Mu Riƙa Kula Da Kuma Ƙarfafa Juna
“Bari kuma mu lura da juna domin mu tsokani juna zuwa ga ƙauna da nagargarun ayyuka.”—IBRAN. 10:24.
1, 2. Mene ne ya taimaki Shaidun Jehobah guda 230 su rayu sa’ad da suke tafiyar mutuwa bayan Yaƙin Duniya na biyu?
SA’AD DA gwamnatin Nazi ta taɓarɓare bayan Yaƙin Duniya na biyu, an ba da wani umurci cewa a halaka dubban mutanen da suka rage a sansani. Za a kai fursunonin da ke sansanin Sachsenhausen baƙin teku inda za a saka su cikin jirgin ruwa kuma a juye su cikin tekun. Shi ya sa daga baya aka kira wannan ƙullin tafiyar mutuwa.
2 Fursunoni guda 33,000 sun yi tafiyar mil 155 daga sansanin da ke Sachsenhausen zuwa baƙin tekun da ke birnin Lübeck, a ƙasar Jamus. Akwai Shaidun Jehobah guda 230 daga ƙasashe shida a cikin waɗannan fursunonin. Duk fursunonin sun yi kasala saboda rashin abinci da kuma ciwo. Mene ne ya taimaki ’yan’uwanmu su rayu? Wani cikinsu ya ce, “Mun ci gaba da ƙarfafa juna.” Ƙaunar da suke wa juna haɗe da “mafificin girman iko” daga Allah ya taimake su a wannan mawuyacin yanayi.—2 Kor. 4:7.
3. Me ya sa muke bukatar mu ƙarfafa juna?
3 Duk da cewa ba ma tafiyar mutuwa irin tasu, amma muna bukatar mu jimre da matsaloli da yawa. Bayan Mulkin Allah ya soma sarauta a shekara ta 1914, an kori Shaiɗan daga sama zuwa duniya. Mene ne sakamakon hakan? Yana “matsanancin fushi, don ya san lokacinsa ya ƙure.” (R. Yoh. 12:7-9, 12, Littafi Mai Tsarki) Yayin da yaƙin Armageddon yake kusatowa, Shaiɗan yana amfani da gwaje-gwaje don ya ga cewa ya ɓata abokantakarmu da Jehobah. Muna kuma ji da tattali na yau da kullum. (Ayu. 14:1; M. Wa. 2:23) A wasu lokatai, dukan waɗannan wahalar za su iya sa mu kasala har mu yi sanyin gwiwa kome ƙoƙarinmu. Alal misali, wani ɗan’uwa ya ƙarfafa mutane da dama cikin shekaru da yawa su kasance da aminci ga Jehobah. Amma sa’ad da ya soma tsufa, shi da matarsa suka yi rashin lafiya, sai ya soma sanyin gwiwa. Dukanmu muna bukatar “mafificin girman iko” daga Jehobah da kuma ƙarfafa daga juna kamar wannan ɗan’uwan.
4. Idan muna so mu ƙarfafa mutane, wane gargaɗin manzo Bulus ne ya kamata mu bi?
4 Idan muna so mu riƙa ƙarfafa mutane, wajibi ne mu bi shawarar da manzo Bulus ya ba Kiristoci Ibraniyawa. Ya ce: “Bari kuma mu lura da juna domin mu tsokani juna zuwa ga ƙauna da nagargarun ayyuka; kada mu fasa tattaruwanmu, kamar yadda waɗansu sun saba yi, amma mu gargaɗar da juna; balle fa yanzu, da kuna ganin ranan nan tana gusowa.” (Ibran. 10:24, 25) Ta yaya za mu iya bin wannan shawarar?
“MU LURA DA JUNA”
5. Mene ne furucin nan “mu lura da juna” yake nufi, kuma yaya za mu iya yin hakan?
5 Furucin nan “mu lura da juna” yana nufin yin tunani game da bukatun wasu. Idan muka gai da ’yan’uwanmu a Majami’ar Mulki da garaje ko idan muka tattauna abubuwan marar amfani da su, ba za mu iya sanin bukatunsu ba. Bai kamata mu riƙa shisshigi game da abin da bai shafe mu ba. (1 Tas. 4:11; 1 Tim. 5:13) Amma ya kamata mu san ’yan’uwanmu, wato mu san yanayinsu da halayensu da abubuwan da suke so da abubuwan da ba sa so da kuma yadda suka ɗauki bautar Jehobah. Zai dace mu nuna musu cewa mu abokansu ne kuma muna ƙaunarsu. Muna bukatar mu kasance tare da su a kowane lokaci har ma sa’ad da suke sanyin gwiwa saboda mawuyacin yanayi.—Rom. 12:13.
6. Mene ne zai taimaki dattijo ya “lura” da waɗanda ke ikilisiyarsu?
6 An aririce dattawa su ‘yi kiwon garken Allah wanda ke wurinsu,’ kuma su yi hakan da yardar rai da kuma ƙwazo. (1 Bit. 5:1-3) Ta yaya za su yi kiwon garken Allah da kyau idan ba su san ’yan’uwansu sosai ba? (Karanta Misalai 27:23.) Idan dattawa suka nuna cewa suna a shirye su taimaka wa ’yan’uwansu kuma suna jin daɗin kasancewa tare da su, zai yi wa ’yan’uwa a cikin ikilisiyarsu sauƙi su nemi taimako daga wurinsu. Kuma ba za su ji nauyin gaya musu abin da ke damunsu ba. A sakamako, dattawa za su samu zarafin taimaka wa kowa.
7. Me ya kamata mu tuna sa’ad da mutum ya yi “magana da rashin hankali”?
7 Manzo Bulus ya gaya wa Kiristoci Tasalonikawa cewa su taimaki “marasa-ƙarfi.” (Karanta 1 Tasalonikawa 5:14.) “Marasa ƙarfi” sun haɗa da masu raunanan zukata da kuma waɗanda suke sanyin gwiwa. Littafin Misalai 24:10 ya ce: “Idan ka yi suwu cikin ranar ƙunci, ƙarfinka kaɗanna ne.” Mutum da ke baƙin ciki sosai zai iya yin “magana da rashin hankali.” (Ayu. 6:2, 3) Za su iya faɗan wani abu da za su yi da-na-sani daga baya. Abin da ya faru da wata mai suna Rachelle ke nan wadda mahaifiyarta take ciwon baƙin ciki sosai. Ta ce: “Mahaifiyata tana baƙar magana a wasu lokatai. Amma a waɗannan lokutan, na tuna wa kaina cewa ita ainihi mace ce mai ƙauna da kirki da kuma karimci. Na koya cewa masu ciwon baƙin ciki za su iya faɗin abin da za su yi da-na-sani daga baya. Idan mutum ya mai da martani, hakan zai zama babban kuskure.” Littafin Misalai 19:11 ya ce: “Hankalin mutum yakan sa fushinsa shi yi jinkiri: Daraja ne kuwa a gareshi shi ƙyale laifi.”
8. Wane ne ya kamata mu “gwada” wa ƙaunarmu kuma me ya sa?
8 Ta yaya za mu iya “lura” da mutumin da yake sanyin gwiwa sanadin zunubin da ya taɓa yi bayan ya riga ya tuba? Manzo Bulus ya yi furuci na gaba game da wani mutumi a ikilisiyar Korinti da ya tuba daga zunubinsa. Ya ce: “Ku gafarta masa, ku yi masa ta’aziya kuwa, kada ya zama da ko ƙaƙa irin wannan shi dulmaya domin yawan baƙin cikinsa. Domin wannan fa ina roƙonku ku gwada masa aikin ƙauna.” (2 Kor. 2:7, 8) Furucin nan “ku gwada” yana nufin a “nuna” ko kuma a “tabbatar” da abu. Ɗan’uwa ba zai san cewa muna ƙaunarsa da kuma kula da shi ba sai idan muna nuna hakan ta furucinmu da kuma ayyukanmu.
“MU TSOKANI JUNA ZUWA GA ƘAUNA DA NAGARGARUN AYYUKA”
9. Mene ne yake nufi mu “tsokani juna zuwa ga ƙauna da nagargarun ayyuka”?
9 Manzo Bulus ya ce: “Bari kuma mu lura da juna domin mu tsokani juna zuwa ga ƙauna da nagargarun ayyuka.” Muna yin hakan ta wajen taimaka wa ’yan’uwanmu su nuna ƙauna kuma su yi abin da ya dace. Alal misali, idan muna gashi da wutar gawayi kuma wutar ta soma ƙasa, me za mu iya yi don wutar ta ci gaba da ci? Wajibi ne mu kakkabe tokar kuma mu hura wutar. Hakazalika, za mu iya taimaka wa ’yan’uwanmu su yi marmarin ci gaba da bauta wa Jehobah. Hanya mafi kyau da za mu iya yin hakan, ita ce ta wajen yaba wa ’yan’uwanmu don ayyukansu masu kyau.
10, 11. (a) Su waye ne suke bukatar ƙarfafa? (b) Ka ba da misalin yadda ƙarfafa za ta iya taimaka wa mutum ya yi abin da ya dace.
10 Dukanmu muna bukatar ƙarfafa, ko muna sanyin gwiwa ko a’a. Wani ɗan’uwa ya ce: “Mahaifina bai taɓa ce na yi wani abu mai kyau ba.” Saboda haka, sa’ad da ya yi girma, bai taɓa ganin cewa ya yi wani abu mai kyau ba. Ko da yake shi ɗan shekara 50 ne yanzu, yana farin ciki sa’ad da wani ya yaba masa don ayyuka masu kyau a matsayin dattijo. Abin da ya faru da wannan ɗan’uwan ya koya masa cewa ƙarfafa mutum yana da muhimmanci sosai, kuma hakan ya sa yana neman zarafin ƙarfafa wasu. Yaya kake ji sa’ad da wani ya yi maka godiya don wani abu mai kyau da ka yi? Babu shakka, hakan yana ƙarfafa ka. Majagaba da tsofaffi da kuma waɗanda suke sanyin gwiwa za su iya amfana idan an ƙarfafa su.—Rom. 12:10.
11 Sa’ad da dattawa suke ƙoƙarin su taimaki wani da ya yi laifi, zai dace su ambata wasu ayyuka masu kyau da ya yi a dā, kuma hakan zai iya sa hankalinsa ya dawo kuma ya yi nagarta. (Gal. 6:1) Abin da ya taimaki wata ’yar’uwa mai suna Miriam ke nan. Ta ce: “Sa’ad da wasu ƙawayeta suka bar ƙungiyar Jehobah kuma mahaifina ya kamu da ciwon ƙwaƙwalwa, hakan ya sa ni baƙin ciki sosai.” Don na magance baƙin cikin da nake yi, sai na soma fita zance da wani saurayi da ba ya bauta wa Jehobah. Mene ne sakamakon hakan? Ta ji kamar ba ta cancanci Jehobah ya ƙaunace ta ba, kuma ta so ta daina bauta masa. Amma, wani dattijo ya tuna mata dukan ayyuka masu kyau da ta yi a ƙungiyar Jehobah kuma ya tabbatar mata cewa har ila Jehobah yana ƙaunarta. Hakan ya ƙarfafa ta. Sai ta rabu da saurayin kuma ta ci gaba da bauta wa Jehobah.
12. Mene ne zai iya faruwa sa’ad da muka gwada ’yan’uwanmu da wasu ko kushe su ko kuma sa su yi takaici?
12 Ya kamata mu lura don kada mu wuce kima a yadda muke ƙarfafa ’yan’uwa don su ci gaba da bauta wa Allah da ƙwazo. Bai kamata mu gwada su da wani ba ko mu kushe su don ba su bi ra’ayinmu ba ko kuma mu sa su yi takaici domin ba su yi iya ƙoƙarinsu a wani aikin da suka yi ba. Ko da yake yin hakan zai iya sa su farfaɗo, amma ba zai daɗe ba. Hanya mafi kyau da za mu motsa ’yan’uwanmu ita ce ta wajen yaba musu da kuma taimaka musu su san cewa ƙaunarmu ga Allah ce ta sa muke iya ƙoƙarinmu a hidimarsa.—Karanta Filibiyawa 2:1-4.
“MU GARGAƊAR DA JUNA”
13. Mene ne furucin nan “gargaɗar da juna” yake nufi? (Ka duba hoton da ke shafi na farko.)
13 A ƙarshe, manzo Bulus ya ce muna bukatar mu riƙa “gargaɗar da juna.” Za mu iya gwada ƙarfafa wani da zuba fetur cikin wuta don ta ci gaba da ci ko ta daɗa ci sosai. “Gargaɗar da juna” yana nufin ƙarfafa ’yan’uwanmu don su ci gaba da bauta wa Allah. Sa’ad da muke so mu taimaki wani da ke sanyin gwiwa, wajibi ne mu furta kalmomin da za su nuna cewa muna ƙaunarsu kuma muna da kirki. (Mis. 12:18) Bugu da ƙari, ya kamata mu riƙa “hanzarin ji” da kuma “jinkirin yin magana.” (Yaƙ. 1:19) Idan muka saurari ɗan’uwanmu kuma muka fahimci abin da ya ce, za mu iya sanin dalilin da ya sa yake sanyin gwiwa kuma mu faɗi abin da zai ƙarfafa shi.
14. Ta yaya wani dattijo ya taimaki wani ɗan’uwa da ke sanyin gwiwa?
14 Ka yi la’akari da yadda wani dattijo mai kirki ya taimaki wani ɗan’uwa da ya daɗe ba ya wa’azi da ƙwazo. Yayin da dattijon ya saurare shi, ya kasance a bayyane cewa har ila yana ƙaunar Jehobah sosai. Yana yin nazarin dukan Hasumiyar Tsaro kuma yana ƙoƙari ya halarci dukan taro a kai a kai. Amma, wasu a cikin ikilisiya sun yi wani abu da ya ɓata masa rai. Dattijon ya saurara sosai kuma ya fahimci yadda ɗan’uwan yake ji ba tare da kushe shi ba. Bayan haka, ya tabbatar masa cewa ’yan’uwa da kuma Jehobah suna ƙaunarsa. Da sannu-sannu, ɗan’uwan ya fahimci cewa ya ƙyale abin da ya faru tun da daɗewa ya hana shi bauta wa Allahn da yake ƙauna. Dattijon ya gayyaci ɗan’uwan su fita wa’azi tare kuma ya sa ya sake soma wa’azi da ƙwazo kuma daga baya ya sake zama dattijo.
15. Mene ne za mu iya koya daga Jehobah game da ƙarfafa mutane?
15 Wataƙila, mutumin da ke sanyin gwiwa ba zai yi saurin amince da taimakon da muke so mu yi masa ba. Mai yiwuwa, za mu bukaci taimaka masu na ɗan lokaci. Manzo Bulus ya ce: “Ku taimaki marasa tsayayyiyar zuciya, ku yi haƙuri da kowa da kowa.” (1 Tas. 5:14, LMT) Kada mu gaji da waɗanda suke sanyin gwiwa, amma mu ci gaba da ‘taimaka’ da kuma tallafa musu. Jehobah ya yi haƙuri da bayinsa da suka yi sanyin gwiwa a zamanin dā. Alal misali, Allah ya yi haƙuri da Iliya kuma ya yi la’akari da yadda yake ji. Ya tanadar masa da bukatunsa don ya ci gaba da hidimarsa. (1 Sar. 19:1-18) Sa’ad da Dauda kuma ya yi zunubi, ya tuba da gaske kuma Jehobah ya gafarce shi. (Zab. 51:7, 17) Allah ya kuma taimaka wa marubucin Zabura ta 73 wanda ya kusan daina bauta masa. (Zab. 73:13, 16, 17) Jehobah yana bi da mu cikin haƙuri da kuma kirki, musamman ma sa’ad da muke sanyin gwiwa. (Fit. 34:6) Littafi Mai Tsarki ya ce jin ƙan Jehobah “sabuwa ce kowace safiya,” kuma ba za su “halaka ba.” (Mak. 3:22, 23) Jehobah yana so mu yi koyi da shi kuma mu bi da masu sanyin gwiwa da kirki.
MU ƘARFAFA JUNA DON MU KASANCE A HANYAR RAI
16, 17. Mene ne ya wajaba mu yi yayin da ƙarshen wannan duniyar ke daɗa kusatowa, kuma me ya sa?
16 Fursunoni 33,000 sun baro sansanin Sachsenhausen, kuma dubbai cikinsu sun mutu. Amma, dukan Shaidu 230 da suka bar sansanin sun rayu. Me ya sa? Domin dukansu sun ƙarfafa da kuma taimaka wa juna.
17 A yau, muna bin hanya “wadda ta nufa wajen rai.” (Matt. 7:14) Nan ba da daɗewa ba, dukan bayin Jehobah za su shiga sabuwar duniya ta adalci. (2 Bit. 3:13) Bari mu duƙufa wajen taimaka wa juna don mu ci gaba da yin tafiya a kan hanyar rai.