KU KOYAR DA YARANKU
Ana Iya Ɓata wa Allah Rai—Ta Yaya Za Mu Iya Sa Shi Farin Ciki?
An taɓa sa ka baƙin ciki har ka yi kuka?—a Mai yiwuwa hakan ya taɓa faruwa da kowannenmu. A wani lokaci za a iya yin ƙarya a kanmu ko kuma a faɗi wani abu da ba mu yi ba. Hakan zai ɓata mana rai sosai, ko ba haka ba?— Allah ma yana baƙin ciki a duk lokacin da aka yi ƙarya a kansa. Bari mu tattauna wannan batun don mu ga yadda za mu iya sa Allah farin ciki maimakon baƙin ciki.
Littafi Mai Tsarki ya ce wasu mutane da suka faɗa cewa suna ƙaunar Allah sun “ɓata masa rai.” To, bari mu ga dalilin da ya sa Jehobah yake jin haushi a duk lokacin da muka ƙi yin abin da ya ce mu yi.
Mutane biyu da Jehobah ya fara halitta a duniya sun sa shi baƙin ciki sosai. Jehobah ya sa su a cikin Aljanna, inda ake kira “gonar Adnin.” Su wane ne mutanen nan?— Hakika, da farko Adamu, daga baya kuma Hawwa’u. Bari mu ga abin da suka yi da ya ɓata wa Jehobah rai.
Bayan Jehobah ya sa su a cikin wannan gonar, ya gaya musu su kula da ita. Ya kuma gaya musu cewa za su iya haifan ’ya’ya kuma su zauna a cikin gonar ba tare da mutuwa ba. Amma kafin Adamu da Hawwa’u su haifi ’ya’ya, wani mummunan abu ya faru. Ka san ko mene ne wannan abin?— Wani mala’ika ya sa Hawwa’u sa’an nan Adamu su yi wa Jehobah tawaye. Bari mu ga yadda hakan ya faru.
Mala’ikan ya sa wani maciji ya yi kamar yana magana. Hawwa’u ta ji daɗin abin da macijin ya faɗa. Ya gaya mata cewa za ta zama “kamar Allah.” Sai ta yi abin da macijin ya gaya mata ta yi. Ka san abin da macijin ya ce ta yi?—
Hawwa’u ta ci ’ya’yan itacen da Jehobah ya gaya wa Adamu cewa kada su ci. Kafin Allah ya halicci Hawwa’u, ya gaya wa Adamu cewa: “An yarda maka ka ci daga kowane itacen gona a sāke: amma daga itace na sanin nagarta da mugunta ba za ka ɗiba ba ka ci: cikin rana da ka ci, mutuwa za ka yi lallai.”
Hawwa’u ta san wannan dokar. Amma ta ci gaba da kallon wannan itacen sai ta ga cewa “yana da kyau domin ci, abin sha’awa ne kuma ga idanu, . . . sai ta ɗiba ’ya’yansa, ta ci.” Daga baya ta ba Adamu ’ya’yan itacen, “shi kuwa ya ci.” Kana ganin me ya sa ya yi hakan?— Dalilin shi ne cewa Adamu ya ƙaunaci Hawwa’u fiye da Jehobah. Ya gwammace ya faranta mata rai maimakon Allah. Amma yi wa Jehobah biyayya ya fi muhimmanci da yi wa mutane biyayya!
Ka tuna da macijin da ya yi magana da Hawwa’u? Kamar yadda mutum zai iya sa ’yar tsana ta yi kamar tana magana; wani ne ya sa macijin ya yi kamar yana magana. Muryar wane ne aka ji ta bakin macijin?— Muryar ‘tsohon macijin nan, shi wanda ake ce da shi Iblis da Shaiɗan.’
Ka san yadda za ka iya sa Jehobah farin ciki?— Ta wajen yin ƙoƙari ka yi masa biyayya a kowane lokaci. Shaiɗan ya ce zai iya sa dukan mutane su yi masa biyayya. Saboda haka, Jehobah ya umurce mu cewa: “Ɗana [ko ’yata], ka yi hikima, ka fa faranta zuciyata: domin in mayar da magana ga wanda ya zarge ni.” Shaiɗan yana zagi ko kuma yi wa Jehobah gwalo. Ya ce zai iya sa dukan mutane su daina bauta wa Allah. Saboda haka ka sa Jehobah farin ciki ta wajen yi masa biyayya da kuma bauta masa! Za ka ƙoƙarta ka yi hakan?—
Ka karanta a naka Littafi Mai Tsarki
- Zabura 78:40, 41 
- Farawa 1:26-28; 2:15-17; 3:1-6 
- Ru’ya ta Yohanna 12:9; Misalai 27:11 
a Idan kana karatun da yaro ne, wannan alamar fid da ma’ana tana nufin ka dakata ka ƙarfafa shi ya faɗi ra’ayinsa.