Tambayoyi Daga Masu Karatu
Ta yaya mutuwar amintattun bayin Allah ‘abu mai daraja ne a gaban Jehobah’?
▪ Wani marubucin zabura da aka hure ya rera waƙa: “Mutuwar ɗaya daga cikin tsarkakansa, Abu mai daraja ne!” (Zab. 116:15) Jehobah yana daraja ran kowanne bawansa. Amma, Zabura sura ta 116 ba ta magana game da mutuwar bawan Jehobah guda ɗaya kawai.
Sa’ad da muke ba da jawabin wani ɗan’uwa Kirista da ya rasu, ba zai dace ba mu karanta Zabura 116:15 kuma mu bayyana cewa wannan ya shafi ɗan’uwan ko da yana bauta wa Jehobah da aminci. Me ya sa? Domin wannan kalamin marubucin zabura yana da wata ma’ana dabam. Hakan yana nufin cewa Jehobah ba zai ƙyale a halaka amintattun bayinsa gabaki ɗaya ba domin yana ɗaukansu da tamani.—Duba Zabura 72:14; 116:8.
Littafin Zabura 116:15 ya tabbatar mana cewa Jehobah ba zai ƙyale a halaka amintattun bayinsa gabaki ɗaya daga duniya ba. Tarihinmu ya nuna cewa mun riga mun jimre da gwaje-gwaje da tsanantawa masu tsanani. Kuma hakan ya sa mu kasance da tabbaci cewa Allah ba zai ƙyale a halaka mu gabaki ɗaya daga duniya ba.
Domin Jehobah shi ne mai iko duka kuma dole ne ya cika nufinsa, ba zai ƙyale kowa ya halaka mu a matsayin rukuni ba. Idan Allah ya ƙyale hakan ya faru, za a yi tunani cewa maƙiyansa sun fi shi ƙarfi. Amma, hakan ba zai taɓa yiwu ba. Nufin Jehobah ne cewa amintattun mutane su kasance a duniya har abada, kuma babu shakka, hakan zai faru. (Isha. 45:18; 55:10, 11) Idan dukan bayin Jehobah da ke duniya sun mutu, hakan zai sa a daina bauta wa Jehobah a duniya. Kuma, mutanen da za su zama “sabuwar duniya,” wato, amintattun bayin Jehobah da za su kasance a ƙarƙashin “sabuwar sama” ba za su kasance ba. (R. Yoh. 21:1) Kuma Yesu ba zai yi Sarauta ta Shekara Dubu ba idan babu amintattun mutane a duniya.—R. Yoh. 20:4, 5.
Idan Allah ya ƙyale maƙiyansa su halaka dukan bayinsa daga duniya, za a yi shakkar matsayinsa da kuma sunansa. Hakan zai nuna cewa Allah ya kasa a matsayinsa na Maɗaukaki. Ƙari ga hakan, don darajarsa da kuma sunansa, Jehobah ba zai yarda a halaka amintattun bayinsa a matsayin rukuni ba. Ka yi la’akari da wannan: Tun da Allah “mara-mugunta” ne, zai kiyaye rukunin mutane da suke bauta masa da aminci. (K. Sha 32:4; Far. 18:25) Kuma, barin maƙiyansa su halaka bayinsa gabaki ɗaya zai saɓa wa Kalmar Allah, wadda ta ce: “Ubangiji ba za ya yar da jama’atasa ba sabili da sunansa mai-girma.” (1 Sam. 12:22) Hakika, “Ubangiji ba za ya yar da mutanensa ba: ba kuwa za ya yi ɓari da gādonsa ba.”—Zab. 94:14.
Sanin cewa ba za a taɓa halaka mutanen Jehobah gabaki ɗaya daga duniya ba abin ƙarfafa ne! Saboda haka, bari mu ci gaba da kasancewa da aminci ga Jehobah, muna dogara ga alkawarinsa, wanda ya ce: “Babu alatun da aka halitta domin cutarki da za ya yi albarka; iyakar harshe kuma da za shi tashi gaba da ke, a shari’a za ki kayar da shi. Gadōn bayin Ubangiji ke nan, adalcinsu wanda shi ke daga wurina, in ji Ubangiji.”—Isha. 54:17.
[Bayanin da ke shafi na 22]
Allah ba zai taɓa ƙyale a halaka bayinsa gabaki ɗaya daga duniya ba