Iyaye—Ku Koyar da Yaranku Tun Suna Jarirai
LITTAFI MAI TSARKI ya ce: “’Ya’ya gādo ne daga wurin Ubangiji: ’ya’yan ciki kuma ladansa ne.” (Zab. 127:3) Dalilin da ya sa iyaye suke murna sosai ke nan, sa’ad da suka samu ƙaruwa.
Ban da murnar da iyaye suke yi sa’ad da suka sami ƙaruwa, suna da hakki masu muhimmanci da za su cika. Suna bukatar su ciyar da yaron da kyau kowace rana don ya girma kuma ya kasance da koshin lafiya. Amma don yaron ya ƙulla dangantaka ta kud da kud da Jehobah, iyayen suna bukatar su koya masa ƙa’idojin Allah da ke cikin Littafi Mai Tsarki. (Mis. 1:8) A yaushe ne ya kamata su soma koyar da yaron kuma mene ne za su koya masa?
IYAYE SUNA BUKATAR TAIMAKON ALLAH
A cikin Littafi Mai Tsarki, akwai wani mutum mai suna Manoah daga ƙabilar Dan. Mutumin yana da zama a garin Zorah a ƙasar Isra’ila ta dā. Matarsa ba ta taɓa haihuwa ba, amma mala’ikan Jehobah ya gaya mata cewa za ta haifi ɗa. (Alƙa. 13:2, 3) Hakan ya sa su farin ciki sosai, amma sun damu da yadda za su yi rainon yaron. Manoah ya yi addu’a cewa: “Ya Ubangiji, ina roƙonka, ka bar mutumin nan na Allah da ka aiko shi, shi sake zuwa garemu, shi koya mana abin da za mu yi da yaron da za a haifa.” (Alƙa. 13:8) Sun koya wa ɗansu Samson dokokin Allah kuma ya amince da abin da suka koya masa. Littafi Mai Tsarki ya ce ‘ruhun Ubangiji ya soma motsa [Samson]’ kuma hakan ya sa ya soma yin ayyuka masu ban al’ajabi a matsayin alƙalin Isra’ilawa.—Alƙa. 13:25; 14:5, 6; 15:14, 15.
A yaushe ne ya kamata iyaye su soma koyar da ’ya’yansu? Afiniki mahaifiyar Timotawus da kakarsa Lois sun soma koya masa “littattafai masu-tsarki” tun yana “jariri.” (2 Tim. 1:5; 3:15) Hakika, an soma koya wa Timotawus Nassosi tun yana jariri.
Ya dace iyaye su roƙi Jehobah ya yi musu ja-gora kuma su yi shiri tun da wuri don su soma koyar da ɗansu tun yana “jariri.” Littafin Misalai 21:5 ya ce: “Tunanin mai-himma zuwa yalwata kaɗai su ke nufa.” Kafin mace ta haihu, ita da mijinta sukan yi shiri da kyau kuma wataƙila su rubuta dukan abubuwan da suke bukata. Hakazalika, yana da muhimmanci su shirya da kyau yadda za su riƙa koya wa jaririn game da Jehobah. Ya kamata su kafa maƙasudin soma wannan koyarwar jim kaɗan bayan haihuwa.
Wani littafin da ya yi bayani a kan yadda yara suke girma ya ce ƙwaƙwalwar jariri tana soma koyon abubuwa sosai nan da nan cikin ’yan watanni bayan an haife shi. Saboda haka, yana da kyau iyaye su koya wa jaririn game da Jehobah da kuma ƙa’idojinsa a wannan lokacin.
Wata majagaba ta kullum ta ce game da ’yarta: “Na soma zuwa wa’azi da ita tun tana ’yar wata ɗaya. Ko da yake ba ta san kome ba, na san cewa abin da na yi ya amfane ta. Sa’ad da ta zama ’yar shekara biyu, sai ta soma ba mutane warƙa da gaba gaɗi.”
Iyaye za su sami sakamako mai kyau sosai idan suka soma koyar da ’ya’yansu tun da wuri. Duk da haka, iyaye sun san cewa yin hakan ba cin tuwo ba ne.
KU RIFTA ZARAFI
Koyar da yaro ba shi da sauƙi domin abu kaɗan zai iya janye hankalinsa. Yara suna son su koya game da duk abin da suka gani kusa da su. Mene ne iyaye za su iya yi don su taimaka wa yaron ya mai da hankali ga abin da suke koya masa?
Ka yi la’akari da abin da Musa ya faɗa a cikin littafin Kubawar Shari’a 6:6, 7. Ya ce: “Waɗannan zantattuka fa, da ni ke umurce ka yau, za su zauna cikin zuciyarka: kuma za ka koya wa ’ya’yanka su da anniya, za ka riƙa faɗinsu sa’anda kana zaune cikin gidanka, da sa’anda ka ke tafiya a kan hanya, da sa’anda kana kwanciya, da sa’anda ka tashi.” Domin yara su koya, iyaye suna bukatar su riƙa maimaita abin da suke koya musu sau da sau. Ƙaramin yaro yana kamar tsiron itace da ke bukatar ruwa a kai a kai. Kamar yadda manya sukan riƙe wani batu da sauri sa’ad da suka maimaita shi sau da sau, yara ma sukan tuna da abin da aka koya musu idan aka maimaita shi.
Iyaye suna bukatar su ba da lokaci sosai wajen koya wa yaransu game da Allah. Amma, yin hakan ba shi da sauƙi domin iyaye suna shagala da ayyuka da yawa. Manzo Bulus ya ƙarfafa Kiristoci su “rifta zarafi” don yin ayyuka masu muhimmanci. (Afis. 5:15, 16) Ta yaya iyaye za su iya yin hakan? Wani dattijo da matarsa take hidimar majagaba na kullum ya lura cewa yin rainon yaro da kula da ayyukan ikilisiya da yin aiki bai kasance musu da sauƙi ba. Ta yaya za su keɓe lokaci don koyar da ɗiyarsu? Mahaifin ya ce: “Kowace safiya kafin mu tafi aiki, mukan karanta mata Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki ko kuma ƙasidar nan Examining the Scriptures Daily. Mukan yi mata karatu da yamma kafin ta kwanta kuma idan za mu je wa’azi, muna tafiya tare da ita. Ba ma so mu yi wasa da wannan lokacin da take ƙarama.”
’YA’YA SUNA KAMAR KIBIYOYI
Muna so yaranmu su iya kula da kansu sa’ad da suka girma. Amma, abin da ya fi muhimmanci shi ne mu koya musu su ƙaunaci Jehobah.—Mar. 12:28-30.
Littafin Zabura 127:4 ya ce: “Kamar yadda kibawu a hannun ƙaƙarfan mutum, haka nan ne ’ya’yan ƙuruciya.”’Ya’ya suna kamar kibiyoyi a hannun maharbi. Wajibi ne ya yi saiti da kyau kafin ya yi harbi. Me ya sa? Domin idan ya yi harbin, kibiyar ta tafi ke nan. Hakazalika, yara ba za su kasance da iyayensu tuttur ba. Shi ya sa ya kamata su taimaka wa yaransu su koya kuma su so mizanan Allah kafin su bar gida.
Manzo Yohanna ya ce game da mutanen da ya taimaka musu su zama masu bauta wa Jehobah: “Ba ni da wani farinciki wanda ya fi wannan, in ji labarin ’ya’yana suna tafiya cikin gaskiya.” (3 Yoh. 4) Iyaye Kirista a yau ma za su yi irin wannan farin cikin sa’ad da ’ya’yansu suka ci gaba da “yin tafiya cikin gaskiya.”