Ku Zama Masu Himma Wajen Ƙarfafa ’Yan’uwa Su Yi Nagargarun Ayyuka
Littafin Ibraniyawa 10:24 ya ce mu “lura da juna” don mu ƙarfafa “juna zuwa ga ƙauna da nagargarun ayyuka.” Muna iya ƙarfafa ’yan’uwanmu su yi abubuwa masu kyau ta misalinmu mai kyau da kuma furucinmu da ke nuna cewa muna da bangaskiya. Ku gaya wa ’yan’uwa labarai masu kyau da kuke da su. Ku bari ’yan’uwa su ga yadda kuke farin cikin bauta wa Jehobah. Amma kada ku gwada iyawarsu da naku ko kuma na wasu. (Gal. 6:4) Ku yi amfani da iyawarku a hanyar da za ta ƙarfafa ’yan’uwa kuma ta sa su zama masu “ƙauna” da kuma masu yin “nagargarun ayyuka,” ba a hanyar da za ta sa su riƙa ji kamar sun kasa ba. (Ka duba littafin nan Benefit From Theocratic Ministry School Education shafi na 158, sakin layi na 4.) Idan muka ƙarfafa ’yan’uwa su zama masu ƙauna, su da kansu za su yi ayyuka masu kyau kamar taimaka ma wasu da abin hannu ko kuma yin wa’azi.—2 Kor. 1:24.