Kana Ƙaunar Ƙa’idodin Jehovah Da Zuciya Ɗaya?
“Ina biyayya da ka’idodinka, ina ƙaunarsu da zuciya ɗaya.”—ZABURA 119:167.
1. A ina musamman muke samun maimaici game da ka’idodin Jehovah?
JEHOVAH yana son mutanensa su yi murna. Don mu more farin ciki na gaske, hakika, dole ne mu yi tafiya cikin dokar Allah kuma mu yi biyayya da umurninsa. Saboda haka, ya ba mu ƙa’idodi. Waɗannan ya maimaita su a cikin Nassosi, musamman a cikin Zabura ta 119, mai yiwuwa mafi ƙanƙancin ɗan sarki na Yahuda Hezekiya ne ya rubuta. Wannan waƙar mai kyau ta fara da waɗannan kalmomi: “Masu farin ciki ne, marasa laifi cikin zamansu, waɗanda suke zamansu bisa ga dokar Ubangiji. Masu farin ciki ne waɗanda suke bin umarnansa, waɗanda suke yi masa biyayya da zuciya ɗaya.”—Zabura 119:1, 2.
2. Ta yaya ƙa’idodin Allah suka shafi farin ciki?
2 Muna ‘tafiya cikin dokar Jehovah’ ta wajen ɗaukar cikakken sanin Kalmarsa da kuma ta amfani da su a rayuwarmu. Tun da muna ajizai, muna bukatar ƙa’idodinsa. Kalmar Ibrananci da aka fassara “tuni” yana nuna cewa Allah yana tunasar mana da dokarsa, ƙa’idodinsa, da kuma umurnansa. (Matiyu 10:18-20) Za mu ci gaba da farin ciki idan muka ci gaba da kiyaye ƙa’idodinsa, domin suna taimakonmu mu guje wa tuntuɓe na ruhaniya da zai kawo bala’i da baƙin ciki.
Manne wa Ƙa’idodin Jehovah
3. Bisa ga abin da Zabura 119:60, 61 ta ce, wane tabbaci ne muke da shi?
3 Mai Zabura yana ƙaunar ƙa’idodin Allah wanda ya rera waƙa: “Ba tare da ɓata lokaci ba, zan gaggauta in kiyaye umarnanka. Mugaye sun ɗaure ni tam da igiyoyi, amma ba zan manta da dokarka ba.” (Zabura 119:60, 61) Ƙa’idodin Jehovah suna taimakonmu mu jure wa tsanantawa domin mun tabbata cewa Ubanmu na samaniya zai iya yanke igiyar hani da abokan gaba suka ɗaure mu da shi. Idan lokaci ya kai, zai ’yantar da mu daga tangarɗa saboda mu ci gaba da wa’azinmu na Mulki.—Markus 13:10.
4. Yaya za mu mayar da martani ga tunasarwar Allah?
4 Wasu lokatai, ƙa’idodin Jehovah suna yi mana gyara. Bari mu yi godiya domin irin wannan gyara kamar yadda mai Zabura ya yi. Cikin addu’a ya gaya wa Allah: “Umarnanka suna faranta mini rai . . . ina ƙaunar koyarwarka.” (Zabura 119:24, 119) Muna da ƙa’idodin Allah fiye da waɗanda mai Zabura yake da su. Ayoyi ɗarurruwa na Nassosin Ibrananci da suka bayyana a Nassosin Helenanci sun tunasar da mu ba kawai umurnan Jehovah ga mutanensa na ƙarƙashin Doka ba amma kuma nufe-nufensa game da ikilisiyar Kirista. Lokacin da Allah ya ga ya dace ya tunasar da mu abubuwa da sun shafi dokokinsa, muna godiya saboda irin wannan ja-gorar. Kuma ta wajen ‘manne wa ƙa’idodin Jehovah,’ za mu guje wa sha’awa ta zunubi da take ɓata wa Mahaliccinmu rai kuma ta hana mu farin ciki.—Zabura 119:31.
5. Ta yaya za mu zo ga ƙaunar ƙa’idodin Jehovah da zuciya ɗaya?
5 Har yaya ya kamata mu ƙaunaci ƙa’idodin Jehovah? Mai zabura ya rera waƙa, “Ina biyayya da ka’idodinka, ina ƙaunarsu da zuciya ɗaya.” (Zabura 119:167, tafiyar tsutsa tamu ce.) Za mu zo ga ƙaunar ƙa’idodin Jehovah da zuciya ɗaya idan muka ɗauke su kuma muka amince da su gargaɗi ne na Uba wanda yake ƙaunarmu da gaske. (1 Bitrus 5:6, 7) Muna bukatar ƙa’idodinsa, kuma ƙaunarmu gare su za ta ƙaru lokacin da muka ga yadda sukan amfane mu.
Abin da Ya Sa Muke Bukatar Ƙa’idodin Allah
6. Wane dalili ɗaya ya sa muke bukatar ƙa’idodin Jehovah, kuma menene zai taimake mu mu tuna su?
6 Dalili ɗaya da ya sa muke bukatar tunasarwa ta Allah domin muna mantuwa ne. The World Book Encyclopedia ya ce: “Galibi dai, da shigewan lokaci mutane suna ƙara mantuwa. . . . Wataƙila ka taɓa mantuwar wani suna ko kuma wani abin da ka sani sosai. . . . Irin wannan mantuwa na ɗan lokaci, da yake faruwa sau da yawa, ana kiranta sha’afa. Masana kimiyya sun gwada shi da neman wani abu a cikin ɗakin da kayayyaki suke a baje. . . . Hanya ɗaya ta tuna wani abu ita ce a yi nazarinsa da daɗewa bayan kana tunanin ka san shi ƙwarai.” Nazari da ƙwazo da kuma maimaitawa zai taimake mu mu tuna ƙa’idodin Allah kuma mu yi amfani da su domin amfanin kanmu.
7. Me ya sa ake bukatar ƙa’idodin Allah yanzu fiye da ko yaushe?
7 Muna bukatar ƙa’idodin Jehovah a yau fiye da kowane lokaci domin mugunta ta wuce gona da iri a tarihin ’yan Adam. Idan muka mai da hankali ga ƙa’idodin Allah, za mu samu fahimi da muke bukata mu guje wa yaudara zuwa hanyar mugunta ta duniya. Mai Zabura ya ce, “Ganewata ta fi ta dukan malamaina, saboda ina ta tunani a kan koyarwarka. Na fi tsofaffi hikima, saboda ina biyayya da umarnanka. Nakan guje wa halin mugunta saboda ina so in yi biyayya da maganarka.” (Zabura 119:99-101) Ta kiyaye ƙa’idodin Allah, za mu guji ‘kowace muguwar hanya’ kuma za mu guji zama kamar tarin talikai, waɗanda “duhun zuciya gare su, bare suke ga rai wanda Allah ke bayarwa.”—Afisawa 4:17-19.
8. Ta yaya za mu kasance a shirye mu yi nasara wajen fuskantar gwajin bangaskiya?
8 Ana bukatar ƙa’idodin Allah kuma domin suna ƙarfafa mu mu jure wa gwajinmu masu yawa a wannan “kwanaki na ƙarshe.” (Daniyel 12:4) Idan ba tare da irin wannan tunasarwar ba za mu zama ‘masu ji su manta.’ (Yakubu 1:25) Amma nazari na kai da na ikilisiya daga Nassosi da ƙwazo da taimakon littattafai daga “amintaccen bawan nan mai hikima” za su taimake mu mu yi nasara wajen fuskantar gwajin bangaskiya. (Matiyu 24:45-47) Irin waɗannan tanadi na ruhaniya suna taimaka mana mu ga abin da dole mu yi domin mu faranta wa Jehovah rai lokacin da muka samu kanmu cikin yanayi na gwaji.
Muhimmancin Taronmu
9. Su wanene ne ‘kyauta a mutane,’ kuma ta yaya suke taimakon ’yan’uwa masu bi?
9 Ana cika ɓangaren bukatarmu ta ƙa’idodin Allah a taronmu na Kirista, inda ’yan’uwa da aka naɗa suke ba mu umurni. Manzo Bulus ya rubuta cewa lokacin da Yesu ya ‘hau sama ya bi da rundunar kamammu ya kuma bayar da kyauta a mutane.’ Bulus ya daɗa: “[Kristi] ya kuma yi wa waɗansu baiwa su zama manzanni, waɗansu annabawa, waɗansu masu yin bishara, waɗansu makiyaya masu koyarwa, domin tsarkaka su samu, su iya aikin hidimar ikilisiya domin inganta jikin Almasihu.” (Afisawa 4:11, 12) Abin godiya ne cewa waɗannan ‘kyauta a mutane’—dattawa da aka naɗa su—suna mai da hankalinmu ga ƙa’idodin Jehovah lokacin da muka taru domin sujjada!
10. Menene ainihin darassin Ibraniyawa 10:24, 25?
10 Godiya ga tanadin Allah za ta motsa mu mu kasance a taron ikilisiya biyar kowanne mako. Muna bukatar mu taru a kai a kai kamar yadda Bulus ya nanata. Ya rubuta: “Mu kuma riƙa kula da juna, ta yadda za mu ta da juna a tsimi mu yi ƙauna da aiki nagari. Kada mu bar yin taronmu, yadda waɗansu ke yi sai dai mu ƙarfafa wa juna zuciya, tun ba ma da kuka ga ranan nan tana kusatowa ba.”—Ibraniyawa 10:24, 25.
11. Ta yaya muke amfana a kowanne taronmu na mako mako?
11 Kana godiya ga abin da taronmu yake yi mana? Nazarin Hasumiyar Tsaro kowanne mako yana ƙarfafa bangaskiyarmu, yana taimakonmu mu yi amfani da ƙa’idodin Jehovah, kuma yana ƙarfafa mu wajen tsayayya wa “ruhun duniya.” (1 Korantiyawa 2:12; Ayyukan Manzanni 15:31) A Taronmu ga Jama’a, masu jawabi suna gabatar da umurnai daga Kalmar Allah, haɗe da ƙa’idodin Jehovah da kuma maganar Yesu mai ban mamaki “maganar rai madawwami.” (Yahaya 6:68; 7:46; Matiyu 5:1–7:29) A Makarantar Hidima ta Allah ana inganta koyarwarmu. Taron Hidima yana da muhimmanci ƙwarai wajen taimaka mana mu inganta gabatar da bishararmu daga gida zuwa gida, a komawa ziyara, a wajen nazarin Littafi Mai Tsarki na gida, da kuma wasu hanyoyin hidimarmu. Ƙaramin rukuni na Nazarin Littafi na Ikilisiya yana ba mu damar mu yi furci da sau da yawa ya ƙunshi ƙa’idodin Allah.
12, 13. Ta yaya mutanen Allah a wata ƙasar Asiya suka nuna godiya ga taron Kirista?
12 Halartar taron ikilisiya a kai a kai yana tunasar da mu umurnan Allah kuma yana taimaka mana wajen ƙarfafa mu a ruhaniya lokacin da ake yaƙi, lokacin da muke fuskantar talauci, da wasu gwaji na bangaskiyarmu. Wasu Kiristoci 70 a wata ƙasa ta Asiya sun ga muhimmancin taro lokacin da aka tilasta musu su bar gidajensu suka koma zama a cikin ƙurmi. Don anniyarsu su ci gaba da taruwa a kai a kai, suka komo cikin gari da yaƙi ya ragargaza, suka kwashe abin da ya rage a Majami’ar Mulki, suka sake ginawa a cikin ƙurmin.
13 Bayan sun jure wa yaƙin na shekaru a wani ɓangaren wannan ƙasar, mutanen Jehovah har yanzu suna hidima da himma. Aka tambayi wani dattijo na wajen: “Menene ya fi taimako wajen tara ’yan’uwan wuri ɗaya?” Menene amsarsa? “A cikin shekara 19, ba mu taɓa fasa taro ba. Wasu lokatai domin bom da ake jefawa ko kuma wasu matsaloli, wasu ’yan’uwa ba su samu damar zuwa wajen taro ba, amma ba mu taɓa fasa taro ba.” Waɗannan ’yan’uwa ƙaunatattu babu shakka sun fahimci muhimmancin ‘ka da su bar yin taronsu.’
14. Menene za mu koya daga al’adar tsohuwa Hannatu?
14 Hannatu gwauruwa ’yar shekara 84 “ba ta rabuwa da Haikali.” Domin haka, tana wajen lokacin da aka kawo Yesu yana jariri ba da daɗewa ba bayan an haife shi. (Luka 2:36-38) Ka ƙudiri anniyar ba za ka bar taro ba? Kana iyakacin ƙoƙarinka ka kasance a dukan sashen manyan taro da kuma taron gunduma? Umurnai masu amfani na ruhaniya da muke samu a waɗannan taron suna ba da tabbaci cewa Ubanmu na samaniya yana ƙaunar mutanensa. (Ishaya 40:11) Irin wannan taron yana kawo farin ciki, kuma kasancewarmu a wajen yana nuna godiyarmu ga ƙa’idodin Jehovah.—Nehemiya 8:5-8, 12.
Ƙa’idodin Jehovah Ya Ware Su
15, 16. Ta yaya kiyaye ƙa’idodin Jehovah suka shafi ɗabi’armu?
15 Kiyaye ƙa’idodin Allah ya taimaka wajen ware mu daga wannan muguwar duniya. Alal misali, kiyaye ƙa’idodin Allah ya hana mu yin lalata. (Maimaitawar Shari’a 5:18; Karin Magana 6:29-35; Ibraniyawa 13:4) Jarabar yin ƙarya, rashin gaskiya, ko kuma sata za a iya yin nasara wajen magance su ta wajen bin ƙa’idodin Allah. (Fitowa 20:15, 16; Littafin Firistoci 19:11; Karin Magana 30:7-9; Afisawa 4:25, 28; Ibraniyawa 13:18) Kiyaye ƙa’idodin Jehovah har ila suna hana mu ɗaukan fansa, yin gaba, ko kuma yin tsegumi.—Littafin Firistoci 19:16, 18; Zabura 15:1, 3.
16 Ta wajen kiyaye ƙa’idodin Allah, muna kasancewa tsarkakku, ko kuma keɓaɓɓu, domin hidimarsa. Kuma yana da muhimmanci ƙwarai mu ware daga wannan duniyar! Da yake addu’a ga Jehovah a daren ƙarshe na rayuwarsa a duniya, Yesu ya yi roƙo domin mabiyansa: “Na faɗa musu maganarka, duniya kuwa ta ƙi su, domin su ba na duniya ba ne, kamar yadda ni ma ba na duniya ba ne. Ba na roƙonka ka ɗauke su daga duniya, sai dai ka kare su daga Mugun nan. Su ba na duniya ba ne, kamar yadda ni ma ba na duniya ba ne. Ka tsarkake su cikin gaskiya. Maganarka ita ce gaskiya.” (Yahaya 17:14-17) Mu ci gaba da ƙaunar Kalmar Allah, wadda ta keɓe mu domin tsarkakkiyar hidimarsa.
17. Menene zai iya faruwa idan muka ƙyale ƙa’idodin Jehovah, to, menene ya kamata mu yi?
17 Mu bayin Jehovah, muna so mu kasance karɓaɓɓu a hidimarsa. Amma idan muka ƙyale ƙa’idodin Allah, ruhun wannan duniyar zai yi nasara a kanmu, da ake ɗaukakawa ta wajen magana, adabi, nishaɗi, da kuma ɗabi’a. Kuma babu shakka ba ma so mu zama masu son kuɗi, da masu ruba, da masu girmankai, da masu butulci, da marasa tsarkaka, da maƙetata, da masu taurinkai, da masu homa, da masu son annashuwa fiye da son Allah—a ambata kaɗan kawai daga cikin halayen da waɗanda suka ware daga Allah suke yi. (2 Timoti 3:1-5) Tun da mun yi nisa sosai cikin kwanaki na ƙarshe na wannan mugun tsarin abubuwa, mu ci gaba da addu’a domin Allah ya taimake mu mu ci gaba da kiyaye ƙa’idodinsa ‘ta wurin biyayya da umarnansa.’—Zabura 119:9.
18. Kiyaye ƙa’idodin Allah zai motsa mu mu ɗauki waɗanne mataki masu kyau?
18 Ƙa’idodin Jehovah suna yin fiye da tunasar da mu abubuwa da dole ne mu yi. Kiyaye ƙa’idodinsa zai sa mu ɗauki mataki mai kyau, zai motsa mu mu dogara ga Jehovah kuma mu ƙaunace shi da zuciya ɗaya, da ranmu, da tunaninmu, da kuma ƙarfinmu. (Maimaitawar Shari’a 6:5; Zabura 4:5; Karin Magana 3:5, 6; Matiyu 22:37; Markus 12:30) Ƙa’idodin Allah suna motsa mu mu ƙaunaci maƙwabtanmu. (Littafin Firistoci 19:18; Matiyu 22:39) Musamman muna nuna ƙauna ga Allah da kuma maƙwabci ta wajen yin nufin Allah da kuma gaya wa wasu “sanin Allah” da yake ba da rai.—Karin Magana 2:1-5.
Kiyaye Ƙa’idodin Jehovah Yana Nufin Rai!
19. Ta yaya za mu nuna wa wasu cewa daidai ne kuma yana da kyau a kiyaye ƙa’idodin Jehovah?
19 Idan muka kiyaye ƙa’idodin Jehovah kuma muka taimaki wasu su yi hakan, za mu ceci kanmu da waɗanda suka saurare mu. (1 Timoti 4:16) Ta yaya za mu nuna wa wasu cewa bin ƙa’idodin Jehovah daidai ne kuma yana da amfani? Ta wajen amfani da mizanan Littafi Mai Tsarki a rayuwarmu. Waɗanda suke da “zuciyar kirki don rai na har abada” za su samu tabbacin cewa tafarkin da aka kafa a cikin Kalmar Allah lalle mafi kyau ne a bi. (Ayyukan Manzanni 13:48, NW ) Za su kuma ga cewa ‘lalle Allah na cikinmu’ kuma za su motsa su haɗu da mu a bauta wa Mamallaki Duka Ubangiji Jehovah.—1 Korantiyawa 14:24, 25.
20, 21. Menene ƙa’idodin Allah da kuma ruhunsa za su taimake mu mu yi?
20 Ta wajen ci gaba da nazarin Nassosi, da kuma amfani da abin da muka koya, da kuma yin amfani da dukan tanadi na ruhaniya da Jehovah yake yi, za mu zo ga ƙaunar ƙa’idodinsa da zuciya ɗaya. Idan muka kiyaye su, waɗannan ƙa’idodin za su taimake mu mu ɗauki “sabon halin nan da aka halitta bisa ga kamannin Allah da hakikanin adalci da tsarki.” (Afisawa 4:20-24) Ƙa’idodin Jehovah da kuma ruhunsa mai tsarki za su taimake mu mu nuna ƙauna, farin ciki, salama, haƙuri, kirki, nagarta, aminci, tawali’u, kamunkai—halaye waɗanda ba su yi kama da na duniya ba wadda take cikin ikon Shaiɗan! (Galatiyawa 5:22, 23; 1 Yahaya 5:19) Saboda haka, za mu iya godiya lokacin da aka tunasar da mu abin da Jehovah yake bukata ta wajen nazarinmu na Littafi Mai Tsarki, ta dattawa da aka naɗa, a wajen taronmu, manyan taro, da kuma na gunduma.
21 Domin muna kiyaye ƙa’idodin Jehovah, muna iya yin murna, ko lokacin da muke wahala saboda adalci. (Luka 6:22, 23) Muna zuba wa Allah ido ya cece mu daga yanayi na ban tsoro. Wannan ma ya fi muhimmanci yanzu da dukan al’ummai ana tara su saboda “yaƙin a babbar ranan nan ta Allah Maɗaukaki” a Har–Magedon.—Wahayin Yahaya 16:14-16.
22. Menene ya kamata ya zama niyyarmu game da ƙa’idodin Jehovah?
22 Idan za mu samu kyautar da ba mu cancanci ba ta rai madawwami, to, dole ne mu yi ƙaunar ƙa’idodin Jehovah da zuciya ɗaya kuma mu kiyaye su da dukan zukatanmu. Saboda haka, mu kasance da ruhun mai Zabura wanda ya rera waƙa: “Koyarwarka masu adalci ne har abada, ka ba ni ganewa domin in rayu.” (Zabura 119:144) Mu nuna tabbaci da ya bayyana a kalmomin mai Zabura: “Ina kira gare ka [Jehovah], ka cece ni, zan bi ka’idodinka!” (Zabura 119:146) Hakika, ta wajen kalmomi da ayyuka, mu nuna cewa lalle muna ƙaunar ƙa’idodin Jehovah da zuciya ɗaya.
Ta Yaya Za Ka Amsa?
• Yaya mai Zabura ya ɗauke ƙa’idodin Jehovah?
• Me ya sa muke bukatar ƙa’idodin Allah?
• Wane aiki taronmu yake yi in ya zo ga ƙa’idodin Allah?
• Ta yaya ƙa’idodin Jehovah suke ware mu daga wannan duniyar?
[Hoto a shafi na 25]
Mai Zabura ya yi ƙaunar ƙa’idodin Jehovah da zuciya ɗaya
[Hotuna a shafuffuka na 26, 27]
A bin misalin Hannatu, ka ƙudiri anniyar ba za ka bar taro ba?
[Hoto a shafi na 28]
Kiyaye ƙa’idodin Jehovah ya ware mu tsabtattu kuma karɓaɓɓu domin hidimarsa