Ka Koma don Ka “Ƙarfafa ’Yan’uwanka”
BAYAN Bitrus ya yi musun sanin Yesu, ya yi kuka mai zafi. Ko da yake almajirin zai yi aiki tuƙuru don ya sake samun dangantaka mai kyau da Allah, amma Yesu yana so ya yi amfani da shi don ya taimaka wa wasu. Saboda haka, Yesu ya gaya masa: “Lokacin da ka sāke juyowa, sai ka ƙarfafa ’yan’uwanka.” (Luk 22:32, 54-62) Bitrus ya zama ginshiƙin ikilisiyar Kirista a ƙarni na farko. (Gal. 2:9) Hakazalika, ɗan’uwan da shi dattijo ne a dā a cikin ikilisiya zai iya sake samun wannan gatan kuma ya ƙarfafa dangantakar ’yan’uwansa da Jehobah.
An sauke wasu ’yan’uwa da suka yi hidima a matsayin dattawa kuma wataƙila hakan ya sa su baƙin ciki sosai. Wani ɗan’uwa mai suna Julio,a wanda ya yi hidima a matsayin dattijo sama da shekara 20 a Amirka ta Kudu, ya ce: “Ina jin daɗin shirya jawabai da ziyartar ’yan’uwa da kuma ƙarfafa ’yan’uwa a cikin ikilisiyarmu! Amma farat ɗaya, sai waɗannan abubuwan suka bi ruwa. Hakan ya jawo mini taƙaici da ɓacin rai sosai.” A yau, an sake naɗa Julio a matsayin dattijo.
“KU MAISHE SHI ABIN FARIN CIKI SARAI”
Manzo Yaƙub ya ce: “Ya ku ’yan’uwana, duk sa’ad da gwaje-gwaje iri iri suka same ku, ku mai da su abin farin ciki ƙwarai.” (Yaƙ. 1:2, Littafi Mai Tsarki) Yaƙub yana magana ne a kan gwaje-gwajen da muke fuskanta sanaddiyar tsanantawa da kuma ajizancinmu. Ya yi magana a kan mugun buri da nuna bambanci da dai sauransu. (Yaƙ. 1:14; 2:1; 4:1, 2, 11) Za mu iya yin baƙin ciki sa’ad da Jehobah ya yi mana horo. (Ibran. 12:11) Amma bai kamata mu bari hakan ya ɓata mana rai ba.
Ko da an sauke mu a matsayin dattijo a cikin ikilisiya, muna da zarafin bincika bangaskiyarmu da kuma nuna cewa muna ƙaunar Jehobah. Za mu kuma iya yin bimbini a kan dalilin da ya sa muke wannan hidimar. Shin mun yi hakan ne don mu amfani kanmu ko domin muna ƙaunar Allah kuma mun gaskata cewa ikilisiyar tasa ce, don hakan muna bukatar bi da ita cikin ƙauna? (A. M. 20:28-30) Dattawan da aka sauke da suka ci gaba da bauta wa Jehobah da aminci suna nuna wa kowa har da Shaiɗan cewa suna ƙauna Jehobah sosai.
Sa’ad da Jehobah ya yi wa Sarki Dauda horo don zunubi mai tsanani da ya yi, Dauda ya karɓi horon kuma Allah ya gafarce shi. Dauda ya ce: “Mai-albarka ne mutum wanda an gafarta masa laifinsa, wanda an rufi zunubinsa. Mai-albarka ne mutum wanda Ubangiji ba ya lissafta mugunta gareshi ba, wanda ba shi da algus cikin ruhunsa ba.” (Zab. 32:1, 2) Horon da Jehobah ya yi wa Dauda ya taimaka masa ya zama makiyayi mai kyau ga bayin Allah.
A yawancin lokaci, ’yan’uwan da aka sake naɗawa a matsayin dattawa suna kasancewa da hali mai kyau sosai fiye da dā. Wani dattijo ya ce: “A yanzu, na san yadda ya fi dacewa in bi da mutanen da suka yi laifi.” Wani kuma ya ce: “Yanzu, ina daraja gatan da nake da shi na yi wa ’yan’uwan hidima sosai fiye da dā.”
SHIN ZA KA IYA DAWOWA?
Wani marubucin zabura ya ce: Jehobah ba zai “ta tsautawa kullum ba.” (Zab. 103:9) Saboda haka, bai kamata mu yi tunani cewa Allah ba zai sake amincewa da mutumin da ya taɓa yin kuskure mai tsanani ba. Wani ɗan’uwa mai suna Ricardo wanda aka sauke shi daga dattijo bayan ya yi hidimar shekaru da yawa, ya ce: “Kuskuren da na yi ya sa ni baƙin ciki sosai. Yin tunani cewa ban cancanta ba ya hana ni ɗaukan matakan da za su taimaka mini in sake yi wa ’yan’uwa hidima a matsayin dattijo. Ban tabbata cewa zan sake zama amintacce ba. Amma tun da ina jin daɗin taimaka wa wasu, na sami damar yin nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane da ƙarfafa ’yan’uwa a Majami’ar Mulki da kuma yin wa’azi tare da su. Hakan ya taimaka mini in sake samun gaba gaɗi, kuma a yau na sake zama dattijo.”
Ƙin gafarta wa mutane zai iya hana mutum zama dattijo. Ya fi dacewa mu zama kamar Dauda bawan Jehobah wanda ya gudu daga Sarki Saul mai ƙishi. Dauda ya ƙi yin ramako a kan Saul ko da ya sami zarafin yin hakan. (1 Sam. 24:4-7; 26:8-12) Sa’ad da aka kashe Saul a yaƙi, Dauda ya yi kuka sosai, ya ce Saul da ɗansa Jonathan “abin ƙauna ne abin ƙawa.” (2 Sam. 1:21-23) Dauda bai riƙe su a zuciya ba.
Idan kana ji cewa wani ya bi da kai yadda bai dace ba, kada ka riƙe shi a zuciya. Alal misali, wani ɗan’uwa a Biritaniya mai suna William ya yi wajen shekara 30 yana hidima a matsayin dattijo, amma sa’ad da aka sauke shi, bai ji daɗi ba kuma ya riƙe wasu dattawa a zuciya. Mene ne ya taimaka wa William ya daina wannan halin? Ya ce, “Karanta littafin Ayuba ya taimaka mini. Na koyi cewa idan Jehobah ya taimaka wa Ayuba ya kasance da salama da abokansa uku, zai iya taimaka mini ma in kasance da salama da dattawa a ikilisiya.”—Ayu. 42:7-9.
ALLAH YANA SAKA WA WAƊANDA SUKA SAKE ZAMA DATTAWA
Idan ka yanke shawara cewa kana so a sauke ka a matsayin dattijo, zai dace ka yi la’akari a kan dalilin da ya sa ka yi haka. Shin matsaloli sun shawo maka kai ne? Shin ka fi ɗaukan wasu abubuwa da fifiko ne a rayuwarka? Laifin da wani ya yi maka ne ya sa ka sanyin gwiwa? Ko da mene ne ya jawo hakan, zai dace ka tuna cewa kana taimaka wa mutane sosai a matsayinka na dattijo. Jawabanka da misalinka sun ƙarfafa su kuma ziyarar ƙarfafa da kake kai musu tana taimaka musu su jimre gwaje-gwaje. Ƙari ga haka, hidimarka a matsayin dattijo mai aminci ya faranta wa kai da kuma Jehobah rai.—Mis. 27:11.
Jehobah ya taimaka wa maza su sake yin farin ciki da kuma kasance da muradin yin ja-gora a cikin ikilisiya. Idan ka sauka a matsayin dattijo ko kuma an sauke ka, za ka iya sake “burin aikin kula da ikilisiya.” (1 Tim. 3:1) Bulus bai “fasa yin addu’a” cewa Kiristocin da ke Kolosi su cika da sani na gaskiya game da Allah ba domin su ‘yi tafiya wadda ta cancanta ga Ubangiji, suna gamshe shi sarai.’ (Kol. 1:9, 10) Idan ka sake samun gatan yin hidima a matsayin dattijo, ka roƙi Jehobah ya sa ka kasance da ƙarfi da jimiri da kuma farin ciki. Bayin Jehobah suna bukatar mutanen da za su taimaka musu su ƙarfafa dangantakarsu da Allah a waɗannan kwanaki na ƙarshe. Shin kana da dama kuma kana a shirye ka ƙarfafa ’yan’uwanka?
a An canja wasu sunaye.