Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 1/15 pp. 27-31
  • Dattawa Kirista—​Suna Aiki Don Mu Yi ‘Farin Ciki’

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Dattawa Kirista—​Suna Aiki Don Mu Yi ‘Farin Ciki’
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • BANGASKIYARMU DA FARIN CIKINMU
  • “KU GAI DA BARSISA ƘAUNATACCIYA”
  • ‘TA YI AIKI DA YAWA CIKIN UBANGIJI’
  • “KU YI KIWON IKILISIYAR ALLAH”
  • ‘ABISHAI YA YI MASA GUDUNMUWA’
  • “KU SAN ƘAUNA WADDA NA KE YI MUKU”
  • Dattawa—Ku Ci-gaba da Yin Koyi da Manzo Bulus
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • “Ku Girmama Waɗanda Suke Aiki Tuƙuru A Cikinku”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ka Koma don Ka “Karfafa ’Yan’uwanka”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Yadda Aka Tsara Ikilisiya
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 1/15 pp. 27-31

Dattawa Kirista Suna Aiki Don Mu Yi ‘Farin Ciki’

‘Mu abokan aiki ne na farin zuciyarku.’—2 KOR. 1:24.

MECE CE AMSARKA?

  • Ta yaya Bulus ya nuna cewa ba ya sarauta bisa bangaskiyar ’yan’uwansa, amma shi ‘abokin aiki ne na farin zuciyarsu’?

  • Ta yaya dattawa Kirista suke sa ’yan’uwansu farin ciki a yau?

  • Ta yaya dukanmu za mu iya sa ikilisiya ta kasance da farin ciki?

1. Me ya sa Bulus ya yi murna game da Kiristocin da ke Korinti?

A SHEKARA ta 55 a zamanin Yesu, manzo Bulus ya samu labari cewa ’yan’uwan da ke Korinti suna yawan cin musu. Bulus yana ƙaunarsu kamar yadda uba yake ƙaunar ’ya’yansa. Hakan ya motsa shi ya aika musu wasiƙa don ya gargaɗe su. (1 Kor. 1:11; 4:15) Bulus ya ce wa abokinsa Titus ya ziyarce su, kuma bayan haka, ya haɗu da shi a Taruwasa domin ya gaya masa abin da ya faru. Bulus ya yi watanni yana jiran Titus a Taruwasa, domin ya gaya masa sakamakon ziyarar. Amma, Titus bai dawo ba. Hakan ya sa Bulus baƙin ciki sosai. Sai ya shiga jirgi zuwa Makidoniya, kuma ya yi farin ciki sosai sa’ad da ya haɗu da Titus a wurin. Titus ya gaya wa Bulus cewa ’yan’uwan sun yi na’am da gargaɗinsa kuma suna ɗokin ganinsa. Sa’ad da Bulus ya ji hakan, sai ya “daɗa yin murna.”—2 Kor. 2:12, 13; 7:5-9.

2. (a) Mene ne Bulus ya rubuta wa Korintiyawa game da bangaskiya da murna? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna?

2 Ba da daɗewa ba, sai Bulus ya sake rubuta wa Korintiyawa wata wasiƙa. Ya ce musu: ‘Ba sarauta muke yi bisa bangaskiyarku ba, amma abokan aiki ne na farin zuciyarku: gama da bangaskiyarku kuke tsayawa.’ (2 Kor. 1:24) Mene ne Bulus yake nufi da waɗannan kalmomin? Kuma mene ne dattawa Kirista za su iya koya daga waɗannan kalmomin?

BANGASKIYARMU DA FARIN CIKINMU

3. (a) Mene ne Bulus yake nufi sa’ad da ya ce: ‘Da bangaskiyarku kuke tsayawa?’ (b) Ta yaya dattawa suke koyi da Bulus a yau?

3 Bulus ya ambata bangaskiya da farin zuciya, kuma waɗannan halayen suna da muhimmanci sosai ga Kiristoci. Da farko Bulus ya ambata bangaskiya, kuma ya ce: ‘Ba sarauta muke yi bisa bangaskiyarku ba, gama da bangaskiyarku kuke tsayawa.’ Bulus ya san cewa bangaskiya ce ta sa Korintiyawa suke bauta wa Allah da aminci, ba ’yan Adam ba. Saboda haka, Bulus ba ya son ya yi sarauta bisa bangaskiyarsu. Yana da tabbaci cewa suna da aminci kuma suna son su yi nagarta. (2 Kor. 2:3) Hakazalika, dattawa a yau suna yin koyi da Bulus ta wajen amince cewa ’yan’uwansu suna bauta wa Allah domin suna da bangaskiya kuma suna son su bauta masa. (2 Tas. 3:4) Ba sa kafa wa ikilisiya dokoki masu wuyan bi. Maimakon haka, suna taimaka wa ’yan’uwa su bi ƙa’idojin Littafi Mai Tsarki da kuma na ƙungiyar Jehobah idan za su tsai da shawara. Kuma, dattawa a yau ba sa nuna iko bisa bangaskiyar ’yan’uwansu.—1 Bit. 5:2, 3.

4. (a) Mene ne Bulus yake nufi sa’ad da ya ce: ‘Mu abokan aiki ne na farin zuciyarku’? (b) Ta yaya dattawa suke yin koyi da Bulus a yau?

4 Su wane ne Bulus yake nufi sa’ad da ya ce, mu ‘abokan aiki ne na farin zuciyarku’? Yana nufin abokansa ne da suka yi aiki tare wajen ƙarfafa Korintiyawa. Ta yaya muka san hakan? Domin ya ambata sunayen abokansa biyu a wasiƙarsa ga Korintiyawa. Ya ce: ‘Yesu wanda aka yi wa’azinsa a cikinku ta bakinmu, ni da Silwanus da Timotawus.’ (2 Kor. 1:19) Ƙari ga haka, duk sa’ad da Bulus ya ambata ‘abokan aiki’ a wasiƙarsa, yana nufin abokansa na kud da kud kamar su Afolos da Akila da Bilkisu da Timotawus da Titus da kuma sauransu. (Rom. 16:3, 21; 1 Kor. 3:6-9; 2 Kor. 8:23) Sa’ad da Bulus ya ce, mu ‘abokan aiki ne na farin zuciyarku,’ yana nufi cewa da shi da abokan aikinsa suna ƙoƙari su taimaka wa ikilisiya ta bauta wa Allah da farin ciki. Abin da dattawa ma suke ɗoki ke nan a yau. Suna yin iya ƙoƙari su taimaka wa ’yan’uwansu su “bauta wa Ubangiji da farin zuciya.”—Zab. 100:2; Filib. 1:25.

5. Wace tambaya ce za mu tattauna, kuma me ya kamata mu yi bimbini a kai?

5 A kwana kwanan nan, an yi wa wasu ’yan’uwa daga ƙasashe dabam-dabam wannan tambayar, “Waɗanne furuci da kuma halayen dattawa ne kuka fi so?” Bari mu ji abin da suka ce. Yayin da muke yin hakan, ka ga ko amsarsu ta jitu da ra’ayinka. Kuma bari dukanmu mu yi tunani a kan yadda za mu iya sa ikilisiyarmu ta kasance da farin ciki.a

“KU GAI DA BARSISA ƘAUNATACCIYA”

6, 7. (a) A wace hanya ce dattawa za su iya yin koyi da Yesu da Bulus da kuma wasu bayin Allah? (b) Me ya sa ’yan’uwa suke murna sa’ad da aka kira su da sunansu?

6 ’Yan’uwa da yawa sun ce suna farin ciki sosai sa’ad da dattawa suka nuna cewa sun damu da su. Ta wajen yin hakan, dattawa suna bin misalin Dauda da Elihu da kuma Yesu. (Karanta 2 Sama’ila 9:6; Ayuba 33:1; Luka 19:5.) Waɗannan bayin Jehobah sun nuna cewa sun damu da wasu ta wajen kiransu da sunayensu. Bulus ma ya san cewa yana da muhimmanci sosai a tuna da kuma ambata sunayen ’yan’uwa. Sa’ad da yake dasa aya a wata wasiƙarsa, ya ambata sunayen ’yan’uwa maza da mata fiye da ashirin da biyar. Ya ambata wata ’yar’uwa mai suna Barsisa, cewa: “Ku gai da Barsisa, ƙaunatacciya.”—Rom. 16:3-15, Littafi Mai Tsarki.

7 Ba dukan dattawa ba ne suke saurin tuna sunayen mutane ba. Amma idan dattawa suka ƙoƙarta su yi hakan, suna nuna wa ’yan’uwa cewa sun damu da su. (Fit. 33:17) Idan dattijo ya kira wani ɗan’uwa da sunansa sa’ad da yake son ya ba da kalami a Nazarin Hasumiyar Tsaro ko a wani taro dabam, hakan zai sa ɗan’uwan farin ciki sosai.—Gwada Yohanna 10:3.

‘TA YI AIKI DA YAWA CIKIN UBANGIJI’

8. A wace hanya ce ta musamman Bulus ya yi koyi da Jehobah da kuma Yesu?

8 Bulus ya kuma nuna cewa yana kula da mutane ta wajen yaba musu sosai. Wannan wata hanya ce da dattawa za su iya taimaka wa ’yan’uwa maza da mata su bauta wa Allah da farin ciki. Sa’ad da Bulus ya rubuta wa Korintiyawa wasiƙa, ya ce musu yana alfahari da su. Ya ce: “Fahariyata kuma a kanku mai-yawa ce.” (2 Kor. 7:4) Babu shakka, Korintiyawa sun yi farin ciki sosai domin waɗannan kalmomin. Bulus ya yaba wa wasu ikilisiyoyi ma domin ayyukansu masu kyau. (Rom. 1:8; Filib. 1:3-5; 1 Tas. 1:8) Bayan da Bulus ya ambata Barsisa a wasiƙarsa ga ikilisiyar Roma, sai ya ce ta yi “aiki da yawa cikin Ubangiji.” (Rom. 16:12) Ko shakka babu, waɗannan kalaman sun ƙarfafa ta. Bulus ya yi koyi da Jehobah da kuma Yesu Kristi sa’ad da yake yaba wa mutane.—Karanta Markus 1:9-11; Yohanna 1:47; R. Yoh. 2:2, 13, 19.

9. Me ya sa ’yan’uwa a cikin ikilisiya suke farin ciki sa’ad da suka yaba wa juna?

9 Dattawa ma a yau sun san muhimmancin yaba wa ’yan’uwa. (Mis. 3:27; 15:23) A duk sa’ad da dattijo ya yi hakan, kamar yana ce wa ɗan’uwan: ‘Ina lura da ayyukanka. Ina ƙaunarka sosai.’ Kuma babu shakka, irin waɗannan kalmomin suna ƙarfafa ’yan’uwa maza da mata a cikin ikilisiya. Akwai wata ’yar’uwa da ta yi wa shekaru hamsin baya, ta ce: ‘Da ƙyar mutum zai yaba maka a wajen aiki. Ba su damu da kowa ba, sai dai yin gasa da juna. Amma, idan dattijo ya yaba mini domin na yi wani aiki a cikin ikilisiya, hakan yana ƙarfafa ni sosai. Yana sa in san cewa Ubanmu na sama yana ƙaunata.’ Wani ɗan’uwa gwauro mai yara biyu yana ji kamar wannan ’yar’uwar. Wani dattijo ya yaba masa sosai a yan kwana kwanan nan. Yaya hakan ya shafe shi? Ya ce: “Kalamansa ya ƙarfafa ni sosai.” Hakika, idan dattijo ya yaba wa ’yan’uwa, zai daɗaɗa su da kuma sa su farin ciki. Hakan zai daɗa ƙarfafa su, su ci gaba da kasancewa a hanya ta rai ba tare da yin “suwu ba.”—Isha. 40:31.

“KU YI KIWON IKILISIYAR ALLAH”

10, 11. (a) Ta yaya dattawa za su iya bin misalin Nehemiya? (b) Mene ne zai taimaka wa dattijo ya ƙarfafa ’yan’uwansa a lokacin da ya kai musu ziyarar?

10 A wace hanya ce ta musamman dattawa suke nuna ƙauna ga ’yan’uwansu, kuma suke taimaka musu su bauta wa Allah da farin ciki? Suna ɗaukan mataki nan da nan don taimaka wa waɗanda suke bukatar ƙarfafa. (Karanta Ayyukan Manzanni 20:28.) Sa’ad da dattawa suka yi hakan, suna yin koyi da dattawa na zamanin dā. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya ce sa’ad da Nehemiya ya lura cewa wasu cikin ’yan’uwansa Yahudawa sun yi sanyin gwiwa, sai ya ƙarfafa su. (Neh. 4:14) Ya kamata dattawa ma a yau su yi koyi da shi. Sa’ad da suka lura cewa ’yan’uwansu suna sanyin gwiwa, ya kamata su ƙarfafa su. Zai dace su ziyarce su a gidansu idan zai yiwu, kuma su yi musu ‘baiwa ta ruhu,’ wato su ƙarfafa su. (Rom. 1:11) Mene ne zai taimaki dattawa su yi hakan?

11 Dattijo yana bukatar ya yi tunani sosai game da waɗanda yake son ya ƙarfafa kafin ya ziyarce su. Alal misali, zai iya tambayar kansa: ‘Waɗanne ƙalubale ne suke fuskanta? Waɗanne kalmomi ne za su ƙarfafa su? Wane nassi ko labari na Littafi Mai Tsarki ne zai ƙarfafa su?’ Idan dattijo ya yi tunani kafin ya kai ziyara, zai samu damar faɗin abin da zai taimake su, ba abu marar amfani ba. A lokacin ziyararsa, zai dace dattijon ya ƙyale ɗan’uwan ko ’yar’uwar ta yi magana, kuma ya saurare ta. (Yaƙ. 1:19) Wata ’yar’uwa ta ce: “Idan dattijo ya saurare ni da dukan zuciyarsa, hakan yana ƙarfafa ni sosai.”—Luk 8:18.

12. Su waye ne suke bukatar ƙarfafa a cikin ikilisiya, kuma me ya sa?

12 Wane ne zai amfana daga ziyarar ƙarfafa? Bulus ya shawarce dattawan Kirista. Ya ce: ‘Ku tsare dukan garke.’ Babu shakka, kowa a cikin ikilisiya yana bukatar ƙarfafa. Har da masu shela da kuma majagaba da suka kwashe shekaru da yawa suna bauta wa Jehobah. Me ya sa suke bukatar ƙarfafa daga dattawa? Domin su ma suna yin sanyin gwiwa a wasu lokatai a wannan mugun zamanin. Misalin Sarki Dauda zai nuna mana dalilin da ya sa wasu amintattun bayin Jehobah suke sanyin gwiwa a wasu lokatai.

‘ABISHAI YA YI MASA GUDUNMUWA’

13. (a) A wane lokaci ne Ishbi-benob ya kusan kashe Dauda? (b) Yaya Abishai ya kāre Dauda?

13 Jim kaɗan bayan an naɗa Dauda Sarki, ya yi yaƙi da Goliath, wanda ƙato ne daga ƙabilar Rapha. Dauda ya kasance da gaba gaɗi, kuma ya kashe shi. (1 Sam. 17:4, 48-51; 1 Laba. 20:5, 8) Bayan shekaru da yawa, Dauda ya sake yin yaƙi da wani ƙato Ba’filisti. Sunansa Ishbi-benob ne, daga ƙabilar Rapha. (2 Sam. 21:16) Amma a wannan karon, ƙaton ya kusan kashe Dauda. Me ya sa? Ba domin ya yi sanyin gwiwa ba, amma domin ya yi kasala. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Dauda ya yi suwu.” Da zarar Ishbi-benob ya lura da hakan, sai ya “yi tsammani za ya kashe” Dauda. Amma, kafin ƙaton ya cika muradinsa, sai “Abishai ɗan Zeruiah ya yi masa [Dauda] gudunmuwa, ya bugi Ba-philisti, ya kashe shi.” (2 Sam. 21:15-17) Dauda ya tsallake rijiya da baya. Babu shakka, Dauda ya yi farin ciki domin Abishai ya lura da shi, kuma ya kāre shi sa’ad da aka kusan kashe shi. Wane darassi ne za mu iya koya daga wannan labarin?

14. (a) Mene ne zai taimaka mana mu kasance da aminci a mawuyacin yanayi? (b) Ta yaya dattawa za su iya taimaka wa ’yan’uwa su kasance da aminci kuma su yi farin ciki? Ka ba da misali.

14 Ko da yake Shaiɗan da bayinsa suna tayar da rigima, amma bayin Jehobah a faɗin duniya suna bauta wa Allah. Za a iya kwatanta matsalolin da wasu cikinmu suke fuskanta da wannan ƙaton. Amma, muna dogara ga Jehobah baki ɗaya kuma yana taimaka mana mu kasance da aminci, kamar yadda ya yi wa Dauda. Duk da haka, akwai wasu lokatai da muke kusan suwu domin matsalolin da Shaiɗan yake haddasawa. Ba ya yin wuya mu yi sanyin gwiwa a waɗannan lokatan. Amma, wani dattijo yana iya lura da yanayinmu kuma ya taimaka mana a kan kari. Kuma hakan zai iya sa mu ci gaba da bauta wa Allah. Wata ’yar’uwa ’yar shekara 65 ta ce: “Na yi rashin lafiya a kwanakin baya, kuma yin wa’azi ya yi mini wuya. Wani dattijo ya lura da hakan, kuma ya zo waje na. Muka tattauna wasu batutuwa daga Littafi Mai Tsarki. Na yi amfani da shawarar da ya ba ni, kuma na amfana.” Ta daɗa cewa: “Ina matuƙar godiya ga wannan dattijon domin ya lura da ni kuma ya taimaka mini.” Hakika, abin ƙarfafa ne sanin cewa akwai dattawa da suke kula da mu, kuma suna a shirye su taimaka mana kamar yadda Abishai ya taimaki Dauda.

“KU SAN ƘAUNA WADDA NA KE YI MUKU”

15, 16. (a) Me ya sa ’yan’uwa suka ƙaunaci Bulus? (b) Me ya sa muke ƙaunar dattawanmu?

15 Dattawa suna yin aiki tuƙuru. A wasu lokatai, ba sa yin barci sosai domin suna tunani game da ’yan’uwansu a cikin ikilisiya, kuma za su iya tashi da tsakar dare don su yi addu’a a madadinsu kuma su taimake su. (2 Kor. 11:27, 28) Duk da haka, dattawa suna yin aikinsu da farin ciki, kamar yadda Bulus ya yi. Ya ce wa Korintiyawa: “Ni kam, zan kashe dukan abin hannuna da dukan zarafina da matuƙar farin ciki saboda ranku.” (2 Kor. 12:15, LMT) Bulus ya yi amfani da dukan ƙarfinsa don ya ƙarfafa ’yan’uwa. (Karanta 2 Korintiyawa 2:4; Filib. 2:17; 1 Tas. 2:8) Shi ya sa ’yan’uwan suka ƙaunaci Bulus sosai.—A. M. 20:31-38.

16 Mu ma muna ƙaunar dattawanmu, kuma muna godiya ga Jehobah domin yana amfani da su don ya kula da mu. Muna farin ciki domin suna lura da mu kuma suna ƙarfafa mu. Kuma, muna godiya sosai domin suna a shirye su taimake mu sa’ad da muka kasala. Hakika, irin waɗannan dattawan suna aiki tuƙuru don mu yi farin ciki.

a An sake tambayar waɗannan ’yan’uwan cewa, “Wane hali na dattijo ne ka fi so?” Yawancinsu sun ce sun fi son dattijo mai kirki da fara’a. Za mu tattauna wannan halin a talifi na gaba.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba