan muguwar duniya. Amma har ila suna iya ƙoƙarinsu a hidimar Jehobah. (Zab. 92:14) Sun san cewa maganar Allah mai-rai ce kuma cewa alkawuran Jehobah za su cika. Sun san cewa yana aiki don ya cika nufinsa ga duniya da kuma ’yan Adam. Domin nufin Allah yana da muhimmanci a gare shi, yana sa shi farin ciki sa’ad da muka nuna cewa nufinsa yana da muhimmanci a gare mu. A wannan lokacin hutu na kwana bakwai, babu abin da zai hana Jehobah cika nufinsa. Kuma ya san cewa mutanensa a matsayin rukuni za su ci gaba da ba da haɗin kai ga nufinsa. Kai kuma fa? Ka shiga cikin hutun Allah?

[Hasiya]

a Shugabannin addinin Yahudawa da yawa sun yi ƙoƙari su bi kome da Dokar da Aka Ba da ta Hannun Musa ta faɗa. Amma sa’ad da Yesu ya zo duniya, ba sa son su gaskata cewa shi Almasihu ne. Sun yi gāba da nufin Allah.

b Ka duba littafin nan “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah,” shafuffuka na 207-209.

c A yau, Allah yana mana magana ta hanyar Littafi Mai Tsarki. Littafi Mai Tsarki yana da ikon canja rayukanmu. Saboda haka, abin da muka karanta a Ibraniyawa 4:12 game da Littafi Mai Tsarki gaskiya ce.

Ka Tuna?

• Mene ne muke bukatar yi don mu shiga cikin hutun Allah a yau?

• Sa’ad da muka fahimta daga Littafi Mai Tsarki abin da Allah yake son mu yi, ta yaya muke nunawa cewa muna son mu faranta wa Allah rai?

• A waɗanne hanyoyi ne yin biyayya ga ja-gorar Nassi za ta iya kasance mana da wuya, amma me ya sa yake da muhimmanci sosai mu yi biyayya?

• A waɗanne hanyoyi biyu ne za mu iya fahimtar Ibraniyawa 4:12?

[Hoto a shafi na 31]

Iyayen sun yi baƙin ciki sosai!

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba