Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 5/15 pp. 23-27
  • Kana Nuna Ɗaukakar Jehobah Kuwa?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kana Nuna Ɗaukakar Jehobah Kuwa?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • MUNA SON MU ƊAUKAKA JEHOBAH
  • NUNA ƊAUKAKAR JEHOBAH
  • BARI MU YI KOYI DA ALLAH
  • KA CI GABA DA ƊAUKAKA JEHOBAH
  • Za Ka Nuna Ɗaukakar Allah Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Kada Ka Ƙyale Kome Ya Hana Ka Samun Girma
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Mu Daukaka Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Su Waye Suke Ɗaukaka Allah A Yau?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 5/15 pp. 23-27

Kana Nuna Ɗaukakar Jehobah Kuwa?

“Muna nuna ɗaukakar Ubangiji kamar madubi.”—2 KOR. 3:18, Littafi Mai Tsarki.

MECE CE AMSARKA?

Me ya sa zai yiwu mu nuna ɗaukakar Jehobah ko da yake mu ajizai ne?

Ta yaya addu’o’inmu da kuma taronmu na Kirista suke taimaka mana mu nuna ɗaukakar Allah?

Mene ne zai taimaka mana mu ci gaba da nuna ɗaukakar Jehobah?

1, 2. Me ya sa zai yiwu mu yi koyi da halayen Jehobah?

DUKANMU mun yi kama da iyayenmu. Kuma wataƙila mun taɓa jin wani ya ce wa ƙaramin yaro, ‘Gaskiya ka yi kama da babanka’ ko ga ƙaramar yarinya, ‘Gaskiya kin yi kama da mamarki.’ Kuma yara suna yin abubuwan da iyayensu suke yi. Amma mu kuma fa? Shin za mu iya yin koyi da Ubanmu na sama, Jehobah? Ko da yake ba mu taɓa ganinsa ba, amma za mu iya sanin halayensa masu kyau ta wajen yin nazarin Kalmarsa. Abubuwan da ya halitta za su kuma iya koya mana game da halayensa masu kyau. Za mu iya yin koyi da halayensa masu kyau ta wajen yin nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma yin bimbini a kan abin da muka karanta, musamman game da abin da Ɗansa Yesu ya ce da kuma yi. (Yoh. 1:18; Rom. 1:20) Zai yiwu mu yi koyi da halayen Jehobah kuma ta hakan za mu iya nuna ɗaukakarsa.

2 Kafin Allah ya halicci Adamu da Hauwa’u, ya san cewa za su iya yin nufinsa da yin koyi da halayensa da kuma ɗaukaka shi. (Karanta Farawa 1:26, 27.) A matsayinmu na Kiristoci muna son mu yi koyi da Allah. Idan mun yi hakan, muna da gatan nuna ɗaukakarsa. Idan muna bin wata al’ada ko kabila ko kuma mun je makaranta ko a’a. Za mu iya nuna ɗaukakar Jehobah. Me ya sa? Domin “Allah ba mai-tara ba ne: amma a cikin kowace al’umma, wanda yake tsoronsa, yana aika adalci kuma, abin karɓa ne gare shi.”—A. M. 10:34, 35.

3. Yaya muke ji yayin da muke bauta wa Jehobah?

3 Kiristoci shafaffu suna nuna ɗaukakar Jehobah. Manzo Bulus wanda shi ma shafaffe ne ya rubuta: “Dukanmu, da fuska ba luluɓi muna [nuna] darajar Ubangiji kamar madubi, muna sākuwa zuwa cikin wannan sura daga daraja zuwa daraja.” (2 Kor. 3:18) Bulus yana magana game da lokacin da Musa ya sauƙo daga Dutsen Sinai riƙe da Dokoki Goma da Allah ya ba shi. Kuma a lokacin, fuskar Musa tana walƙiya kamar wuta mai haske sosai domin Jehobah ya yi magana da shi. (Fit. 34:29, 30) Abin da ya faru da Musa bai taɓa faruwa da mu ba, kuma sa’ad da mutane suka kalli fuskarmu ba ta walƙiya. Amma muna ganin farin cikin da muke samu sa’ad da muka tattauna da wani game da Jehobah da halayensa da kuma nufinsa ga ’yan Adam. Saboda haka, ko mu shafaffu ne ko kuma waɗansu tumaki, muna kama da madubin zamanin dā domin muna nuna ɗaukakar Jehobah a rayuwarmu da kuma hidimarmu. (2 Kor. 4:1) Shin kana nuna ɗaukakar Jehobah ta halayenka da kuma ayyukanka a matsayin mai wa’azin Mulki?

MUNA SON MU ƊAUKAKA JEHOBAH

4, 5. (a) Kamar Bulus, wane fama ne muke yi? (b) Ta yaya zunubi yake shafar mu?

4 A matsayinmu na bayin Jehobah, muna son mu nuna ɗaukakarsa a dukan abubuwan da muke yi. Amma sau da yawa, muna yin abin da bai dace ba ko da yake muna son mu yi abin da ke da kyau. Bulus ma ya fuskanci wannan matsalar. (Karanta Romawa 7:21-25.) Ya bayyana dalilin da ya sa dukanmu muke wannan famar: “Dukan mutane sun yi zunubi, sun kasa kuma ga darajar Allah.” (Rom. 3:23) An haifi dukan mutane cikin zunubi domin Adamu ya yi zunubi. Kuma zunubi yana kama da mugun sarki da ke sarauta.—Rom. 5:12; 6:12.

5 Mene ne zunubi? Zunubi kowane abu ne da bai jitu da halayen Jehobah ba. Kuma abu ne da Jehobah ba ya so kuma ba ya son mu yi. Zunubi yana ɓata dangantakar mutum da Jehobah. Zunubi yana hana mu nuna ɗaukakar Allah, kamar yadda wani abu zai iya hana maharbi samun dabbar da yake son ya harba. A wasu lokatai muna yin zunubi da gangan, amma a wasu kuma ba da gangan ba. (Lit. Lis. 15:27-31) Zunubi yana da tasiri sosai a kan ’yan Adam kuma yana raba su da Mahaliccinsu. (Zab. 51:5; Isha. 59:2; Kol. 1:21) Yawancin mutane suna rayuwa a hanyar da ke raba su da Allah kuma saboda hakan, ba sa nuna ɗaukakar Allah. Babu abin da ke da tasiri a kan ’yan Adam kamar zunubi.

6. Me ya sa zai yiwu mu nuna ɗaukakar Jehobah ko da yake mu ajizai ne?

6 Ko da yake an haife mu cikin zunubi, amma Jehobah ya ba mu bege. (Rom. 15:13) Ya aiko da Ɗansa Yesu Kristi zuwa duniya don ya fanshe mu daga zunubi. Kuma idan mun yi imani ga wannan fansar za mu samu ’yanci daga “bauta wa zunubi,” kuma za mu iya nuna ɗaukakar Jehobah. (Rom. 5:19; 6:6; Yoh. 3:16) Idan mun ci gaba da bauta wa Jehobah yadda ya dace, zai albarkace mu yanzu da kuma a nan gaba. Kuma zai sa mu zama kamilai kuma mu samu rai na har abada. Ko da yake har yanzu mu ajizai ne, amma gata ne sosai mu samu zarafin nuna ɗaukakar Allah!

NUNA ƊAUKAKAR JEHOBAH

7. Idan muna son mu nuna ɗaukakar Allah, mene ne ya kamata mu amince game da kanmu?

7 Idan muna son mu nuna ɗaukakar Jehobah, wajibi ne kowannenmu ya san inda yake da kasawa. (2 Laba. 6:36) Ya kamata mu amince cewa muna da waɗannan kasawar kuma mu magance su don mu iya ɗaukaka Allah. Alal misali, idan muna yin zunubi ta wajen kallon hotunan batsa, wajibi ne mu amince cewa muna bukatar taimako daga wajen dattawa kuma mu ce su taimaka mana. (Yaƙ. 5:14, 15) Wannan matakin ne ya kamata mu fara ɗauka idan muna son mu ɗaukaka Allah. Wajibi ne kuma mu tabbata cewa muna yin rayuwa yadda Jehobah yake so. (Mis. 28:18; 1 Kor. 10:12) Ko da mene ne kasawarmu, dole ne mu ci gaba da yin ƙoƙari don mu kawar da su kuma mu nuna ɗaukakar Allah.

8. Ko da yake mu ba kamilai ba ne, mene ne ya kamata mu yi?

8 Yesu ne kaɗai mutumin da ya taɓa yin rayuwa a duniya kuma ya mutu ba tare da yin zunubi ba ko kuma ƙin nuna ɗaukakar Allah. Ko da yake mu ba kamilai ba ne kamar Yesu, amma ya kamata mu yi koyi da misalinsa. (1 Bit. 2:21) Jehobah yana lura da yadda muke nuna ɗaukakarsa kuma yana lura da ƙoƙarin da muke yi don yin hakan.

9. Ta yaya Littafi Mai Tsarki yake taimaka mana mu nuna ɗaukakar Allah?

9 Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka mana mu fahimci yadda za mu iya nuna ɗaukakar Allah yadda ya dace. Muna bukatar yin nazarin Littafi Mai Tsarki sosai kuma mu yi bimbini a kan abin da ya ce. (Zab. 1:1-3) Karanta Nassosi kullum zai taimaka mana mu samu ci gaba. (Karanta Yaƙub 1:22-25.) Abin da muka koya daga Littafi Mai Tsarki yana ƙarfafa bangaskiyarmu. Ya kuma taimaka mana mu ƙuduri aniya cewa ba za mu yi zunubi mai tsanani da zai ɓata wa Jehobah rai ba.—Zab. 119:11, 47, 48.

10. Ta yaya addu’a za ta taimaka mana mu bauta wa Jehobah yadda ya dace?

10 Idan muna son mu nuna ɗaukakar Allah, ya kamata kuma mu “lizima cikin addu’a.” (Rom. 12:12) Ya kamata mu yi addu’a ga Jehobah don ya taimaka mana mu bauta masa yadda ya dace. Za mu iya roƙonsa ya ba mu ruhunsa mai tsarki da bangaskiya sosai da kuma ƙarfin jimrewa da gwaje-gwaje. Za mu kuma iya roƙonsa ya taimaka mana mu zama malaman Littafi Mai Tsarki da suka ƙware. (2 Tim. 2:15; Mat. 6:13; Luk 11:13; 17:5) Muna bukatar mu dogara ga Ubanmu Jehobah, yadda ƙaramin yaro yake dogara ga mahaifinsa. Idan mun roƙe Jehobah ya taimaka mana mu bauta masa yadda ya dace, za mu iya kasance da tabbaci cewa zai taimaka mana. Kada mu taɓa yin tunani cewa muna damunsa idan mun yi addu’a. Maimakon haka, bari mu ɗaukaka shi a cikin addu’o’inmu, muna masa godiya. Muna kuma roƙonsa cewa ya ja-gorance mu musamman sa’ad da muke fuskantar gwaje-gwaje kuma mu ce ya taimaka mana mu bauta masa yadda ya dace.—Zab. 86:12; Yaƙ. 1:5-7.

11. Ta yaya taron ikilisiya yake taimaka mana mu nuna ɗaukakar Allah?

11 Allah ya ba “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” aikin kula da tumakinsa masu tamani. (Mat. 24:45-47; Zab. 100:3) Bawan nan mai-aminci yana son ya taimaka wa dukanmu mu nuna ɗaukakar Jehobah. Kuma hanya ɗaya da yake yin hakan ita ce ta taron ikilisiya. Taronmu yana taimaka mana mu yi gyare-gyare a halayenmu na Kirista, kamar yadda tela yake yin gyara a tufafinmu don mu fita zan-zan. (Ibran. 10:24, 25) Shi ya sa bai kamata mu riƙa zuwa taro a makare ba. Idan mun saba zuwa taro a makare, ba za mu amfana daga dukan abubuwan da za su iya taimaka mana ba.

BARI MU YI KOYI DA ALLAH

12. Ta yaya za mu iya yin koyi da Allah?

12 Idan muna son mu nuna ɗaukakar Jehobah, dole ne mu “zama fa masu-koyi da Allah.” (Afis. 5:1) Hanya ɗaya da za mu yi koyi da Allah ita ce ta kasancewa da ra’ayinsa. Idan muna abu a hanyar da ba ta jitu da ra’ayinsa ba, za mu ɓata masa rai kuma mu jawo wa kanmu matsala. Tun da duniya tana ƙarƙashin ikon Shaiɗan Iblis, wajibi ne mu yi ƙoƙari mu tsane abubuwan da Jehobah ba ya so kuma mu yi ƙaunar abubuwan da yake so. (Zab. 97:10; 1 Yoh. 5:19) Ya kamata mu kasance da tabbaci cewa hanyar da ta dace ta bauta wa Allah ita ce ta yin abu duka don girmama shi.—Karanta 1 Korintiyawa 10:31.

13. Me ya sa ya wajaba mu tsane zunubi kuma mene ne hakan zai motsa mu mu yi?

13 Jehobah ya tsani zunubi kuma ya kamata mu ma mu yi hakan. Idan mun tsane zunubi, za mu ƙi yin kowanne abu da zai sa mu yi zunubi. Alal misali, ya kamata mu tsane ridda. Waɗanda suka zama ’yan ridda ba sa ɗaukaka Allah. (K. Sha 13:6-9) Saboda haka, ya kamata mu nisanta kanmu daga ’yan ridda ko kuma kowanne mutum da ya ce wai shi ɗan’uwa ne, amma ba ya ɗaukaka Allah. Ya kamata mu yi nisa da shi ko da shi danginmu ne. (1 Kor. 5:11) Ba za mu amfana ba idan muna neman mu bayyana wa ’yan ridda da waɗanda suke kushe ƙungiyar Jehobah cewa ra’ayinsu ba daidai ba ne. Bai ma kamata ba mu so sanin abin da suka ce ko a cikin mujallu ko a Intane domin hakan yana ɓata dangantakarmu da Jehobah.—Karanta Ishaya 5:20; Matta 7:6.

14. A wace hanya ce mafi kyau za mu nuna ɗaukakar Allah kuma me ya sa?

14 Hanya mafi kyau da za mu yi koyi da Jehobah ita ce ta wajen yin ƙauna. (1 Yoh. 4:16-19) Hakika, ƙaunar da muke da ita ga juna tana nuna cewa mu almajiran Yesu ne da kuma bayin Jehobah. (Yoh. 13:34, 35) Ko da yake a wasu lokatai ajizancinmu zai iya sa ya kasance mana da wuya mu nuna ƙauna. Amma ya kamata mu yi ƙoƙari a kowanne lokaci don mu nuna ƙauna. Nuna ƙauna da kuma wasu halayen Kirista za su taimaka mana mu guji yin zunubi da kuma abubuwa marasa kyau.—2 Bit. 1:5-7.

15. Ta yaya ƙauna take shafar dangantakarmu da mutane?

15 Ƙauna tana sa mu so yin abubuwa masu kyau ga mutane. (Rom. 13:8-10) Alal misali, idan mata da miji suna ƙaunar juna, za su kasance da aminci ga juna. Idan muna ƙaunar dattawa kuma muna daraja aikinsu, za mu yi musu biyayya kuma za mu sarayar da kanmu a gare su. Yaran da suke ƙaunar iyayensu suna musu biyayya kuma ba sa zaginsu a baya. Idan muna ƙaunar mutane, ba za mu ɗauke su kamar ba su da muhimmanci ba ko kuma mu yi musu baƙar magana. (Yaƙ. 3:9) Kuma dattawan da suke ƙaunar tumakin Allah suna bin su cikin tausayi.—A. M. 20:28, 29.

16. Ta yaya ƙauna za ta taimaka mana a aikin wa’azi?

16 Ya kamata mu nuna ƙauna ma sa’ad da muke wa’azi. Domin muna ƙaunar Jehobah sosai, ba za mu yi sanyin gwiwa ba idan mutane ba su saurare mu ba. Maimakon haka, za mu ci gaba da yin wa’azin bishara. Za mu yi shiri sosai sa’ad da za mu fita yin wa’azi kuma za mu yi ƙoƙarin koyar da Kalmar Allah sosai. Idan muna ƙaunar Allah da kuma maƙwabtanmu da gaske, ba za mu ɗauki yin wa’azi kamar aiki kawai ba. Amma za mu ɗauke shi a matsayin babban gata kuma za mu yi shi da farin ciki.—Mat. 10:7.

KA CI GABA DA ƊAUKAKA JEHOBAH

17. Da yake mun san cewa zunubi ne yake hana mu nuna ɗaukakar Jehobah, mene ne ya kamata mu yi?

17 Mutane da yawa a duniya ba su san tsananin zunubi ba. Amma mun sani. Kuma, hakan ya sa mu san cewa muna bukatar mu ƙi kowanne abu da zai sa mu yin zunubi. Mun san cewa muna bukatar mu koyar da lamirinmu don ya taimaka mana mu yi abin da ya dace da zarar mun soma tunanin banza. (Rom. 7:22, 23) Muna da kasawa da yawa domin mu ’yan Adam ne, amma Allah zai iya taimaka mana mu yi abin da ya dace a kowane yanayi.—2 Kor. 12:10.

18, 19. (a) Mene ne ke taimaka mana mu yi nasara wajen ƙin rinjayar Shaiɗan da aljanunsa? (b) Mene ne ya kamata mu ƙuduri aniyar yi?

18 Idan muna son mu ɗaukaka Jehobah, dole ne mu tsayayya wa Shaiɗan da aljanunsa. Za mu iya yin nasara idan mun “ɗauki dukan makamai na Allah.” (Afis. 6:11-13) Shaiɗan yana iya ƙoƙarinsa don ya hana ɗaukakar da ya kamata a ba wa Jehobah kaɗai. Shaiɗan yana kuma yin ƙoƙari sosai don ya ɓata dangantakarmu da Allah. Shi ya sa Shaiɗan yake fushi sosai idan mu da kuma miliyoyin mutane ajizai, maza da mata da kuma yara muna kasance da aminci ga Allah. Saboda haka, bari mu ci gaba da yaba wa Jehobah kamar mala’ikun sama da suka ce: “Kai ne mai-isa ka karɓi ɗaukaka da daraja da iko, ya Ubangijinmu da Allahnmu: gama kai ka halicci dukan abu, saboda nufinka kuma suka kasance, saboda nufinka aka halicce su.”—R. Yoh. 4:11.

19 Bari mu ƙuduri aniya cewa za mu ci gaba da ɗaukaka Jehobah. Yana matuƙar farin ciki sa’ad da ya ga bayinsa da yawa suna iya ƙoƙarinsu don su yi koyi da shi kuma su nuna ɗaukakarsa. (Mis. 27:11) Bari mu ji kamar Dauda wanda ya yaba wa Jehobah da dukan zuciyarsa kuma ya rera waƙa: “Ya Ubangiji Allahna, da dukan zuciyata zan yabe ka; in darajanta sunanka kuma har abada.” (Zab. 86:12) Muna ɗokin ganin ranar da za mu nuna ɗaukakar Jehobah yadda ya dace kuma za mu yaba masa har abada. Yin rayuwa a wannan lokacin zai zama abin farin ciki sosai. Shin kana nuna ɗaukakar Allah yanzu, kuma kana ɗokin yin hakan har abada?

[Hotona a shafi na 27]

Shin kana nuna ɗaukakar Jehobah a waɗannan hanyoyin?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba