Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w11 8/15 pp. 6-7
  • Wasu Hanyoyin Yin Bauta ta Iyali da Nazari na Kai

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Wasu Hanyoyin Yin Bauta ta Iyali da Nazari na Kai
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Makamantan Littattafai
  • Taimako ga Iyalai
    Hidimarmu Ta Mulki—2011
  • Shawara a kan Yin Nazari
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Mece Ce Bauta ta Iyali?
    Su Wane Ne Suke yin Nufin Jehobah A Yau?
  • Yin Taro don Ibada
    Mulkin Allah Yana Sarauta!
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
w11 8/15 pp. 6-7

Wasu Hanyoyin Yin Bauta ta Iyali da Nazari na Kai

A FARKON shekara ta 2009, ikilisiyoyin Shaidun Jehobah sun soma yin taron yamma ɗaya kawai a kowanne mako maimakon yamma biyu. Saboda wannan canjin, Hukumar Mulki ta ƙarfafa mu mu yi amfani da yamma guda a mako don bauta ta iyali da kuma nazari na kai. Shin kana yin amfani da wannan lokacin da kyau? Kana amfana sosai kuwa?

Me ya kamata mu yi nazarinsa a lokacin bautarmu ta iyali? Hukumar Mulki ba ta gaya wa iyalai abin da ya kamata su nazarta kowanne mako ba. Tun da kowace iyali tana da nata bukatu, ya kamata shugabanan iyalai ko ɗai-ɗanmu mu yi tunani a kan bukatun iyalin da kuma abin da zai taimaka mana sosai.

Wasu iyalai suna shirya tarurrukan ikilisiya tare. Amma ba shi ke nan abin da za mu iya yi a bauta ta iyali ba ne. Wasu iyalai suna karanta Littafi Mai Tsarki ko kuma su tattauna wasu talifofi na littattafanmu tare. Wasu kuma suna shirya wasan kwaikwayo na labarin Littafi Mai Tsarki. Wannan yana da amfani sosai don ƙananan yara. Bai kamata bautarmu ta iyali ta ɗauki fasalin tarurruka na ikilisiya ba, inda muke karanta sakin layi kuma mu yi tambayoyi. Ya kamata lokacin bauta ta iyali ya zama lokacin da za mu iya tattauna da kuma faɗi abin da ke cikin zuciyarmu. Lokaci ne da za mu iya yin amfani da idanunmu na zuci kuma mu yi tattaunawa mai daɗi a kan abin da muka karanta a cikin Littafi Mai Tsarki. Da hakan, yamman za ta kasance lokacin farin ciki ga kowa a cikin iyalin.

Wani mahaifi mai ’ya’ya uku ya rubuta: “Iyalina takan karanta ayoyin Littafi Mai Tsarki na makon don bautarsu ta iyali. Da farko kowa yana karanta ayoyin. Sai yaran su zaɓi abin da za su so su daɗa nazarta. Sai su gaya wa iyayensu abin da suka koya daga baya. Michael ɗan shekara 7 yana yawan zana hoto ko kuma ya rubuta wani abu a kan abin da ya karanta. A wasu lokatai David da Kaitlyn masu shekara 13 da 15 suna iya rubuta game da wani labari na Littafi Mai Tsarki kamar suna kallon abin da yake faruwa. Alal misali, akwai makon da iyalin ta karanta Farawa sura 40 game da lokacin da Yusufu ya bayyana wa bayi biyu na Fir’auna ma’anar mafarkansu. Kuma Kaitlyn ta rubuta game da wannan kamar tana cikin kurkukun tana kallon abin da yake faruwa.”

Wannan misali ne na abin da iyalai za su iya yi a lokacin bautarsu ta iyali. Tun da yadda muke ya bambanta, kowanne mutum ko iyali za ta iya tsai da shawara a kan abin da ta fi so. Akwati na gaba ya ba mu wasu shawara game da abin da za mu iya yi a lokacin bautarmu ta iyali ko kuma nazari na kai. Za ka iya tunani a kan wasu hanyoyi ma.

[Akwati/​Hoto a shafi na 6, 7]

Don iyalai masu yara da ba su kai shekara ashirin ba:

• Ku karanta kuma ku tattauna littattafan nan Questions Young People Ask—Answers That Work.

• Ku gwada yanayin “Idan . . kuma fa?” (Ku duba Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Yuni, 1996, shafi na 12, sakin layi na 17-18.)

• Ku yi magana game da maƙasudai na dogon lokaci da kuma na ɗan lokaci da za a iya cim ma.

• Lokaci lokaci, ku kalli kuma ku tattauna bidiyo da ke bisa Littafi Mai Tsarki.

• Ku tattauna talifin nan “Domin Matasa” a cikin Hasumiyar Tsaro.

Don ma’aurata da ba su da yara:

• Ku tattauna babi na 1 da 3 da 11 zuwa 16 na littafin nan Asirin Farinciki na Iyali.

• Ku tattauna abin da kuka gano daga bincike da kuka yi na karatun Littafi Mai Tsarki.

• Ku shirya Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya ko kuma Nazarin Hasumiyar Tsaro.

• Ku tattauna hanyoyi da za ku faɗaɗa hidimarku a matsayin ma’aurata.

Don ’yan’uwa maza da mata da ba su yi aure ba ko waɗanda iyalinsu ba masu bi ba ne:

• Ku yi nazarin sababbin littattafai da aka fito da su a taron gunduma.

• Ku karanta sabo da kuma tsofaffin Yearbook.

• Ku yi bincike a kan tambayoyi da ake yawan yi a yankinku.

• Ku shirya gabatarwa da za ku yi a hidimar fage.

Don iyalai masu ƙananan yara:

• Ku yi wasan kwaikwayo na labaran Littafi Mai Tsarki.

• Ku yi wasanni da za su sa ku yi tunani, kamar waɗanda suke shafi na 30 da 31 na Awake!

• Jifa-jifa ku yi wani abu da zai sa a yi kwatanci a zuci (Ka duba “Kwalliya Ce da Ke Biyan Kuɗin Sabulu!” a cikin Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Fabrairu, 2011, shafi na 11.)

• Ku tattauna talifin nan “Ku Koyar da Yaranku” a cikin Hasumiyar Tsaro.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba