Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 5/15 pp. 28-30
  • ‘Ku Yi Hankali da Yisti na Farisawa’

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • ‘Ku Yi Hankali da Yisti na Farisawa’
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Makamantan Littattafai
  • “Ku Koya Daga Wurina”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Yesu Ya Yi Warkarwa a Ranar Assabaci
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Ka Yi Koyi da Yadda Jehobah Yake Nuna Adalci da Jin Kai
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 5/15 pp. 28-30

‘Ku Yi Hankali da Yisti na Farisawa’

Yesu ya gargaɗi almajiransa: ‘Ku yi hankali da yisti na Farisawa, munafunci ke nan.’ (Luk 12:1) Matta ma ya rubuta wannan gargaɗin kuma hakan ya taimaka mana mu fahimci cewa yana magana ne game da koyarwar ƙarya da Farisawa suke yi.—Mat. 16:12.

A wasu lokatai, Littafi Mai Tsarki yana yin amfani da ‘yisti’ don bayyana abin da ke gurɓatar da mutum. Babu shakka, koyarwar Farisawa da halinsu suna sa masu sauraronsu su yi abubuwa marasa kyau. Me ya sa koyarwar Farisawa take kamar guba?

1 Farisawa suna da fahariya kuma suna tunani cewa sun fi kowa ƙaunar Allah.

Yesu ya yi magana game da wannan hali marar kyau a wani misalin da ya ba da. Ya ce: “Shi Ba-farisin ya tsaya yana addu’a da kansa haka, Ya Allah, na gode maka ba kamar sauran mutane ni ke ba, azalumai, marasa-adalci, mazinata, ko irin wannan mai-karɓan haraji. Lahadi ɗaya ni kan yi azumi biyu, ina bada zakka daga cikin dukan abin da na samu. Amma shi mai-karɓan haraji, da ya ke tsaye daga nesa, ba ya yarda ya tada ko idanunsa sama ba, amma sai ya bugi ƙirjinsa, ya ce, Ya Allah, ka yi mani jinƙai, ni mai-zunubin.”—Luk 18:11-13.

Yesu ya yaba wa mai-karɓan harajin domin yana da tawali’u, kuma ya ce: “Ina ce maku, Wannan mutum ya tafi gidansa baratace ne bisa ga wancan: gama dukan wanda ya ɗaukaka kansa za shi ƙasƙanta; amma wanda ya ƙasƙantadda kansa za shi ɗaukaka.” (Luk 18:14) Mutane da yawa sun yi zato cewa masu-karɓan haraji macuta ne, amma Yesu yana son ya taimaka wa masu-karɓan haraji da suke son koyarwar Yesu. Mun san cewa masu karɓan haraji guda biyu sun zama almajiran Yesu. Kuma sunansu Matta da Zakka.

Wataƙila mun ƙware sosai a wasu fannoni na rayuwa ko kuma muna da wani gata a cikin ƙungiyar Jehobah. Ko kuma wataƙila mun san kurakuren wasu. Mene ne ya kamata mu yi idan mun soma yin tunani cewa mun fi wasu? Ya kamata mu kawar da irin wannan tunanin nan da nan domin Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ƙauna tana da yawan haƙuri, tana da nasiha; ƙauna ba ta jin kishi; ƙauna ba ta yin fahariya, ba ta yin kumbura, ba ta yin rashin hankali, ba ta biɗa ma kanta, ba ta jin cakuna, ba ta yin nukura, ba ta yin murna cikin rashin adalci, amma tana murna da gaskiya.”—1 Kor. 13:4-6.

Ya kamata mu kasance kamar manzo Bulus. Ya ce “Kristi Yesu ya zo cikin duniya domin ceton masu-zunubi.” Kuma bayan haka, ya daɗa cewa: “Cikinsu kuwa ni ne babba.”—1 Tim. 1:15.

Tambayoyin da za ku yi tunani a kai:

Shin na fahimci cewa ni mai zunubi ne kuma Jehobah ne kaɗai zai iya cece ni domin yana mini alheri sosai? Ko kuwa ina zato cewa na fi kowa kyau domin na kwashe shekaru da yawa ina bauta wa Jehobah da aminci ko kuwa ina da gata a ƙungiyar Jehobah ko kuma na goge sosai a wasu fannonin rayuwa?

2 Farisawa suna abubuwa don su burge mutane kuma a ce su masu adalci ne. Suna kuma neman suna.

Yesu ya ba da gargaɗi: “Amma dukan ayukansu su kan yi domin mutane su gani: gama su kan faɗaɗa layunsu, su kan yalwata shafunan rigunansu, suna son mazaunai na manya cikin bukukuwa da mazauna na manya cikin majami’u, da gaisuwa kuma cikin kasuwanni, mutane su kira su, Malam, kuma.” (Mat. 23:5-7) Koyarwar Yesu ta yi dabam da na Farisawa. Yana da tawali’u ko da yake shi Ɗan Allah ne kuma kamili ne. Sa’ad da wani mutum ya kira shi “managarci,” Yesu ya ce: “Don me ka ke ce da ni managarci? babu wani managarci sai ɗaya, Allah.” (Mar. 10:18) A wani lokaci kuma, Yesu ya wanke kafaffun mabiyansa domin ya nuna musu cewa ya kamata su riƙa kasancewa da tawali’u.—Yoh. 13:1-15.

Ya kamata Kirista na gaskiya ya riƙa wa ’yan’uwansa hidimomi. (Gal. 5:13) Kuma ya kamata waɗanda suke son su zama masu kula a cikin ikilisiya su riƙa yin haka sosai. Yana da kyau ɗan’uwa ya yi ayyukan da za su sa ya cancanci samun wannan gatan. Amma zai yi hakan ne domin yana son ya taimaka wa mutane. Mai kula bai fi sauran ’yan’uwan daraja ba kuma bai kamata ya riƙa amfani da wannan matsayin don ya mallake su ba.Ya kamata ya zama kamar Yesu kuma ya zama “mai-ƙasƙantar zuciya.”—1 Tim. 3:1, 6; Mat. 11:29.

Tambayoyin da za ku yi tunani a kai:

Shin ina ɗaukan ’yan’uwan da suke da gata a cikin ikilisiya da daraja fiye da wasu domin ina sa rai cewa za su ba ni ƙarin gata? A bauta ta ga Jehobah, shin na fi son yin ayyukan da za su sa mutane su lura da ni kuma su yaba mini? Shin ina son na fi kowa adalci?

3 Dokoki da al’adu na Farisawa sun sa ya yi wa mutane wuya su yi biyayya da dokokin Jehobah.

Jehobah ya ba Isra’ilawa Doka domin ya nuna musu yadda za su bauta masa. Amma ba kome ba ne dokar ta bayyana musu ba. Alal misali, Dokar ta hana yin aiki a ranar Assabaci, amma bai faɗi ayyukan da za su yi da waɗanda ba za su yi ba. (Fit. 20:10) Farisawa sun daɗa wasu dokoki da kuma al’adu domin suna ganin cewa Dokar da Jehobah ya bayar ba ta ba da cikakken bayani ba. Yesu ya yi biyayya ga Dokokin Allah, amma bai bi dokokin da Farisawa suka kirkiro ba. (Mat. 5:17, 18; 23:23) Ya san dalilan da suka sa Allah ya ba da Dokokin kuma ya san cewa Allah yana son mutane su nuna jin ƙai da kuma tausayi. Yesu yana da kirki, ko sa’ad da almajiransa suka ɓata masa rai. Alal misali, a daren da aka kama Yesu, ya gaya wa almajiransa uku su yi tsaro. Amma sun ci gaba da yin barci sau da yawa. Ko da yake sun yi barci, amma Yesu ya ji tausayinsu kuma ya ce: “Gaskiya ruhu ya yarda, amma jiki rarrauna ne.”—Mar. 14:34-42.

Tambayoyin da za ku yi tunani a kai:

Shin ina kirkiro dokoki kuma na tilasta wa mutane su bi su? Shin ina yawan son mutane su yi abin da nake ganin cewa ya dace? Shin ina son mutane su yi abin da ya fi ƙarfinsu?

Koyarwar Yesu ta yi dabam da na Farisawa. Shin akwai abubuwan da za ka iya yi don ka zama kamar Yesu? Idan haka ne, zai dace ka ƙuduri aniyar yin hakan.

[Hoto a shafi na 28]

Farisawa suna ɗaura ƙaramin akwati da aka saka nassosi a ciki a goshinsu.—Mat. 23:2, 5

[Hotona a shafi na 29]

Dattawan Kirista sun yi dabam da Farisawa masu fahariya, suna da tawali’u kuma suna wa mutane hidima

[Hoto a shafi na 30]

Kana yin yadda Yesu yake yi ko kuwa kana son mutane su yi abin da ya fi ƙarfinsu?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba