An Fallasa Wanda Yake Mulkin Duniya a Ɓoye
AKWAI lokacin da Yesu ya gaya wa mutane cewa, “za a fitar da mai-mulkin wannan duniya.” Daga baya ya ce, ‘mai mulkin duniyar nan ba shi da wani hannu a kaina’ kuma “an yi wa sarkin duniyan nan shari’a.” (Yohanna 12:31; 14:30, 16:11; Littafi Mai Tsarki) Game da wane ne Yesu yake magana?
Idan muka yi la’akari da abin da Yesu yake cewa game da “mai mulkin wannan duniya,” a bayyane yake cewa ba ya nufin Ubansa, Jehobah Allah. To, wane ne “mai-mulkin wannan duniya”? Ta yaya za a “fitar da” shi kuma a wace hanya ce aka yi masa “shari’a”?
‘Mai Mulkin Wannan Duniyar’ Ya Bayyana Kansa
Kamar yadda gogaggen mai aikata laifi yake yin alfahari da ikonsa, Iblis ya yi alfahari da ikonsa sa’ad da yake jarraba Yesu, Ɗan Allah. Bayan ya nuna wa Yesu “dukan mulkokin” duniya, Shaiɗan ya ce masa: “A gareka zan bada wannan sarauta duka, da ɗaukakarsu; gama ni aka ba; dukan wanda na nufa kuma, sai in ba shi. Idan fa kai ka yi sujada a gabana, duka za ya zama naka.”—Luka 4:5-7.
Idan Iblis tunani ne a zukatan mutane da ke sa su aikata mugunta, kamar yadda wasu suka ce, ta yaya za mu fahimci wannan jarrabawa? Shin wani mugun tunani da ke zuciyar Yesu ne ya jarraba shi ko kuma ruɗewa ce da ta biyo bayan baftismarsa? Idan haka ne, me ya sa aka ce “a cikinsa kuwa babu zunubi”? (1 Yohanna 3:5) Maimakon ya musanta ikon da Iblis yake da shi bisa ’yan Adam, Yesu ya tabbatar da hakan sa’ad da ya kira shi “sarkin duniya,” kuma ya kwatanta shi da “mai-kisan kai” da kuma “maƙaryaci.”—Yohanna 14:30; 8:44.
Bayan wajen shekara 70 da haɗuwar Kristi da Iblis, manzo Yohanna ya tuna wa Kiristoci tasiri mai girma da Shaiɗan yake da shi, yana cewa “duniya duka kuwa tana kwance cikin Shaitan.” Yohanna ya ce shi ne mai “ruɗin dukan duniya.” (1 Yohanna 5:19; Ru’ya ta Yohanna 12:9) A bayyane yake cewa Littafi Mai Tsarki yana magana ne a kan wani ruhun da ba a gani, wanda shi ne “sarkin duniya.” Amma yaya girman tasirin da yake da shi a kan ’yan Adam?
Sarkin Duniya Ya Ba da Iko ga Abokansa
Sa’ad da yake rubutu game da faɗan bangaskiya da Kiristoci suke yi, manzo Bulus ya bayyana magabtansu mafi girma ɓaro-ɓaro. Ya ce: “Gama kokuwarmu ba da nama da jini take ba, amma da mulkoki, da ikoki, da mahukuntan wannan zamani mai-duhu, da rundunai masu-ruhaniya na mugunta cikin sammai.” (Afisawa 6:12) Saboda haka, wannan faɗan ya fi ƙarfin ’yan Adam, domin faɗan “ba da nama da jini” ake yi ba, amma da “rundunai masu-ruhaniya na mugunta.”
Furucin nan “rundunai masu-ruhaniya na mugunta” yana nufin mugayen halittun ruhohi masu iko, ba kawai wani mugun tunani ba. Saboda haka, Iblis yana nuna ikonsa ne ta hanyar mala’ikun da suka yi tawaye ‘waɗanda ba su riƙe matsayin su ba.’—Yahuda 6.
Annabcin Daniyel da ke Littafi Mai Tsarki ya bayyana yadda “mahukuntan wannan zamani” suke sarautar duniya tun zamanin dā. Cike da damuwa game da ’yan’uwansa Yahudawa da suka koma Urushalima daga zaman bauta a ƙasar Babila a shekara ta 537 K.Z., annabi Daniyel ya yi addu’a a madadinsu har tsawon mako uku. Wani mala’ikan da Allah ya aika don ya ƙarfafa annabin ya gaya masa dalilin da ya sa bai zo da wuri ba. Ya ce: “Sarkin mulkin Persia ya yi mani tsayayya kwana ashirin da ɗaya.”—Daniyel 10:2, 13.
Wane ne wannan ‘sarkin Persia’? Hakika, mala’ikan ba ya nufin Sarki Cyrus na Farisa wanda a lokacin ya yi wa wa Daniyel da mutanensa alfarma. Ƙari ga haka, ta yaya za a ce sarki ɗan Adam ya yi tsayayya da ruhu har tsawon makonni uku bayan da mala’ika ɗaya ne tak ya halaka gwarzayen mayaƙa guda 185,000 cikin dare guda? (Ishaya 37:36) Wannan mugun ‘sarkin Persia’ wakilin Iblis ne, wato, wani aljani da aka ba iko bisa Daular Farisa. Daga baya a cikin labarin, mala’ikan Allah ya ce zai sake yaƙar “sarkin Persia” da kuma wani sarki aljani, “sarkin Hellas.”—Daniyel 10:20.
Mene ne za mu iya kammalawa daga wannan labarin? A taƙaice, akwai sarakuna aljanu masu iko, wato, “mahukuntan wannan zamani” waɗanda ba a gani da ido, kuma suna juya duniya a ƙarƙashin ikon shugabansu, Shaiɗan Iblis. Amma, har yanzu mene ne muradinsu?
Sarkin Duniya Ya Bayyana Kansa
A Ru’ya ta Yohanna, littafi na ƙarshe a cikin Littafi Mai Tsarki, , manzo Bulus ya bayyana yadda Yesu, wato, Mika’ilu shugaban mala’iku, ya ci nasara a kan Iblis da aljanunsa kuma ya ambata munanan sakamakon da za su biyo bayan koro su daga sama. Mu karanta: “Kaiton duniya . . . domin Shaiɗan ya sauko wajenku, hasala mai-girma kuwa gare shi, domin ya san sauran zarafinsa kaɗan ya rage.”—Ru’ya ta Yohanna 12:9, 12.
Ta yaya Iblis ya nuna hasala sosai? Kamar yadda da dama cikin masu aikata laifi suke da ra’ayin ‘a mutu ko a yi rai,’ Iblis da aljanunsa sun ƙudurta ɓata duniya kuma su yi mutuwar kasko da mazauna cikin ta. Sanin cewa lokacinsa ya ƙure, Iblis yana amfani da ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da ke tsakanin al’ummar da ke ƙarƙashin ikonsa, wato, manyan kasuwanci, domin ya ɗaukaka halin sayen abubuwa , wanda yake kai ga ƙarewar arzikin ƙasa da ɓata mahalli a ko’ina a duniya, kuma hakan yana yi wa rayuwar ’yan Adam barazana.—Ru’ya ta Yohanna 11:18; 18:11-17.
Tun farkon tarihin ’yan Adam, halin Shaiɗan na son yin mulki ya bayyana a siyasa da addini. Littafin Ru’ya ta Yohanna ya kwatanta ikon ’yan siyasa a matsayin bisashen da Iblis ya ba “iko mai girma.” Ya kuma nuna cewa ƙawancen da ke tsakanin addini da siyasa abin kunya ne, shi ya sa ya kira hakan karuwanci ta ruhaniya. (Ru’ya ta Yohanna 13:2; 17:1, 2) Ka yi tunanin zalunci da zaman bauta da yaƙe-yaƙe da kuma faɗace-faɗace tsakanin ƙabilu da suke aukuwa ƙarnuka da dama yanzu, waɗanda suka jawo hasarar miliyoyin rayuka. Akwai wanda zai iya cewa abubuwan da suka faru da suka razanar da mutane a tarihin ’yan Adam aikin hannun mutane ne kawai? Ko kuma hakan sakamakon tasirin miyagun ruhohi ne?
Littafi Mai Tsarki ya fallasa wanda yake juya shugabanni ’yan Adam da kuma ƙasashe masu iko a duniya. A sane ko cikin rashin sani, al’ummar ’yan Adam tana nuna irin halin shugabanta da kuma halinsa na ‘a mutu ko a yi rai.’ Amma har yaushe ’yan Adam za su ci gaba da shan wahala a ƙarƙashin mulkin Iblis?
Ƙarshen Iblis
Hidimar Kristi a duniya a ƙarni na farko ya nuna cewa ƙarshen Iblis da aljanunsa ya kusa. Sa’ad da almajiran Yesu suka gaya masa yadda suka fitar da aljanu, ya ce musu: “Na ga Shaiɗan ya faɗo daga sama kamar walƙiya.” (Luka 10:18, Littafi Mai Tsarki) Waɗannan kalmomi sun nuna cewa Yesu yana murna saboda nasarar da zai ci nan gaba bisa mai mulkin duniya da zarar Yesu ya koma sama a matsayin Mika’ilu shugaban mala’iku. (Ru’ya ta Yohanna 12:7-9) Cikakken nazarin annabce-annabcen da ke cikin Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa wannan nasarar ta samu ne a sama a shekara ta 1914 ko jim kaɗan bayan hakan.a
Tun daga lokacin, Iblis ya san cewa halakarsa ta kusa. Ko da yake ‘duniya duka kuwa tana kwance cikin ikonsa,’ akwai miliyoyin mutanen da bai yi nasarar yaudara ba duk da ƙoƙarce-ƙoƙarcensa na son yin tasiri a kan su. Littafi Mai Tsarki ya wayar musu da kai game da ko shi wane ne da kuma dabarunsa. (2 Korintiyawa 2:11) Suna samun bege daga kalmomin Bulus ga ’yan’uwa Kirista: “Allah na salama in an jima za ya ƙuje Shaiɗan daga ƙarƙashin sawayenku.”b—Romawa 16:20.
Ba da daɗewa ba, za a halaka Iblis! A ƙarƙashin sarautar da Kristi zai yi cikin ƙauna, mutane adilai za su mai da duniya ta zama aljanna. Mugunta da ƙiyayya da haɗama za su shuɗe har abada. “Ba za a tuna da al’amura na dā ba,” in ji Littafi Mai Tsarki. (Ishaya 65:17) Babu shakka, dukan waɗanda suka yi tsayayya da mai mulkin duniya a ɓoye kuma suka guje wa tasirinsa za su samu kwanciyar rai!
[Hasiya]
a Don ƙarin bayani game da wannan shekarar, ka duba rataye na wannan littafin Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? shafuffuka na 215 zuwa 218, Shaidun Jehobah ne suka wallafa.
b Waɗannan kalmomin Bulus suna maimaita annabcin farko a cikin Littafi Mai Tsarki da aka rubuta a Farawa 3:15, wanda yake nuni ga halakar Iblis a nan gaba. Don ya kwatanta abin da zai faru, Bulus ya yi amfani da wata kalma a Helenanci da take nufin “a ragargaje, warwatsa, farfasa ta wajen murƙushewa.”—Vine’s Complete Expository Dictionary of Old and New Testament Words.
[Bayanin da ke shafi na 5]
A ƙarƙashin sarautar da Kristi zai yi cikin ƙauna, mutane adilai za su mai da duniya ta zama aljanna