Kada Ka Kuskura Ka Yi Gunaguni Da Jehobah
“Wautar ɗan Adam ta kan ɓata hanyarsa: zuciyarsa kuma tana gunaguni da [Jehobah].”—MIS. 19:3.
1, 2. Me ya sa bai dace mu ce Jehobah ne sanadin matsalolin ’yan Adam ba? Ka ba da misali.
A CE ka yi aure shekaru da yawa yanzu kuma kuna zama lafiya lau. Sai ka dawo gida wata rana kuma ka tarar cewa an yi kaca-kaca da dukan abubuwan da ke cikin gidanka. An ɓata kujeru da kafet kuma an farfasa dukan kwanoni. Gidanka mai ban sha’awa ya zama kamar wurin da aka yi girgizar ƙasa. Laifin wa za ka ga? Shin za ka ce, “Me ya sa matata ta yi hakan”? ko kuma, “Wane ne ya yi irin wannan abin”? Babu shakka, tambaya ta biyun ce za ka yi. Me ya sa? Don ka san cewa matarka ƙaunataciya ba za ta taɓa yin irin wannan ɓarnar ba.
2 Ana gurɓatar da ƙasa da ruwa da kuma iska a yau. Mutane suna daɗa yin mugunta da kuma lalata. Amma, mun san cewa Jehobah ba zai taɓa zama sanadin waɗannan matsalolin ba. Ya halicci duniyar nan don ta kasance wurin zama mai kyau da kuma ban sha’awa. (Far. 2:8, 15) Jehobah Allah ne mai ƙauna. (1 Yoh. 4:8) Ta wajen yin nazarin Littafi Mai Tsarki, mun fahimci cewa Shaiɗan ‘sarkin duniyar’ nan ne yake haddasa matsaloli da yawa da suke faruwa.—Yoh. 14:30; 2 Kor. 4:4.
3. Ta yaya za mu iya soma yin tunanin da bai dace ba game da matsalolinmu?
3 Amma, ba za mu ɗora wa Shaiɗan laifin kowace matsala ba. Me ya sa? Domin kurakuranmu ne sukan jawo mana wasu matsaloli. (Karanta Kubawar Shari’a 32:4-6.) Za mu iya cewa mun amince da hakan, amma da yake mu ajizai ne, za mu iya soma yin tunanin da bai dace ba game da matsalolinmu. (Mis. 14:12) Maimakon mu ga laifin kanmu ko kuma Shaiɗan, za mu iya ɗora wa Jehobah laifin ko kuma mu soma yin “gunaguni da [Jehobah].”—Mis. 19:3.
4, 5. Ta yaya mutum zai iya yin gunaguni da Jehobah?
4 Shin zai yiwu mu soma yin gunaguni da Jehobah? Hakika, yin hakan ɓata lokaci ne. (Isha. 41:11) Ba wanda zai iya yin faɗa da Allah. Yin hakan aikin banza ne, kamar harara a duhu. Wataƙila ba za mu taɓa furta cewa muna fushi da Jehobah ba, amma littafin Misalai 19:3 ya ce wautar mutum “ta kan ɓata hanyarsa, zuciyarsa kuma tana gunaguni da Ubangiji.” Gaskiyar ita ce, mutum zai iya yin fushi da Jehobah kuma ya soma gunaguni a cikin zuciyarsa. Hakan zai iya soma shafan ayyukan mutumin. Alal misali, zai iya yin sanyi a hidimarsa ko kuma ya daina halartar taro.
5 Mene ne zai iya sa mu yi gunaguni da Jehobah? Ta yaya za mu guji faɗawa cikin wannan tarkon? Amsoshin waɗannan tambayoyin suna da muhimmanci sosai a gare mu, domin za su taimaka mana mu ci gaba da kasancewa da dangantaka ta kud da kud da Jehobah.
ME ZAI IYA SA MU YI GUNAGUNI DA JEHOBAH?
6, 7. Me ya sa Isra’ilawa a zamanin Musa suka soma yin gunaguni da Jehobah?
6 Me zai iya sa amintaccen bawan Jehobah ya soma yin gunaguni da Allah a cikin zuciyarsa? A wannan talifin, za mu tattauna abubuwa biyar da za su iya jawo hakan, kuma za mu tattauna misalan wasu a cikin Littafi Mai Tsarki da suka faɗa cikin wannan tarkon.—1 Kor. 10:11, 12.
7 Gunaguni da wasu suke yi zai iya shafarmu. (Karanta Kubawar Shari’a 1:26-28.) Ka yi tunanin abin da Jehobah ya yi don ya fitar da Isra’ilawa daga ƙasar Masar. Ya sa annoba goma suka faɗa wa Masarawa kuma ya halaka Fir’auna da sojojinsa a cikin Jar Teku. (Fit. 12:29-32, 51; 14:29-31; Zab. 136:15) Isra’ilawa suna ɗokin shigar Ƙasar Alkawarin. Duk da haka, suka soma yin gunaguni da Jehobah. Me ya sa suka yi rashin bangaskiya? Rahoton da ’yan leƙen asiri guda goma suka kawo ya tsoratar da su kuma ya sa su sanyin gwiwa. (Lit. Lis. 14:1-4) Saboda haka, Jehobah bai ƙyale tsarar ta shiga “ƙasar nan mai-kyau” ba. (K. Sha 1:34, 35) Mene ne hakan ya koya mana? Gunaguni ko kuma baƙar magana da wasu suke yi game da yadda Jehobah yake bi da mutanensa zai iya sa mu yi rashin bangaskiya, kuma mu soma gunaguni da Jehobah.
8. Me ya sa mutanen zamanin Ishaya suka soma ɗora wa Jehobah laifi?
8 Matsaloli za su iya sa mu sanyin gwiwa. (Karanta Ishaya 8:21, 22.) Yahudawa sun shiga wahala sosai a zamanin Ishaya. Magabta sun shinge su. Hakan ya jawo ƙarancin abinci da kuma yunwa. Amma babbar matsalar ita ce sun daina sauraron Jehobah kuma sun ƙyale dangantakarsu da shi ta yi tsami. (Amos 8:11) Maimakon su nemi taimakon Jehobah, sai suka ɗora masa da kuma sarakunansu laifin haddasa matsalolinsu. Hakazalika, idan muka shiga wata matsala ko kuma bala’i ya faɗa mana, za mu iya soma ganin laifin Jehobah kuma mu ji kamar ya ƙi ya taimaka mana.
9. Me ya sa Isra’ilawa a zamanin Ezekiyel suka ji cewa Jehobah ba ya gudanar da abubuwa a hanyar da ba ta dace ba?
9 Ba mu da cikakken bayani. A zamanin Ezekiyel, Isra’ilawa sun soma ji kamar Jehobah ba ya gudanar da abubuwa a hanyar da ta dace. Me ya sa? Domin ba su da cikakken bayani game da abubuwan da suke faruwa. (Ezek. 18:29) Kamar dai sun mai da kansu alƙalai, kuma sun shar’anta Jehobah bisa ga ƙa’idojinsu. Ta yaya hakan zai iya faruwa da mu? Wataƙila mun karanta wani labari a Littafi Mai Tsarki kuma mun ɗan rikice, ko kuma ba mu fahimci abin da ya sa wani abu yake faruwa da mu ba. Hakan zai iya sa mu ji kamar “hanyar Ubangiji ba daidai ba ce.”—Ayu. 35:2.
10. Ta yaya mutum zai iya bin mugun misalin Adamu?
10 Muna neman hujja don zunubi ko kuskuren da muka yi. Adamu ya ɗora wa Allah laifin zunubin da ya yi. (Far. 3:12) Da gangan ne Adamu ya yi zunubi kuma ya san cewa Allah zai yi masa horo. Duk da haka, ya ga laifin Jehobah cewa bai ba shi matar kirki ba. Tun daga lokacin, mutane da yawa sun bi mugun misalin Adamu ta wajen ɗora wa Allah laifin kurakuran da suka yi. Zai dace mu tambayi kanmu, ‘Shin kurakuran da na yi za su iya sa ni takaici da kuma baƙin ciki har in soma tunanin cewa ƙa’idojin Jehobah suna taƙura mini?’
11. Mene ne za mu koya daga misalin Yunana?
11 Yawan son kai. Annabi Yunana ya ga laifin Jehobah domin ya yi wa mutanen ƙasar Nineba ji ƙai. (Yun. 4:1-3) Me ya sa? Yana ganin cewa za a mai da shi annabin ƙarya idan ba a zartar da shelar hukuncin da ya yi ba. Yunana ya ƙyale son kai ya hana shi jin tausayin mutanen Nineba da suka tuba. Hakan zai iya faruwa da mu kuwa? Idan muna tunani game da kanmu kaɗai, za mu iya mancewa da bukatun wasu. Alal misali, mun daɗe muna wa’azi cewa ranar Jehobah ta kusa. Amma sa’ad da mutane suka soma mana ba’a ko dariya cewa ranar ta makara, shin hakan zai sa mu soma ji kamar Jehobah yana jinkiri ne?—2 Bit. 3:3, 4, 9.
YADDA ZA MU GUJI YIN GUNAGUNI DA JEHOBAH
12, 13. Mene ne ya kamata mu yi idan muka soma yin gunaguni game da wasu ayyukan Jehobah?
12 Mene ne za mu iya yi sa’ad da muka soma yin shakkar yadda Jehobah yake yin wasu abubuwa ko kuma yake ƙyale su faru? Ka tuna cewa irin wannan tunanin rashin hikima ne. Littafin Misalai 19:3 ya tuna mana cewa jahilci yana sa mu ga laifin Jehobah don matsalolin da muka jawo wa kanmu. Saboda haka, bari mu tattauna abubuwa biyar da za su taimaka mana kada mu yi gunaguni da Jehobah.
13 Kada ka sa dangantakarka da Jehobah ta yi tsami. Ƙulla dangantaka ta kud da kud da Jehobah za ta hana mu yin fushi da shi. (Karanta Misalai 3:5, 6.) Muna bukatar mu dogara ga Jehobah. Kada mu ga cewa mun fi shi sani ko kuma bukatunmu sun fi muhimmanci. (Mis. 3:7; M. Wa. 7:16) Wannan ra’ayin zai hana mu ganin laifin Jehobah sa’ad da mugayen abubuwa suka faru.
14, 15. Mene ne zai taimaka mana don kada gunagunin wasu ya shafe mu?
14 Kada ka ƙyale gunagunin wasu su shafe ka. Isra’ilawa da suke zamanin Musa suna da dalilan tabbata cewa Jehobah zai taimaka musu su shiga cikin Ƙasar Alkawari. (Zab. 78:43-53) Amma, sa’ad da masu leƙen asiri suka ba da mugun rahoto, Isra’ilawa ba su “tuna da hannunsa ba,” wato sun manta da abin da Jehobah ya yi musu. (Zab. 78:42) Idan muka yi bimbini a kan dukan abubuwa masu ban al’ajabi da Jehobah ya yi mana, hakan zai sa mu kusace shi. Saboda haka, kada mu ƙyale gunagunin wasu ya sa mu daina bauta wa Jehobah.—Zab. 77:11, 12.
15 Wani abu kuma da zai iya raba mu da Jehobah shi ne idan muka kasance da halin da bai dace ba game da ’yan’uwanmu. (1 Yoh. 4:20) Alal misali, Isra’ilawa sun yi gunaguni sa’ad da aka naɗa Haruna a matsayin babban firist, amma Jehobah ya ɗauka hakan a matsayin shi ake wa gunaguni. (Lit. Lis. 17:10) Hakazalika, idan muka soma gunaguni game da waɗanda Jehobah yake amfani da su don ja-gorar aikinsa a duniya, zai ɗauka hakan a matsayin shi ake wa gunagunin.—Ibran. 13:7, 17.
16, 17. Mene ne ya kamata mu tuna sa’ad da muke fuskantar matsaloli?
16 Ka tuna cewa ba Jehobah ke jawo matsalolinmu ba. A zamanin Ishaya, Jehobah yana so ya taimaka wa Isra’ilawa, ko da yake sun daina bauta masa. (Isha. 1:16-19) Sanin cewa Jehobah yana kula da mu kuma yana so ya taimaka mana sa’ad da muke fuskantar matsaloli yana ƙarfafa mu. (1 Bit. 5:7) Jehobah ya yi alkawari cewa zai ƙarfafa mu mu kasance da aminci a gare shi.—1 Kor. 10:13.
17 Ayuba ya sha wahala ko da yake ya kasance da aminci ga Jehobah. Sa’ad da muke shan wahala, ya kamata mu tuna cewa ba Jehobah ba ne sababin hakan ba. Jehobah ya tsani rashin gaskiya amma yana son adalci. (Zab. 33:5) Ya kamata mu zama kamar Elihu, abokin Ayuba wanda ya ce: “Daɗai Allah shi yi mugunta! Mai-iko duka shi yi aikin saɓo!” (Ayu. 34:10) Maimakon Jehobah ya jawo mana matsaloli, yana ba mu “kowace kyakkyawar baiwa da kowace cikakkiyar kyauta.”—Yaƙ. 1:13, 17.
18, 19. Me ya sa bai kamata mu taɓa yin shakkar Jehobah ba? Ka ba da kwatanci.
18 Kada ka kuskura ka yi shakkar Jehobah. Allah kamiltacce ne kuma tunaninsa ya fi namu. (Isha. 55:8, 9) Idan mu masu tawali’u ne, ya kamata mu amince cewa akwai wasu abubuwan da ba mu sani ba. (Rom. 9:20) A yawancin lokuta, ba mu da cikakken labari game da wani batu. Babu shakka, wannan karin maganar gaskiya ne: “Wanda ya fara kawo da’awatasa shi a ke gani da gaskiya: Amma maƙwabcinsa ya kan zo ya tone shi.”—Mis. 18:17.
19 Alal misali, a ce amininmu ya yi wani abu da ba mu fahimta ba ko kuma muna ganin ba yadda ya kamata a yi abubuwa ba. Shin za mu yi saurin tunani cewa ya yi wani abin da bai dace ba? A’a. Maimakon haka, wataƙila za mu yi tunani cewa ba mu san cikakken abin da ya faru ba. Idan muna shirye mu bi da abokanmu ajizai hakan, za mu nuna cewa muna dogara ga Ubanmu da ke cikin sama, wanda hanyoyinsa da kuma tunaninsa suka fi namu girma
20, 21. Me ya sa bai kamata mu ga laifin Jehobah sa’ad da muke fuskantar matsaloli ba?
20 Kada mu ga laifin Jehobah. Me ya sa bai kamata mu yi hakan ba? Domin mu ne sanadin wasu matsalolin da muke fuskanta. Kuma idan muka lura cewa wani abu da ya faru laifinmu ne, ya kamata mu amince da hakan. (Gal. 6:7) Kada ka taɓa ɗora wa Jehobah laifi. Me ya sa ba zai dace mu yi hakan ba? Ka yi la’akari da wannan misalin: A ce wani yana da mota mai gudu sosai. Sai ya soma tuƙi kuma gudun da yake yi ya wuce kima. Sa’ad da ya kai kan kwana sai ya ƙi rage gudun kuma hakan ya sa ya yi hatsari. Wane ne yake da laifi? Shin mutumin da ya ƙera motar ne? A’a! Hakazalika, Jehobah ya halicce mu da ’yancin yin zaɓi. Amma ya kuma ba mu ƙa’idojin da za su taimaka mana mu yi zaɓi masu kyau. Shin kana gani zai dace mu ga laifinsa Mahaliccinmu sa’ad da muka yi kuskure?
21 Babu shakka, ba dukan matsaloli ba ne laifinmu. Wasu abubuwa suna faruwa sanadin ‘sa’a da tsautsayi.’ (M. Wa. 9:11) Kada mu taɓa manta cewa Shaiɗan Iblis ne ainihin sanadin mugunta. (1 Yoh. 5:19; R. Yoh. 12:9) Shi ne magabcin, ba Jehobah ba.—1 Bit. 5:8.
KA DARAJA DANGANTAKARKA DA JEHOBAH
22, 23. Me ya kamata mu tuna idan muka yi sanyin gwiwa sanadin matsalolinmu?
22 Sa’ad da kake fuskantar matsaloli masu tsanani sosai, ka tuna da misalin Joshua da Kaleb. Masu leƙen asirin ƙasa guda goma sun kawo rahoto marar kyau game da Ƙasar Alkawari, amma Joshua da Kaleb ba su goyi bayansu ba. (Lit. Lis. 14:6-9) Sun kasance da bangaskiya ga Jehobah. Amma su ma sun yi ta kai-da-kawowa tare da sauran Isra’ilawa a cikin jeji har na tsawon shekara 40. Shin Joshua da Kaleb sun soma gunaguni cewa bai kamata su ma su sha wannan wahalar ba? A’a. Sun dogara ga Jehobah kuma ya albarkace su. Ko da yake yawancin Isra’ilawan sun mutu a cikin jejin, Jehobah ya sa Joshua da Kaleb su shiga Ƙasar Alkawari. (Lit. Lis. 14:30) Hakazalika, Jehobah zai albarkace mu idan ba mu yi “suwu” da yin nufinsa ba.—Gal. 6:9; Ibran. 6:10.
23 Me ya kamata ka yi idan kana sanyin gwiwa sanadin matsaloli ko kuskuren wasu ko kuma naka kuskuren? Ka tuna cewa Jehobah Allah ne mai ban al’ajabi. Ka kwatanta a zuci abubuwa masu kyau da Jehobah ya yi alkawari cewa zai ba ka. Ka tambayi kanka, ‘Shin da ba ni da dangantaka da Jehobah da yaya rayuwata za ta kasance?’ Ka ci gaba da kusantar Jehobah kuma kada ka taɓa kuskura ka yi gunaguni da shi!