Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 8/15 pp. 25-29
  • Ka Yi Tsayayya Da Shaiɗan Kuma Ka Guji Tarkunansa!

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Yi Tsayayya Da Shaiɗan Kuma Ka Guji Tarkunansa!
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • SON ABIN DUNIYA TARKO NE DA KE SHAƘEWA
  • ZINA TANA KAMA DA RAMIN DA KE ƁOYE
  • “Ka Yi Murna Da Matar Kuruciyarka”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Za Ka Iya Yin Tsayayya da Shaidan Kuma Ka Yi Nasara!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Ka Guji Faɗawa Cikin Tarkunan Iblis!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 8/15 pp. 25-29

Ka Yi Tsayayya Da Shaiɗan Kuma Ka Guji Tarkunansa!

“Ku yi tsayayya da dabarun Shaiɗan.”—AFIS. 6:11.

MECE CE AMSARKA?

Mene ne bawan Jehobah zai yi don kada tarkon Shaiɗan na son abin duniya ya kama shi?

Mene ne zai taimaki Kiristan da ya yi aure don kada ya yi zina?

Waɗanne amfani ne za mu samu idan ba mu so abin duniya ba kuma ba mu yi lalata ba?

1, 2. (a) Me ya sa Shaiɗan ba ya tausaya wa shafaffu da kuma “waɗansu tumaki”? (b) Waɗanne tarkunan Shaiɗan ne za mu tattauna a wannan talifin?

SHAIƊAN IBLIS ya tsani mutane sosai, musamman waɗanda suke bauta wa Jehobah. Shaiɗan yana yaƙi da shafaffun da suka rage a duniya. (R. Yoh. 12:17) Waɗannan Kiristoci sun yi ja-gora a aikin wa’azi game da Mulkin Allah da gaba gaɗi, kuma sun nuna wa mutane cewa Shaiɗan ne yake mulkin duniya. Shaiɗan ya kuma tsani “waɗansu tumaki” waɗanda suke goyon bayan shafaffu a aikin da suke yi kuma suna da begen yin rayuwa a duniya har abada. (Yoh. 10:16) Shaiɗan bai da begen yin rayuwa har abada, shi ya sa yake yin fushi. Ko da muna da begen yin rayuwa har abada a sama ko kuma a duniya, Shaiɗan yana gāba da mu. Yana son mu faɗa cikin tarkonsa.—1 Bit. 5:8.

2 Don ya cim ma burinsa, Shaiɗan ya ɗana tarkuna dabam-dabam. Yana iya ƙoƙarinsa don ya ‘makantar’ da marasa gaskiya domin kada su ji bishara kuma kada su ga tarkunan da ya ɗana. Amma, wasu da suke bauta wa Jehobah suna faɗa wa tarkunan Shaiɗan. (2 Kor. 4:3, 4) A talifin da ya gabata, mun koyi yadda za mu guje wa tarkuna uku da Shaiɗan yake ɗanawa: (1) yin magana da garaje da (2) tsoro da matsi da kuma (3) yawan jin laifi. Amma yanzu, bari mu tattauna yadda za mu yi tsayayya da wasu tarkuna biyu da Shaiɗan yake ɗanawa, wato, son abin duniya da matsin yin zina.

SON ABIN DUNIYA TARKO NE DA KE SHAƘEWA

3, 4. Ta yaya ɗawainiyar duniyar nan za ta iya sa wasu su faɗa cikin tarkon neman abin duniya?

3 A wani misalin da Yesu ya bayar, ya yi magana game da iri da aka shuka a cikin ƙayoyi. Ya bayyana cewa mutum zai iya jin saƙon Mulkin, “amma ɗawainiyar duniya, da ruɗin dukiya, su kan shaƙe maganar, ta zama marar-amfani.” (Mat. 13:22) Son abin duniya tarko ne da maƙiyinmu Shaiɗan yana yin amfani da shi don ya kama mu.

4 Abubuwa biyu za su iya “shaƙe maganar.” Na ɗaya shi ne ‘ɗawainiyar duniya.’ Akwai abubuwa da yawa da za su iya sa mu ɗawainiya a waɗannan “miyagun zamanu.” (2 Tim. 3:1) Yadda abubuwa suke tsada yanzu da kuma rashin aiki za su iya sa mu kasa biyan bukatun rayuwa. Za ka iya yawan damuwa game da abin da zai faru a nan gaba, kuma ka tambayi kanka, ‘Zan samu isasshen kuɗin kula da kaina sa’ad da na tsufa?’ Waɗannan dalilai za su iya sa wasu su riƙa neman kuɗi ƙarfi da yaji, suna zato cewa hakan zai kāre su daga talauci.

5. Ta yaya “ruɗin dukiya” yake yaudarar mutum?

5 Yesu ya kuma yi magana game da ‘ruɗin dukiya.’ Wannan matsalar tare da ɗawainiya za su iya sa mu faɗa cikin tarkon son abin duniya. Littafi Mai Tsarki ya ce ‘kuɗi kāriya ce.’ (M. Wa. 7:12) Wannan ayar ta nuna cewa kuɗi zai iya taimaka mana mu biya bukatunmu. Amma, bai dace mu riƙa neman kuɗi ƙarfi da yaji ba. Mutane da yawa sun shaida cewa yin hakan yana sa a faɗa cikin tarkon Shaiɗan da sauƙi. Wasu ma sun zama bayi ga dukiyarsu.—Mat. 6:24.

6, 7. (a) Wane yanayi ne a wurin aikinka zai iya sa ka soma sha’awar abin duniya? (b) Mene ne ya kamata Kirista ya yi tunani a kai idan an ce masa ya yi abataya?

6 Za ka iya soma son abin duniya ba tare da saninka ba. Alal misali, ka yi la’akari da wannan yanayin. Shugaban aikinka ya zo wurin aiki ya ce maka: “Albishirinka! Kamfaninmu ya samu wani babban kwangila. Hakan na nufin cewa za ka riƙa yin abataya a kai a kai na tsawon ’yan watanni. Amma ina son in gaya maka cewa za a ƙara maka albashinka.” Yaya za ka ji game da wannan tayin? Ko da yake yana da muhimmanci ka biya bukatun iyalinka, amma ba shi ke nan hakkin da kake da shi ba. (1 Tim. 5:8) Akwai wasu abubuwa da ya kamata ka yi tunani akai. Abataya ɗin sa’o’i nawa ne zan riƙa yi? Shin aikin zai shafi ayyukan da nake yi a hidimar Jehobah, kamar halartar taron ikilisiya da yin Bauta ta Iyali da yamma?

7 Ka yi tunani a kan abin da ya fi muhimmanci a gare ka. Shin ƙarin kuɗi ne ko kuwa dangantakarka da Jehobah? Zan daina saka hidimar Jehobah farko a rayuwata domin ina son ƙarin kuɗi? Shin ka lura da yadda son abin duniya zai shafe ka idan ba ka kiyaye dangantakarka da na iyalinka da Jehobah ba? Idan hakan fuskantar wannan matsalar, mene ne za ka yi don kada son abin duniya ya shawo kanka?—Karanta 1 Timotawus 6:9, 10.

8. Waɗanne misalai na Littafi Mai Tsarki ne za su taimaka maka ka yi la’akari da salon rayuwarka?

8 Idan ba ka son abin duniya ya shawo kanka, ya kamata ka riƙa bincika salon rayuwarka a kai a kai. Ya kamata mu yi tir da irin halin Isuwa wanda ya nuna cewa bai daraja abubuwa masu tsarki ba. (Far. 25:34; Ibran. 12:16) Kuma bai kamata mu zama kamar attajirin da Yesu ya ce ya sayar da dukiyarsa, ya rarraba wa talakawa kuɗin kuma ya zama almajirinsa ba. Amma, mutumin bai yi biyayya ga umurnin Yesu ba, maimakon haka, “ya tafi yana baƙin ciki; gama mai-arziki ne shi ainu.” (Mat. 19:21, 22) Wadatar mutumin yana kamar tarko da ya kama shi. Ya rasa gata mai girma sosai, na zama almajirin mutum mafi girma da ya taɓa rayuwa a duniya. Ya kamata mu yi hankali don kada mu rasa gatan zama almajiran Yesu Kristi.

9, 10. Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce game da son abin duniya?

9 Idan ba ma son abin duniya ya shawo kanmu, wajibi ne mu yi biyayya ga gargaɗin Yesu. Ya ce: “Kada ku yi alhini fa, kuna cewa, Me za mu ci? ko kuwa, Me za mu sha? ko kuwa, Da minene za mu yi sutura? Gama waɗannan abubuwa duka al’ummai suna ta biɗa; gama Ubanku na sama ya sani kuna bukatar waɗannan abubuwa duka.”—Mat. 6:31, 32; Luk 21:34, 35.

10 Idan ba ma son mu faɗa cikin tarkon son abin duniya, ya kamata mu kasance da irin ra’ayin wani marubucin Littafi Mai Tsarki mai suna Agur, wanda ya ce: “Kada ka ba ni ko talauci ko wadata: Ka ciyar da ni da abincin da ke daidai bukatata.” (Mis. 30:8) Hakika Agur ya fahimci cewa ana bukatar kuɗi don biyan wasu bukatu na rayuwa, amma ya san cewa kuɗi yana yaudarar mutane sosai. Ya kamata mu san cewa ɗawainiyar duniyar nan da ruɗin wadata za su iya ɓata dangantakarmu da Jehobah. Cika damuwa game da abin duniya zai iya cin lokacinmu da ƙarfinmu kuma zai hana mu saka Mulkin Allah farko a rayuwarmu. Saboda haka, ka yi hankali don kada ka faɗa cikin tarkon son abin duniya da Shaiɗan ya ɗana.—Karanta Ibraniyawa 13:5.

ZINA TANA KAMA DA RAMIN DA KE ƁOYE

11, 12. Ta yaya Kirista zai iya faɗa cikin tarkon yin zina a wurin aiki?

11 Idan maharba suna son su kama wata babbar dabba, suna haƙa rami a hanyar da dabbar take wucewa. Sai su rufe ramin da kara da kuma yayi. Wani tarko da Shaiɗan yake amfani da shi kuma yana cin kasuwa sosai da shi shi ne zina. (Mis. 22:14; 23:27) Wasu Kiristoci sun saka kansu a cikin yanayin da zai sa su yi zina da sauƙi. Wasu Kiristoci sun yi zina bayan sun soma soyayya da wani ko wata da ba abokiyar aurensu ba.

12 Za mu iya soma dangantakar da ba ta dace ba a wurin aiki. Bincike ya nuna cewa rabi cikin mata da fiye da rabi cikin maza da suka yi zina sun yi hakan ne a wurin aiki. Idan kai na miji ne, kana aiki ne tare da tamace? Ko kuma idan kai tamace ce, kina yawan yin aiki ne da namiji? Idan haka ne, wace irin dangantaka ce ke tsakaninku? Shin kuna mai da hankali don kada ku soma sha’awar juna? Alal misali, Kirista za ta iya riƙa tattaunawa da abokin aikinta. Amma da sannu-sannu, ta soma gaya masa matsalolin da take fuskanta a aurenta. Ko kuma ɗan’uwa Kirista ya yi abota da wata abokiyar aikinsa. Sai ya soma tunani cewa: “Tana daraja ra’ayina kuma tana saurare ni sa’ad da na yi mata magana. Kuma tana mini ladabi. Da a ce ma hakan matata take.” Ka lura cewa wannan yanayin zai iya sa Kirista ya yi zina da sauƙi?

13. Ta yaya mutum zai iya soma dangantaka da ba ta dace ba a cikin ikilisiya?

13 Dangantaka da ba ta dace ba za ta kuma iya somawa a cikin ikilisiya. Ka yi la’akari da wannan labarin da ya faru. Daniel da matarsa Sarah,a majagaba na kullum ne. Daniel dattijo ne da ba ya ƙin kowanne irin aikin da aka ba shi a cikin ikilisiya. Ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki da matasa biyar kuma uku cikinsu sun yi baftisma. Waɗannan ’yan’uwan da suka yi baftisma suna bukatar taimako sosai. Amma, sa’ad da Daniel yake kula da ayyukansa a cikin ikilisiya, sai Sarah ta riƙa taimaka wa waɗannan ’yan’uwa matasan. Amma, a wasu lokatai ma da take bukatar taimako, tana samunsa daga wurin waɗannan ’yan’uwan. Daniel ya ce: “Bayan matata ta yi watanni tana taimaka wa waɗannan ’yan’uwan, dangantakarta da Jehobah ta raunana kuma tana bukatar taimako na motsin rai. A waɗannan watannin, na daina kula da ita kuma hakan ya jawo matsala sosai. Matata ta yi zina da ɗaya cikin ɗan’uwan da na yi nazari da shi. Na shagala da aiki sosai har ban san cewa dangantakarta da Jehobah ta raunana ba.” Ta yaya za mu iya kāre kanmu daga irin wannan matsalar?

14, 15. Mene ne zai iya taimaka wa ma’aurata don su guji yin zina?

14 Idan kana son ka guji faɗawa cikin tarkon yin zina, ya kamata ka yi la’akari sosai da ma’anar kasancewa da aminci ga aboki ko abokiyar aurenki. Yesu ya ce: “Abin da Allah ya gama fa, kada mutum shi raba.” (Mat. 19:6) Kada ka taɓa yin tunani cewa hakkinka a cikin ikilisiya ya fi matarka ko mijinki muhimmanci. Ƙari ga hakan, ka san cewa idan kana yawan kasancewa ba tare da matarka ba hakan zai iya raunana aurenku. Kuma za ka iya yin zina.

15 Idan kai dattijo ne kuma fa, ta yaya za ka kula da ikilisiyar? Manzo Bitrus ya ce: “Ku yi kiwon garken Allah wanda ke wurinku, kuna yin shugabanci, ba kamar na tilas ba, amma da yardan rai, bisa ga nufin Allah; ba kuwa domin riba mai-ƙazanta ba, amma da karsashin zuciya.” (1 Bit. 5:2) Hakika, ba ka bukatar ka yashe ’yan’uwan da ke ikilisiyarku. Bai kamata ka kula da ikilisiyar bakuma ka yi banza da matarka. Zai zama wauta idan mun yi amfani da dukan lokacinmu wajen kula da ikilisiya amma mun yashi matarmu a gida. Daniel ya ce, “Bai dace ka yi amfani da dukan lokacinka wajen kula da hakkin a cikin ikilisiyar kuma ba ka kula da iyalinka ba.”

16, 17. (a) Mene ne Kiristoci da suka yi aure za su iya yi a wurin aiki don su nuna cewa sun riga sun yi aure? (b) Ka ba da misalin talifofi a cikin mujallunmu da za su taimaka mana mu guji yin zina.

16 Mujallun Hasumiyar Tsaro da Awake! Suna ɗauke da shawarwari da yawa da za su taimaki ma’aurata Kiristoci su guji yin zina. Alal misali, ka yi la’akari da shawarar da Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Oktoba, 2006 ta ba da: “Ka lura da yanayi da zai iya kai wa ga soyayya a wajen aiki ko kuma a wani waje. Alal misali, idan ka ɗauki ƙarin lokaci kana aiki tare da wata, zai iya jawo gwaji. Ma’aurata maza ko mata, ku nuna ta furcinku da halayenku cewa ba za ku yi soyayya da wadda ba abokiyar aurenku ba ce. Mai tsoron Allah, bai kamata ta jawo wa kanta mutane ta wurin yadda take sa tufafi da kuma kwalliya ba. . . . Idan ka ajiye hoton matarka da na yaranka a wajen aikinka, hakan zai tuna maka da kuma wasu cewa kana son iyalinka. Kada ka yarda wasu su rinjaye ka.”

17 Talifin Awake! na Afrilu 2009, mai jigo “Marital Fidelity—What Does It Really Mean?” [Mene ne Kasancewa da Aminci a Aure Yake Nufi] ya yi gargaɗi a kan yin sha’awar mutum da ba matarka ko mijinki ba. Talifin ya nuna cewa wannan sha’awar zai iya sa ya kasance maka da sauƙi ka yi zina. (Yaƙ. 1:14, 15) Idan ka yi aure, zai dace kai da matarka ku riƙa karanta talifofi game da wannan batun a kai a kai. Jehobah ne ya tsara aure kuma aure abu mai tsarki ne. Ka tabbata cewa kana rifta zarafi don kai da matarka ku tattauna game da aurenku. Yin hakan zai nuna cewa kana daraja abubuwan da suke da muhimmanci a gaban Allah.—Far. 2:21-24.

18, 19. (a) Mene ne sakamako marar kyau na yin zina? (b) Waɗanne sakamako masu kyau ne ake samu idan an kasance da aminci a aure?

18 Idan kana fuskantar gwajin soma soyayya da bai dace ba, ka yi tunani a kan sakamako marar kyau na yin lalata da zina. (Mis. 7:22, 23; Gal. 6:7) Mutanen da suke yin zina suna ɓata wa Jehobah rai kuma suna ɓata wa kansu da abokin aurensu rai. (Karanta Malakai 2:13, 14.) Maimakon haka, ka yi tunani a kan sakamako mai kyau da za ka samu idan kana da hali mai kyau. Za ka kasance da begen yin rayuwa har abada a nan gaba. Za ka more rayuwa mai amfani a yanzu kuma zuciyarka ba za ta riƙa damunka ba.—Karanta Misalai 3:1, 2.

19 Wani marubucin zabura ya rera waƙa: “Salama mai-yawa tana ga waɗanda su ke ƙaunar shari’arka [Allah]; ba kuwa wani dalilin tuntuɓe garesu.” (Zab. 119:165) Saboda haka, ka yi ƙaunar gaskiya kuma ka duba “a hankali yadda kuke yin tafiya, ba kamar marasa-hikima ba, amma kamar masu-hikima” a waɗannan miyagun kwanaki. (Afis. 5:15, 16) Shaiɗan yana yin amfani da tarkuna da yawa don ya kama masu bauta wa Jehobah. Amma, Jehobah ya ba mu dukan abin da muke bukata don mu kāre kanmu daga dukan tarkunan da Shaiɗan ya ɗana!—Afis. 6:11, 16.

[Hasiya]

a An canja wasu sunaye.

[Hoto a shafi na 26]

Son abin duniya zai iya raunana dangantakar mutum da Jehobah. Kada ka taɓa ƙyale hakan ya faru maka

[Hoto a shafi na 29]

Yin kwarkwasa ko ƙyale wani ya yi hakan da kai, zai iya sa ka yi zina

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba