Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 9/15 pp. 12-16
  • Bari Umurnan Jehobah Su Sa Ka Farin Ciki

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Bari Umurnan Jehobah Su Sa Ka Farin Ciki
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • KA CI GABA DA DOGARA GA ALLAH TA YIN ADDU’A
  • KA YI BIMBINI A KAN UMURNAN ALLAH
  • KA DOGARA GA ALLAH TA YIN IBADA
  • Umurnan Jehobah Tabbatattu Ne
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Kana Ƙaunar Ƙa’idodin Jehovah Da Zuciya Ɗaya?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Ka Dogara ga Jehobah a Koyaushe!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Za Ku Iya Yarda da ’Yan’uwanku
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 9/15 pp. 12-16

Bari Umurnan Jehobah Su Sa Ka Farin Ciki

“Na ɗauki [umurnanka] su zama gādo a gareni har abada.”—ZAB. 119:111.

MECE CE AMSARKA?

  • Waɗanne dalilai ne muke da su na yin farin ciki saboda umurnan Jehobah?

  • Ta yaya za mu iya dogara ga Jehobah?

  • Me ya sa yake da muhimmanci mu ci gaba da yin hidimar Jehobah?

1. (a) A waɗanne hanyoyi ne mutane suke ɗaukan umurnai kuma me ya sa? (b) Ta yaya fahariya take shafan yadda mutum yake ɗaukan gyara da aka yi masa?

’YAN ADAM suna bin umurni a hanyoyi dabam-dabam. Alal misali, wasu suna amincewa da umurnin da wani mai iko ya ba su, amma idan umurnin daga tsaransu ne, za su yi watsi da shi. Sa’ad da aka yi wa wasu horo ko kuma gyara, sukan yi baƙin ciki ko sanyin gwiwa ko kuma su ɗauka cewa an kunyatar da su. Amma, wasu kuma za su ɗauka an ƙalubalance su ne kuma hakan zai ba su gaba gaɗin yin abin da ya dace. Shin me ya sa ake samun waɗannan bambance-bambancen? Wani dalili shi ne fahariya. Sa’ad da aka yi wa mutum mai fahariya gyara, yakan ɗauka cewa bai cancanta a yi masa gyara ba, kuma saboda haka, ba ya amfana daga gyarar.—Mis. 16:18.

2. Me ya sa Kiristoci na gaskiya suna godiya sa’ad da suka sami shawara daga Littafi Mai Tsarki?

2 Amma Kiristoci na gaskiya suna godiya sa’ad da aka ba su shawara mai kyau, musamman ma idan shawarar daga Littafi Mai Tsarki ne. Umurnan Jehobah suna sa mu kasance da basira kuma suna koyar da mu ta wajen taimaka mana mu guje wa abubuwan da za su lahanta mu kamar son abin duniya da lalata da kuma shaye-shaye. (Mis. 20:1; 2 Kor. 7:1; 1 Tas. 4:3-5; 1 Tim. 6:6-11) Ƙari ga haka, bin umurnin Jehobah yana sa mu “murna a zuci.”—Isha. 65:14.

3. Wane halin marubucin zabura ne ya kamata mu yi koyi da shi?

3 Wajibi ne mu riƙa bin umurnan Jehobah a rayuwarmu idan muna so mu ci gaba da kasancewa da dangantaka mai kyau da shi. Ya dace mu yi koyi da halin wannan marubucin zabura da ya ce: “Na ɗauki [umurnanka] su zama gādo a gareni har abada. Gama su ne ƙawar zuciyata.” (Zab. 119:111) Shin muna yin farin cikin bin umurnan Jehobah, ko kuma muna ɗauka cewa ɗawainiya ne a wani lokaci? Ko da a wasu lokatai yana kasance mana da wuya mu amince da shawara, kada mu yi sanyin gwiwa. Za mu iya kasancewa da tabbaci cewa umurnan Jehobah suna da kyau kuma za su amfane mu a kowane lokaci. Bari mu tattauna abubuwa uku da za su taimaka mana mu fahimci hakan.

KA CI GABA DA DOGARA GA ALLAH TA YIN ADDU’A

4. Mene ne Dauda ya ci gaba da yi a rayuwarsa?

4 Ko da yake sarki Dauda ya fuskanci yanayi dabam-dabam a rayuwarsa, ya ci gaba da dogara ga Mahaliccinsa. Ya ce: “Ya Ubangiji a gareka ni ke ɗaukaka raina. Ya Allahna a gareka na dogara.” (Zab. 25:1, 2) Mene ne ya taimaka wa Dauda ya dogara sosai ga Ubansa na sama?

5, 6. Mene ne Littafi Mai Tsarki ya bayyana mana game da dangantakar Dauda da Jehobah?

5 Mutane da yawa suna addu’a ga Allah a lokacin da suke cikin matsala kaɗai. Irin waɗannan mutanen suna kamar wani da ya ce shi abokinka ne, amma ba ya magana da kai sai lokacin da yake bukatar kuɗi ko kuma wani abu daga wurinka. Da shigewar lokaci, za ka soma shakka ko wannan abokinka yana ƙaunar ka da gaske. Amma ba haka Dauda yake ba. Dangantakarsa da Jehobah ta nuna cewa yana da bangaskiya kuma yana ƙaunar Allah a dukan fannonin rayuwarsa.—Zab. 40:8.

6 Ka lura da waƙar godiya da yabo da Dauda ya yi ga Jehobah: “Ya Ubangiji, Ubangijinmu, Ina misalin darajar sunanka cikin duniya duka! Kai da ka sa girmanka bisa sammai.” (Zab. 8:1) Daga waɗannan kalmomin za ka fahimci cewa Dauda ya kasance da dangantaka ta kud da kud da Ubansa na sama, ko ba haka ba? Iko da kuma ɗaukakar Jehobah sun burge Dauda sosai kuma hakan ya sa shi yabon Jehobah dukan “yini.”—Zab. 35:28.

7. Ta yaya yin addu’a a kai a kai yake amfanar mu?

7 Ya kamata mu riƙa yin addu’a ga Jehobah a kai a kai don mu dogara gare shi kamar Dauda. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku kusato ga Allah, shi kuwa za ya kusato gare ku.” (Yaƙ. 4:8) Yin addu’a ga Jehobah zai sa mu kusace shi, ƙari ga haka, hanya ce ta musamman na samun ruhu mai tsarki.—Karanta 1 Yohanna 3:22.

8. Me ya sa ya kamata mu guji maimaita kalmomi sa’ad da muke addu’a?

8 Sa’ad da kake addu’a, shin kana maimaita wasu kalmomi ko furuci a kowane lokaci? Idan haka ne, kafin ka yi addu’a, ka ɗan dakata don ka yi tunani a kan abin da kake so ka faɗa. Alal misali, idan kana yawan maimaita kalmomi sa’ad da kake magana da abokinka, kana ganin zai ji daɗin maganar ne? Wataƙila ba zai so ya saurare ka kuma ba. Ko da yake Jehobah ba zai so ya ƙi jin addu’ar bayinsa ba, amma yana da muhimmanci mu guji maimaita kalmomi sa’ad da muke addu’a.

9, 10. (a) Waɗanne abubuwa ne ya kamata mu yi addu’a a kai? (b) Mene ne zai sa addu’o’inmu su kasance da ma’ana sosai?

9 A bayyane yake cewa idan muna so mu kusaci Allah, ba zai dace mu riƙa yin addu’a a kan batutuwan da ba su da muhimmanci ba. Idan muna bayyana wa Jehobah abin da ke cikin zuciyarmu sa’ad da muke addu’a, hakan zai sa mu daɗa dogara a gare shi. Shin waɗanne abubuwa ne ya kamata mu yi addu’a a kai? Kalmar Allah ta ce: “Cikin kowane abu, ta wurin addu’a da roƙo tare da godiya, ku bar roƙe roƙenku su sanu ga Allah.” (Filib. 4:6) A taƙaice, sa’ad da muke addu’a, zai dace mu ambata duk wani abin da ya shafi dangantakarmu da Allah ko kuma rayuwarmu a matsayin masu bauta masa.

10 Za mu iya koyan abubuwa da dama daga addu’o’in amintattun maza da mata da suka bauta wa Allah a dā. (1 Sam. 1:10, 11; A. M. 4:24-31) Littafin Zabura yana ɗauke da addu’o’i da waƙoƙi masu ratsa zuciya da aka yi ga Jehobah. Waɗannan addu’o’i da waƙoƙi sun ƙunshi batutuwa na baƙin ciki da na farin ciki. Yin nazarin waɗannan addu’o’in zai sa addu’o’inmu su kasance da ma’ana ga Jehobah.

KA YI BIMBINI A KAN UMURNAN ALLAH

11. Me ya sa muke bukata mu yi bimbini a kan ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki?

11 Dauda ya ce: “Umarnan Ubangiji abin dogara ne, Sukan ba da hikima ga wanda ba shi da ita.” (Zab. 19:7, Littafi Mai Tsarki) Ko da a ce ba mu da hikima, za mu iya zama masu hikima ta wajen bin dokokin Allah. Amma akwai wasu ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da ya kamata mu yi bimbini a kai idan muna so su amfane mu. Alal misali, yin bimbini a kan ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka mana mu kasance da aminci sa’ad da aka matsa mana mu yi abin da bai dace ba a makaranta ko kuma a wurin aiki. Kuma zai iya taimaka mana mu bi dokokin Allah game da ƙin karɓan jini da zama tsakatsaki da kuma yin ado da ya dace. Idan muka yi bimbini a kan waɗannan batutuwa, hakan zai sa mu san abin da ya kamata mu yi sa’ad da muka sami kanmu a cikin yanayin. Irin wannan bimbinin zai taimaka mana mu guji yin da-na-sani.—Mis. 15:28.

12. Yin bimbini a kan waɗanne tambayoyi ne zai taimaka mana mu bi umurnan Allah?

12 Yayin da muke jiran cikar alkawuran da Allah ya yi, shin muna nuna cewa mun tabbata da waɗannan alkawuran kuma nufin Allah ne ya fi muhimmanci a rayuwarmu? Alal misali, shin mun ba da gaskiya cewa za a halaka Babila Babba nan ba da daɗewa ba? Muna ɗaukan albarka da za mu samu a nan gaba, kamar su yin rayuwa har abada a aljanna a duniya da muhimmanci a yanzu kamar yadda muka ɗauke su lokacin da muka soma koyan gaskiya? Muna kasancewa da himma ne a wa’azi ko kuma muna sa al’amuranmu kan gaba a rayuwa? Begen tashin matattu da tsarkake sunan Allah da nuna cewa shi ne ya fi dacewa ya zama Maɗaukakin Sarki kuma fa? Shin waɗannan batutuwan suna da muhimmanci a rayuwarmu har ila? Yin bimbini a kan waɗannan tambayoyin zai iya taimaka mana mu bi umurnan Allah kuma su ‘zama gādo a gare mu har abada.’—Zab. 119:111.

13. Me ya sa Kiristoci na farko suka kasa fahimtar wasu abubuwa? Ka ba da misali.

13 Akwai wasu abubuwa da ke cikin Littafi Mai Tsarki da ba mu gama fahimta ba domin lokaci bai yi da Jehobah zai bayyana mana su ba. Yesu ya sha gaya wa manzanninsa cewa wajibi ne ya sha wahala kuma ya mutu. (Karanta Matta 12:40; 16:21.) Amma manzannin ba su fahimci abin da yake nufi ba. Sun fahimci hakan ne bayan Yesu ya mutu kuma ya tashi ya bayyana a gaban wasu almajiransa, kuma ya “buɗe hankalinsu, domin su fahimci littattafai.” (Luk 24:44-46; A. M. 1:3) Hakazalika, sai bayan da ruhu mai tsarki ya sauko musu a ranar Fentakos na shekara ta 33 a zamaninmu suka fahimci cewa a sama ne za a kafa Mulkin Allah.—A. M. 1:6-8.

14. Wane misali mai kyau ne ’yan’uwa da yawa suka kafa a ƙarni na ashirin, duk da cewa ba su da cikakken fahimi game da kwanaki na ƙarshe?

14 Hakazalika, a ƙarni na ashirin, Kiristoci na gaskiya sun kasance da ra’ayin da bai dace ba game da abin da zai faru a “kwanaki na ƙarshe.” (2 Tim. 3:1) Alal misali, a shekara ta 1914, wasu sun ɗauka cewa za a ɗauke su zuwa sama ba da daɗewa ba. Amma da hakan bai faru ba, sai suka sake bincika Littafi Mai Tsarki kuma suka fahimci cewa akwai gagarumin aikin wa’azi da za a yi tukuna. (Mar. 13:10) Saboda haka, a shekara ta 1922, Ɗan’uwa J. F. Rutherford, da ya ja-goranci aikin wa’azi a lokacin ya gaya wa waɗanda suka halarci taron gunduma na ƙasashe da aka yi a birnin Cedar Point, Ohio, a ƙasar Amirka cewa: Duba, Sarkin yana sarauta! Ku ne ma’aikatansa. Saboda haka, ku yi shela, ku yi shela, ku yi shelar Sarkin da kuma mulkinsa.” Tun daga lokacin, an fi sanin Shaidun Jehobah da yin wa’azin ‘bishara ta mulki.’—Mat. 4:23; 24:14.

15. Ta yaya za mu amfana idan muka yi bimbini a kan yadda Allah ya cika alkawuran da ya yi wa mutanensa?

15 Idan muka yi bimbini a kan yadda Jehobah ya cika alkawuransa ga mutanensa na zamanin dā da kuma na yanzu, za mu ƙara kasancewa da gaba gaɗi cewa zai iya cika alkawuran da ya yi game da nan gaba. Yin bimbini a kan alkawuran da Allah ya yi zai sa mu kasance da farin ciki da kuma tabbaci sosai cewa zai cika alkawuransa.

KA DOGARA GA ALLAH TA YIN IBADA

16. Wace albarka ce za mu samu idan muka kasance da ƙwazo a hidima?

16 Jehobah, Allah ne mai aikatawa. Marubucin zabura ya ce: “Wane ne mai-ƙarfi kamarka, ya Yahweh? Hannunka mai-ƙarfi ne, hannun damarka maɗaukaki ne.” (Zab. 89:8, 13) Da yake Jehobah Allah ne mai aikatawa, sa’ad da muka yi iya ƙoƙarinmu a hidimarsa, hakan yana faranta masa rai kuma yana sa ya albarkace mu. Yana ganin dukan mabiyansa maza da mata, manya da ƙanana, a matsayin waɗanda ba sa “cin abincin ragonci.” (Mis. 31:27) Saboda haka, bari mu ci gaba da kasancewa da ƙwazo a hidimarsa. Hakika, yin iya ƙoƙarinmu a hidimar Jehobah yana sa mu farin ciki kuma yana faranta wa Jehobah rai.—Karanta Zabura 62:12.

17, 18. Ta yaya ayyukan bangaskiya da muke yi suke taimaka mana mu ƙara dogara ga Jehobah? Ka ba da misali.

17 Ta yaya ayyukan bangaskiya da muke yi suke taimaka mana mu ƙara dogara ga Jehobah? Ka yi la’akari da abin da ya faru a lokacin da Isra’ilawa suke dab da shiga Ƙasar Alkawari. Jehobah ya umurci firistocin da ke ɗauke da sunduƙin alkawarin su yi tafiya zuwa cikin Kogin Urdun. Amma yayin da mutanen suka zo kusa da kogin, sai suka ga cewa ruwan sama da aka yi a lokacin ya sa ruwan kogin ya ƙaru. Shin mene ne Isra’ilawan za su yi? Za su ya da zango a bakin kogin ne kuma su jira makonni da dama ko fiye da hakan sai ruwan ya sauka? A’a, sun dogara ga Jehobah kuma sun bi umurnansa. Mene ne sakamakon? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Sa’anda . . . ƙafafun firistoci da ke ɗaukan sanduƙin suka nutsa cikin gefen ruwa, . . . sai ruwayen da suka gangaro daga bisa suka tsaya, . . . mutane kuwa suka haye daidai inda Jericho ta ke. Su firistoci kuma masu-ɗauke da sanduƙin alkawari na Ubangiji, suka tsaya da ƙarfi a kan sandararriyar ƙasa a cikin tsakiyar Urdun, dukan Isra’ila kuwa suka ƙetare a bisa sandararriyar ƙasa.” (Josh. 3:12-17) Ka yi tunanin yadda Isra’ilawa suka yi farin ciki sa’ad da suka ga ruwan kogin ya daina gudu! Hakika, hakan ya ƙarfafa bangaskiyar Isra’ilawa don sun bi umurnin Jehobah.

18 Gaskiya ne cewa Jehobah ba ya yin mu’ujizai a madadin mutanensa a yau, amma sa’ad da muka bi umurninsa, muna samun albarka. Ruhu mai tsarki yana taimaka mana mu cika aikinmu na yin wa’azi game da Mulkinsa a faɗin duniya. Yesu Kristi, babban Mashaidin Jehobah, ya ba almajiransa tabbaci cewa zai tallafa musu a wannan aiki mai muhimmanci. Ya ce: “Ku tafi fa, ku almajirtarda dukan al’ummai, . . . ina tare da ku kullayaumi har matuƙar zamani.” (Mat. 28:19, 20) Shaidun Jehobah da yawa waɗanda a dā suna jin tsoro ko kuma kunya, za su iya shaida cewa ruhun mai tsarki ya taimaka musu su kasance da gaba gaɗin yin wa’azi ga waɗanda ba su taɓa haɗuwa da su ba.—Karanta Zabura 119:46; 2 Korintiyawa 4:7.

19. Wane tabbaci ne muke da shi duk da kasawarmu?

19 Wasu ’yan’uwa ba sa iya yin ayyuka a hidimar Jehobah kamar yadda za su so su yi saboda rashin lafiya ko kuma tsufa. Duk da haka, za su iya kasancewa da tabbaci cewa “Uba mai yawan jinƙai, Allah na dukan ta’aziyya” ya san yanayin kowannensu. (2 Kor. 1:3) Yana farin ciki sa’ad da muka yi iya ƙoƙarinmu a hidimarsa. Kuma ya kamata mu tuna cewa cetonmu ya dangana ne a kan imani ga fansar Kristi.—Ibran. 10:39.

20, 21. A waɗanne hanyoyi ne za mu iya nuna cewa mun dogara ga Jehobah?

20 Bautarmu ta ƙunshi ba da lokacinmu da kuzarinmu da kuma dukiyarmu a hidimar Jehobah. Ya kamata mu “yi aikin mai-bishara” da dukan zuciyarmu. (2 Tim. 4:5) Kuma muna farin cikin taimaka wa mutane su zo “ga sanin gaskiya.” (1 Tim. 2:4) A bayyane yake cewa ɗaukaka da kuma yaba wa Jehobah, yana ƙarfafa dangantakarmu da shi. (Mis. 10:22) Kuma yana sa mu dogara ga Mahaliccinmu a kowane yanayi.—Rom. 8:35-39.

21 Kamar yadda muka tattauna, yin dogara ga Jehobah yana bukatar aiki tuƙuru. Saboda haka, ka ci gaba da dogara ga Jehobah ta yin addu’a. Ka riƙa yin bimbini a kan yadda Jehobah ya cika alkawuransa a dā, da kuma yadda zai yi hakan a nan gaba. Ka ci gaba da dogara ga Jehobah ta yin ibada. Hakika, umurnan Jehobah za su kasance har abada. Kai ma idan ka bi waɗannan umurnan, za ka rayu har abada!

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba